BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   48 / 64

141K to 144K   out of 190K words

daga masallaci, sai na raka ku" Duk s karɓi lambobin wayar su, su ma suka karɓi ta ta.

Suka shirya tsaf za su tafi, Nana ta fito ta tarar ya dawo daga masallacin.

Ta ce "Sayyid, za su tafi zan raka su ko bakin titi ne, su hau adaidaita sahu, su je tasha".

Ya ce "Bari mu je tare"

"Idan mutanen gidan su na neman ka fa?"

"Wata ta ƙone a gidan, sun tafi kai ta Asibiti"

Nana ta waro ido, ta ce "Wace ta ƙone?"

"Ban sani ba, kawai na buɗe gate sun ce mini za su Asibiti, wata ta ƙone da ruwan zafi"

Nana ta ce "Ikon Allah, Allah ya sauwwaƙe."

Su Adda Saude, su ka fito, suka tafi raka su tare da Sayyid.

Su na tafe su na ci gaba da yi musu nasiha, a bakin titi, suka tarar musu adaidaita sahu. Nasiru dama tun da ya raka su, gida ya koma saboda zai je makarantar Islamiyya.

Nana ta tambayi mai Napep ta ce "Nawa za ka kai su tasha" hararta Buzu ya yi, ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu, ya bawa mai adaidaita sahun.

Ya sake ɗaukko baƙar leda, ya ajiye wa Anty Fati a kan cinyar ta, ya ce "Mun gode sosai"

"A'a ba zamu karɓa ba, ɗawainiyar ta yi yawa"

Nana ta ce "A'a Anty Fati, ba zai ji daɗi ba. A ce ina gaida Mama, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi magana idanunta na cika da hawaye.

"A'a Nana, kar fa ki je ki zauna ki yi ta koke-koken nan, idan haka ne, za mu daina zuwa"

Ta goge hawayen ta ce "Na daina, ku gaida gida"

Sai da su ka ja motar su ka tafi, sannan su ka dawo gida.

Nana ta zuba masa Abinci, ya ce "A'a ba na jin yunwa yanzu"

"Sayyid ina jin daɗin yadda ka ke mutunta 'yan uwana idan sun zo, kuma na ji daɗin yadda yau ka yi magana da su, har ka yi raha, har cikin zuciyata na ji daɗi sosai da sosai. Allah ya nuna mini 'yan uwanka haka, zan yi iya yi na, na kyautata musu nima, Allah ya sa su amince su karɓe ni a matsayin ɗaya daga cikin ahalainsu".

"Na ji kin ce a gaida Mama, mamanki na nan ta bari, a ka aura miki ni?"

Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ba ga Maman nawa nan ka gani ba, ranar da mu ka je duba Baba?"

"Ba maman ki ba ce, kuma ko mamanki ba ta so na, ba za ta din yi mana irin kallon da waccan matar ta yi mana ba. Amma wannan da su ka zo, na ga su na murna sosai da sosai da ganina, har suka yi mana addu'a, duk da ban san me yasa ki ka yi kuka ba da suka zo"

Nana ta haɗiye abu mai ɗaci da ya tsaye mata a wuyanta, ta san yanzu ba ta da wani mutum mafi kusanci da ita, sama da shi, dan haka babu buƙatar ɓoye masa komai, dan haka ta numfasa ta ce "Tabbas ba Mamana ba ce wadda ka gani a gidanmu. Mamana sun rabu da Baba, tun ban fi shekaru tara ba. Ba komai nake iya tunawa ba, kawai dai na san Mama ba sa jituwa da dangin su Babanmu, su na yawan samun saɓani. Har dai suka rabu. Ta ce Baba ya bata mu, ni da yayana amma ya hana ta. Ba ta daɗe da rabuwa da shi ba, ta yi wani auren. Abin ya ɓata wa Baba rai sosai da sosai, ya ce kamar ta sane ta kashe auren dan ta fita ta auri wani, wanda ta aura ɗin kuma an ce ya taɓa son ta, ba ta aure shi ba.
Adda Saude ta zo ta ɗauke ni ta ƙarfin tsiya, ta tafi da ni, amma da ƙyar na kwana a gidan da Mama take, mijinta ya ce sai an fita da ni. Abin dai duk babu daɗi, aka sake mayar da ni gidan Baba. Na fi shekara bakwai ban ganta ba, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Ya rungume Nana a jikinsa yana shafa bayanta a hankali.

"Ki daina kuka, za mu je mu ganta in sha Allah, ke gara ke a kan ni ai. Ban sani ba ma ina da maman ko ba ni da ita, ni ke kaɗai na sani"

Ya jima yana rarrashinta, sannan ta ɗan tsagaita da kukan da take yi. Ta fara buɗe kayan da suka kawo mata. Ba masu tsada ba ne ba, amma ta yi ƙoƙari. Bedsheet kawai biyar ne, huɗu na gida, ɗan waje ɗaya. Ga kwanuka har da kayan sakawa.
Sai da ta bari an kira magariba ya fita, sannan ta sake fashewa da kuka, ta yi kuka sosai sai da kanta ya fara ciwo,  sannan ta haƙura ta yi shiru.

*****

Jikin Shukura ya yi kyau, ta warware, wannan kumburin duk ta sace, aka rubuta mata sallama.
Doctor Sharif ya sha jinin jikinsa, dan sai da ya tsorata ya fara wasi-wasin ko dai Shukura ta san abin da ya aikata mata, saboda yadda ta canza gaba ɗaya. Wasa da dariyar ma da suke yi, gaba ɗaya ta daina, da ya shigo sai ta tsuke fuska. Sai dai wani sashi na zuciyarsa ya din ga ba shi, kawai yanayin da take ciki ne, na rasa ɗan ta da ta yi, ya sanya duk ta canza ta daina walwala.

Hajiya Amina ta dube ta, ta ce "To Shukura yaya? Gidanki zan mayar da ke, ko gida za ki taho?"

"Mummy mu je gida na ɗan huta tukuna"

Sagir ya harari Shukura ya ce "Mummy, a dawo da ita kawai, ke ma ki huta da ɗawainiya tun da ta samu lafiya"

Su na cikin mujadalar, Alhaji Zailani ya kira waya, ya ce "An sallame ku ne ko kuwa? Ya ce mini yau za a sallame ku"

"Eh, an sallame mu, ta ce gidan zata taho, mijinta ya ce ta koma gida"

"Saboda me? Ta koma ta yi masa me? A dawo mini da 'ya ta gida ta huta, kafin ta koma, me za ta je ta yi masa da yanka a jikinta".

Hajiya Amina ya ce "A'a kar a yi haka, mijinta ne fa"

"Ni kuma ubanta ne, ki ce masa na ce a kai mini 'ya ta gida ta huta, idan ba za ki faɗa ba, ni zan kira shi"

Sagir yana ji yana gani, haka ya haƙura, aka mayar da Shukura gida, maimakon gidansa.

****

Nana ta kira su Adda Saude, suka tabattar mata da sun je Bauchi lafiya, ta yi musu bangajiya.

Yana ta shirin kwanciya, Nana kuma ta ƙura masa ido, zuciyarta ta yi mata nauyi, ba ta jin daɗin komai.

Ya zo kusa da ita, hannunsa riƙe da kofi ya miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa, tana kallon sa.

"Na ga ba ki ci abinci ba, madara ce na kuma karɓo miki"

Ta buɗe kofin, ta kalli madarar, da wani baƙin abu a kai.

"Habattussauda ne a ciki, ko na fara sha ne?" Ya yi magana yana miƙa hannunsa zai karɓi kofin.

Ta kafa kai, ta fara shan madarar, sai da ta shanye ta ajiye kofin.

Ta dube shi ta ce "Me yasa ka ke bani madarar nan?"

"Na ji wani likita ya faɗa a radiona, yana ƙara wa mata lafiya sosai"

Ta ɗan yi murmushi, sannan ta numfasa ta ce "Sayyid, da gaske ƙabilarku, ba sa auren macen da ba ta su ba?"

Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce "Duk abin da zai fito daga bakina a yanzu, ƙarya zan yi miki, saboda ba zan iya tuna komai a kan ƙabilar tamu ba"

Cikin rawar murya ta ce "To yanzu idan Allah ya sa ka tuna waye kai, da asalin rayuwar ka, ni mece ce makomata? Za ka karɓe ni a matsayin matarka kuwa?. Idan kuma aka samu akasi ka manta da ni baki ɗaya fa? Yaya zan yi? Mece ce makomata?"

Ayshercool
08081012143
41


Ya yi shiru yana nazarinta, hawaye ya wanke mata fuska, har cikin ranta maganganun da suke fitowa daga bakinta. Tabbas! Tambayoyin nata a kan hanya suke, kuma sun cancanci ta samu amsar su, amma ta yaya zai bayar da amsar abin da shi kansa bai sani ba?

Ya dake ya tattaro nutsuwar sa, ya ɗago fuskarta, su ka haɗa ido.

"Ba na so, ganin wannan na ɗaya daga cikin abin da yake tayar mini da hankali, na rasa nutsuwa, hawayen ki zafi yake haifar mini a zuciyata, kuma yau wuni ki ka yi kuka" ya yi maganar yana share mata hawayen da yake kan fuskarta.

"Sayyid ka bani amsa, zuciyata ta cika da tsoro da fargaba, da kuma wasi-wasi"

Ya sassauta muryarsa ya ce "Ma vie. Idan har tunawa da rayuwata da waye ni, zai sanya na manta da ke a cikin rayuwata, ina fatan na dauwwama ba tare da na tuna waye ni ba. A jikina ina jin rayuwar da nake yi tare da ke, ita ce rayuwa mafi aminci da kwanciyar hankali. Ba ki yadda ba da na ce miki rayukanmu na cikin na juna ba? Muddin ruhinki na yawo a doron duniya, ba zai taɓa barin ruhina cikin nutsuwa ba, saboda abokan rayuwa ne"

"Sayyid"

"Duniyata"

Wani kyakyawan murmushi ne ya suɓucewa Nana, ta ce "Kalaman ka na ƙara mini ƙwarin gwiwa, har ba na son na ji muryar ka ta ɗauke ko sau ɗaya"

"Da gaske?"
Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, mai ƙayatarwa.

Sai da zuciyarta ta motsa, wani irin shauƙi ya mamaye ta, ji take tamkar ta furta abin da take ji a cikin zuciyarta, amma ta danne, sai kallonsa da take yi.

Ya ce "Faɗi mana, ki furta"

"Me zan furta?"

"Abin da yake zuciyar ki, da ki ke son faɗa" ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"A'a, ruhina ne a jikinki fa, ko in gaya miki abin da ki ke son cewa?"

Ta girgiza kai alamar a'a. Ya saki wani irin murmushi, mai cike da ƙasaita yana kallon fuskarta.

Haka ya sakankance, ya tattara duk hankalinsa da lokacinsa a kan Nana, sai da ya mantar da ita damuwar da ta shiga, wani nannauyan bacci, ya sace ta.

*****

Hajiya Sa'a ce take mita iya yin ta, "Wallahi Jamila, ban da yayan ki ne ya yi miki wannan dukan, da sai na rufe shi, wannan ai take haƙƙin ɗan Adam ne. Tun da kin kai shekaru goma sha takwas, ai kin sa abin da ya dace da rayuwar ki".

"Wallahi haka Mama ma ta faɗa, da police station za a kai shi, Baba ya yi ta bata haƙuri, nima na ce kar a kai shi, ta yi haƙuri"

"Saboda me ki ka hana a kai shi, ai gara a kai shi, ya san cewa ke da shi akwai bambanci yanzu"

Jamila ta ce "Kaii babban yayanmu ne fa Mummy"

"Shi ɗin fa, shi ba dukan ki ya yi ba?"

"A'a ai bai kamata ba, da kunya abun"

"Ke Jamila, kalle ni da kyau. Irin wannan lamarin, dole ki sakawa kowa tsoron ki idan ki na son ki zauna lafiya ki taka duk wanda ki ke so. Ba a tausayi ba kuma a tuna danganta kan ki kawai za ki kalla, ki gina rayuwar ki. Babu wani abu da dangantaka ke ƙara wa banda koma baya da hassada da fitintinu"

Jamila ta jinjina kai ta ce "Haka ne"

"Dan haka duk wanda ya yi yinƙurin taɓa ki, ki yi maganinsa kawai. Ni zan fita ba daɗewa zan yi ba amma"

"To a dawo lafiya" Jamila ta yi maganar tana kashingiɗa a jikin kujerar 3 seater da ke ɗakin.

Har bacci ya fara ɗaukar ta, ta ji ana sallama, ta buɗe idonta ya ce "Yi haƙuri na tashe ki, Mummy ta fita ne?"

Ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin mayar da kai ta kwanta.

"Ta daɗe da fita ne?"

"A'a"

Ya ce "Ok thanks " ta mayar da idonta, ta lumshe shi kuma ya ɗan ƙura mata ido, kan ya fice.

****
Alhaji Zailani na zaune, yana jiran ta gama haɗa tea ta ba shi, kiran wayar Hajiya Sa'a ya shigo wayarsa. Ya ɗaga su ka gaisa. Ta ce "Zailani, matarka ta fi ƙarfin ta je duba Hanifah a Asibiti, har an sallame su sun koma gida"

"Dan Allah ki daina kamabama abu, wane irin fin ƙarfi, ni na je, su Rauda su je, maman su ta je, duk bai isa ba? Ba ta da lafiya ne, mu na ta yawon asibiti"

"Ba ta da lafiya me ya same ta?"

Ya ce "We are expecting another Muhsin in sha Allah, cikin yana ta ba da matsala ne yana neman ya fita, so an bata complete bed rest ne, kin ga ba zai yiwu ta din ga yawo ba"

Hajiya Sa'a ta ɗan yi jimm sanan ta ce "Yayi Allah ya raba lafiya"

Uwargidan sa da ke ƙoƙarin haɗa masa tea kuwa, ji ta yi tamkar ta kurma ihu. Da ta ji batun cikin Fadila, kuma wani namijin ne. Ita nata yaran biyar duk mata ne.

"Ya dai lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon ta.

Ajiye masa tea ɗin ta yi, ta bar falon saboda takaici, dan kuwa ji ta yi, tamkar ta watsa masa shayin a kansa.

Ya karya abin sa a nutse, yana yi yana communicating da mutane ta waya.

Tashi ya yi zai je ya duba Fadila, dan ba a gurin ta ya kwana ba, kuma ba ta jin daɗi sosai. Sai dai ya ji tamkar an ɗora masa dutse a kansa, kuma an saka igiya an ɗaure shi. Ya yi miƙa ko zai ji dai-dai, amma ya kasa jin ya dawo normal.

Ya lallaɓa ya fita, kansa na sara masa ya nufi sashin ta. Ya yi iya ƙoƙarin sa, bai bari ta fahimci wani abu ba, saboda kar ya ƙara mata damuwa, ya zauna har su ka yi hira, sannan ya fita.

****
Ya na zaune yana kallon Nana, ta na ta fafutukar yin breakfast, saboda ƙoƙari meatpie ta tsiri yi da safen.

Ta kammala ta zuba masa nasa, ta haɗa masa tea. Ta zuba masa ido. Ya saka hannu ya ɗauka ya kai bakinsa ya ci, ya yi murmushi ya sake kaiwa bakinsa.

Ta ce "Da daɗi?"

Ya ɗaga mata babban yatsansa, alamar jinjina.

"To ka ce Allah ya yi mini albarka"

Murmushin sa ya ƙara faɗaɗa ya sumbaci goshinta, sannan ya shafa gashinta ya ce "Allah ya yi albarka"

"Amin Shugabana" ta yi maganar tana dariya.

"Ga Nonon can a kan mudubi, ki fara sha kan ki karya"

Ta tsuke fuska ta ce "Nonon raƙuma dai ba nawa ba" A tare su ka tuntsure da dariya, har ya kusa ƙwarewa, ta ɗaukko ruwa ta ba shi ya sha.

Ta ce "Ba ruwana, kar ka ƙware ka ce ni ce"

Duk da ba ta da cikakkiyar masaniyar dalilin ba ta Nonon raƙumin, amma ta fara jin daɗin sa sosai da sosai a jikinta.

"Sayyid, bari na kaiwa ƙawata ko za ta ci"

"Wa?"

"Yusra" ya jinjina kai. Ta fita ta shiga cikin gidan.

Ko da ta yi sallama, a falo ta tarar da Siyama, hannunta duk ya ƙone, a ɓare mata ƙunar.

"Sannu ina kwana?"

Ta kalli Nana ta amsa ciki-ciki. Ba ta sake bi ta kan Siyama ba, ta haye benen. Ɗakin Yusra ta shiga da sallama.

Yusra ta ɗago, amma ba ta amsa ba. Ta ganta a zaune a kan gado ta yi tagumi, amma tana ganin Nana ta saki murmushi.
Nana ma ta yi mata murmushi ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita ta ce "Yayata, kin tashi lafiya?"

Yusra ta ce "Lafiya ƙalau"

"Abinci na kawo miki, ko kin karya?" Ta ce "A'a"

"To ga wannan" ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode" Nana ta din ga yi mata hira, har ta cinye meatpie ɗin.

Ta ɗan numfasa ta ce "Dan Allah Nana, kema ki na jin kin gaji da duniya, idan ki ka ga wuƙa ki ji kamar ki cakawa kanki, ko ki faɗo daga saman bene ki mutu? Irin duniyar babu daɗi ɗin nan?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Sosai, na taɓa yinƙurin kashe kaina ma, amma addu'a nake yi sosai da sosai. Ina roƙon Allah ya kiyaye ni. Kuma nake yin alwala sosai nake zama da ita"

"Kin tabattar idan na yi hakan zai daina ji, idan na yi addu'a Allah ba ya karɓa, salla ma kamar ba daidai nake yi ba." Nana ta rufe mata baki ta ce "Ki daina faɗar haka, nima da ina wannan tunanin amma na yi ta istigfari. Allah ya na karɓar addu'armu, ba dan haka ba da wataƙila haukacewa zamu yi gaba ɗaya"

Yusra ta ce "Haka ne, wallahi na ji daɗin zuwan ki gidan nan, duk kin san me nake ji, kuma kin san abubuwan da nake ji ba ƙarya nake yi ba"

"Ai kamar yadda na gaya miki ne, mukaɗai mu ka san abin da muke ji. Ki daina damuwa sai kowa ya san halin da ki ke ciki, an fahimce ki an daina cewa ƙarya ki ke yi. Idan an kai ki gurin likita ya baki magani, ki din ga sha. A gefe kuma ki din ga addu'a ki na fatan Allah ya yaye miki"

Ta girgiza kai ta ce "Ba na son maganin likitan nan, bacci suke saka ni, kuma ba na iya baccin sam, sai dai jikina ya mutu, kuma damuwa ta ƙara yi mini yawa". Nana ta din ga rarrashinta da ba ta haƙuri.

Sun yi hira sosai, sannan ta ce za ta raka Nana bakin ƙofa.

Su na tafe ta ce "Kin ga Siyama ta ƙone ko? Tana shiga kitchen za ta juye ruwa a flask, na sheƙe mata shi a hannunta. Nana ta tsaya cak ta ce "Saboda me?"

"Ta ɓata miki rai, ni kuma muddun aka ɓata miki rai na san zuciyar masoyina sai ta sosu, ni kuma ba na fatan hakan. Dan da na ƙyale ta ma, ban san shi wani matakin zai ɗauka a kan ta ba"

"Ba zaki ƙyale matar nan ta huta ba ko Haula? Ki ji tsoron Allah"

Ta maze ta ce "Ai ko dan saboda ke, ina sassauta mata, ba har hira ku ke yi ba? Ina dattijon arziki?"

Nana ja ta tsaya, ta ce "Me yasa ki ke kiran mijina da dattijo, alhalin matashi ne?"

Ta yi dariya, ta naɗe hannunta a ƙirjinta ta ce "Ni ina ruwana da mijinki? Ba da shi nake ba, duk da na san ki na ganin komai wasu lokuta."

"Ki gaya mini, me ki ka sani game da mijina? Da tsohon da nake ganin su tare, tun da na san a kan sa ki ke magana."

Ta girgiza kai ta ce "Wannan wani hurumi ne da shigarsa ka iya kawo mini matsala,

48 / 64