BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   16 / 64

45K to 48K   out of 190K words

huta ne"

Ta jinjina kai, ta tashi ta nufi ƙofa, har ta kusa fita ya ce "Ki na ji?"

Ta waiwayo ta ga har ya kwanta.

"Ki ci gaba da addu'a da karatun Alƙur'ani, duk da idan kin yi kin fi shan wahala, kar ki daina. Kuma kar ki yadda wani abu ya baki tsoro, wasu lokutan da tsoron ka ake amfani a cutar da kai, ki cigaba da addu'a duk tsanani akwai sauƙi a biye. Wataƙila tsanani da ƙaddarar gobe ta fi wadda ki ke ciki yau" ta yi shiru tana jinjina maganganun sa.

Ta ɗago ta ce "To na gode sosai da sosai. Ka ajiye mini naman maciji an jima zan zo in gwada ci" ya yi dariya ya ce "Kamar gaske. Zo mu ga tafin hannunki"
Ta koma gurin da ta bar shi, ta durƙusa ta nuna masa tafin hannunta hagu da dama. Ya yi shiru yana kallo sannan ya ce " Ki kula sosai zanen X ɗin da yake kusa da layin zuciyarki na nuni da tsagwaron gwagwarmayar rayuwa. sannan layukan ƙasan babban ɗan yatsanki suna nuni da za ki yi wasu tafiye-tafiye, wasu daga ciki na jin daɗi wasu na wahala. Sai kuma alamar ido, da ke babbar ɗan yatsarki da alamar sarƙar da ke jikin babban yatsan akwai wani abu amma ba zan gaya miki ba, shi ma wani karatun ne daban, yana da alaƙa da aure da kuma matsalar iyali"
Ta kalli Sarkin baka ta ce "Abin mamakin  ka ba ya ƙarewa sarki, bayan layuka ban ga komai a hannun nawa ba, ko kana ganin wani abu da bana gani a hannun, kuma dai sanin gaibu sai Allah ai"

Ya kwashe da dariya ya ce "Wani karatun ne daban, duk da na san ji na kawai ki ke yi ba yarda ki ke yi ba. Je ki an jima ki zo ki ci naman. Na so na je da ke taron wasan maharba da muke yi duk shekara, ni ke ɗauke da kambun har yanzu, sai dai ba na iya tunanin bana za ayi wasan da ni, ƙaisar ya yi mini illa. Maza je ki sai an jima" ta tashi tsam ta nufi hanyar fita tana kallon hannunta. Wannan tsohon mai kama da Ƙaisar ta gani, cikin wannan fararen kayan nasa, tamkar yanar gizo gizo saboda tsufa.

Sai kuma ya ɓacewa ganinta, a hankali ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ga baya nan, sannan ta fita, tana tafe a hankali tana duba tafin hannunta tana kallon zanukan da sarkin baka ya faɗa, da tunanin shi kuma wani kalar siddabarun ne. Ji ta yi zafin rana ya ƙaru kamar lokaci ɗaya temperature ta canza. Ta ɗaga kai kawai ta ganta a bakin layinsu. Ta waiwaya da sauri ta ga ba ta cikin gidan sarkin baka. Ta sake dubawa ta ga dai bakin layinsu ne dai.

Hatta kayan jikinta ba su bane ba, dogon hijjabi ne da aka ba ta take sakawa lokacin salla, sai kuma wata jaka da take rataye da ita ta fata. Ta din ga ƙifta idanunta domin ta ji ko bacci take yi amma ta ga ido biyu ne, kawai ta nufi gida.

Ko da ta shiga gidan da sallama, babu kowa a tsakar gidan. Ta sake yin sallama Nasiru ya shigo gidan da gudu ya dawo daga aike, ya ce "Laa mama Nana ta dawo"

Hakan ya yi daidai da fitowar Mama daga ɗaki, hannunta riƙe da tsintsiya da abin kwashe shara.

Sakin tsintsiyar ta yi tana kallon Nana kamar baƙuwar halitta.

Nana ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Mama sannu da gida?"

"Uban me yasa ki ka dawo gidan nan yanzu?" Cikin mamaki Nana t tsaya tana kallonta.

"Ke idan ki na da kunya ma kya dawo gidan nan, duk da ta'asar da ki ka yi?"

Cikin mamaki Nana ta ce "Wace ta'asar?"

"Ban sani ba" ta yi magana tana ɗaukar wayarta a kan taga"

Nana ta nufi ɗakinsu, amma Mama ta dako tsalle ta tare ta, ta ce "Ai kuma zamanki ya ƙare a gidan nan, abin da na yi na riƙon ki Allah ya ba ni lada. Ba za ki ci gaba da zama ki kashe mini 'ya 'ya ba"

"Mama kisa kuma? Wa na kashe?"

Ba ta kula Nana ba, ta fara magana a waya "Ko ma ina ka tafi, ka dawo ka zo ga Nana ta dawo, ka zo ka fitar mini da ita daga gida, dan wallahi ba zan zauna da ita ba" ta kashe wayar.

Nana ta tsaya tana kallon ikon Allah, Fafur Mama ta hana ta shiga ɗakinsu, ba a fi mintuna goma sha biyar ba, sai ga Baba ya dawo gida.

Cikin mamaki yake kallon Nana ya ce "Ina Gaddafin yake?"

"Gaddafi kuma Baba?" Nana ta tambayi Baba cikin mamaki.

"Eh mana, ba wancan jarababben ɗan nema ya kai ƙarar mu ba, wai mun kai ki inda ba a sani ba, aka haɗa Gaddafi da jami'an tsaro a je a taho da ke"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ni da kaina na dawo, ban ga Gaddafi ba"

Suwaiba ce ta fito daga ɗakin Mama, sai da Nana ta tsorata, ta yi wani irin haske, duk da tana shafe-shafe, amma hasken da ta yi, da gani na rashin lafiya ne.

"Ka fa san yadda za ka yi da ita, dan wallahil azim ba zan ci gaba da zama da masifa da annoba ba, shi kansa wanda aka ce an kashe ɗin nan, ina kyautata zaton ma ita ce ba wani ba, to wallahi jinin 'ya'yana ba zai shawu a sha banza ba"

Baba ya ce "Wai Rabi me yasa ki ke haka? Idan ta bar gidan nan ta je ina?"

"Ta koma gurin uwatta, ta je ta sha nata jinin"

"Ba zai yiwu ba, har duniya ta naɗe, ba zan bawa maijidda ɗa na ba."

Nana ta yi ajiyar zuciya cike da tsantsar damuwa da baƙin ciki.

Ya sake kallon ta ya ce "Wai ba makonni biyu aka ce za ki yi ba, me ya dawo da ke gidan nan yau?"

"Shi ne ya sallamo ni" ta amsa a hankali.

Baba ya ci gaba da faɗa "Wallahi Ina takaicin haihuwar Imarana, ya haɗa Gaddafi da jami'an tsaro, shi kuma an zo nemansa a kama shi ya gudu, yanzu ma kalli 'yan sandan ne suke kirana ga kuma wannan masifar"

"Baba a kama shi kuma? Me ya yi?"

"Eh ai ke ce mai jin tausayinsa dama, sun haɗa kai da 'yan iskan abokansa, sun kashe wannan malamin naku, ana ta nemansa ruwa a jallo"

Nasiru ya yi farat ya ce "Baba ba fa Yaya imarana ne ya yi kisan ba, abokansa ake nema, shi ne ake nemansa dan ya nuna inda suke"

"Duk ba abu ɗaya ba ne dai?" Baba ya faɗa cikin takaici.

Jikin Nana na rawa ƙirjinta na dukan uku-uku ta ce "Wai wani malamin namu?"

Nasiru ya yi farat ya ce "Malam Auwal aka kashe da daddare, ya fita sayayya ana gobe za a kai ki gidan mai magani"

Kanta ne ya yi wata irin sarawa, ta yi saurin dafe kanta tana tunanin kamar ta san zancen amma ta manta a ina.
Iya ƙarfinta take kokowa tsakanin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta a kan sai ta farka daga nannauyan baccin da take yi.

Ayshercool
08081012143.

15

Suwaiba ta shiga banɗaki ta koma ɗaki, babu wanda ta kula a tsakar gidan.

Mama kuwa bala'i ta ci gaba da yi. "Wallahi baban Jamila ba zan zauna da Nana ba, idan ta gama da yaran nan kaina za ta dawo, shi kansa wannan yaron an fara maganar saboda yaƙi aurenta ya rasa ransa".

Baba ya ce "A'a Rabi, wannan dai zance ki ne, idan da wanda zai mutu dan bai aureta ba ai Suleiman ne, kuma duk abin da ake yi mata a gidan nan babu wanda ya mutu, dan Allah ki daina wannan maganar"

Kamar ta mari Baba ta ce "Abin da ya samu Suwaiban bai ishe ka hujja ba, sai ka buɗe ido ka ga gawar ta tukuna? Ni fa wallahi sai dai ka zaɓa, ko ta bar gidan nan ko ni na bar gidan"

"A'a ba za ayi haka ba, yanzu idan ki ka ce ta bar gidan nan ina za ta tafi? Haba Rabi Nanan nan fa 'ya ta ce ita ma. Kuma idan kin kwantar da hankalinki, kin san na karɓi kuɗin auren ta, nan da sati biyu za a ɗaura mata aure, ta bi mijinta Ikko, duk mene ne abin tayar da jijiyar wuya?"

Nana tun da ta dafe kanta, ta sunkuya ba ta ko motsa ba, sai yanzu da ta ɗago ta fara magana iya ƙarfinta "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan, ya za ayi malam Auwal ya mutu? Dan Allah ku tashe ni kafin ƙwaƙwalwata ta samu matsala, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan" ta ɗago da idanunta suka yi wani irin ja kamar za su kama da wuta, hawaye ne tare da mijina suke rige-rigen zuba a fuskarta.

Baba ya ce "Nana meye haka? Zuwa islamiyyar na banza dama ki ke yi? Ko ni na mutu ai ba kya yi haka ba" jefar da jakar hannunta ta yi, tai waje.

Baba ya bita da sauri, amma tamkar walƙiya bai ga ko sahunta ba.

Kai tsaye Nana rukunin ofisoshin malamai ta nufa a islamiyyar su.
Malam Nura ta tunkara, babban abokin malam Auwal.

Cikin yanayi na ɗimuwa ta ce "Wai an kashe malam Auwal? Dan Allah kai ma ka iya ruƙiyya ai ka na yi mini, dan Allah ka karanta mini koma mene ne ko zai sake ni na tashi daga wannan baccin."

Ya ƙarewa Nana kallo, da gaske a ɗimauce take, cikin sigar rarrashi ya ce "Zauna mu yi magana"

"Ba zan zauna ba, kawai ka yi mini ruƙiyya na tashi. A nan fa na same shi a ofishin sa, muka yi magana, ya gaya mini gaskiya ba zai iya aurena ba, kuma duk na fahimce shi, ya ce mini zai tafi Qatar, to kuma daga na yi tafiya sai ace mini ya mutu?"

"Al mautu haƙƙun Nana Asma'u, mun yi rashin Auwal. Ɓata gari ne suka soka masa makami su ka ƙwace masa waya kafin a kai shi Asibiti rai ya yi halinsa, ki yi masa addu'a"

Jikinta na karkarwa ta ce "Ya sayyadi Nura. Na yi rashi ba zan manta Yaya Auwal ba, yanzu waye zai din ga bani addu'oin? Waye zai yadda da abubuwan da nake ji a jikina na ciwo, ba tare da ya ƙaryata ni ba?" Tuni malamai suka cika ofishin, kowa da abin da yake faɗa, wasu na kuka domin mutuwar ta dawo musu sabuwa. Da yawa ba su san ya so ya auri Nana ba sai yanzu.

An daɗe ana rarrashin Nana, da yi mata nasiha, ba a taɓa yi wa Nana mutuwa mai shiga jiki ba sai a wannan lokaci, Alkhairinsa kawai take tunawa.

Halin da take ciki, bai hana kunnuwanta jiyo maganganun wasu malaman, su na cewa yayanta ake nema ruwa a jallo shi ya kashe Auwwal. Sauti komai ƙanƙantarsa Nana na iya jiyo shi, wasu lokutan da haka take gane ƙaisar na daf da ita.

Malam Nura ya saka ta a gaba, ya tafi raka ta gida, suna tafe yana yi mata nasiha.

A ƙofar gida malam Nura ya yi mata sallama, ta shiga cikin gida tana taku da ƙyar.

Ko sallama ba ta iya yi ba, ta nufi ƙofar ɗakinsu, ta ga an saka tsumma an ɗaure ƙofar ɗakin. Ta ɗauki jakar da ta dawo da ita daga gidan sarkin baka, duk da har a wannan lokaci ba ta san mene ne a ciki ba.

Ta fara ƙoƙarin kwance ƙofar ɗakin, jin motsi ya sanya Mama sake fitowa, tana ƙoƙarin nufo Nana tana bala'i. Nana ta ɗago a hankali ta kalli Mama, sai kuwa ta ja ta tsaya, dan ba ta taɓa ganin Nana ta yi mata irin wannan kallon ba. Gani ta yi tamkar walƙiya idanun Nana suka yi. Ta buɗe ɗakin ta shiga ta kwanta.

Aka jima Baba ya dawo, dan yawon neman in da Nana ta yi ya yi. Yana dawowa suka ci gaba da faɗa da Mama a kan lallai sai ya fitar da Nana daga gidan.

Nana tana ji Baba ya kira Yaya Atine yana roƙonta. Baba ba ya iya waya sai ya saka ta a hansfree, kuma sai ya ta ɗaga murya tamkar yana magana da aradu.

"Atine dan Allah idan da hali Nana ta zo gidanki, ta zauna kafin a ɗaura mata aure. Rabi taƙi yadda ta zauna da ita, kin san halin da Suwaiba take ciki"

"Wace Nana kuma? Ba tana gidan mai magani ba?"

"Ta dawo ɗazu, wai mai maganin ne ya sallamo ta, kuma ga 'yan sanda sun tafi da Gaddafi a taho da ita, shi kuma Imarana ya gudu nemansa ake yi ana zargin sun kashe wannan yaron da ake ta magana a kansa a radio, wanda ya ƙi auren Nanan"

Nana na jiyo Yaya Atine, kasancewar wayar Baba a ragargaje take kuma China ce ta na cewa "Taɓ lallai Isa Allah ya jarabce ka, wannan masifar duk a gidan ka? To mai magani ma ya kasa ya sallamo ta balle kuma ni, ya zan yi da ita ina ma na ga gurin ajiyeta? Ka yi haƙuri ta zauna a gurinka kafin lokacin bikin nata"

Ya marairaice ya ce "Me nake da shi, ba wani biki aure kawai za a ɗaura su tafi, ai kin san ba shi ne da ni ba"

Yaya Atine ta ce "To ai shikenan, amma ka riƙe 'yar ka, ba zan je nima na gogi bala'i ba, dan ni na fara tsorata da al'amuranta"

"Amma yay... Ba ta bari ya gama maganar ba, ta kaste kiran.

"Ka gani ko? Ita ba za ta karɓi bala'i ba, ni kuma a bar ni da bala'i ya ci gaba da kashe mu ba zai yiwu ba"

Sallamar da ake kwaɗawa a waje, ya sanya Baba fita, ya tarar da 'yan sada tare da Gaddafi.

Ɗaya daga 'yan sandan ya ce, "Yauwwa barka malam, zamu tafi da kai station ne"

Baba ya ce "Saboda me?"

"Mun je in da aka ce an kai yarinyar ɗanka ya yi ta raina mana hankali muna yawo, babu wani a gurin nan, kuma ga wanda ya kawo ƙarar ana nemansa ruwa a jallo"

Baba ya ce "Ai bayan tafiyar ku ta dawo"

Gaddafi ya ce "Ta dawo kuma? Ni fa har gurin da muka ajiye mota muka shiga, bamu ga gidan nan ba"

"Wallahi ta dawo, tana cikin gidan nan"

Sai da aka tafi tare da Nana har police station, aka yi rubuce-rubuce sannan aka saki Gaddafi suka taho gida. Tana jin yadda Gaddafi yake rantsuwa shi da sake shiga duk abin da ya shafe ta har gaban abada.

Kwanaki biyu suka shuɗe, Nana ko rintsawa ba ta iya yi, sai da ta gwammace dama a gidan sarkin baka ta yi zamanta.
Mama kuma ba su fasa faɗa da Baba a kan lallai ya nemi in da Nana zata zauna ba. Dama normally ma ba abinci ake ba ta ba sai an ga dama, yanzu kuwa tun da ta dawo Baba ne ma ya kan bayar a sayo mata kunu ko awarar naira ɗari, shi ma ba iya ci take yi ba.
Dama ba su fiye shiri da Suwaiba ba, sun fi shiri da Jamila, sai dai a wannan karon tun da ta dawo, babu wanda yake shiga sabgarta, hatta ɗakin da take ba sa shigowa. Tana jin yadda idan aka yi baƙi, ko aka zo duba Nana mama take muzanta ta, tana cewa aljanunta ne suka halaka Auwal, wanda ya fasa aurenta kuma suke ƙoƙarin kashe Suwaiba.

Nana tana ganin yadda wasu daga hudar jikin Nana suka fara warkewa, sai dai wasu ba su fasa zubar da jini ba.

Turaren da Jamila ta kawo mata ta gani a kan tagar su, an feshe fiye da rabi. Ita dai ta san turaren nata ne, amma ta kasa tuna yadda aka yi ta same shi.

Cikin dare ta kasa bacci, ta tashi zaune ta haɗe gwiwoyinta ta kifa kanta, har yanzu gani take kamar za ta farka daga bacci, ace mata Auwal bai mutu ba.
Kwanakin nan da aka ɗauka kuma, ta gazagata da gaske malam Auwal ya rasu. Tana so ta je ta yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya amma ba ta sani ba ko ta santa, ga kuma surutun da ake ta yi a kanta.

"Ya Allah ka yafe mini rashin tawakalli da na yi, na bari ɗimuwa ta sanya ni yin abin da bai kamata mai imani ya yi su ba. Ya Allah Auwal bawanka ne, mai kwaɗaitar da al'umma bin ka da manzonka, mai hidima ga addini, mai ƙaunar Manzon Allah ma'abocin Alqur'ani ya Allah ka yafe masa ka yi masa rahama" ta yi maganar kuka yana ƙwace mata.

Dariyar da ta ji ne, ya sanya ta ɗaga kanta. Ta ganta a zaune jikin wata bishiyar tsamiya, ita kaɗai ƙwal a daji.

"Iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu duk saboda soyayyar ki ka koma haka? Kamar gaske mutumin nan ya riga ya mutu, kuma ba fa wai son shi ki ke yi ba, shaƙuwa da tausayi ne a tsakanin ku" tashi ta ya tsaye a fusace tana waiwayen in da za ta ga ƙaisar. Domin kuwa sai a lokacin ta tuna ya nuna mata mutuwar malam Auwal, amma da ta tashi a wancan lokacin ta manta da komai.

"Kai ne ka kashe shi ko?"

"Idan zan kashe shin ne zan soka masa wuƙa? Kwanansa ne ya ƙare ba zan iya kashe shi ba ai, ni ba na kisan kai sai an dame ni, kamar yadda Sarkin baka ya taɓo ni, nima na taɓa shi wataƙila na karya alkadsrinsa wannan maitar wataƙila ita ce ajalinsa"

Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Kenan kashe shi za ka yi? Wai kai wani irin halitta ne azzalumi mara imani? Duk wanda na mu malanta sai ka cuce shi?"

"A'a ni ba na taɓa kowa sai ya taɓa ni. Ba ya fara lallaɓa ki ki sadaukar masa da ni ba? Ba ki yi tunanin ta wace hanya zai yi amfani da ni ba, kawai saboda ki rabu da ni, ki ka amsa masa kuma ke ba ki san ya ake sadaukarwar ba, ki ka amsa. Ya shiga gonata ni kuma na shata masa layi" yayi maganar yana bayyana a gabanta.

Cikin kuka Nana take faɗin "Allah ya yi mini maganin ka ya saka mini, idan ka fi ƙarfina ba ka fi ƙarfin Allah ba ai. Kuma kana kallo aka kashe malam Auwal ba ka yi komai a kai ba, banda zalunta ta ta azabtar da ni ba abin da ka

16 / 64