BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   28 / 64

81K to 84K   out of 190K words

kwana jiya"

"To shikkenan, na gode sosai da sosai, baban nata fa ka yi aikin a kansa?".

Ya ce "Kar ki damu, ba wanda ban yi ba fa"

Ta ajiye wayar, tana kuma tunanin me yakamata ta yi.

Kafin azahar ɗan aiken Alhaji Zailani ya zo, ya kawo uban kayan abinci kamar za a buɗe ƙaramin shagon sayar da kayan abinci. Bakin Baba ya ƙi rufuwa, sai shiga yake yana fita yana washe baki, yana ƙiyasata irin abin da zai yi wa Nana muddin ta bijirewa auren Alhaji Zailani.
Yaron nasa ya sanar da Baba cewar, tafiyar gaggawa ta kama Alhaji Zailani, washegari zai dawo, amma ko baya nan bai dawo a goben ba, za a ɗaura auren nan ranar Juma'a, kuma ba ya buƙatar taron jama'a, waliyyai kawai sun isa.
Baba yana tsuma ya tabattarwa da yaron Alhaji Zailani, mai suna Sani cewa ya tabattarwa da Alhaji Zailani ba za a samu wata matsala ba.

Nana kuwa gaba ɗaya ji ta yi jikinta ya ƙara sanyi, tun da garin Allah ya waye, komai ba ya yi mata daɗi, tamkar ta mutu ta huta.
Duk mutanen gidan sun koma baccin safe, ta shirya ta fice daga gidan.

A hanya gari ya ƙarasa wayewa Nana, ta je ta din ga bubbuga gate ɗin, aka zare sakata aka buɗe. Sai dai maimakon ya ba ta hanya, sai ya zura mata idanunsa yana kallonta. Hankaɗa ƙofar ta yi ta shiga a fusace, ta tsani wannan ɗan iskan kallon da yake yi mata, shi kuma kullun fuska a rufe, ba a ganin fuskarsa sai dai ya yi ta kallon mutane.
Burki ta ja ta tsaya, tana kallon yadda ƙosassun karnukan nan, suke safa da marwa a harabar gidan. Ta waiwayo ta kalle shi, ya kawar da kansa kamar bai gan ta ba, ya mayar da gate ɗin ya rufe ya saka mukulli, ya nufi ɗakinsu na masu gadi.
Karnukan suka yi cirko-cirko suna kallon Nana, su na haushi.

"Dan Allah ka raka ni bakin ƙofar shiga" ta yi maganar a marairaice. Bai kulata ba ya cigaba da tafiya. "Dan Allah idan ba za ka raka ni ba ka buɗe mini ƙofa na koma". Ganin da gaske ba zai rakata ba, kuma ba zai buɗe mata ba, ga karnuka su na nufo ta, kawai ta rufa masa baya da gudu. Ya tsaya ya waiwayo ya kalleta. Ta ja ta tsaya cikin tsananin tsoro.

Sule ne ya fito yana miƙa da alama a lokacin ya tashi, ya kalle su ya ce "Nana lafiya na ganki da sassafen nan? Kuma ya na ganku a tsaye haka lafiya dai?"

"Tsoro nake ji, na ce ya raka ni yaƙi, kuma ya kalle ƙofa ya ƙi buɗe mini na koma gida, kuma so suke su biyo ni su cije ni" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye saboda tsoro.

Sule ya yi dariya ya ce "yi haƙuri, ni ban san dalilin da ya sanya ku ke yawan samun saɓani da Buzu ba. Jira ni na ɗaure karnukan sai ki wuce"

Ta goge hawayen ta ce "To na gode sosai" Shi kuwa tuni ya shige ɗakin su, ya bar ta da Sule.

Ko da Nana ta shiga cikin gidan, ɗakin Haidar ta nufa kai tsaye, yana kwance yana ta baccinsa. Ajiyar zuciya ta din ga saukewa, ta durƙusa a gabansa ta dafa kansa, tana karanto masa addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Tana ɗan tofa masa. Wata irin razana ya yi a baccin, har da ɗan ihunsa, Nana ta rungume shi, ya ƙanƙameta ta cigaba da yi masa addu'a.

Yau Shukura ta na gida, sun yi hutun makaranta. Har mamaki take yi yadda Nana ba ta gajiya da abin da Haidar yake yi mata na hayyata irin ta su ta yara.
Duk motsin da ya yi, ta san me yake nufi, zuwan Nana gidan ya yi ƙiba ya zama ƙato saboda yadda yake cin abinci. Ga kuma karatu da take koya masa, har da addu'oi.

Nana ta ce "Shukura" karon farko da ta taɓa kiran sunanta, Shukura ta kalli Nana da mamakin tsaurin idon da ta yi.

"Na san ba zan dauwwama ina kula da Haidar ba, amma dan Allah ina son ko yaya ki ajiye aƙidar boko, ki din ga jansa a jiki, kuma ki tsayawa azkar ɗin sa da kula da yi masa addu'a. Ke kanki ki ƙara ƙaimin addu'a sosai da sosai, ka na da ido ne kawai amma ba na ganin gari ba, abin da Allah ya so kawai shi muke gani"

"To da na ce miki ba na addu'a ne, da za ki buɗe ƙazamin bakin ki, kina kiran sunana haka kai tsaye ni sarki ce?"

Nana ta kalli Shukura ido cikin ido ta ce "Ni ki ke cewa mai ƙazamin baki! To kar ki yi abin da na ce, idan kin ƙi ji ai ba za ki ƙi gani ba"

Babban abin da ya bawa Shukura mamaki, bai wuce yadda ta ji tamkar an saka mukulli an rufe mata baki ba, bayan sun haɗa ido da Nana ba, ta yi gum ta kasa cewa komai.

Gaba ɗaya Nana ta manta da wani sharaɗi da Baba ya kafa mata ma, hatta batun auren Alhaji Zailani ma sai ta daina jin ya dame ta, mummunan mafarkin da ta yi da su Shukura ne kawai yake damunta. Sai kuma wata irin fargaba da ta rasa ko ta mece ce.
Domin ragewa kanta damuwa, tare suka yi girkin dare da Jummai. Hajiya Amina ce ta ce "Nana ki zo ki tafi, na ga alamun hadari a garin nan, kuma tun da ba abin da ki ke yi"

"A'a kar ki tafi" Haidar ya yi maganar yana riƙe rigar Nana.

Nana ta kalle shi da murmushi a fuskarta ta ce "Idan na zauna zaka goya ni?"

"Eh zan goya ki, ki yi bacci" ya yi maganar cike da shirirtar su ta yara.

Da ƙyar a ka yi masa wayo, Hajiya Amina ta ɗauke shi, Nana har za ta fita, Jummai ta biyo ta da kular abinci ta ce "Dan Allah Nana ki ajiyewa masu gadi, na san yanzu su na can waje shan wannan shayin nasu na ibada, ba za su dawo ba sai cikin dare. ki ɗan tura ɗakinsu ki ajiye musu, idan ba su san an ajiye ba, karnuka ne suke zubar musu. Jiya da na ajiye musu a waje ba su sani ba, su ka kwance karnuka, aikuwa su na sako su, suka je in da aka ajiye abincin suka kifar, suka hau ci" Nana ta ɗan yi Jimm sannan ta karɓa ta fita.

Kamar yadda Jummai ta faɗa kuwa, Nana tun kafin ta ƙarasa bakin gate ɗin, take jiyo hayaniyar buzayen a ƙofar gida, alamun duk su na waje a ƙarƙashin bishiyar da suke zama da yamma su sha shayi, su yi wasan takobuna.
Amma duk da haka sai ta tsaya a ƙofar ɗakin nasu tana sallama, ko za ta ji an amsa, amma ta ji shiru. Sai ta ɗan tura ƙofar ɗakin, wani irin ƙamshin turare ya kawo wa hancinta ziyara.
Ta zura flask ɗin abincin, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta ji kukan Haidar a cikin ɗakin yana kiran sunanta. "Anty Nana, ki zo)
Ba ta yi nazarin komai ba, balle tunanin ta baro Haidar ɗin a cikin gida ba, kawai sai ta ɗimauce ta hankaɗa ƙofar ɗakin ta shiga.
Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli inda take tsaye. Daga shi sai dogon wando, hannunsa riƙe da mataji, yana taje dogon gashinsa da ya kwanta a kan kafaɗarsa zuwa dokin wuyansa. Gefensa butar shayi ce, take ta dahuwa a kan wuta, kuma da alama a cikin wutar aka zuba turaren wutar da yake tashi.
Cikin matsanancin tashin hankali tsoro da razani, ta yi yinƙurin juyawa ta fita, amma ƙofar ɗakin da tagogi suka kulle, sautin wata irin guguwa ya karaɗe ɗakin. A take ya rikiɗe daga kamaninsa zuwa wannan tsohon mai kama da Ƙaisar, ya bayyana cikin suffa mai matuƙar ban tsoro, ya buɗe ƙaton bakinsa mai kama da bakin tsohuwar rijiya, ya fara fito da wata irin wuta Jawur tana wani irin hayaƙi, lamar gobarar tankar mai.
Iya ƙarfinta ta dafe kanta, ta ƙwala ihu ta faɗi a gurin sumammiya. Jin ihunta ya sanya ya sake waiwayawa ya kalle ta, ya ganta a ƙasa ba ta ko motsi. Ya ƙarewa ɗakin kallo domin ya ga abin da ya razanata amma bai gani ba.
Ya mayar da hankali ya ƙarasa taje gashinsa, ya tufke abinsa, ya zira rigarsa, ya shafa turare sannan ya kawo rawaninsa ya naɗa. Ya zauna a gaban shayinsa, ya fara tsiyayowa yana kurɓa a hankali tamkar shikaɗai ne a cikin ɗakin babu wata halitta kuma.

Gidansu Nana tun da aka yi sallar magariba, Nasiru ya shigo gida yake tambayar ko Nana ta dawo.
Suwaiba ta ce "wai kai Nasiru Nanan nan uwarka ce ne?"

"Ban sani ba, idan ma uwar ta wa ce ina ruwan ki?"

Cikin hasala ta ce "Idan na kama ka wallahi sai na gwara kanka"

"Ba ki da wannan ƙarfin wallahi" ya yi maganar yana fita. Ya zauna a ƙofar gida yana kallon hanya, amma babu Nana babu alamar ta. Tsoro ne ya fara kama shi, kar ya je ko ta sake ɓata aljanun nata sun kai ta wani gurin.
Yana zaune ya hango Baba ya nufo gida, hannunsa riƙe da manyan ledoji.
Nasiru ya tashi ya karɓo masa kayan suka shiga gida.

Su na shiga Nana ya fara tambayar Mama, amma ta ce ba ta dawo ba. A take hankalin Baba ya tashi, ya fara tunanin ko dai ta gudun ne?
Sai a lokacin ya fara binciken ina ne gidan da Nana take aiki, tun da take zuwa bai taɓa bibiyar ina take zuwa aikin ba.
Gaddafi baya nan, dan haka ya ɗauki Nasiru, suka fita neman Nana.

Gurin ƙarfe tara na dare, Gaddafi ya dawo gida, ya shigo cikin gida zai wanke kayansa, yana neman Nasiru zai aike shi. Suwaiba ta gaya masa halin da ake ciki. Ya yi saroro ya ce "Yanzu har ƙarafe tara ba a san inda take ba? Kuma babu wanda ya san gidan aikin nata?"

Jamila ta ce "Ni dai ta taɓa kwatanta mini, can wajen quarters ɗin markaz ne, wai gidan Alhaji Zailani"

"Sako hijjabin ki mu je, mu duba"

Mama ta ce "Ku je ina? Babu inda za ta je"

Ya haɗe rai ya kalli Jamila ya ce "Ba magana nake yi miki ba, sai na taka wuyanki tukuna?" Ba Jamila ba ita kanta Mama sai tsuke bakinta ta yi, dan iya ashariyar Gaddafi ta ishe su.

Sam ba su sha wahalar gano gidan ba, kasancewar Alhaji Zailani sanannen mutum, saboda yawan kyautar da yake yi da taimakon al'umma.
A tsatstsaye suka tarar da mutane a ƙofar gidan, buzaye sai magana suke yi da yaren su.

Kai tsaye Gaddafi ya kutsa suka shiga cikin gidan, mutane ne a tsaye a ƙofar ɗakin masu gadi, ga matar gidan a tsaye fuskarta ɗauke da damuwa.

Gaddafi ya nufe ta, suka gaisa ya ce "Dan Allah ni yayan yarinyar da take yi muku aiki ne, Nana tun da ta fita tun safe bamu ganta ba, shi ne muka zo nan ko ta zo?"

Hajiya Amina ta ce "Alhamdilillah mu na ta tunanin yadda za a yi, tun bayan la'asar muka yi sallama, ta tafi gida. yanzun nan yarona ya shigo yana gaya mini wai masu gadi sun ganta a ɗakinsu a sume, su suna waje, mutum ɗaya suka bari a ɗakin, shi kuma ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, ya ƙi magana an rasa wanda zai taɓa ta ma. Yanzu nake tunanin ya za a yi a samo wani daga gidansu, dan ni ban san gidansu ba"

Gaddafi ya ce "Ɗakin masu gadi kuma?" Ya juya ya nufi ɗakin.

Nana na sume a tsakar ɗakin, gefe guda shi kuma yana zaune yana kaɗa ƙafafuwan sa, tamkar ba ya jin hayaniyar da ake yi.

Gaddafi ya nufi Nana da sauri, ya ɗago ta, yatsun hannunta da na ƙafarta duk sun ƙandare kamar wadda ta daɗe da mutuwa, ga jikinta sanyi ƙalau.

Ya ɗaga kai ya kalli Buzun nan da duk abin da ake yi, sabgar gabansa kawai yake yi, ya kalli Nana. Duk da ba shiri suke yi da ita ba, amma ya san Nana ba ta cikin jerin yara marasa ji, amma me ya kawo ta ɗakin masu gadi?.

Hajiya Amina ce ta saka Yusuf ya ɗauki su Gaddafi ya tafi kai su gida.

Cikin damuwa Habu yake dubansa ya ce "Buzu, ya aka yi yarinyar nan ta shigo ɗakinmu, me ya same ta? Me yasa kuma ba ka kira wani daga cikinmu ba?" Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Habu, a dole Habu ya ja bakinsa ya tsuke, duk da tarin tambayoyin da suke bakinsa.

Cike da takaici, da matsananciyar tsana da damuwa, Baba yake kallon Nana yake maimaita a ɗakin masu gadi ka gano Nana?"

"Idan an yi magana a ce aljanu ne suka hanata aure, ga haƙiƙanin abin da ya hanata aure nan ai" Mama ta din ga faɗar maganganu. Jamila ta ce "Mama ba lallai abin da ki ke tunani ba ne ba, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya"

"Eh ban sani ba sai yanzu da ki ke gaya mini, rashin lafiya ne za a ganta a ɗakin masu gadi da wani?"

"To ai an ce mahaukaci ne, har fa muka taho yana kallon dandazon mutane, bai yi magana ba, kuma bai fito ba" cewar Jamila, dan ta ƙi yarda zuciyarta ta bata wani mugun abin Nana take aikatawa.

Kawai Baba ya tafi ɗaki, Mama ta bishi tana faɗin "Yanzu baban Jamila, baka gudun a zo a ji kunya? Wallahi tun da ta fara haka, ko an yi auren nan ba za ta zauna ba, kunyata ka za ta yi, tun da ta furta maka ba ta son auren nan, take ta wannan iskancin. Maza nawa ta ce ba ta so? ko dai ka san abin yi ko kuma abin da za ta yi a gaba sai ya fi na yanzu muni"

Wata irin tafasa zuciyar Baba ta din ga yi, tafasar da tun da yake bai taɓa jin zuciyarsa ta yi ba, wata irin matsananciyar tsanar Nana ta mamaye zuciyarsa.
Kamar mahaukaci haka ya fito fiuu ya yi waje.

Ayshercool
08081012143
25

Ko da Baba ya fita Gaddafi ya nemo, a gurin masu shayi.

Gaddafi ya ce "lafiya kuwa?"

"Ofishin 'yan bijilanti zaka raka ni"

"Amma a daren nan? Me ya faru?"

"Mu je za ka gani"

Gaddafi ya bi Baba zuwa gurin 'yan bijilanti.

Baba ya shigar da ƙorafi, a kan zargin yin lalata da yarinyar sa.

Gaddafi ya ce "Baba, babu tabbacin abin da ka ke faɗa fa?"

"Babu tabbaci, aka same ta a ɗaki tare da shi sama da awanni?"

Gaddafi ya ce "Amma ai ka san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba"

"Ka rufe mini baki Gaddafi" Gaddafi ya yi shiru, 'yan bijilanti suka bayar da mutum biyu, tare da Gaddafi aka tafi taho da Buzu.

Hankalin Habu ya yi mummunan tashi, ganin wai an zo a tafi da ɗan uwansu gurin hukuma. Cikin damuwa ya ce "Wallahi ina da tabbacin babu abin da ya yi mata, ba shi da cikakkiyar lafiya ƙwaƙwalwa ne, amma ba wani abin ya yi mata ba, ai mutane sun ga a yadda muka tarar da su"

Jami'in bijilanti ya ce "To ka ɗaukko takardar shaidar ba shi da hankalin, ka haɗo da ita mu tafi, ko ce maka aka yi mahaukaci ba zai iya wani abun ba" sauran buzayen ma duk hankalinsu a tashe.

Haka aka tasa Buzu da Habu, da wasu daga cikin buzayen, suka tafi ofishin 'yan bijilanti.

Shugaban gurin ya ce "Waye daga cikin su, aka tarar da su a ɗakin? Ina kuma ita yarinyar?"

Baba ya ce "Tana gida a sume"

"A sume kuma? Shekararta nawa?"

"Shekara ashirin da ɗaya"

"Ikon Allah, to waye a cikin su?" Gaddafi ya nuna Buzu.

"Kai malam ya aka yi aka tarar da kai daga kai ita a ɗaki, tsawon awanni, sauke rawanin nan na fuskarka ina magana kana kallona"

Habu ya ce "Yallaɓai ba shi da cikakkiyar lafiya fa, wallahi taɓin hankali ne da shi, ina da tabbacin babu abin da ya haɗa shi da yarinyar nan"

Sule ya ce "Ba ma sa shiri da ita, wallahi rashin fahimta aka samu, na ga kwanon abinci a ɗakin, ina kyautata zaton ma abinci ta kai mana, akwai dai abin da ya faru tabbas"

"Ba da ku nake magana ba, ka buɗe baki ka yi mana bayani, ko kurma ne?" Shugaban bijilanti ya yi maganar yana kallon Buzu. Amma bai ko motsa ba, balle ya yi magana.

Ya sake tsuke fuska ya ce "Sauke rawanin nan kafin na saka a sauke maka shi yanzun nan, ka ƙunshe fuska kamar ɗan taliban" ƙura masa ido ya yi bai yi magana ba.

Habu ya ce "Ka cire rawanin dan Allah, ka yi maganar abin da ya faru"

Sule ne ya kai hannu zai sauke masa rawanin, amma ya riƙe masa hannu.

"Dattijo, alamu sun nuna fa mutumin nan da gaske mahaukaci ne"

Baba ya ce "Wallahi ko dawanau ce a kansa sai an bi mini hakkina, dama 'yan kwanakin nan shi ne yake hure mata kunne, sai ta kai bayan magariba a waje ba ta dawo ba. Ta ƙi aure fafur kowa ya zo ba ta so"

"To kai Baba ya ka ke so a yi? Kana gani ya ƙi magana, ita yarinyar ba ku zo da ita ba, ni wannan case a bari gobe in Allah ya kaimu ku tafi gurin 'yan sanda".

Baba ya ce "Duk fa wata shaida da ake nema, ta tabatta tun da abin da suke yi kenan, sai ya aure ta ya je su ƙarata" gaba ɗaya suka kalli Baba. Cikin tashin hankali Habu ya ce "Dan Allah dattijo ka yi haƙuri, wallahi ba su saba yin komai ba, wannan karon ma rashin fahimta ne, Nana mutuniyar kirki ce, shi kuma ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, dan Allah ka yi haƙuri"

"Wallahi ba zan haƙura ba, daga nan har kotun ƙoli mu je, a karɓa mini hakkina na ci mini mutunci ta hanyar yin lalata da 'ya ta, ana daf da ɗaura mata aure" Gaddafi dai ya yi shiru yana kallon ikon Allah, bai ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki irin wannan matakin ba.

"Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga nan ba ƙasarmu ba ce ba, idan aka kai mu gaban shari'a wahalar da mu za a yi, dan Allah ka yi haƙuri" Sule ya yi maganar cikin magiya. Baba ya fututtuke ya din ga bala'i, buzayen nan su na ba shi haƙuri.

"Payer la dot" ya furta cikin harshen faransanci yana

28 / 64