BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   45 / 64

132K to 135K   out of 190K words

Lallai na zaune bai ga gari ba, kalli gidaje"

Hajiya Sa'a ta yi dariya ta ce "Jamila kenan, a garin nan gidajane sun fi huɗu, akwai arziki Jamila, muddin za ki yi biyayya ki riƙe sirri, to za ki samu arzikin da sai ya kankare baƙin talaucin da yake bibiyar zuriyar ku. Dan ma mun kasa samun jinin yayar ki ne, da tuni ta fashe mana tana da taurarin arziki amma ba ta san yadda za ta yi amfani da su ba ne ba"

Cikin shauƙi da zumuɗi Nana ta ce "Kai in sha Allah, zan riƙe amana da sirri babu wanda zai ji komai"

"Yauwwa yarinyar kirki, wannan yana ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyarmu, tun da ya amince da ke, tare da ke za mu je taron shekara, ina saka ran a karɓe ki a ƙungiya"

*****

Har wajen ƙarfe goma na dare, bai shigo ɗakin ba, Nana ta kashe fitila, ta ɗaga labule, ta hange shi a zaune a kan benci yana ta kore sauro, yana shan shayi.

Kawai ta girgiza kai ta nemi guri ta zauna, ta yi addu'oin kwanciya bacci, ta kwanta.

Ta kai a ƙalla mintuna arba'in, tana tunanin yadda rayuwa za ta ci gaba da juyawa a haka. Zama da mutumin da ba ta san ma waye shi ba.

Tana kallon ƙofa, ta ga ya shigo, ya ajiye kayan shayinsa ya tafi banɗaki. Ya jima a ciki sannan ya fito daga ciki, ya rataye kayan da ya cire, ya nufo kan katifar.

A ranta take jinjina ƙarfin hali na maza, da a ƙasa yake zamansa, ko ya kwana a waje a kan benci, amma yanzu kansa tsaye yake ɗarewa katifa.

Ba ta gama tunanin ba, ta ji shi a jikinta.

"Me yasa ki ke kallona?"

"Ya aka yi ka san ina kallon ka a duhu?"

"Na sani, tun da na shigo ki ke kallona"

"Shi ne tun da mu ka dawo, ka ƙi kula ni"

Ya ɗan yi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce "Ba na son na ga wani yana yi miki magana, zuciyata na yi mini ciwo. Ba na son kowa ya kalle ki, ba na son kowa ya ji muryar ki, ba na son wani ya raɓi inda ki ke, sai nikaɗai ban san dalili ba amma ina jin kamar zuciyata za ta tsaya ne, ba na so"

"Amma wanda ka ganmu tare, Yayana ne fa, babanmu ɗaya da shi" Ya yi shiru bai yi magana ba.

Ita ma ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Sayyid a ina ka samu kuɗi ne? Na ga ka bawa Haidar, ka bawa Baba, kuma ka na sayo mana abubuwa"

"Allah ne ya bani"

"Eh na sani, amma waye yake baka?"

"Habu" ya amsa kai tsaye.

"Shi ba shi da nasa buƙatun zai din ga kashe mana kuɗi har haka?"

Ya yi shiru bai amsa mata ba.

A hankali Nana ta ce "Sayyid"

"Husnahh"

"Dan Allah ya ake yi ka ke yin wasu abubuwan, ka san na ce maka, ba ni da cikakkiyar lafiya wasu lokutan gaba ɗaya a rikice nake ba na tantance ainihin zahiri da mafarki, amma sai na ga kana abubuwan da mutane normal ba sa iya yi"

"Kamar me?"

Ta ce "Ammm ka na shigowa cikin mafarkina"

Kawai ta ji ya yi dariya "Dama wani na shiga cikin mafarkin wani ne? Ba mafarkinki nake shiga ba, ruhina ne yake rayuwa a cikin naki, kuma naki yake rayuwa a nawa. Na fuskanci hakan a ranar da na fara ganin ki, zuwa ranar da aka ɗaura mana aure"

"Ban gane ba, ka yi mini bayani sosai"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ƙirjina ya fara nauyi"

"Saboda me?"

Ya yi mata shiru.

"Amma Sayyid.... "Shhhh zan yi bacci"

Ta ce "Tambaya ɗaya zan yi maka dan Allah"

"A'a"

"Allah fa na ce"

"Na ce A'a"

Ta ɗan ja numfashi ta ce "To amm... Tsit ta yi dalilin bakinsa da ta ji a nata.

Ya riƙe hannunta a nasa yana matsa nata a hankali.

"Dan Allah ka bari yau mu samu isasshen bacci, ni dan Allah ka ƙyale ni"

Ya ce "Idan ma kin yi baccin, zan biyo ki har cikin baccin naki. Na gaya miki ruhinki a cikin nawa yake rayuwa, ko fushi ki ke yi a cikin jikina nake ji".

Haka ya yi ta tsaro maganganun, da suka ci gaba da dagulawa Nana lissafi, da birkita mata ƙwaƙwalwa, wanda ba ta gama warwarar su ba, har ya nufi inda yake son zuwa.

*****

Tun bayar tafiyar Nana, da Shukura ta ga mahaifinta ta ji gabanta ya faɗi, ta kalle shi cike da tsoro da razani.

Cikin kulawa ya ce "Sannu Auta, haka ki ka koma? Ya jikin naki?"

A tsorace ta ce "Daddy dama yau zaka dawo, Mummy ba ta gaya mini ba"

Cikin damuwa ya ce "Ina can hankalina ya ƙi kwanciya, na ce bari na zo na ganki, na kira Sharif ya ce mini jikinki da saura, shi yasa na ce gara na zo na gan ki"

Ta dai yi shiru, gabanta na ci gaba da faɗuwa, ya gama yi mata sannu ya tashi suka fita tare da doctor Sharif.

"Sharif "

"Na'am ranka ya daɗe"

"Muddin yaron nan zai rayu, ka yi duk mai yiwuwa a cire shi kawai, a matsa nake"

"Zan yi iya ƙoƙarina, amma ka san wannan sabga ce mai haɗarin gaske, sai an yi taka tsantsan yadda ba za a bar duk wani trace da za a gane wani abu ba, zan yi setting date da komai da yadda abin zai kasance"

"Better" Alhaji Zailani ya furta yana yin gaba.

Gidansu Nana har ƙarfe goma na dare Jamila ba ta dawo ba, Baba yana tsakar gida yana yi wa Mama bala'i.

"Yanzu Rabi sakarcin naki har ya kai Jamila ta kai bayan goma a waje? Gidan uwar wa ta tafi haka?"

"Wai dan Allah Jamila za ta gudu ne? Na ga dai ba yarinya ce ƙarama ba, na ce maka za ta dawo"

"Za ta dawi gidan uban ta je? Goma na dare ta riga ta wuce, me take yi a waje a wannan lokacin?"

"Dan Allah ni kar ka ɗaga mini hankali, na ga dai yarinyar nan ba sauke hakkin da Allah ya ɗora maka ka ke yi ba, abinci ma ba bamu ka ke yi ba, sai ma dai ta samo ka ci"

"Da ba na sana'a sai na zuba ido su lalace? Sana'ar uwar me take fita?"

"Ni fa 'ya ta ba lalacewa ta yi ba, na ga dai nan Nana take nata yawo, ba ka yi magana ba"

"Ai Nana na san me take fita yi, Jamila fa, na san dai tana yawon maƙota, bayan wannan uwar me take yi?" Sosai su ka ci gaba da jayayya tsakanin Mama da Baba, sai sha ɗaya da rabi na dare, sai ga Jamila ta yi sallama, hannunta niƙi-niƙi da ledoji.

Duk da ledojin hannunta, sun ɗauki hankalin Baba, amma ya dake ya fara tuhumar ta daga ina take.
Mama ta kankane, ta hana Jamila magana, ta din ga karewa.

Ƙarshe sai haƙura ya yi, ya rabu da su.

Ita kanta Suwaiba jiki a sanyaye take kallon kayan da Jamila ta zo da su, tana fargabar Allah ya sa ba kauce hanya 'yar uwarta ta fara yi ba. Sai dai Mama ko a jikinta, musamman da Jamila ta ce mata, Hajiya Sa'a ce ta saya mata, wai gidan 'yar uwatta ta raka ta.

Wajen Sha biyu na dare, Jamila na ta bawa Suwaiba, labarin abin duniyar da ta gani.
Suwaiba ta yi tsuru da ido tana kallon Jamila, daga bisani ta ce "Ni dai Jamila na fara jin tsoron matar nan, anya haka kurum take yi miki wannan ɗawainiyar. Jamila kar ki kai kan ki ga halaka, idan rayuwar ki ta lalace ba ki da wata makoma wallahi"

Jamila ba ta yi magana ba, Gaddafi ya faɗo ɗakin ya kalli Suwaiba ya ce "Bar ɗakin nan" Jamila ta miƙe ita ma a tsorace tana kallon sa"

"Fita na ce" ya yi wa Suwaiba tsawa.

Jamila na ƙoƙarin fita, ya danna ƙofar ɗakin ya saka sakata, ya fito da wani irin danƙo na injin markaɗe, ya kalle ta ya ce "Gidan uban wa ki ka je, ki kai yanzu ba ki dawo ba?"

Jamila ta rikice jikinta yana tsuma, amma ta kasa magana.

"Ba magana nake yi miki ba?"

"Babu inda na je?"

"Ƙarya ki ke yi, uban waye ya sauke ki a mota?"

"Hajiya Sa'a ce"

"Babar ki ce ita? Meye tsakanin ki da ita?" Jin ta tsaya inda inda, ya sanya ya fara zuba mata danƙon nan a jikinta.

Cikin kururuwa Mama take dukan kofar ɗakin, tana neman agajin mutane, kar Gaddafi ya kashe mata 'ya.

Ya zuba wa Jamila danƙon nan, ya fi sau sha biyar, sai da ya zamana daga ita sai underwear.

Sai da aka taru aka yi ta yi masa magiya, sannan ya buɗe ƙofar ɗakin ya yo ball da ita waje.

Mama hankali a tashe ta nufi Jamila tana salati, saboda wahala ko kukan ba ta iya yi, sai wani yawu da yake fita daga bakinta.

Baba ya ce 'Haba Gaddafi, ba kowane lokaci duka da zuciya yake aiki ba, yanzu idan ka illata ta fa, mace ce fa"

Gaddafi bai saurari Baba ya ce "Wallahi ta sake sai na karairayata, ba za ta ɓata mana suna a banza ba"

Cikin ƙaraji Mama ke faɗin "Wallahi ba zan yarda ba, sai na kai ka gurin hukuma"

Nasiru da yake gefe ya ce "Allah sarki, Nana na can, da yanzu an ce ta hana mutane bacci" babu wanda ya saurari abin da Nasiru yake faɗa, suka ci gaba da hayaniyar su.

****
Ko da Nana ta fito daga wanka, yana tsaye a ƙofar banɗaki yana jiran ta, ta murguɗa masa baki, za ta wuce ya riƙe ta yana murmushi ya ce "Meya faru?"

"Ni rabu da ni, ka hana ni bacci, ga jiƙa kai sai na yi ciwon kai"

"Ba dai fi na gashi ki ka yi ba" ya yi maganar yana taɓa gashin nata.

Nana ta kalle shi ta ce "To yi mini gori" bakinta ya sake sumbata yana murmushi.

Ta gyara shimfiɗa ta hau, shi ma ya haye yana buɗe bargo.

"Ni gaskiya katifar nan ta yi mana kaɗan"

Ya ce "Ya za ayi?"

"Ka saukar mini daga kan katifa, ai na ga ma ba a ɗakin nan ka ke kwana ba"

"Na gama yi miki amfani dole ki kore ni, ba inda zan je" ya yi maganar yana kwanciya"

Nana ta ce "Na shige su, idan muka futa sai ka yi gumm, sai na yi ta yi wa mutane bayanin ka na magana, ba kurma ba ne ba, amma daga ni sai kai ka yi ta wasu maganganu"

Tana jin sautin dariyar sa, cikin nutsuwar sa, da ta fi kama da Iyayi ya ce "Asma'u ke duniyata ce, tun da na farka a cikin wannan duniyar, nake jin tamkar nikaɗai ne baƙo, Habu yana iya ƙoƙarin sa a kaina, amma ba ya wadatar da ni. Fatana da burina na yi na gama mafarkin nan na tashi, na koma ainihin rayuwata.
Ba na jin daɗin komai a wannan rayuwar, sai ranar da na fara ganin ki, tare da yayar ki da suka zo kun je gidan mai magani, har ki ka faɗi. Ina ganin ki na ji kamar ina da wata alaƙa mai ƙarfi da ke."

"Ni ɗin? Yanzu dama kai na gani ranar da muka je?"

"Mun haɗu a gidan sarkin baka ma."

A zabure ta ce "Sayyid ka san sarkin baka?"

Ya ce "Na sani, Habu sun kai ni, ko zan iya tuna ni waye. Ban taɓa maganar awanni biyu cikakkiya a rana ba, ban taɓa shafe sati guda ina iya magana ba. Duk sai bayan zamanmu a guri guda. Ni na ce Habu ya biya mini sadakin auren ki, tun ranar da na ganki kullum sai na yi mafarki da ke. Shi yasa da mai gidan da muke yi wa gadi ya ce na sake ki, zai biya ni na ji kamar na kashe shi. Na san ni mahaukaci ne, amma mahaukaci bai kyautu a kyautata rayuwar sa ba.
Ke Duniyata ce, a tare da ke nake iya doguwar magana, na ci abinci, na daɗe hankalina bai gushe ba. Ba na son kowa ya raɓe ki, ko ya kula ki, saboda ina jin tsoron kar na buɗe ido na ga ba kya kusa da ni."

Ya kwantar da kansa a ƙirjinta ya ce "Ke ce Ahalina, kuma Duniyata. Ke Duniyata ce"

Haka ya din ga maimaitawa har muryarsa ta fara rawa, tamkar zai fashe da kuka.

Nana ta saka hannu ta zagaye bayansa, ta rintse idanunta, sai dai ta kasa magana a dalilin sanyi da ta fara ji.

Sauti ta fara ji na tasowar guguwa, ta buɗe idonta, ta gansu a cikin sahara tsakiyar dare, sai hasken farin wata da ya gauraye ko ina.

Tsohon nan ta gani a tsaye a kan su, hannunsa riƙe da sandarsa.

Ayshercool
08081012143
"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" Haka Nana ta rintse idanunta tana maimaitawa. Tana jin yadda yake sauke numfashi a jejjere, yana ƙara ƙanƙame ta.

Ta sake buɗe idanunta a hankali, ta gansu still a cikin saharar.

Tamkar wani zai ƙwace shi, haka ita ma ya rirriƙe shi, tana ci gaba da karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Zuwa jimawa ta daina jin sanyin,  ta buɗe idanunta ta gansu a cikin ɗaki, jikinta ya gaji saboda yadda ya sakar mata nauyin shi.

"Sayyid" ta kira shi a hankali. Amma shiru, sai dai tana jin yadda cikin sa yake ɗagawa yana sauka a hankali alamar bacci yake yi. Ta motsa a hankali ta gyara kwanciyarta ta ci gaba da shafa kansa, tana tofa masa addu'a.

Wani irin nishi ta ji ya yi, ya yinƙura a gigice cikin ɗaga murya ya ce "Imam"

Cikin azama Nana ta tare shi, duk da ya fi ƙarfinta, ta riƙe shi gam.
Haki yake yi tamkar wanda aka biyo ya ƙwace da ƙyar.

Ta yinƙura ta kunna fitilar ɗakin, ta dawo ta zauna a kusa da shi. Cikin sanyin murya ta ce "Sayyid. Me ya faru? Waye Imam ɗin?"

Hannunta ya kamo, ya ɗora a saitin zuciyarsa, ya riƙe hannun nata yana sauke numfashi.

"Sannu" ya jinjina kai.

Ya sunkuyar da kansa ya yi shiru, fuskar sa na bayyanar da matsananciyar damuwa. Ta sanya ɗaya hannun nata ta dafa shi ta ce "Sayyid mene ne?" Ya ɗago da ƙyar ya kalle ta, ya buɗe baki zai yi magana amma sai ya kasa.

Can tamkar an jefo maganar bakinsa ya ce "Wani abu ne yake damun zuciyata, ban san mene ne ba, amma ya yi mini nauyi, kamar zan bar duniya"

"Ya isa, ya isa haka ka yi shiru, in sha Allah babu wani abu, ka yi haƙuri" ta yi maganar tana shafa gadon bayansa. Ga mamakin ta kawai ta ga hawaye na gangarowa daga idanunsa. Rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta ce "Sayyid mene ne? Meye ya saka ka kuka?"

Ya girgiza mata kai alamar bai sani ba.
Tun yana yi a hankali, kukan nasa ya din ga ƙaruwa, har da jijjiga. Ganin ta rasa abin yi kawai ta fashe da kukan ita ma, ta hau taya shi.

Ya janye ta daga jikinsa, ya kwantar da ita a kan pillow, shi ma ya kwanta a gefen ta, yana son ya yi mata magana amma tilas ya haƙura ya kasa ce mata uffan.

*****

Hajiya Amina na kwance tana bacci, a kan carfet, a ɗakin da take jinyar Shukura, ita kuma tana kan gadon marasa lafiya tana bacci, ta ji an kama hannunta. Ta yinƙura za ta yi magana amma wani irin jiri ya ɗebe ta daga kwancen da take, duk yadda ta so ta yi wani yinƙuri ko ta yi magana, ta kasa sannu a hankali jikinta ya yi sanyi, ya mutu murus, daga nan hankalinta ya gushe baki ɗaya.

*****

Fuska ɗauke da damuwa, Nana take kallon inda Ƙaisar yake ta haɗe-haɗen maganunansa, ba tare da ya dubi inda ma Nanan take ba.

"Ƙaisar"

"Na'am"

"Karo na farko zan roƙi alfarmarka"

"Ina jin ki" ya amsa ba tare da ya kalli inda take ba.

"Abu na farko ina roƙon ka, dan Allah ka yi haƙuri, ka saki ƙafar mahaifina, abu na biyu dan Allah ka bar ni mu zauna lafiya da mijina, ka daina wahalar da mu har haka dan Allah ka yi haƙuri."

Ya ajiye abin da yake yi, ya dawo gaban Nana ya zauna, ya kalle ta ya ce "Na riga na rantse sai na hukunta mahaifinki, mijinki ya shiga gona ta, ya kwance ƙullin da na yi wa mahaifinki a ƙafa, zai ɗanɗana kuɗarsa zan nuna masa gaba ma akwai gabanta"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Ta yaya ya kwance ƙullin da yake ƙafar Baba?"

"Oho ya dai kwance, kuma zai ga abin da zan yi a kai, sannan ki daina yi mini magiya a kan wani da yake faruwa, wannan wani abu ne da ki ka amince da shi da kan ki, dan haka dole ki jure duk abin da za ki gani. Sauran tambayoyin da ki ke son yi mini kuma ki adana abin ki, dan amsa miki su, dai-dai yake da amincewa da sharuɗana"

Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah Ƙaisar kar ka cutar da shi, shi kansa bai san wasu abubuwan na faruwa ba"

Ƙaisar ya miƙe tare da cewa "Allah ko?"

"Da gaske, bai san su na faruwa ba, dan Allah ka bar mu, mu ji da ƙalubalen rashin lafiyarsa, da rashin sanin waye shi"

Wata irin guguwa ce, ta gauraye cikin Libraryn, da sauri Ƙaisar ya buɗe rigarsa, ya kare Nana.

Tsohon nan ne ya bayyana a cikin libraryn, ya tsaya yana kallon Nana.

Ƙaisar ya tsaya a gaban Nana ya ce "Me ya kawo ka inda nake? Da izinin wa ka shigo gurin nan?"

"Ba na buƙatar izini, kafin zuwa inda farauta ta yake"

"Kar ka ƙetare layin da ka iya kawo, gagarumin tashin hankali da rashin jituwa tsakaninmu"

"Hannun agogo za ka mayar baya, ka gyaro ɓarnar da ka tafka, idan kuwa ba zai gyaru ba, to ba zaka hana ni, aikata abin da na yi niyya ba".

"Ka aikata duk abin da ka so, amma ka taɓa uwar gijiyata a wannan karon ƙarshen rayuwarka zan kawo a doron Duniya"

Jin tarin da Nana ta yi ne, ya sanya ta farkawa.

A ƙasa ta hango shi, maimakon kan katifa, yana wannan jijjigar da ya yi.

A rikice ta tashi ta nufe shi, tana ambaton Allah.

"Sayyid jikin ne dai?"

Wayarta ta ɗaukko, ta kunna karatun Alqur'ani, sannan ta ɗakko bargo ta lulluɓe shi da shi, ta zauna ta saka shi a gaba, ta zura masa ido cike da damuwa.

Har gefin Asuba, sannan Allah ya sanya ya daina wannan rawar sanyin.

*****

An kai ruwa rana da Mama sosai da sosai, kafin ta amince ta haƙura, amma da rantsuwa ta

45 / 64