BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   36 / 64

105K to 108K   out of 190K words

yi mana batsa"

Nana ta yi murmushi ta ce "Ya Baba, ina mama su ba za su zo ba?"

Ummi ta ce "Za su zo ne, Baba babu lafiya ƙafarsa ce take ciwo"

Nana ta ce "Ciwon ƙafa kuma?"

"Wallahi kuwa, ba za ki kira mijin naki mu gaisa ba"

Nana ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Ba kula ku zai yi ba, Nasiru ya makaranta" ta karkatar da zancen ga Nasiru. "Makaranta lafiya ƙalau Alhamdilillah"

A ƙofar ɗakin ya yi gyaran murya ya tsaya, Nana ta yinƙura ta tashi, ta ɗaga labulen. Babu hijjabi a jikinta, sai doguwar rigar atamfa.

Ya miƙo mata leda, ta saka hannu biyu ta karɓa, bai ce mata komai ba, ya juya ya koma bakin gate.

Fura da Nono ne kaya guda, abin sai da ya bawa Nana mamaki, ba ta san a ina ya samo su ba. Ta ajiye musu suka dama, suka sha.

Jamila ta miƙa wa Nana ɗan ƙaramin flask ta ce "Nana ga mutuniyar ki na yi miki wainar fulawa" Nana ta haɗiyi yawu cikin murna ta din ga yi wa Jamila godiya. Ta ce "Wannan sai dare zan dafa shayi na ci da ita"

Suwaiba ta ce "Ashe fa buzu ki ke aure, ba za a gaya miki shayi ba yanzu"

Nana ta ce "Kamar kin sani, ni yanzu shayi ai sai dai na koya wasu, kwana muke mu wuni shan shayi babu ƙaƙƙautawa" suka yi dariya.
Har magariba su na gidan, sai da suka yi sallar magariba, Nana ta fito har bakin gate ta rako su, sai dai baya nan.

Ummi ta ce "Kin ga har zamu tafi, bamu haɗu mun gaisa ba"

Nana ta ce "Ina ga yana masallaci"

Suka yi sallama, suka tafi Nana ta koma ɗaki. Har cikin ranta ta ji daɗin zuwan su.

Ta yi wanke-wanke ta gyara ɗakin fes. Ta ɗaukko flask ɗin wainar fulawar, ta saka a gaba ta fara ci. Ba ta ci da yawa ba, Haula ta yi sallama.

Nana ta amsa cikin sakin fuska, duk da ta yi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin.

"Anty Haula ba ki yi fushi ba? Haryanzu ban fara fita ba, shi yasa ban shigo miki ba"

Haula ta ce "Allah sarki, kar ki damu wallahi, ashe baƙi ki ka yi?"

Ba tare da Nana ta yi tunanin komai ba, ta ce "Eh, 'yan gidanmu ne su ka zo, bismillah matso mu ci abinci" Aikuwa Haula ta gyara zama ta zura hannu a kwano, ta fara cin abincin. Kafin Nana ta yi loma ɗaya ta yi huɗu da rabi, kafin wani lokaci Nana sai filin kwanon ta gani, Haula na ta suɗar baki saboda yajin wainar.

Sai da ran Nana ya sosu, dan kuwa ta so cin wainar nan ta ƙoshi.

Labulen ɗakin kawai ya ɗaga ya shigo, Haula ta tashi zumbur. Ta kalli Nana ta ce "Na gode sosai sai anjima" sai da Haula ta fice sannan ya shigo ɗakin.

Ya zauna a gurin da ya saba zama, Nana ta ɗaukko ta sa furar da ta ajiye masa, da cin-cin da dubulan a plate, ta nufe shi.

"Sannu da zuwa" ya jinjina mata kai.

" 'yan gidanmu ne fa suka zo" ta yi maganar fuskarta na bayyanar da annashuwa. Ya gyaɗa mata kai.

"Na gode sosai da sosai, da karamcin da ka yi mini, ga taka furar ga kuma wannan" ta yi magana tana tura masa plate ɗin dubulan.

Ya saka hannu biyu ya karɓi kofin furar, Nana ta zauna a gefensa, a tsanake yake sha, ya ɗauki cin-cin ya saka a bakinsa, maimakon ya tauna yadda yakamata, amma ya din ga tauna shi a hankali kamar mai tsoron tauna dutse.

"Da daɗi?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Nana ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce "Dan Allah ka din ga yi mini magana mana. Haryanzu ban san sunanka ba" ya kalle ta yana ci gaba da tauna cin-cin ɗin sa.

"Ka gaya mini sunan ka" ya ajiye kofin hannunsa yana hamma, ya jingina da jikin bango yana lumshe idanunsa.

Ta gaji ta ƙyale shi, ta fara shirin kwanciya, ta shiga banɗaki domin kama ruwa ta yi alwalar kwanciya bacci.

A sukwane ya miƙe, duk da bacci ya fara ɗaukarsa, kwanon da Nana ta ci wainar nan ya ɗauka, ya jujjuya kwanon ya ga babu komai a ciki.

Ya ajiye kwanon, ya koma gurin da yake kwanciya, ya zauna ya yi shiru.

Nana kuwa tana saka ƙafarta a banɗakin, ta ganta a cikin wani gida, mai dogon gini, mai ɗauke da ƙofofi daban-daban. Ɗaya daga cikin kofofin ta bi, tana neman hanyar fita, amma da ta shiga sai ta ga ta koma ainihin gurin da take da farko.

Tana cikin laluben ƙofar, kawai ta ci karo da Baba, ƙafarsa ɗaya an nannaɗe ta da sarƙa, an ɗaure ta tamau.
Da sauri Nana ta nufe shi, cikin tashin hankali ta ce "Baba lafiya kuwa? Me ya same ka haka?"

"Ni ma ban sani ba Nana, dan Allah ki kwance mini sarƙar nan, ina jin ƙafata kamar za ta cire, ba na iya bacci"

Cikin damuwa ta ce "Ka kwantar da hankalinka, bari na gani idan zan iya kwance maka" Ta durƙusa ta fara ƙoƙarin kwance masa sarƙar, sai dai ta rasa ina ne ainihin gurin da aka ƙulle ƙafar.

"Idan ki ka kuskura ki ka kwance masa, ba zai sake taka ƙafarsa ba har abada" Nana ta ɗago tana kallon Ƙaisar.

"Dan me za ka ce kar na kwance masa? Ba ka ga halin da yake ciki ba, ko iya taka ƙafar baya yi ba?"

Ƙaisar ya ce "Ban gaya miki sai na hukunta shi ba? Har yanzu ba ki yadda mu na cikin mummunan haɗari daga ni har ke ba, a dalilin wannan auren. Dan haka dole shi ma ya ɗanɗana kuɗarsa"

Cikin ɗaga murya ta ce "Ƙaisar baban nawa? Ka kwance masa ƙafarsa" kawai tana waiwayewa ta daina ganin Baba.

"Idan duniya za ta taru, babu wanda ya isa ya kwance masa ƙafar nan, idan bai yi wasa ba sai ta yi ajalinsa" yayi maganar cikin ɗaga murya.

Tamkar mai shirin haukacewa ta ce "Ba zai yiwu ba, wallahi sai ka kwance shi, wai kai wane irin halitta ne da babu ɗigon imani, a zuciyar ka?"

Ƙaisar ya ce "Ko ma dai mene ne, abu ɗaya za ki yi ki kwance masa ƙafar nan, wanda kin san mene ne, ba sai na gaya miki ba. Mu ajiye wannan a gefe tukuna, ban san iya adadin lokacin da za a ɗauka kafin ki san ciwon kanki ba, ki daina wasa da rayuwar ki ba. A wannan karon ma an baki abu kin ci, za kuwa ki ɗanɗana kuɗar ki, a nan na nuna miki an tsaface ƙanwar ki, amma ta kawo abu ta baki ki ka ci"

Nana ta ce "Idan ma ka nuna mini, da na tashi nake manta komai, kuma ba zan taɓa yarda da maganganun ka ba, yaudarata kawai ka ke so ka yi, domin na amince da mugun nufin ka, kuma har abada ba zan amince ba, ko da ba ma jituwa da su, na san ba za su cutar da ni ba"

Ya ce "Shikenan, zamu gani"

A hankali ta yi kokarin yin juyi a kan katifar, amma ta ji wani irin azababben fitsari, tamkar mararta za ta yi bindiga, ga wata irin ƙullewa da mararta ta yi har cikin bayanta da ƙafafuwanta. Da ƙyar da dabara, ta tashi ta tafi banɗaki. A zaton ta da ta yi fitsarin shikenan, za ta ji marar ta saki, amma babu abin da ya canza.

Da bin bango ta fito ,ta dawo kan katifar ta kwanta. Bacci ne a kanta, amma wani irin azababben ciwon mara ya turnuƙe ta.
Yana kwance yana jin nishinta sama-sama, tun farkawar ta da shigarta Banɗaki, duk a kan idanunsa.
Murƙususu ta din ga yi a kan katifar, tana numfarfashi. Rabonta da ciwon mara mai irin wannan azabar, tun farko-farkon fara period ɗin ta. Da idan ta fara sai an kai ta chemist an yi mata allurai.
Daga baya abin ya ragu sosai, amma na yau kam, ba ta taɓa makamancin irin sa ba, ji take tamkar ba za ta wayi gari ba.

Ko na minti ɗaya ciwon baya lafawa, ga shi ya haɗe mata da ciwon ciki, da na ƙirji kamar za ta bar duniya. A duƙe ta sake komawa banɗaki ta saka pad.

A haka ta wayi gari, cikin mawuyacin hali, ta yi kukan ta gaji. Ta saukko daga kan katifar ta kwanta a ƙasa amma babu afuwa. Ko sau ɗaya bai ce mata sannu ba, da gari ya yi haske ma bar mata ɗakin ya yi, saboda yadda kukanta ya cika masa kunne.

Tamkar za ta haihu, haka ta fita daga hayyacinta, gaba ɗaya ta manta da batun ba itakaɗai ce a ɗakin ba, ta cire kayan jikinta, ta bar vest da underwear. Rashin tanka matan da ya yi ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba.

Can amai ya din ga taso mata, ga wata irin gudawa ta azaba da fitar ta kawai, yake ƙara gigita ta saboda sai cikin ya haɗu ya ƙule da marar sannan take yin ta. Ga fitarta tamkar tana zawon wuta haka take ji, ta ga duniyar tana juya mata, ta din ga salati tana ambaton Allah. Tun tana iya zuwa banɗakin a duƙe, ta koma rarrafe.

Ta din ga wani irin amai, mai wari da ƙarni. Idanunta suka yi zuru-zuru, kamar ta yi wata da watanni tana rashin lafiya.

Ta kwanta ta yi rub da ciki, ta lumshe idonta. Ta ji an ɗagota. Sosai ya ɗago ta ya haɗa ta da ƙirjinsa. Babu rawani a kansa, ya kwance gashin kansa, ya sauka a kan kafaɗarsa. Suna haɗa ido, ta sake fashewa da kuka, saboda ta ji zafin rashin kula ta da ya yi balle ya yi mata sannu.

Ya kai dogwayen yatsunsa ya share hawayen da yake fitowa daga idonta. Ta saka hannu ta ture hannunsa, da yake share mata hawayen.

Ya kama bayan hannunta ya kai bakinsa ya sumbuta, ya ɗago ya ƙura mata ido, yana matsa hannunta a hankali. Zuba masa ido Nana ta yi, sai ta ga kamar ba shi ba. Ya sake kai bakinsa goshinta ya sumbaci goshin nata.
Ta sake fashewa da kuka, ya haɗa goshinsa da nata ya ce "Shhhhh"
Gabanta ya faɗi, sai da ta razana jin ya ɗora hannunsa a kan marar ta.

A hankali ta fara jin releif, daga wannan matsanancin ciwon da take ji.
Bai ɗauke goshinsa daga nata ba, numfashin sa da yake shiga nata, jikinta ne ya saki ya mutu murus, ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. A hankali ta fara jin bacci yana ɗaukar ta.

*****

Su Jamila kuwa bayan sun dawo daga gidan Nana, Baba ya tambaye su ya suka baro ta.

Suwaiba ta ce "Tana nan lafiya kalau, ta ce a gaishe ka"

"Ina amsawa, ya gidan nata akwai abinci kuwa?"

Nasiru ya yi farat ya ce "Baba ɗaki dai, a ɗaki ɗaya take da banɗaki, amma akwai abinci a ɗakin. Har mijinta ya kawo mana fura da Nono".

Baba ya ce "Ko ma dai a rami suke ba ɗaki ɗaya ba, ai ita ta jiyo, tun da Allah ya nufi ya rufa mata asiri, ya bata miji na gari na rufin asiri ta zaɓi ta tonawa kanta asiri, yanzu ta ƙare a tantalbatete"

Jamila dai kawai fatan ta, Allah ya sa ta yi nasara a kan Nana.
Babu kunya Mama ta saka Nasiru a gaba, tana yi masa tambayar ƙawaƙwaf da son sanin halin da Nana take ciki na daɗi ko akasin haka.

****
Bangaren Shukura, duk da ta kan yi mafarkai na ban tsoro barkatai, amma bai fiye damunta ba, wasu lokutan da ta farka ma shikenan, mussaman idan tana da ciki ta fi irin wannan mafarkan. Amma a wannan karon ta kasa mantawa da wannan mafarkin da ta yi, a cikin jikinta take jin tsoro da fargaba a kan mafarkin.

Duk da ba ta iya gaya wa Sagir abin da ta gani a mafarki ba, kawai ta ce masa mummunan mafarki ne, ya yi ta kwantar mata da hankali, da tabattar mata da mafarki ba gaskiya ba ne ba.

Sai dai jin abin take yi, tamkar ma ya riga ya faru ne, ko kuma yana daf da faruwa, haka kurum sai ta ji gabanta ya faɗi ta razana.

****

Tare da su Habu ta hange shi zaune kan wani ƙaton carfet fari tas, a cikin sahara , suna ta shan shayi su na hira cikin nishaɗi, gaban su dabino kala-kala a cikin tasoshi, yana cikin su ba ya magana sai murmushi. Ƙyam ta tsaya tana ƙare masa kallo. Karaf ya ɗago kai suka yi ido huɗu.

Ya yinƙura ya nufo ta yana murmushi. Ta kawar da kanta gefe ta haɗe rai.

Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta yana ci gaba da murmushi ya ce "Ya aka yi ne?"

"Ni rabu da ni, bayan ka ƙi yi mini sannu" ta yi magana cikin shagwaɓa.

"Tuna dai, na yi miki fa, to yanzu ya jikin naki, me ki ke ji?"

"Ba komai"

"Kin tabatta?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya zagayo da hannunsa, ya ɗora a kan mararta, ya sunkoyo daidai kunnenta ya ce "Hmm haka ne, na ji da sauƙi, na yi uzuri a wannan karon, amma idan aka ƙara zan ɗauki mataki"

Nana ta ce "Me aka yi da zaka ɗauki mataki?"

"Komai ma"

Ta yi murmushi ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce "Har yanzu ba ka gaya mini sunan ka ba"

Ya yi dariyar da ta ƙara masa kyau, ya ce "Sunana ki ke son sani?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Cikin raɗa ya ce mata "BUZU"

"Buzu" ta maimaita a hankali tana buɗe idonta.

Shiru ta yi tana jin mafarkin da ta yi a ƙwaƙwalwarta, sai kuma abun da ya faru da ya rungume ta ɗazu, ya fara dawo mata. Ta nutsu sosai ta ga shi ma a mafarki abin ya faru. Ta ƙarewa ɗakin kallo, babu kowa a cikin sa sai ita kaɗai.
Sai dai ta ji mararta ta daina ciwon, ta tashi ta ɗora ruwa ta yi wanka, ta gyara jikin ta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga shi ta kasa cin abincin. Dabinon da ya taɓa bata ta ɗaukko ta hau ci.

Bayan sallar magariba, ya shigo ɗakin da leda, kai tsaye ya tafi kusa da ita ya zauna.
Ko kallon gurin da yake ta ƙi yi, saboda ta ji haushin yadda ya kasa kula ta duk wannan azabar wahalar da ta sha.

"Ki ci" ya yi maganar yana ajiye mata ledar.

Murguɗa baki ta yi ta ce "Ba na ci" ya yi shiru yana kallon ta.
Ta kawar da kanta gefe tana ci gaba da ƙunƙuni. Ƙarshe ma ta tashi ta koma can gefe ta yi zamanta.

Ta ɗago ta ce "Ka ci ni na ƙoshi, ba zan iya girki ba, ba na son ƙamshin abinci" kawai ya yi shiru bai ce komai ba.

Ta kunna kallo a wayarta, tana yi tana cin dabinonta.

"Salamu Alaikum" suka ji ana sallama a wajen ɗakin.

"Wa'alaikum salam warahmatullah. Viens" ta ji ya amsa, ganin abin ta yi banbarakwai. Habu ne ya shigo da sallama fuskarsa ɗauke da damuwa.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Hankalina duk a tashe, ya kira ni ya ce ba ki da lafiya, ba ki ci abinci ba tun safe" Nana ta waiwaya ta kalle shi, ya maze abin sa.

"Ta ina ya gaya maka?"

"Ta waya" Habu ya amsa mata.

Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Abin da ma bai ce mini sannu ba, kuma yana kallo na kusa mutuwa"

Habu ya yi murmushi ya ce "Amma ya damu sosai ai, tun da ya kira ni kuma ya saka na tafi neman abin da za ki ci." Ya ajiye mata ledar ya ce "Ga abin da ya ce na sayo miki"

Ta ce "Ni idan bai ce mini sannu ba, ba zan ci ba"

Habu ya kalle shi yana murmushi, ya yi masa magana da french.

Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce "Na faɗa ɗazu"

"Da yaushe?"

"Ki na bacci"

Mamaki ne ya cika ta, jin ya yi doguwar magana, dan haka ta yi yinƙurin jan maganar.

"Dama mutum ya san abin da ake yi ne, idan yana bacci, ni na ƙoshi"

"Sannu" ya faɗa a taƙaice.

Habu ya ce "Lallai abin mamaki, abin ya burge ni, ga kayansa nan an wanke an goge, tun da jikin naki da sauƙi, Alhamdilillah ni zan tafi"

Nana ta ce "Mun gode sosai, ka gaida gida"

"Allah ya sauwwaƙe ya ƙara lafiya" bayan tafiyarsa Nana ta ci gaba da kallo, ba tare da ta taɓa ledar da Habu ya kawo ba, balle wadda ya shigo da ita.
Babu tsammani ta ji an fizge wayar hannunta, sai da ta tsorata, a fusace yake kallonta.

"Ki ci abinci" ya faɗa a hasale. Murmushi ne ya so kufce mata, amma a zahiri sai ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka.
Ya janyo ledar da ya fara shigowa da ita, ya buɗe ta kankana ce a ciki. Sai dai ta sha mamaki da ya buɗe ledar da Habu ya kawo ta ga gasashshiyar kaza. Ita dai ta san tsakiyar wata ne, a ina suke samo kuɗin da suke wadaƙa haka?"

"Ci" ta kuma jin muryarsa.

Sai kuma ta yi tsuru-tsuru ganin yadda ya yi mata kwarjini, saboda ya kafe ta da ido. Kamo hannunta ya yi ya ɗora a kan kankanar ya ce "Ci" kamar mara gaskiya ta ɗauka ta kai bakinta.

Duk da gefe guda hankalinta na kan kazar nan, har da haɗiyar yawu, saboda sai tururi take yi ga ƙamshi.

Ya tashi ya ɗauki kofi, ya tsiyayo shayi, a cikin butar shayinsa, ya zo ya ajiye a gefen sa.

"Ki ci" ya kuma maganar yana zaro mata ido.

Ba shiri ta tattarata nutsuwarta, duk santa da kazar, kasa sakin jiki ta yi ta ci, saboda tsoron yadda ya tsare ta da ido, sai dai tana iya hango tausayi da damuwa a cikin idanun nasa.

"Na ƙoshi" ta faɗa a ɗan tsorace.

Ya ɗauki ɗan ƙaramin kofin da ya zuba shayi, ya miƙa mata, a zaton ta shayi ne, sai dai tana sha, ta ji tamkar ta haɗiyi wuta. A take yanayinta ya sauya ta ji duniyar ta fara juya mata!

Ayshercool
08081012143

Page 32

Gani ya yi ta rintse idanunta, jikinta ya fara karkarwa, mamaki ne ya kama shi, ya duba cikin kofin ya ga shayi ne a ciki. Ya kai bakinsa ya sha, shi bai ji komai ba.

Murƙususu take yi, a galabaice tana jin tamkar ana yayyanka kayan cikinta, ta yi wani yinƙuri sai ta fara aman jini mai yauƙi. Ta ɗauki lokaci tana yi. Ta ɗaga kai da ƙyar, ta ga Buzu a tsaye a kanta,

36 / 64