Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
faɗuwar ta"
Ras Sayyid ya ji gabansa ya faɗi, ya ji maganar Imran ta yi masa nauyi da yawa.
Ya kalli Nasiru ya ce "Mu tafi"
Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Imrana ba zaɓarsa na yi a kan ka ba....
"Shhh ba sai kin yi mini bayani ba ai, tun da ki na farin ciki da auren ki Alhamdilillah" ya juya zai fita ta sake cewa "Ka bani lambar wayar ka, da zan din ga kiran ka a waya" bai waiwayo ba ya girgiza kai, ya ce "Babu buƙata"
Daga bayansa, yanayin yadda ya kai hannu fuskarsa, Ya sanya Nana gane Imran kuka yake yi. Sakin kuɗin hannunta ta yi a ƙasa ta durƙushe a gurin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ita ma.
Ayshercool
08081012143
43
Cikin matsananciyar damuwa, ya durƙusa a gabanta, amma ya rasa ta ina zai fara, ga shi ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Awanni kaɗan kenan da dawowar su daga Asibiti.
"Ba ki da lafiya fa, ki daina kuka"
Ba ta saurare shi, ba sai da ta yi mai isar ta. Ya zauna kawai ya zuba mata ido.
Sai da ta yi ta gama, ta yi shiru dan kanta, sai dai ba ta iya ce masa komai ba.
Ya bata magungunanta na dare ta sha, cikin sanyin jiki ya fara magana. "Duk da ban san girman alaƙar da take tsakanin ki da wands ya zo ba, amma alamu sun nuna dan uwanki ne, da yake son ki sosai. Ba zan iya jurar ganin hawayen ki ba, a dalilina. Idan zuciyar ki za ta samu nutsuwa rabuwar mu, shikenan dan Allah kar ki zauna dani alhalin za ki cutu"
Nana ta gyara zamanta sannan ta numfasa ta ce "Ka yi haƙuri da halin ƙuruciya da muka nuna maka. Da zan bijirewa auren nan, da ba zan yadda na tare da kai ba. Da can ban guji auren ba sai yanzu, wannan cikin na jikina na yi yaya da shi?.
Duk da na tashi a gaban mahaifina, tun mu na yara ƙanana, mahaifiyarmu ta bar gidanmu, babu wani abu da nake kallo na ji daɗi sama da Imrana. Ba ya son na yi kuka, duk da ina da yawan kuka tun ina yarinya n wasu lokutan har dukana yake yi, saboda na daina kuka ba ya so" ta faɗa tana murmushi tana share hawayen ta.
Ta ci gaba da cewa "Rayuwarmu akwai faɗi tashi da kalubale da yawa, gidan yawa ga rashin uwa. Ba ni da ƙarfi sai faɗa a yi ta dukana yana tare mini. Sai ya gama tare mini mu koma gefe ya zane ni yana ce mini nusara. Yana da zafi, ana ganin ba shi da kunya, amma wasu abubuwan a kan gaskiya yake. Zaka ji maganganun nawa wani iri, kamar ina yin su ba a muhallinsu ba. Amma na sha wahala ne, ya yi juriya a kan abubuwa da dama Saboda ni. Mutum ne mai taurin kai da kasada, amma tun da ya zubar da hawaye yau, na san abin da yake ji a zuciyarsa ba ƙarami ba ne ba. Tabbas yana da buri a kaina, yana cewa in sha Allah sai mun zama abin alfahari ga ahalimu, ban san iya abin da ya yi yinƙurin yi, da shirin sa a kan rayuwar mu ba, amma abubuwa suka canza. Ka yi haƙuri da abubuwan da mu ka yi maka Sayyid, kai ma ka na da muhimmanci a rayuwata, ka yi mana uzuri dan Allah"
Ya numfasa ya ce "Ba komai, daina kuka. Ni ban sani ba ma ko ina da iyaye ko ba ni da su"
"Ka na da su ma in sha Allah, kuma za ku haɗu cikin aminci da yardar Allah."
"Allah ya sa"
Nana ta ce "Me yasa Imran ba ka ji haushin zuwansa ba, shi ba ka hana shi shigowa ba?"
"A jikina na ji mutum ne mai muhimmanci a gurin ki, kuma ban ji zuciyata na tafasa da ya shigo ba"
Ta gyaɗa kai kawai, ba ta sake magana ba.
****
Sagir ne zaune tare da Shukura, Haidar yana ta wasansa a gefe, ya kwantar da murya ya ce "Wai dan Allah yaushe za ki koma gida ne? Na gaji da zama nikaɗai wallahi"
Ta kwaɓe fuska ta ce "Ba na jin daɗi komai ne. Dan Allah tambayar ka nake son yi"
Ya gyara zaman sa ya ce "Ina jin ki"
"Lokacin da aka yi mini tiyata, an baka ɗan da rai ka gan shi?"
"Dan Allah ki daina wannan maganar, ki na sane da jininki ya hau, managing ɗin sa ake yi"
Tuni ta fara hawaye ta ce "Amma ka san ban gan shi ba, sai hotonsa kawai na gani"
Ya ce "To ai kin san ba na nan aka yi tiyatar, sai da safe na zo, na lokacin an saka jaririn a kwalba, kuma dai koma mene ne ya rasu, dan Allah ki lallaɓa Daddy ki koma na gaji da zaman nan"
Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah zan yi masa magana, zan dawo ka yi haƙuri"
Ta lallaɓa shi da ƙyar su ka yi sallama. Yana tafiya ta tafi sashin Alhaji Zailani. Ta tarar da shi su na hira da Mummy. Hajiya Amina ta kalle ta ta ce "Ahh har Sagir ɗin ya tafi ne?"
Ta jinjina kai ta nemi guri ta zauna. Alhaji Zailani ya ce " 'Yar auta ya ƙarfin jikin naki. Duk da na ga Alhamdilillah jiki ya yi kyau, sai dai kin rame da yawa".
Ta yi murmushin da a iya laɓɓanta ya tsaya, saboda yadda take jin wata irin tsanar mahaifinta na kama ta. Duk da tana iya kokarin tabattar wa kanta, mafarki ba gaskiya ba ne ba, amma zuciyarta ta kasa ɗauka.
"Jiki Alhamdilillah " ta yi maganar tana mayar da hankalinta, kan Hajiya Amina.
"Mummy, wai dan Allah lokacin da aka yi mini tiyata, da a ka fito da ni, an baki babyn a hannunki kin gani"
Hajiya Amina ta ce "Sau nawa zan yi miki bayani Shukura, ke kaɗai aka fito da ke, ba a bani jaririn ba. Doctor Sharif ya ce na ɗan jira, jaririn ne ake fama, ko ba bu wadatacciyar iska ko me, oho maganganun su na likitoci. Na dawo ɗaki gurin ki, ya shigo ya ce mini, an kai babyn Nursery, da safe na je na gan shi"
Alhaji Zailani ya yi gyaran murya ya ce "Shukura, duk wani abu da za ki yi, abin da ya faru ya faru, ba za ki yi jayayya da ikon Allah ba. Kamata ya yi ki gode wa Allah, da ya baki lafiya. In dai da rai da lafiya, Allah zai baki wani mai amfani. Yanzu lafiyar ki muke buƙata, wannan damuwar ba ta dace da ke ba. Kin rasa babynki, nima ba zan so rasa tawa babyn ba, Please ki yi tawakalli na san kin sha wahala a kan cikin nan, amma ki yi haƙuri"
Shiru Shukura ta yi, zuciyar ta fal wasi-wasi. Ta ƙara ƙaimi gurin yaƙar mummunan tunanin da yake ta yi mata yawo a zuciya, ta hanyar kawar da batun mafarki da ta san ba gaskiya ba ne ba.
Duk mahaifiyarsu ta rasu, amma ba su tashi da zafin maraici ba, Alhaji Zailani ya yi aiki tuƙuru a kan rayuwar su, Hajiya Amina ma kuma ba ta taɓa yi musu mugunta ba, ta riƙe su da gaske tamkar 'ya'yanta. Saboda haka take ganin tamkar zuciyarta ba ta yi mata adalci ba. Amma fafur take jin ƙiyayyar mahaifin nata a cikin zuciyarta, ta kuma kasa yarda da cewa ɗan ta mutuwa ya yi ta haƙiƙa, ba wani abin ne ya faru ba.
****
Kwana biyu Nana ta samu sauƙin jikinta, jikinta ya ɗan yi ƙwari babu zazzaɓin. Sai dai abinci ne ba ya ciwuwa ta daɗin rai.
Ta saka Sayyida a gaba, a kan lallai sai ta yi wa gashinsa kitso, ta gaji da ganin kan a haka. Yana kwance a kan cinyarta, ta saka kibiya tana tsaga gashin nasa. Ta ce "Sayyid kishi nake da gashin nan naka, gaskiya aske shi zan yi, ya za ayi ina matarka a ce ka fi ni gashi?"
Ya yi dariya ya ci gaba da kallon da yake yi da wayarta. Ta yi guda biyu ta ce "To gyara, a yi na can ɓangaren"
Ya girgiza kai ya ce "Ki ƙyale ni"
Ta ce "A'a sai an ƙarasa"
Fafur ya ƙi gyarawa, ya ce shi fa kitson da zafi.
"Dan Allah ka yi haƙuri mu ƙarasa, haba Shugaba ba ka ga yadda kitson nan ya yi kyau ba. Yauwwa nawan" ya ɗago kansa ya harare ta. Ta sakar masa murmushi tana lumshe masa ido.
Ya gyara kwanciyar, ta ci gaba da kitsa gashin nasa, mai matuƙar santsi da laushi.
Babu tsammanni aka bankaɗo labulen ɗakin, sai da Nana ta razana, a hankali ya ɗaga kai ya kalli ƙofar.
Siyama suka gani a tsaye, Kunya ta kama Nana,yanayin da ta tarar da su. Shi kansa dogon wando kawai a jikinsa, ya ɗora kansa a kan cinyar Nana, tana yi masa kitso.
"Amm dama Mami ce ta ce na zo na duba, ko Yusra ta zo ba mu ganta ba da ma. Amma shikenan" Ta saki labulen a hankali ta ja da baya, saboda yadda jikinta ya yi sanyi.
Kamar babu abin da ya faru, ya ci gaba da kallon wayarsa.
" Ya jikinki ya yi sanyi? Me ya faru?"
"Ba komai" ta furta a hankali.
Ya juyo sosai ya kalle ta, sai kuma ya fasa maganar da ya yi niyya, ya sake gyara kwanciyar sa.
Dannewa kawai Nana ta yi, amma sai da ta ji tamkar ta ɗura wa Siyama ashar, saboda kawai su na masu gadi, ya ba ta damar ta shigo musu ɗaki, ba bu izini. Danne fushin ta ta yi, saboda kar ta saka shi a damuwa, amma tana ji a ranta wataran sai ta zagi Siyama.
Da yamma, Nana ta yi kwalliya cikin doguwar rigar material mai taushi, da hula. Ta fesa turare sannan ta ɗora girkin dare, sannan ta kunna turaren wuta a ɗakin.
Neman guri ya yi ya zauna a ɗakin ya ƙi fita, sai aikin kallonta kawai da yake yi.
"Shugaba, ba zaka fita shan shayin ba ne?"
Ya yi dariya ya ce "Kin yi kyau sosai da sosai, ba zan fita ba"
Ta sake cewa "Ka ga yadda ka yi kyau da kitson nan kuwa? Zo ka ga"
Ya yinƙura ya taso, ya zo ya tsaya a gaban ta, ta nuna masa mudubi ta ce "Kalli yadda ka yi kyau fa"
Ya shafa kansa ya ce "Na zama kamar mace"
Ta yi dariya ta ce "Ka yi mini kyau sosai a haka, dama nikaɗai ya dace na ga ka yi kyau".
Ya sunkuyo ya yi mata kiss a goshinta.
Cikin dariya ta ce "Ni idan ka na yi mini wannan abun, kunya ka ke bani"
Ya ce "Wanne?"
"Ko wanne" ya ƙara tsare ta da ido, da sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta saboda kunya.
"To matsa na wuce"
"A'a kirana fa ki ka yi"
Ya yi maganar yana haɗa bakinsa da nata.
Bayan ya cika ta, ta sunkuyar da kanta tana jin kunya. Ji ta yi jikinta ya fara sanyi, ƙirjinta yana bugawa, ta kalle shi ta ga fara'ar fuskarsa ta kau, ya haɗe rai. A tsorace ta ɗan ja jikinta, tana tunanin me ta yi masa. Tana kallon mudubin ta ga duhu ya gauraye ɗakin sai iya wannan tsohon ta iya gani a cikin mudubin a tsaye, sai dai a wannan karon ci yake yi da wuta.
Tattara nutsuwarta ta yi, ta fara Addu'a a cikin zuciyarta, ta waiwayo ta kalle shi.
Ta ga fuskar sa ɗauke da murmushi.
Ya miƙo hannunsa zai taɓa ta, ta riƙe hannunsa, ta yi yinƙurin kallon idonsa amma ta kasa, ta ji tamkar zuciyarta za ta buɗe.
"Waye kai?"
Ya amsa da "Mijinki mana"
Ta yi murmushi ta ce "Ba Sayyid ba ne? Ai na riga na ganka. Me yasa ka zaɓi muzgunawa rayuwata ne? Da ina zargin ko Ƙaisar ne, amma na fara fahimtar kai daban shi daban. Mece ce manufarka a kaina? Me ka ke buƙata?"
Wata irin dariya ya saki, ya ce "Har kin yi ƙwarin da ki ka daina razana da ganina kenan. Haka nake so fansa zan ɗauka, yanzu ne lokacin da ya dace na ɗauki fansata"
"Wani laifi na aikata maka da ka ke iƙrarin ɗaukar fansa a kaina"
Ba tare da tsammani ba, ya shaƙe ta, ya ɗaga ta ya yi jifa da ita, ta bugu da jikin wardrobe ta faɗi.
Ɗakin ya gauraye da matsanancin duhu, ta riƙe wuyanta tana numfarfashi cikin yanayi mai kama da ɗimuwa da kuma suma.
Ta daɗe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid.
"Rayuwata bacci kuma daf da magariba a ƙasa? Ga abincinki ya fara ƙonewa"
Nana ta ɗaga kai ta kalle shi suka haɗa ido, amma ba ta ji komai ba. Ta tashi da ƙyar ta ji mararta ta ƙulle, ga hannunta da ta bugu. Amma ta daure ta kashe gas din, ta shiga yin alwala.
Abubuwa da dama su ka zo zuciyarta, tabbas wannan sabon ƙalubale ne a gare ta. Muddin zai cigaba da fita daga hayyacinsa yana yi mata haka, to tana tsoron wataran ya yi mata illa.
Haka kurum yake jin sa cikin farin ciki, sai dai lokaci ɗaya ya lura ita ba ta cikin walwala.
Su na cin abinci, ya ɗan shafa cinyarta. Ta farga ta kalle shi.
Ya ce "Ba kya cin abinci mene ne?"
Ta yi murmushi ta ce "Lafiya ƙalau, Abincin ne ba na so"
Cikin damuwa ya ce "Na sayo miki buredi za ki ci? Ko ƙos"
"A'a zan ci wannan ɗin" da ƙyar ta tilasta kanta, ta ci.
Yanayin yadda yake ta bin ta da ido, ya sanya ta san akwai abin da yake so, sai dai a ɗan tsorace take. Haka ta ci gaba da addu'oi da neman ɗaukin Ubangiji.
Duk da haryanzu tana jin nauyin sa, amma ta shirya cikin kayan baccinta na gwanjo, da Ummi ta ba ta ta shafa turare. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya a tsinke take.
Kwanciyarta babu jimawa, ya zo ya kwanta shi ma.
"Rayuwata duk kin rage walwala"
Ta ɗan ja numfashi ta ce "'yan kwanakin nan, baki ya buɗe, Ubangiji Allah ya ɗorar da lafiya"
"Amin ma vie. Ina jin daɗin haka sosai"
"Saura kuma, Ubangiji Allah ya sanya ka tuna waye kai. Hankalina zai fi kwanciya"
Ya ɗan yi shiru ya ce "Ina wannan ƙoƙarin, ji nake kamar abin ya fi ƙarfina. Amma ko da nan gaba, idan ban tuna waye ni ba, ki nuna wa ɗa na su Habu a matsayin dangina, tun da ku kaɗai na sani" Ya yi maganar muryarsa na rawa.
"Shikenan mu bar wannan maganar." Ya yi shiru bai kuma magana ba.
"Sayyid fushi ka yi ne?"
"A'a ban yi fushi ba"
Ta din ga shafa kansa zuwa bayansa, sai dai daga ƙoƙarin rarrashin sa, ya fara ƙoƙarin zarcewa.
A hankali ta fara jin wannan ƙamshin turaren, yana ratsa kafofin hancinta.
"Sayyid ba ka jin wani ƙamshin turare?"
"Ina ji a jikinki"
"A'a ji nake kamar ba a ɗakinmu muke ba"
Ya yi dariya, ya cika ta ya ce "Ba sai kin yi mini wayo ba, na ƙyale ki" Ya ɗan ja jikisa ya koma gefe, yana ajiyar zuciya. Ta ɗora hannunta a kan nasa ta ce "Ba wayo zan yi maka ba, ai ka san ba na gudun ka."
"Kar ki damu, ki yi bacci" ya ɗora kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta.
*****
Shukura ji take yi, tamkar za ta haukace, sai kokawa take da sashe daban-daban na ƙwaƙwalwarta, domin samawa kanta nutsuwa.
Gari ya tsit amma ita sai kaiwa take yi tana komowa a cikin ɗaki, tamkar mai jiran saƙon wani abun.
Ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta yi tagumi.
Ta sake tashi tsaye, ta tafi bakin taga ta tsaya tana kallon waje. Ta ƙudurce a ranta, sai ta tuntuɓi doctor Sharif ta ji mene ne ya kashe mata ɗa? Haryanzu ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Alhaji Fatuhu kuwa, ƙarfin hali kawai yake yi, ji yake tamkar an daddane rayuwarsa da jikinaa gaba ɗaya. Babu abin da yake yi masa daɗi, ya daina jin daɗin komai, tamkar ya fasa ihu ko zai ji sanyi a ransa.
Ƙarfin hali ya yi gurin sanya Fadila farin ciki, har ya samu ta yi bacci, tun da ta yi bacci ya raba ta da jikinsa a hankali, ya tashi zaune ya rafka tagumi ya din ga jin tamkar ana buga masa abu mai nauyi a kansa.
Ya shiga banɗaki ya yi wanka, ya yi alwala ya zo ya tayar da salla, amma tunani da wasi-wasi ya mamaye shi, ya kasa nutsuwa a cikin salla. Ya din rafkanuwa. Ya din ga sallamewa yana sake tayarwa har ya gaji ya nemi guri ya zauna.
Tunanin yadda kayansa za su iso, a sallami mutane ya ƙara mamaye kansa, ya rasa bakin zaren matsalar baki ɗaya, haka ya zauna har aka yi kiran sallar asuba.
****
Tari ne ya sarƙe Nana, ta tashi ta ji kamar wadda ta ƙware tana numfashi sama-sama. Ta shafa ta ji Sayyid ba ya gurin, ta ji an kama hannunta an bata kofi, ta karɓa ta shanye ruwan, ta ajiye kofin saboda yadda wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Ƙaisar ta gani a tsaye yana kallonta, jikinsa duk a ƙone, bai yi mata magana ba, ya danƙi wuyanta ya zuba mata wani abu mai kama da hayaƙi a cikin bakinta.
A take ta ji cikinta ya hautsuna, mararta ta ƙulle, ta kalle shi a razane ta ce "Ƙaisar me ka yi mini?".
"Cikin jikinki ba shi da amfani, dole ya bar jikin ki"
"Saboda me, ina ruwanka da cikina?"
"Saboda ba zan ƙarar da rayuwata a matsayin bawa ga zuriyar ku ba, ki na wahalar da ni."
Kafin ta yi magana, ta ji tamkar ana fizgar naman cikin mararta, ta yinƙura ta tashi a gigice.
"Subhnallah, Sayyid, Sayyid" ta kira sunansa a wahale.
Daga banɗaki ya fito a tsorace, ya nufo ta. Ta miƙa masa hannu, ya riƙe ta.
"Kai ni banɗaki" ta faɗa tana rintse idanunta.
Ya kamata ta miƙe, jini ya fara biyo ƙafafuwanta, ya kai ta banɗaki. Su na shiga ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta saka hannu ɗaya ta rirriƙe ƙafarsa tana girgiza kanta cikin matsanancin ciwo. Da ta ja numfashi da ƙarfi, sai ta ji jinin yana zuba da yawa.
Ya rasa yadda zai yi, ga baki ya rufe ya kasa magana.
Can ta yi wani irin nishi, ta ƙara rirriƙe ƙafarsa da ƙarfi, sai ga gudan jini ya faɗo. A hankali ta din ga samun releif, ta jinginar da kanta a jikin ƙafarsa ta kasa motsi. Jin yadda ƙarnin jinin ya ishe ta, ya