Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
haka ya bi, dama abin yana cin sa a rai ƙiri-ƙiri mai kuɗi ya zo ta ce ba ta so"
Ya yi dariya ya ce "Mu ɗin na wasa ne? Gangaran ne ni fa, ai duk taurin buƙata muka ɗauki allo muka hau kan buzu mun gama da ita"
Mama ta ce "Ai kuwa na ga zahiri, malam saura na 'yan matana, a bamu na farin jini. Wallahi duk samarin nasu ba na arziki sai tarkace babu wata mamora a tattare da samarin nasu, ni kuma masu maiƙo nake so, inda zamu jingina mu huta, ka san rayuwar ce sai a hankali, ba zan so mu dauwwama a talauci ba, su yi gadon masifa ba"
Yayi murmushi ya ce"Tabbas wahala abar gudu ce, za a san abin yi, ki bayar da kuɗi, za a sai binta sudan, da ma'u wardi, sai farin goro zan yi musu wani aiki"
"To kamar nawa ka ke ganin zai isa?"
Ya ɗan yi shiru ya ce "Ba da dubu goma sha biyar, akwai turarukan da zan haɗa da su ma, da wasu saiwoyi." Ganin buƙatar ta ta biya a baya, ya sanya babu fargabar komai ta amince ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa, ta yi masa sallama ta tafi.
****
Bayan sallar asuba kallonsa Nana take yi, tana tuna abin da ya faru jiya da daddare.
Fuskarsa daina zahiri ba ta yi kama da ta miyagu ba, ta kalle shi daga sama har ƙasa, babu wata alama da take nuna ba mutum bane, a suffar sa ta zahiri.
Amma dole tana buƙatar tabattar da waye shi, ta kalli inda yake zaune yana ta fama da radio. Akwai aikin jin radio, sai dai magana ce aiki a gurinsa.
"Ina kwana?" Ya ji muryar Nana babu tsammani. Ya ɗago ya kalle ta domin ya tabbatar idan da shi take.
Ta sake cewa "Ina kwana?" Ɗaga mata hannu kawai ya yi, tare da jinjina kai.
Takaici ya kama Nana, maganar ce dai ba zai yi ba.
Kawai ta ga ya tashi ya ɗauki ɗan kurfotin dafa shayinsa, ya zuba ruwa a cikin butarsa. Ya ɗauki wata baƙar leda ya tashi zai bar mata ɗakin. Cikin sauri ta tashi ta ce "Kawo na dafa maka" ya kalle ta ya girgiza mata kai.
Ta miƙa hannu za ta karɓi butar, ya janye ya ce "A'a"
Ya juya zai fita, kawai ya ji ta biyo bayansa. Ya tsaya ya waiwayo, tana ƙoƙarin tsare shi da ido, amma ta kasa. Ya kuma yin gaba ta sake bin sa.
Sai ya fasa fitar, ya dawo ɗakin, ita ma ta biyo shi ta dawo.
Ya samu guri ya zauna, yana kallon butar shayinsa yana kallon Nana, da ta maze.
Bayan wani ɗan lokaci ya tashi ya fara shirin shiga wanka. Nana ta maze ta ɗauki wayarta tana dannawa.
Sai da ya shiga banɗakin, ta bi bayansa da kallo.
Hajiya Amina ta kira a waya, cikin ikon Allah kuwa bugu biyu ta ɗaga tana "Amarya kin sha ƙamshi"
Cikin jin nauyinta Nana ta ce "Hajiya ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke fatan kina lafiya? Ina ta kiran wayar ki a kashe"
Nana ta yi murmushi ta ce "Sai jiya na ga wayar ne. Ina ta ganin abin alkhairi Hajiya, na gode sosai da sosai Allah ya saka miki da mafificin alkhairi. Allah ya baki abin da ki ke nema duniya da lahira, Allah ya jiƙan magabata na gode sosai da sosai"
"Kai Nana kamar wadda na bawa wata duniya, kar ki damu amma yaya ki na ganin babu matsala, ba zai muzguna miki ba? Kuma baya haukan sosai ba zai cutar da ke ba?"
A taƙaice Nana ta ce "A'a babu wata matsala. Ina Haidar?"
"Haidar sun koma gidansu, ya hana kowa sukuni, kullum sai ya yi zancen ki, babansa ya dawo amma ya kasa sakin jiki da shi, ke kawai yake kira"
"Allah sarki, wallahi Hajiya ina kewar Haidar sosai da sosai, dan Allah duk ranar da aka kawo miki shi, ki haɗa ni da shi a waya"
"In sha Allah Nana, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, in sha Allah zan kawo miki ziyara har gidan naku"
"To hajiya na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi"
Suka yi sallama, a daidai lokacin da ya fito daga banɗakin, jikinsa na rawar sanyi.
Gashin sa na ta ɗigar da ruwa, murɗaɗin damatsansa, da ƙirjinsa da yake wayam, sai kwantaccen baƙin gashi tun daga ƙirjinsa zuwa cikin sa, shi ne ya banbanta shi da mace, saboda dogon gashin da yake kansa kamar ba namiji ba.
Da hanzari ya saka maɗauri ya naɗe gashin kan nasa. Ya zura rigar hannunsa, ya nufi wardrobe ɗin su gadan gadan, sai dai yana taɓa ta ya ja da baya, kamar wanda ya taɓa wuta.
Ya ɗago ya kalli Nana, ya nuna mata drower ƙasan wardrobe ɗin. Tasowa ta yi tana kallon wardrobe ɗin.
Ta ce "Mene ne?"
Ya sake nuna mata wardrobe ɗin, ta durƙusa ta buɗe, sai ga jakar fatar gidan sarkin baka, ta bayyana a saman drower. Ya ƙurawa jakar ido. Ta ɗaga kai ta kalle shi. Da hannu ya yi mata alamar ta ciro jakar.
Ta ciro jakar, ba ta ce masa uffan ba, ta canza mata guri, tana fara ƙoƙarin ƙara gazgata Ƙaisar.
Ta nemi guri ta kwanta a kan katifa, ta juya masa baya, domin ya shirya a tsanake, saboda yadda ta fuskanci duk a rikice yake.
Sai da ta ji motsinsa yana ƙoƙarin ɗaukar butar shayi, ta ce "Bawan Allah yunwa nake ji" cak ya fasa ɗaukar butar, ya tsaya yana kallonta.
Ta sake cewa "Ina jin yunwa" magana yake son ya yi mata, amma ya kasa. Sai ya fasa ɗaukar kayan shayin, ya ɗaga labulen ɗakin, ya leƙa ya sake dawowa ya kalle ta amma bai yi magana ba.
Ta sake mazewa ta ce "Bawan Allah ina jin yunwa" kallonta ya yi, amma ta ƙi kallonsa.
Sai ya tafi gaban wardrobe ɗin su, ya buɗe tasa, ya sake ɗaukko robar dabino lubiya, ya zo ya ajiye a gabanta.
Ta kalli dabinon ta ce "Ni ba wannan ba abinci" ta yi maganar tana kawar da kanta gefe, taƙi kallonsa.
Fuskarta yake kallo, amma ta maze, ya miƙe ya ci gaba da zagaya ɗakin, kamar mai jiran wani abu.
Kallonta yake amma ya ga ba ta da niyyar cin dabinon.
Wani irin horn aka yi a gate ɗin, ya juya ya fita daga ɗakin, ya nufi gate ɗin.
Tashi Nana ta yi, ta tafi tana leƙawa ta taga.
Cikin gidan aka shige da motar, dan haka ba ta ga waye a motar ba.
Yana dawowa ɗakin ta kalle shi ta ce "Mutanen gidan sun dawo kenan? Ai da na zata babu kowa a gidan" shi dai bai ce uffan ba, sai dai ya bi ta da ido.
Ta koma kan katifa ta zauna, tana danna wayarta.
Ƙarar tsayuwar adaidaita sahu suka sake ji, ta ga ya ɗan saki fuskarsa.
Habu ne ya shigo da ƙaramin gas cylinder, da kuma kayan abinci.
Harshe suka juye, suka fara magana da yaren su.
Mamaki ya cika ta, tana ta magana ya share ta, amma yana ganin ɗan uwansa ya yi magana. Amma idan ta tabatta shi ba mutum bane ba, su waɗannan da yake tare da su, su ma ba mutane bane ba kenan?.
Habu ya dubi Nana cikin damuwa ya ce "Nana ki yi haƙuri dan Allah, ya ce kin ce yunwa ki ke ji, na je zubo miki abin girki ne, ga abinci ma na zo muku da shi"
Nana ta ce "Au dama ni ce ba zai yi wa magana ba? Kar ka damu mun gode sosai ku na ta ɗawainiya da mu"
Habu ya ce "Ai dole mu kula da ku, kin auri ɗan uwanmu, amma dan Allah ki din ga haƙuri kin san na gaya miki ba shi da cikakkiyar lafiya ne. Ina kyautata zaton wannan ƙaddarar ce ta sanya mu zuwa Nigeria."
Nana ta ce "Na karɓi ƙaddarata, in sha Allah, na miƙa wa Allah lamarina"
A nan Habu ma ya karya, ya zauna su ka yi hira da Nana, shi kuwa da ya gama cin abincin sa, ya koma gefe ya yi musu shiru.
Shi ma bai wani jima sosai ba, ya tafi. Gaba ɗaya zaman shiru ya ishi Nana, shi ba kula ta yake yi ba, sai dai ta wuni a ɗaki shiru, shi kuma yana waje, yana jin radio da aikin dafa shayi kamar ibada, ko hutawa ba ya yi, har mamaki take yi idan yana gane abin da ake yi a radion.
Bayan azahar yana kwance, a ɗakin, radion ta cika wa Nana kunne, ta dube shi ta ce "Dan Allah zan shiga cikin gidan nan, na yi musu sallama, tun da na ga alamar akwai mutane a cikin gidan" ya gyaɗa mata kai kawai.
Ta ɗumama ruwa a kan gas, ta shiga ta yi wanka ta fito, sanye da dogon hijjabi. Ta ɗauki kayan da za ta saka, ta koma banɗaki ta canza ta fito. Doguwar riga ta sako, hannunta riƙe mayafin rigar. Ta cire hular kanta, ta tsaya a gaban mudubi tana shafa mai. Abin ka da mace, kuma amarya, sai ta tsaya a gaban mudubin tana gyara fuskarta.
Ta tsiyayo humra ta shashshafa a jikinta. Ta janyo drower mudubin, inda yake ajiya kayansa ta buɗe a hankali, ta waiwaya ta kalle shi, ta ga idonsa a rufe, ta ɗauki turaren sa, ta tsiyaya a hannunta, ta shafa a wuyanta.
Yana daga kwance yana kallonta, ta ƙasan idonsa. Sai da ta gama tsaf, za ta fita kawai ya yi gyaran murya. Ta tsaya ta waiwayo tana kallonsa.
Ya yinƙura ya tashi, ya nufe ta, ta tsaya ƙyam tana kallonsa. Gani ta yi tamkar zai shige cikin ta, babu shiri ta fara ja da baya, sai da ta dangana da jikin bango.
Ayshercool
08081012143
30
Zazzaro ido Nana take yi, numfashin ta na neman sarƙewa, saboda tsoro da fargaba.
Ya saka hannunsa ya kamo hannunta cikin nasa, wani irin sanyi ya ratso ta, tun daga tafukan hannayenta har zuwa ƙafafuwan ta. Ya kama gefen rigarsa ya goge in da ta shashshafa turare a hannunta. Ya saka hannunsa a gefen wuyanta, nan ma ya goge wanda ta shafa a nan.
Na saman rigarta yake kallo, sannan ya kalli idonta. Ta yi tsuru-tsuru a ranta ta ce "Daga ɗan shafa turaren sa, shi ne yake mini wannan tijarar haka"
Idonta ta saka kwalli, bakinta kuma ta saka man leɓe mai kala, sai girarta da ta gyara. Ba ta gama zancen zucin ba, ya saka hannunsa ya fara goge man da ta saka a leɓenta.
Riƙe hannunsa ta yi za ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kallo da ta rasa na mene ne, babu shiri ta yi tsit. Ya goge leɓenta tsaf. Ya kalli idanunta da suka sha kwalli, ya mayar da hannun sa kan girarta, ya hargitse gashin girarta.
Ya zare mayafin rigar da ta ɗora a kanta, ya ciro hijjabin da ta shiga wanka da shi, ya hau saka mata.
Kamar ta rusa ihu ta ce "wanka fa na yi da shi, ba ka ga duk danshin ruwa a jiki ba?" Bai amsa mata ba, ya jefa mayafin rigar a kan katifa, ya koma gurin da yake zaune ya zauna. Wani irin takaici ya tokare Nana, kamar ta kurma ihu, saura ƙiris ta ce ta fasa fitar, amma ta tuna zaman shiru za ta zauna ta yi a ɗakin, ko ma shi ya fice ya bar ta. Ta ja takalmanta ta fice daga ɗakin tana haɗe fuska.
Fasalin gidan ya yi mata kyau sosai da sosai, sai da ta zagaya ta bayan wata baranda, sannan ta gano ƙofar shiga. Tun daga barandar take ɗan jiyo hayaniya sama-sama.
Ta buɗe ta shiga da sallama. Samari ne su kusan biyar a falon, su na kallon ball su na ta hayaniya. Sallamar ta ce ya sanya su yin shiru, suka amsa mata.
"Sannunku, dan Allah matar gidan nake nema"
Ɗaya daga cikin su mai riƙe da remote a hannunsa ya ce "Tana sama" ya yi maganar yana nuna mata upstairs.
A falon saman benen ta tarar da matar, babba ce mai jiki fara tas da ita, tana shan lemo a kofi tana danna remote.
Ta amsa sallamar Nana, tana yi mata kallon rashin sani.
"Ina wuni?"
Matar fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce "Lafiya ƙalau, zauna mana ga kujera nan" Nana ta zauna, ta kalle ta ta ce "Dama ni ce matar mai gadinku, da muka tare, na ga tun da muka zo ba kwa nan, sai jiya na ji motsin mota a gidan, shi ne na ce bari na zo mu gaisa"
"Allah sarki, sannu ko? Da maigidan ya ce mini buzaye ne"
Nana ta ce "Maigidana ne buzun, ni bahaushiya ce"
"Ohh Allah sarki, ya sunan ki ne?"
"Nana"
Ta ce "Ma sha Allah, sannun ki"
Nana ta ce "Yauwwa, idan akwai wani aiki ma, idan ki na buƙata, idan bai fi ƙarfina ba, a yi mini magana zan yi in sha Allah"
Matar ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai" Matar ta ɗan yi shiru tana kallon Nana. Ta yi mamakin yadda yarinyar mace kamar Nana, ta auri Buzu har yake yawon gadi da ita.
Sanin da Nana ta na idan ta koma, zaman tsuru-tsuru za ta yi da wannan kurman mutumin, ya sanya ta ja ta yi zamanta, ta ci gaba da kallon Tv. Matar kuma ba ta ce mata uffan ba. Can Nana ta ce "Hajiya ba ki da 'yan aiki?"
"Ina da su, ba na zama ne sosai a ƙasar, duk sun watse mun ma dai samu saɓani ne"
"Ke ki ke aikin da kan ki?"
"Ni da yara muke yi"
Nana ta ce "Allah sarki, idan kina buƙatar aikin ma, zan din ga zuwa ina yi miki"
Duk da tana basar da Nana, sai da ta yi murmushi ta ce "To in sha Allah" sai da Nana ta gama kallon, sannan ta tashi ta yi wa matar da ko sunanta ba ta sani ba sallama.
Ta sauka ta fita, sai dai tana fita ta yi kiciɓis da shi, sai da ta tsorata, yana tsaye a bakin ƙofar shiga cikin falon gidan, yana jiran ta
"Lafiya? Ya na ganka a nan?" Yana ganin ta fito kawai ya yi gaba ya bar ta a gurin. Ba ƙaramin ƙuluwa take yi da wannan dunkun-dunkun ɗin da yake yi ba na rashin magana.
*****
Babbar mace ce a ƙalla za ta yi shekara talatin da bakwai zuwa da takwas, hannunta riƙe da waya take kaiwa tana komowa a ɗakin, ta sake kai wayar kunnenta.
"Hello Yaya kina ji na? Dan Allah maganar nan da gaske ki ke?"
Daga ɗaya ɓangaren matar ta ce "Oho ban tabattar ba, amma kin san babu lallai a yi jita-jita da irin wannan maganar, amma abu mafi sauƙi ki saka lokaci mu je mu tabattar"
"Yanzu Yaya idan maganar nan ta tabatta, baban su Imaran ya kyauta mini? A yi auren yarinya ta amma a kasa gaya mini an yi mini adalci a haka? Ba fa shikaɗai yake da hakki a kan yarinyar nan ba"
"To yaya za ki yi maijidda? Kawai mu shirya mu je shi ya fi sauƙi"
Gyaran muryarsa da ta ji ya sanya ta kashe wayar babu shiri, tana faɗin sannu da zuwa.
Ya ƙura mata ido ya ce "Meye haka na ganki wani iri?" Ta so ta jure zuwa ya samu nutsuwa su yi magana ta fahimta, amma ta kasa. Cikin damuwa ta ce "Labari na ji wai an yi wa Nana aure, shi ne nake son in tabattar"
Nan da nan ya haɗe fuska tamkar tasowar hadari lokacin marka-marka.
"Wato ba zaki fasa kiran tsohon mijinki ba ko Maijidda, ni fa na gaji ba zan lamunci wannan iskancin naki ba na shekara da shekaru"
Cikin ƙoƙarin kare kanta ta ce "Ka yi haƙuri, wallahi ba kiransa nake yi ba. Da Yaya nake waya wallahi"
"Bani wayar nan"
Ta ɓoye wayar a bayanta ta ce "Wallahi ba da shi nake waya ba, Yaya ce" za ki bani ko sai na ɓata miki rai. Ta miƙa masa wayar tana kuka ta ce "Dan Allah baban su Walida, ka bani wayar nan, hankalina ba zai kwanta ba sai na tabattar da gaskiyar maganar nan"
Ya tsaya cak yana kallonta ya ce "Allah wadaran halinki, ko kunyar Ubangiji ba kya ji, babu wata Nana da aka yi wa aure, tsohon mijinki ne ki ke bibiya, tirr da halinki" fashewa ta yi da kuka, tana sheshsheƙa mai cike da ƙunar rai.
*****
"Zan yi wanka" ya yi maganar yana tsare ta da ido.
Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ce "To ka yi mana"
Ta yi magana tana ɓata rai, tare da mayar da hankalinta kan wayarta, da ta gano tarin fina-finai a ciki. Tun bayan da Hajiya Amina ta bata wayar, ta nunawa Nasiru, ya karɓi wayar ya fita da ita gurin abokan sa aka yi turi, ba ta taɓa sanin da su a wayar ba.
Shiru ya yi yana kallon Nana, ganin ba ta gane abin da yake nufi ba. Kawai ya shiga banɗakin.
Ƙofar banɗakin ta bi da kallo, gaba ɗaya ta kasa gane kansa, babu yadda za ayi ace mutumin da yake da taɓin hankali, ya din ga gudanar da al'amuransa cikin nutsuwa. Sai dai kuma wannan shirun nasa ma, yana ƙara tabattar da taɓin hankalin nasa. Duk da ma ba wannan ba, hankalinta ya fi karkata ga son sanin ainihin waye shi.
Ya shafe tsawon lokaci a banɗakin, dan sai da Nana ta manta da shi ma, sannan ya fito. Jikinsa sai tsuma yake yi.
Ya nufo kan katifar da Nana take kai tsaye, bai ce mata uffan ba, ya zazzageta ya janye bedsheets ɗin da yake shimfiɗe a kan katifar ya duƙunƙune a ciki.
Galala ta saki baki tana kallonsa.
Lallai babu alamar hankali a nan" ta faɗa a zuciyarta. Sai dai ta lura da yadda jikinsa yake ta tsuma da rawar sanyi.
Ga garin babu sanyi sam, ita gumi ma take yi, amma ta ga yana ta tsuma. Ya jima sosai a haka, daga bisani ya tashi tsaye, ya nannaɗe bedsheet ɗin ya ya jefe mata a ka, ya wuce gaban mudubin.
"Ya haka, me yasa ka jefo mini?"
Waiwayo wa ya yi mata wani mugun kallo, ya juya ya ci gaba da abin da yake yi.
Taɓe baki ta yi, ta tashi ta ɗaukko wani zanin, ta shimfiɗa ta zauna. Hannunsa ɗauke da robar mai, ya nufo ta.
Ya ajiye man a gefenta, ya zauna ya juya mata bayansa.
Ƙuri ta yi wa bayansa da ido, daga bisani ta ce "Me za a yi ne?"
Ya ɗauki robar man, ya saka mata a hannunta, ya nuna mata bayansa da hannunsa.
A ɗan tsorace ta ce "Wai taɓa ka