Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
gare ku, muna son duniya, mu na son tabattuwar duniyarmu" suka haɗa baki su na maimaitawa. Jamila bin su kawai take yi da kallo, jin abin take yi tamkar a mafarki, kuma kamar wani film. Wani irin sauti mara daɗin ji ya karaɗe ilahirin gurin.
Miƙewa mutanen suka yi, suka risuna tamkar za su yi sujuda. Su na ci gaba da karanto wasu irin abubuwa. Wani abu mai kama da guguwa, ya kashe kyanduran gurin. Ƙarar sautin abin, da surutun da suke yi ya karaɗe gurin, baka iya gane komai. Can bayan wani lokaci kuma, sai gurin ya yi tsit hasken kyanduran ya dawo. Suka ɓarke da wata irin shewa. Hasken ya haska gurin sosai da sosai, sai dai ba ta iya gane suwaye a gurin, kuma ta nemi Hajiya Sa'a ta rasa a gurin. Sai daga baya ta fahimci ashe akwai mata a gurin ba wai maza ne kawai ba.
Aka din ga raba wani abu a cikin kofi, aka zo kanta a ka ba ta, ta karɓa ta sinsuna ta ji wani irin ƙarni mara daɗin ji ya daki hancin ta. Ta kawar da kanta yawu na taruwa a cikin bakinta. Ji ta yi an damƙi hannunta, an nufi wata ƙofa da ita. Tana ta ƙoƙarin gane waye, amma abu ya faskara ta kasa gane waye.
Su na shiga ƙofar ta ga duhu ya ƙara gaurayewa, amma ta ji sanyin AC na ratsa ta.
Ta ji an shaƙe mata wuya, an toshe mata hanci, ta fara kiciniyar ƙwacewa amma abu ya gagara, ta buɗe bakinta za ta yi numfashi ta ji an zuba mata wani abu, da ya fi ruwa kauri kaɗan, mara ɗanɗano. Tana gama haɗiyewa ta ji wannan ƙarnin ya mamaye mata hancinta da bakinta. Take ta yi yinƙuri ta fara amai, sai dai ba ta gama aman ba, ta ji jiri ya kwashe ta.
****
Bangaren Nana kuwa, aka shiga kwana biyu, ba tare da ko ruwa Sayyid ya saka a cikin sa ba. Balle Abinci, ba wanka babu salla balle ya sha magungunan sa na matsalar zuciya. Ga shi kuma bai daina haki ba. Idanunsa sun yi jawur tamkar gauta. Laɓɓansa sun yi wata irin bushewa. Ga gashin nan butsu-butsu a hargitse babu gyara, ya koma mahaukaci sosai da sosai. Ga shi da ta tunkaro inda yake, ko ya hankaɗe ta, ko ya shaƙe ta. Ko kallonsa ta fiye yi, sai ya hau huci yana zabure-zabure tamkar zai kai mata duka. Ta yi iya ƙoƙarin ta, babu wanda yake shigar mata ɗaki.
Ga laulayin ciki ya saka ta a gaba, ita kanta lallaɓawa kawai take yi. Ba ta yi da yawa ba a rana ta yi amai sau goma, tun cikin dare take farawa. Tun tana sha'awar ta ci wani abu har ta daina. Daga shayi sai ruwa, ko juice ɗin lemon tsami. Idan ta ga jikinta ya bushe ne, sai ta aika a sayo mata ruwan gishiri ta haɗa ta sha. Ga ranar da za su koma follow up, na Asibiti ya yi amma yana cikin wannan yanayin, a dole ta rabu da shi, ta ci gaba da addu'a.
Sai dai yau gaba ɗaya Jamila ce take ta kaiwa tana komowa a ranta. Sannan ƙasan zuciyarta kuma haka kurum, take tunanin abin da ya sanya ta daina ganin Ƙaisar kwana biyu.
"Allah ya sa dai lafiya" ta furta a fili, sai kuma ta yi saroro bayan wata zuciyar ta ce "Ina ruwan ki da lafiya ko ma babu, abin da ki ke neman maraba da shi?"
Sayyid take kallo, zuciyarta na raya mata, ta matsa kusa da shi, ta jarraba yi masa karatu, amma tsoro ya kama ta, saboda gudun kar ya cutar da ita, ga ƙaramin ciki a jikinta, da take ta lallaɓawa tana fatan Allah ya bar mata.
****
A hankali Jamila ta buɗe idonta, ta ganta a ɗakin da suka sauka da Hajiya Sa'a. Ta yinƙura za ta yaye bargon da take lulluɓe da shi, amma ta ji jikinta na yi mata wani irin ciwo mai tsanani. Ga wani irin raɗaɗi da azaba da ta ji a ƙasanta zuwa gurin bayan gidanta, tamkar an sanya abu mai kaifi an haɗe guraren biyu.
Ta yaye bargon ta ganta a tsirara, jikinta duk an yi mata zane da jini, ta ɗaga ƙafarta ɗaya tana ƙoƙarin tashi zaune, amma ta ji ba za ta iya ba, saboda azabar raɗaɗi da zafin da take ji.
"Wayyo Allah Mama, na shiga uku mene ne ya same ni haka? Nana, Suwaiba dan Allah ku taimake ni na shiga uku"
Hajiya Sa'a ce ta shigo da sauri, tana faɗin "Daughter kin tashi?"
"Mene ne ya same ni, me ya faru da ni?"
"Yi shiru, ki kwantar da hankalinki, zan yi miki bayani. Amma ki daina wannan kukan.
Taso mu je, ki yi wanka ki gasa jikin ki, ki karya tukuna.
Cikin kuka ta ce "Ba na so, ki yi mini bayanin mene ne ya same ni? Ina ne nan? Me yasa nake jin wannan zafin, kuma me ye wannan rubutun a jikina?"
Hajiya Sa'a ta ce "Ke ba na son hauka. A lokacin da Safiyya ta haɗa ni da ke. Nake kashe miki kuɗaɗe a banza zan yi miki ne, ba tare da na amfani komai a tattare da ke ba? Kin gaza kawo mini jinin 'yar uwakki, kin ƙi shiga cikin harkar mata yadda nake so, kuma ga burinki na son abin Duniya, dan haka tallafawa burinki kawai na yi cicciɓa ki"
Hawaye na kwarara daga idonta cikin sanyin murya ta ce "Yanzu me ya same ni?"
"Taronmu na ƙungiya ki ka zo, kuma na nema miki sassauci ta hanyar ki bayar da budurcinki, ga sarki da kuma dodon ƙungiya maimakon a ce ki kawo jini tashin farko.
Aljanin da ke da alhakin bamu kuɗaɗe,da jagorantar ƙungiyar, shi ne ya shiga jikin sarkin ƙungiya ya kwanta da ke, a matsayin barka da zuwa na ƙungiya kuma da sadaukarwar ki ta shekara!!!
(Alhamdillah, da haka muka kawo ƙarshen book 1, sai mun haɗe a kashi na biyu).
Ayshercool 08081012143