Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
ba ma ta cikin hayyacinta. Ni kuma wayata ta lalace, babansu kuma ba ya gari, shi yasa ban kira na sanar muku ba.
Mama ta yi farat ta ce "Wallahi ƙarya ne, ki na nufin tun daga nan ta tafi gidanki a ƙafa? Ƙarya ki ke yi Ummi, ki faɗi gaskiya idan ma, yawon ta zubar ta tafi ki ke kareta"
A fusace Ummi ta ce "Allah ba zai nuna mana mai yawon ta zubar a cikin zuriyarmu ba, baƙin bakinki ya faɗa miki kanki da 'ya'yanki.....
"Ke ummi rufe mini baki kafin na kwaɗe ki" Baba ya katse ta cikin fushi.
Ya ɗora da cewa "Mara kunya wuce ki tafi gidan ki, Allah ya ba da lada"
Nana ji ta yi tamkar ta bi bayan Ummi su koma tare, saboda karɓar da aka yi musu, ko arzikin abin zama ba su samu ba, balle a bawa ko ummin ce ruwa, haka ta kasa magana ta bi bayan ummi da kallo yadda ta fita a fusace.
Ayshercool
08081012143
BUZU
Ayshercool
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002)
BRIGHT PENS 3rd BATCH.
P3
Nana ta tsaya jiran abin da Baba zai ce, bayan fitar ummi, amma ba ta ji ya ce komai ba.
"Wai haka zaka ƙyale yarinyar nan, ba zaka tuhumi ina ta je ta kwana biyu ba?" Mama ta yi maganar tana tsare Baba da ido.
"To rabi ya ki ke so na yi, kin san a cikin larura take, ni wannan larurar ta ta ta ishe ni, Allah ya kyauta kawai"
Tun da Baba ya faɗi haka, mama ta dasa mita da bala'in baya ganin laifin Nana.
Nana kuwa ɗakinsu ta shiga, tana jin yadda maganganun mama ke ratsa zuciyarta, da sanya mata wani irin raɗaɗi da zafi a cikin zuciyarta.
Haka ta wuni sukuku, ba wanda ta kula ta ƙule a ɗaki kamar yadda ta saba.
Sai dai wunin ɗakin nan, ya ƙara sanya zuciyar Nana a cikin ƙunci, haka kurum kewa da son ganin mahaifiyarta ya bijiro mata.
Sai daf da magariba Jamila ta shigo gidan, ta ya da zango a tsakar gida, da abin da ta zo da shi daga gidan uwar ɗakinta.
Ƙamshin abinci har cikin ɗaki in da Nana take, ga yunwa tana ta sakaɗar cikinta, kamar ba ta taɓa cin abinci ba, haka take jin cikinta.
A lokacin ta tsinkayi hirarsu, wai ashe mijin maman khairat, uwar ɗakin Jamila, shi ne ya ɗauki gabarar gyara musu gidan.
Tun tana fahimtar hirar ta su, har ta faɗa duniyar tunani, ba ta iya jin me suke cewa.
"Laa Nana yaushe ki ka dawo ke kuwa?" Firgigit Nana ta kalli Jamila, ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Tun ɗazu, Anty Ummi ce ta rako ni"
"Kuma na zo da abinci amma ki na ƙule a ɗaki, kuma na ga alamar yau gidan ba harka, bari Nasiru ya zo ya sayo miki gurasa"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a a ƙoshe nake, na ci abinci a gidan ummi"
Jamila ta ce "Gidanta ki ka gudu kenan? Kin taimaki kanki, kya rage wata kafar, wannan gida namu da kullum cikin indararon talauci ake, ni ma tun da Allah ya sa na samu wurin fakewa, na riƙe wuta" Murmushin nan na ta da ta saba, shi kawai ta yi wa Jamila. Ta ɗan numfasa ta ce "Dan Allah Jamila idan wayarki da kuɗi, ara mini zan yi kira.
Jamila ta miƙa mata wayar ta fice, wata lamba Nana ta danna, ta din ga kira, a ƙalla sau biyar amma ba a ɗaga ba, jiki a sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta, tare da zuba wa wayar ido, ko za a biyo amma shiru, har aka fara kiraye-kirayen sallar magariba.
Sai da ta fita yin alwala, ta tuna babu damar shiga banɗaki, sai dai ta raɓa ta kama ruwa, haka nan ta shiga banɗakin da dabara, ta kama ruwa ta fito ta yi alwala ta shiga ɗaki ta tayar da salla.
Tana jiyo yadda yaran gidan, suka tattara a tsakar gida, tare da mahaifiyarsu, sai ɓaɓɓaka dariya suke yi suna hira, ita kuwa tana ɗakinsu a zaune tsuuruu, 'yar fitilar ma da ta kunna, babu batir ta disashe babu haske, ga uban sauro da yake ta yi mata majalisi a ka.
Tana nan zaune aka yi kiran sallar isha'i, ta tashi ta gabatar da sallar, ta idar ta fara tasbihi, ita dai ta san ta fara tasbihi, amma ba ta gane kan lissafin abin da take faɗa, ta tafi wasu tunane-tunanen daban.
Wuri ɗaya ta tsurawa ido, yadda inuwar wani ƙwaro, yake ta shawagi a ɗan iya in da hasken fitilar da ta kunna yake. Sai dai sannu a hankali, inuwar ta din ga rikiɗewa zuwa wasu halittun daban.
Tsoro ya mamayeta, amma a zahiri ta kasa motsi, duk iya ƙoƙarinta, na tuna wasu daga cikin adduo'in da ta iya domin ta yi, abu ya gagara.
"Ke Nana!" Suwaiba ta kira sunanta cikin tsawa.
A wahale cikin sauke numfashi, Nana ta amsa tana zare ido.
"Dan wulaƙanci ana ta yi miki magana, kin yi wa mutane banza, kuma ki na ji, ki je wai ana sallama da ke a waje" Nana ta waro ido ta ce "Ni ɗin kuma?"
"Ban sani ba" Suwaiba ta ba ta amsa, tare da ficewa ta bar ɗakin. Ɗan shiru Nana ta yi, tana mamakin waye wannan ya zo wurinta, dan rabonta da wani ya biyo ta ya ce yana so, kusan shekara ta biyu kenan, tun da aka fasa aurenta da Suleiman.
Jin abin take kamar a mafarki, haka ta tashi jiki a sanyaye ta fito.
Tana jin maganganun Mama sama-sama, amma ba ta iya fahimtar me take faɗa, dan haka kawai ta saka kai ta fita.
Duk da babu haske sosai, amma daga yanayin tsayuwarsa, ta gane waye, cikin azama da ladabi, ta durƙusa har ƙasa ta ce "Ya sayyadi ina wuni?"
"Lafiya ƙalau Nana, tashi" yayi maganar yana mata alama da hannunsa, ta miƙe tana sunkuyar da kai cikin jin nauyi.
Cikin kulawa ya ce "Nana ina ki ka tafi aka yi ta faman neman ki, ba a san in da ki ka je ba? Hankalin kowa ya tashi, daga fita na bar ku a aji, na dawo aka ce mini wai kin fita, sai ɗazu ƙaninki ya ce mini a gan ki"
Gaba ɗaya jikin Nana yayi sanyi, ta san ba kowa za ta gaya wa abin da ya faru, ya yadda ba, amma ba ta sare ba ta ce "Wallahi ya sayyadi ni ban san ya aka yi ba, kawai ganina na yi a gidan yayata Ummi, ita ta riƙe ni a gidanta kwana biyu, amma daga nan ba in da na je wallahi" tayi maganar muryarta na rawa cike da karayar, shi ma babu lallai ya gazgata abin da take gaya masa.
Cikin tausayawa malam Auwal ya ce "Ba wani abu, kar ki yi kuka, Ubangiji Allah ya yaye miki Nana, ya kawo miki mafita, amma ki na yin dukkanin azkar ɗin da yakamata?"
Ta jinjina kai ta ce "Ina yi"
"Yauwwa to ki ci gaba, sannan ki yawaita zama da alawala, kamar yadda nake yawan gaya miki, ki riƙe Alqur'ani Nana, Alqur'ani waraka ne"
Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Ko hadda ba na iyawa ko na yi mantawa nake yi"
Cikin tausasawa ya ce "Ki yi haƙuri, jarrabawa ce, ki ci gaba da gaya wa Allah, kuma kar ki daina ƙoƙarin yin haddar. Ayatu shifa'a ɗin nan da na gaya miki, ki din ga karanta su a ruwa ki na sha" ta jinjina masa kai tana share hawayenta.
Baba ne ya tinkaro gidan, dan haka suka yi shiru, ya ƙaraso, Nana tana yi masa sannu da zuwa, malam Auwal na ƙoƙarin gaishe shi.
Baba ya amsa sannan ya ɗora da cewa "Ina fatan ta gaya maka, ni ba a zuwa gidan nan yin dogon zance? In dai da gaske ka ke ka turo magabatanka, ni ba na buƙatar komai da wani ƙaƙale, ku kawo kuɗin aure, a ɗaura aure ba sai ka yi lefe ba, ka yi mata kayan ɗaki dan ni ba ni da halin yi mata kayan ɗaki" Take ran Nana ya ɓaci, wannan soki burutsun da Baba yake yi, duk na mene ne? Idan ma da gaske saurayin nata ne, haka zai yarfata, ta yinƙura za ta yi magana, malam auwal ya riga ta ya ce "To Baba in sha Allah duk ba zai gagara ba, zan yi magana da magabatan nawa in sha Allah"
Baba ya ce "Yauwwa Allah ya yi albarka" yayi maganar yana shigewa cikin gida, Nana tamkar ta kasa da gudu ta bi bayan baba saboda matsananciyar kunya.
Malam Auwal ya ce "Bari na tafi gida, tun da Baba ya dawo, ki shiga gida ki ci gaba da addu'a " cikin girmamawa ta risuna ta ce "Na gode sosai ya sayyadi".
Cikin tausayawa ya ce "Allah yayi miki albarka ya baki lafiya Nana"
Ta amsa da "Amin ya Allah" ta nufi hanyar shiga gida.
A tsakar gida ta tarar da Baba yana tambayar Mama, dama akwai wanda yake zuwa wurin Nana ba a gaya masa ba.
"Babu fa wani wanda yake zuwa wurinta, ni rabon da ace an zo wurinta, tun da aka fasa wancan auren nata, kamar an buga mata hatumin jaɓa, malaminsu ne na islamiyya ba wani ba, kuma Auwwalun gidan mai koko ne ba wani ba, malaminsu ne na islamiyya"
Bab ya ce "Oho ko ma ɗan gidan mai ƙosai ne, na ce ya yi wa iyayensa magana, su zo ayi maganar aure"
"To ce maka yayi yana sonta?"
Baba ya ce "Koma ba sonta yake yi ba, tun da ya zo wurinta ƙofar gida, ai sonta yake yi, tun da ba karatu yake biya mata ba, in samu in aurar da su na huta da wannan wahalar ta ishe ni, riɗa riɗa da su a zaune a gida, mussaman ita ma, ni duk yarana babu wanda yayi daɗewar su ba su yi aure ba".
Mama a zafafe ta ce "A'a itan dai, ta fi uban kowa kwantai, sai an yi magana ace aljani ne ya hanata aure"
Baba ya ce "Ko kuma kece aljanar ba, tun da kin taka muhimmiyar rawa wurin fasa wancan auren nata"
"A'a ka saka munjaye dai, mun taka muhimmiyar rawa zaka ce, ba wai ka ɗora mini laifin nikaɗai ba" raɓawa Nana tayi, tana bin bango za ta wuce ɗakinsu, dan ba ta son ma wani ya ga wucewar ta, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba, Baba ya hangota.
"Yauwwa ke Nana, ki fara shirin ki, dan in dai da gaske yaron nan yake, ko wata guda ba za ayi ba, ki tattara ki tafi ɗakinki, ki samu nutsuwa nima a rage mini wahala" Nana ba ta iya cewa komai ba, sai tsayawa da ta yi tana wasa da yatsunta a cikin hijjabinta, tana jin yadda zuciyara ke bugawa da matsanancin ɓacin rai da damuwa.
Wayar Jamila ce take ringing, Baba ya koma kanta da masifar, ta ɗaga wayar nan ta cika masa kunne.
"Hello" Jamila tayi maganar cikin iyayi, ganin baƙuwar lamba ce, a zatonta ko saurayi ne.
"Assalamu alaikum" muryar babbar mace ta amsa a wayar.
Ta yamutsa fuska ta ce "Wace ke magana?"
Matar ta ce "Kira na gani da wannan layin, bana kusa da wayar ne"
Jamila ta ce "Anya wannan lambar kuwa? Amma wa ke magana?"
"Maijidda ce"
Jamila ta ɗan yi jimm ta ce "Maijidda kuma? Auuu Nana ce dai ta yi kira da wayar ta yi maganar tana miƙewa ta nufi Nana domin bata wayar.
A hasale, Baba ya fizge wayar cikin ɗaga murya ya ce "Halima babu ke babu 'ya ta, kar ki sake kiran waya ki na neman ta, zan yi ƙarar ki wallahi"
Nana ta fashe da kuka ta ce "Baba dan Allah ka yi haƙuri, ni na kira ta"
Ya jefar da wayar ya yo kanta, kamar zai rufeta da duka, ya ce "Da ki ka bar gidan nan wurinta ki ka tafi ko Nana?"
"A'a Baba ba wurinta na tafi ba" tayi maganar tana kuka.
"Wato duk yadda na bi na raba ki da matar nan, ba zaki rabu da ita ba ko? Yadda take mutuniyar banza haka zata lalata miki rayuwa, da tana ƙaunar ki ba za ta tsallake ta bar ku ta tafi ta yi wani auren ba, babu abin da zata tsinana miki, idan kuma ba haka ba sai dai ki zaɓa ko ni ko ita"
Sosai Nana take kuka, tamkar ranta zai fita, ta rasa dalilin da ya sanya abin da ya haɗa su, ya shafe ta yake aibata mata uwa a gaban kowa, yana cin mutuncin ta, ita fa uwa uwa ce, mece ce ribarsa idan ya raba alaƙarta da mahaifiyar ta?. Wucewa ɗaki ta yi tana ci gaba da kuka, masifa goma da ashirin, ga yunwa ga yarfata da Baba yayi a gaban ya sayyadi, ga kuma abin da ya fi ci mata tuwo a ƙwarya, cin zarafin mahaifiyar ta.
Ko hijjabin jikinta ba ta cire ba, kawai ta kwanta tana kuka, ji take tamkar ta kurma ihu ko za ta ji sanyi a ranta, shiru ta yi hawaye na zuba daga idanunta, tana sheshsheƙar kuka, ga kanta ya fara sara mata da wani irin matsanancin ciwo.
Ba ta san iya adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji Jamila ta taɓa ta, ta ɗago ta kalli Jamila.
"Ungo rabu da shi, kirata ku yi magana"
Jiki a sanyaye ta girgiza wa Jamila kai, alamar ba zata karɓa ba.
Jamila ta yi ƙasa da murya ta ce "Ya tafi ya kwanta fa, ki kira ta bari na kira miki ita, ai ban san ki na da lambarta ba, ai da kin din ga karɓa ki na kiranta" tayi maganar tana danna lambar, sai dai layin yaƙi shiga.
"Ba komai Jamila na gode sosai kar ki damu" ta koma ta kwanta.
Ƙoƙarin yin tunani take yi, amma kanta ya ci gaba da sara mata, ba ta san ya aka yi ba, bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ta ba.
Tana tsaye a wani ɗakin library, amma yanayin wurin kamar a wani zamani ne na daban, litattafan wurin duk sun yi ƙura, wasu litattafan duk yana ta yane su, ga ƙauri wurin yake yi, da ta kasa gane wani irin ƙauri ne. Tari ta fara yi saboda ƙaurin ya fara damunta, babu tsammani ta ɗaga kai ta ga wani zanƙalelen mutum, da tsawonsa ya kusa danganawa da rufin ɗakin.
Sai yanzu ta lura, ginin ɗakin ma tsawo ne da shi sosai. A hankali yake tafiya, yana zazzaro litattafai yana duddubawa.
Duk iya ƙoƙarin da Nana tayi, domin karanto addu'a, ta kasa ta fara ja da baya tana waige-waige ko za ta samu hanyar guduwa, amma ta kasa samu.
Ta sake ɗaga kai a dubi in da yake, amma taga ba ya wurin, ta yinƙura za ta tashi, amma ta ji tamkar an ɗaureta a cikin sarƙa.
Ajiyar zuciya ta ji an yi a gefenta, ta waiwaya da sauri, ganinsa ta yi zaune a kusa da ita.
Zuciyarta ce take dukan uku-uku, "Kwana da yawa" yayi maganar yana sanya dogayen faratansa a gefen wuyanta, ya tsaga jini ya fara tsatstsafowa.
Ta kalle shi, amma ta kasa kallon idanunsa.
Yayi gyaran murya ya ce "Yaya maganarmu ne, har yanzu babu abin da ki ka yanke a kai? Kar malaminku ya shiga gonata, saboda shi kashe shi zan yi, ba iya korarsa zan yi ba. Ba na son alaƙar ki da shi"
Cikin ƙwarin gwiwa ta ce "Wallahi ba zan yi abin da ka ke so ba, kuma ba ka isa ka hana Ubangiji ikonsa a kaina ba, ko da me ka ke taƙama kuwa" tayi maganar tana jin kamar zuciyarta za ta fito.
Ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce "Ke ko kewata ba ki yi ba ne? Yaushe rabon da na kawo miki ziyara, na je na yi jinyar abin da ki ka yi mini, na dawo da ƙarfina, mu ci gaba da fafatawa"
A raunane ta ce "Wai dan Allah me na yi maka, me ka ke nema a wurina ne?"
"Kin fi ni sani Nana"
"Ni ba zan yi abin da ka ke so ba, ka nemi wani yayi maka, ni ba zan iya ba"
"Ke aka bani, dan haka ke za ki yi aikin Nana, idan har ki ka amince, zan daina damun ki, zan ma iya barinki ki yi auren ki, amma idan ki ka ci gaba da gardama, wallahi wataran zaki iya tsintar kanki a gidan mahaukata, sai na haukata ki tuburan na hana kowa ya raɓe ki"
Nana tana kuka ta ce "Ba zan yi abin da ka ce ba, ni ba zan yi shirka ba"
"Ni ban ce ki yi shirka ba, bayar da magani za ki yi, wannan shi ne gado da sana'ar gidanku. Waɗannan litattafan duk tarihi ne, na waɗanda na yi wa aiki. Kakar mahaifinki 'yar bori ce, kuma duk wanda aka haifa da irin burujin ki, sai ya yi wannan aikin, ba a samu wanda yake da irin burujin ba wato mai irin tauraronki ba, sai a kanki, abin da baki sani ba, na sadaukar da mahaifina domin kare ki, baban ki yana matuƙar ƙaunarki, a 'yan uwansa waɗanda ba sa shiri, an bayar da jininki a yi masa tsafin kuɗi da ke, muka yi yarjejeniya da aljanin da aka sadaukarwa da jininki, na bashi mahaifina da ya tsufa a matsayin bawa, ya rabu da ke, ke kuma yanzu ki ce ba zaki yi abin da na kare ki saboda shi ba? Ba zai yiwu ba"
"Wallahi ƙarya ka ke yi, dama ai ku babu gaskiya a cikin zantukanku"
"Na yadda, amma ni ba ƙarya nake yi miki ba, samun kyakyawar rayuwarki, yana hannunki Nana" yayi maganar yana kai hannunsa jikinta. Iya ƙarfinta take kai masa duka, tana son ta yi addu'a amma ta kasa sai gurnani, da surutun"Allah ya fika, ba zaka yi galaba a kaina ba, kuma Allah ya isa tsakanina da wadda ta gada mini wannan masifar ni ba mushrika ba ce ba".
A hankali ta buɗe idonta, ta ganta tana ta kaiwa iska naushi tana surutu a fili.
Shiru tayi tana waige-waige, ta duba shimfiɗar su Jamila ta ga basa nan, ta ga ƙofar ɗakinsu a rufe, wani irin zafi ta ji a wuyanta, ta kai hannu ta shafa, ta ga jini, a gurin da ya karce ta da farcen sa. Ta nufi ƙofar ɗakin da nufin ta buɗe, amma ta ji a rufe, ta jijjiga amma taƙi buɗuwa.
Gari ya yi haske ba ta yi sallar asuba ba.
"Suwaiba, suwaiba, mama dan Allah ku buɗe mini ƙofa, waye ya kulle ni, ban yi sallar asuba ba fa" shiru babu wanda ya