Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
ma ahad yake, gidan malam Isa Buda"
"Asma'u" ya maimaita daidai lokacin da ya shigo falon.
Matar ta ce "Ma sha Allah Nana, to ku gaida gida mun gode"
Inna ta ce "mu ke da godiya Hajiya"
Sun juya za su fita, ya ƙarasa shigowa cikin falon, dogon mutum ne mai ƙiba, ya ajiye tumbi ya sanya wata dakkakiyar shadda coffee sai ƙyalli take yi. Suna yin ido huɗu da Nana, gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ga tamkar ta san shi.
Inna ce ta gaishe shi, amma hankalinsa a kan Nana. Cikin rawar baki Nana ta gaishe shi, ba ta jira ya amsa ba ta yi waje.
Inna ta fito tana cewa "Nana ki na da sa'a, kin ga ke ta amince da ke, Allah ya dafa miki"
"Amin" ta faɗa a hankali.
A hankali Nana take takawa, ji take tamkar gangar jikinta ba za ta iya ɗaukanta ba.
Su na daf da ƙarasawa bakin gate, raƙuman nan suka din ga shigowa, kala kala, Nana ta din ga mamakin wannan raƙuman na mene ne take ganinsu ne?. Ta ji jikinta ya ƙara sanyi, gabanta ya ci gaba da faɗuwa, dandazon raƙuman nan sun kewaye harabar gidan Wannan baƙin raƙumin ta gani a cikin raƙuman, idanunsa na ta hayaƙi a hankali ya girgiza ya koma wannan tsohon mai kama da ƙaisar hannunsa riƙe da wata irin sanda doguwa, ya zubo wa Nana ido. Babu abin da yake fitowa daga idanunsa sai tartsatsin wuta.
Ya buɗe bakinsa yana fesowa Nana wata irin wuta, mai ɗauke da baƙin hayaƙi.
Ta ja da baya ta rintse idanunta, tana maimaita "A'uzu bi kalimattilahi tammat"
A hankali ta buɗe idonta, ta ga ko ina ya gauraye da duhu, ba ta iya ganin komai. A take ta karaya ta tabattar da ƙaisar ne ya bayyana.
Ayshercool
08081012143
17
Addu'a ta din ga yi, Allah ya sa ba wani abun ya sanya ta aikata a gaban mutane ba. Kar ma su hanata rainon ɗan nasu.
Ta laluba za ta tashi tsaye, ta ji ƙasa hakan ya tabattar mata ba a kan shimfiɗarta take ba.
Wata irin walƙiyya ce mai tsananin haske, ta bayyana ta haska gurin. Wannan tsohon dai ta sake gani ya bayyana. Iya ƙarfinta ta taƙarƙare ta ƙwala ihu, tare da rintse idanunta.
Ji ta yi tamkar an yi sama da ita, an jefar a gefe guda.
Ta buɗe idonta tana mayar da numfashi da ƙyar. A tsakiyar sahara ta ganta da wannan mutumin da yake tsaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa. Yana tsaye ya zubo mata idanunsa.
Ƙaisar ne ya bayyana a gabanta, ya kalleta a fusace ya ce "Uban me ya kai ki gidan nan na ɗazu?"
Ta kalle shi ta ce "Kai da ka ke ganina ba na ganinka?, Ai bai kamata ka yi mini wannan tambayar ba"
"Ina ɗakin karatu lokacin, ina wani aiki me ki ka je yi gidan?"
Ta yamutse fuska ta ce "Me yasa zaka takura mini? Shi ne ka ke ta tsorata ni, saboda ka yi mini dalilin da zai sanya su kore ni, shi ne ka ke bayyana a suffar wannan tsohon ka na razana ni. Dan Allah ka rabu da ni, ka na kallon abin da zan ci gagarata yake yi, ka rabu da ni na yi aikina"
"Na gaya miki ba ni ne wannan mutumin ba, ki taimaki kanki ki haƙura da aiki a wannan gidan, idan ba haka ba za ki jefa mu a cikin masifa daga ni har ke."
"Na jefa mu ni da wa, meye alaƙa ta da kai? Koma mene ne kaina zan jefa, ka rabu da ni dan Allah"
Cikin tsawa ya ce "Ba kan ki kaɗai za ki jefa ba, har da ni, wani abin ba zan iya baki kariya ba, idan da hali ma ki bar unguwar nan gaba ɗaya." Ya yi maganar bakinsa na fitar da tartsatsin wuta
Nana ta ja da baya saboda yadda ta razana, cikin kuka ta ce "Idan ban nema ba ƙasa zan ci? Gaskiya ka rabu da ni, ka tafi ka rabu da ni, ko ma wani hali zan faɗa babu ruwanka"
"Aikuwa yanzu ki ka fara ganin wannan tsohon, kuma babu lallai na iya kare ki daga farmakinsa, tun da ba za a gaya miki ki ji"
Cikin ko in kula Nana ta ce "Dama Allah ne ya kare ni ba kai ba, kuma na san kai ne ka ke fito mini a suffarsa, so ka ke yi sai na yi hauka tuburan sannan zaka rabu da ni, amma Allah ya fi ƙarfin ka, kuma aiki sai na yi shi da ƙarfin ikon Allah. Ba tsoho ba idan ka ga dama ka zama fatalwar cikin littafin da ka ke rubutawa, durham yake ko wa?"
Tabbas duka yau, duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Gaba ɗaya yanzu Nana ta daina tsoronsa, ta saba da ganinsa, kuma har da siddabarun da sarkin baka ya din ga nuna mata, ya sanya yanzu ba ta tsoron sa kamar da.
Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tashi Nana, dan daga gidan nan, har zuwa yanzu da ta farka, ba ta san me ya faru ba.
Bayan sallar asuba, ta zauna tana azkar, ta duƙufa sosai tana addu'a. Duk da wasu lokutan ta fuskanci idan ta yi addu'a jikinta ya fi ta'azzara, shi yasa wasu lokutan sai ta share ta ƙi yi.
Gari na gama yin haske, ta fara shirin fita.
Duk gidan yanzu daga Baba sai Nasiru ne kawai suke shiga harkarta, duk da Mama tana tsawatar masa ta hana shi, amma ba ya ji, yana mugun ɗasawa da Nana, mussaman da ta kasance komai ta samo sai ta neme shi ta ba shi.
Tana yi wa Imran addu'a sosai da sosai, tare da fatan Allah ya kare shi a duk in da yake.
Bayan sun gaisa da Baba ta yi masa sallama, har za ta fita ta dawo ta ɗaura alwala sannan ta fita.
Tana tafe tana yi wa Allah kirari, da neman tsari daga dukkanin shaiɗanin mutum da aljani.
*****
Habu ne ya kalli Sule, ya ce "Ka ga yau jikin nasa da sauƙi, har ya tashi ya yi salla da kansa"
Sule ya ce "Wallahi kuwa Alhamdilillah, sannu buzu" ya yi maganar yana kallonsa.
Kallonsu kawai ya yi, amma bai ce komai ba, yanayin fuskarsa ya rame sosai.
"Ko zamu fita waje ka sha iska ne?" Girgiza musu kai ya yi alamar a'a.
"To za ka sha bunu"
"A'a" ya furta a hankali.
Cikin zumuɗi suka kalli juna, jin ya yi magana, dan rabon sa da magana ya daɗe.
Tiryan-tiryan Nana ta je gidan, sai dai yau ba ta ga dandazon raƙuman nan ba.
Babban abin da ya bata mamaki, bai wuce ganin layin duk buzaye ba, sun firfito sun haɗu a ƙasan wata bishiya, su na ta shan shayi, su na hira cikin nishaɗi. Gabanta ne ya faɗi, ta fara tunanin ko ita kaɗai take ganinsu.
Ta kawar da kanta, ta nufi ƙofar gate ɗin gidan.
Da azama ɗaya daga cikin su, ya zaburo ya zare takobinsa, cikin gurɓatacciyar hausar ya ce "Kai tsaya nan, gun wa aka zo?" Ganin mutum a tsaye da takobi tsirarta a gabanta ya sanya ta ja da baya tana ayatul kursiyyu a fili. Saboda gaba ɗayansa abin tsoro ne, sai kuma ta ga ta iya haɗa ido da shi, ta san da jama'ar su Ƙaisar ne ba za ta iya kallonsa ba.
"Kai magana nike maka, za ka yi magana ko sai na fille kanka?" Yayi maganar yana kuma matsawa kusa da Nana.
Sule ne ya buɗe gate ya fito, ya tarar da Nana da Wannan buzun, ya dube su ya ce "Lafiya ka tsaya a kanta da takobi haka?"
Buzun ya ce "Mu na ƙasan bishiyar can, mu na ɗumama kanmu, kawai ya nufo zai abka gidan na izini, shiyasa na taso ka san an ajiyemu a gurin nan saboda kama ɓarayi"
Cike da takaici Sule ya ce "Kuma wannan ne ɓarawon? Dan an saka ka gadi, sai ka din ga aza wa jama'a makami a ka?"
"Ai saboda kar mu bar ɓata gari su kai wa masu gida farmaki"
Guntun tsaki Sule ya yi ya ce "Yi haƙuri dan Allah, ke an na gani jiya kun zo ko? An yi mini bayani shigo kawai" Nana ta bi bayansa tana waiwayen na farkon, kar ya biyo ta ya sara mata takobin hannunsa.
Tsoron mai takobi bai sanya ta tsaya ta fuskanci, ko ta shiga halin da ta shiga jiya ba da ta shigo gidan.
Ta shiga falon da suka shiga jiya da suka zo da Inna. Nana ta din ga rafka sallama amma shiru babu kowa a falon.
Tana nan tsaye sai ga wani matashin saurayi ya shigo falon, sanye da singlet da gajeren wando.
Nana ta ɗan rakuɓe ta ce masa "Ina kwana?"
Ya amsa da "Lafiya ƙalau, wa ki ke nema ne?"
"Dama jiya ne aka ce na zo da wuri, zan fara rainon yaro"
"Ohh ke ce mai rainon Haidar, za ki sha rigima, ga shi mutanen gidan ba su tashi ba har yanzu, have a seat zauna kafin su tashi"
Nana ta zauna a kan lallausan carfet ɗin da yake tsakar ɗakin.
Ya wuce gaban tv ya kunna, sannan ya bar falon.
Ta daɗe a falon a zaune, ta fara jiyo taku ana saukkowa daga matattakalar benen da ke falon.
Nana ta ƙara saita nutsuwa, mutumin jiya ne yake saukkowa, yana sanye da ash ɗin jallabiya, tumbinsa ya fito a cikin jallabiyar, kansa babu hula yana sanye da farin glass, hannunsa riƙe da wayarsa.
Kallon kallo suka yi da Nana, Nana ta fara ƙoƙarin tuna wani abu a kan mutumin, ta taɓa ganinsa a wani guri, amma ta kasa tuna a ina ne. Tana ƙoƙarin sansano wani abu a tattare da shi, amma ta kasa tantance komai.
"Asma'u ko?" Ya faɗa yana ƙure ta da ƙwala-ƙwalan idanunsa.
"Eh, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau" ya yi maganar yana ƙarasowa cikin falon, ya samu guri ya zauna a kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da ke falon.
"Meye ma ki ka ce sunan babanki?"
"Malam Isa" ta faɗa tana sunkuyar da kanta.
"Sunan mahafiya fa?" Ya tambayeta ba tare ya sauke idonsa daga kanta ba.
"Kar ki faɗa" ta ji muryar ƙaisar a kunnenta"
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ya ce "Eh jikana za ki raina, mahaifiyar sa 'ya ta ce, dan haka dole na san daga ina ki ke, kuma su waye iyayen ki?"
Ta buɗe baki za ta yi magana, matashin nan ya dawo cikin falon ya ce "Daddy ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, har ka tashi?"
"Eh na ɗan motsa jiki ne, na shigo kuma na tarar da baƙuwa na jiran Shukura, amma tana bacci, na je na taso ta ma"
"Eh, na ga an samu mai rainon, Allah ya sa ta iya da rigimar sa"
Matashin ya nemi guri ya zauna, suka ɗan yi hirar su, Nana dai na gefe, amma hankalin mai gidan a kanta.
Suna cikin hirar aka kira shi Alhajin a waya, ya ɗauki wayar ya fita.
Shukura ce ta shigo falon, bayanta kuma wata mai aiki ce, ɗauke da yaro da bai fi shekara biyu ba, sai uban ihu yake yi yana zillo sai ya sauka daga jikin mai aikin.
Cikin girmamawa Nana ta ce "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau. Ki ɗan jira likitan yana hanya. Ke kuma Jummai ki wuce da shi ki haɗa masa abinci, ya bi ya cika mini kunne da ihu"
Yanayin yadda yaron ke zambarwar ihu, ka san ba iya abu ne na yara ba, har da sangarta, haka jummai ta wuce da shi tana jijjiga shi tare da yin yaƙe tana rarrashin sa.
Shukura na zaune a falo a kawo mata kayan breakfast, ta karya ta gama ta ɗauki remote.
****
Cikin sauri yake tafiya, yana kallon agogon hannunsa, ya buɗe ƙofar falon ya shiga.
Tun daga bakin ƙofar yake faɗin "Ina yake ya fito na kai shi, mun kusa makara"
Turus ya yi yana kallon fuskarta, ganinta itakaɗai a falon, fuskarta ɗauke da yanayin damuwa.
"Lafiya kuwa? Ina boy ɗin?"
"Ba shi da lafiya"
A ɗan diririce Alhaji fatuhu ya ce "Kuma ba ki kira ni kin sanar mini ba, ki ka bar mini yaro ba lafiya?"
Cikin damuwa ta ce "Na rasa ma ya zan yi ne, kwana muka yi ba mu yi bacci ba, yana ta ihu da surutai"
"Fadila garin yaya ki ka bari sauro ya ciji yaron nan, har ya fara zazzaɓi?"
"Daddy ba zazzaɓi ba ne, jikinsa babu alamar zazzaɓi ihu kawai yake yi yana razana" tsaki ya ja ya ce "Dama kina can ki na wannan baccin na mutuwa, ai har zazzaɓi ya kama yaro ya sake shi, ba ki sani ba" yayi maganar yana shiga bedroom ɗin ta.
Ya kalli Muhsin da yake ta bacci, ya kai hannu ya taɓa goshin sa, a razane yaron ya miƙe tsaye yana ihu.
Da sauri Alhaji fatuhu ya rungume Yaronsa, yana faɗin "Is ok, daddy is here, sannu boy"
"Daddy" ya kira sunan babansa cikin razani.
"Na'am boy"
"Ka kai ni gurin Anty Nana"
"Anty Nana kuma muhsin, ai an sallame ta daga makarantar ku"
Cikin kuka yaron ya ci gaba da cewa "Daddy ka kai ni Anty Nana, tsoro nake ji"
"Ikon Allah, to yi shiru bari mu fara zuwa gurin doctor Sharif ya duba ka, sai a san abin yi, sorry dear may be typhoid fever ne, ko severe malaria su ne suke saka yara irin wannan abun. Bari na kai shi asibiti kawai" Ita dai da ido ta bi shi, dan ta san duk abin da za ta faɗa, muddin ya saɓa da abin da likitoci suka gaya masa ba zai yadda ba.
*****
Nana na nan a zaune, likita ya ƙaraso, yanayin yadda suka gaisa da mutanen gidan, da yadda suke jansa da hira, ya sanya Nana gane likitansu ne na iyali da yake duba su.
Shukra ta ce "Ga ga nan, ita ce new Nanny na Haidar, ina son a duba a tabattar ba ta da wata matsala kamar dai yadda na gaya maka a waya"
Ya ce "Ok, sai dai wasu daga gwaje-gwajen za su yiwu yanzu a nan wasu kuma, sai dai na tafi da jinin nata lab.
Amma main abubuwan da yakamata a sani ɗin, Hiv ne da hepatitis, su ne main, za a yi su yanzu sauran kuma zan turo miki result ta gmail ɗin ki"
"Ok gata nan a duba"
Allura na cikin jerin abun da Nana ta tsana a rayuwarta, tsigar jikinta har tashi take yi idan ta ganta. Amma da yake sa kai ya fi bauta ciwo, haka ta dake.
Yana saka allurar a wahale ta ce "Washhh" ya kalli yadda ta haɗa gumi, saboda ɗiban jini.
Ya yi murmushi ya ce "Akwai haihuwa a gaba fa, kar ki fara yi wa allura kuka, dan haihuwa ta fi wahala, ko maman haidar?" Ya yi maganar yana kallon Shukura.
Yamutsa fuska ta yi ta ce "Oho maka dai, kai ina ka san zafin haihuwa tun da ba kai ka ke yi ba, da ku ka haɗa kai da baban haidar ku ka hana ni zubar da wannan cikin, ga shi ina ta fama da wahala"
Ya yi dariya ya ce "Ai saura ƙiris"
"Ku kuka sani dai, daga wannan wallahi sai na yi seven years ban haihu ba, sai na yi master's na gama"
"In dai kin haihun ba komai, mun yarda"
Yana aikinsa su na ta hira, har ya kammala ya kalle ta ya ce "Babu matsala a wannan result ɗin, za ta iya fara aikinta"
"Ok to shikkenan doctor, za ka ji alert in sha Allah na gode sosai da sosai"
Ya tattara jakarsa, ya tashi zai tafi yana cewa bai ga Hajiya ba, ba su gaisa ba. Wata ɗirkekiyar mage ce ta kusa girman jaririn Akuya, baƙa ƙirin da ita, ta zo ta gindaya a tsakiyar falon.
Kallon su Nana ta yi, amma ta lura babu wanda ya ankara da magen, hirar su kawai suke yi. Likitan ya zo wucewa, yana ƙoƙarin taka magen, Nana ta buɗe baki amma ta rasa me za ta ce, tuni ya taka magen, aikuwa yana taka ta ya yi tuntuɓe ya kifa a gurin.
Rige-rigen sannu suka din ga yi masa, cikin dakiya ya tashi yana yaƙe, ya ce carfet ne ya saka shi tuntuɓe, kar su damu yana lafiya. Ya sake yi musu sallama ya fita. Yana yin tuntuɓen magen ta ɓace ɓat.
A baɗini kuwa da kyar ya daure, bai kurma ihu ba saboda azabar raɗaɗi da zafin da ya shige shi. Ji ya yi kamar ƙashin idon sahunsa ya karkace, da jan ƙafa ya ƙarasa gurin motarsa ya ja ya fita.
Shukura ta tashi ta ce Nana ta bi ta, ta yi gaba Nana ta bi ta a baya.
Wani ɗaki ta kai Nana, ɗan matsakaici mai kyau, an yi wa ɗakin fenrin blue, duk in da Nana ta kai idonta teddy ne manya da ƙanana, rakwacam har sun yi yawa.
Gefe ga ɗan madaidaicin gado na yara.
Ta dubi Nana ta ce "Nan shi ne ɗakin Haidar, za ki din ga gyara masa kullum, dan ba kowa na yarda ya raɓi ɗa na ba." Ta buɗe wardrobe ɗaya cike da gwangwanayen madara na yar ta ce "Ba ya cin abinci, sai shayi ko madara, dan haka za ki din ga haɗa masa a kai a kai ki na ba shi. Ga wardrobe ɗin kayansa nan." Tayi maganar tana buɗe ƙofar wardrobe ɗin da aka shaƙe da kaya, ga wani sashe fal da tulin pampers.
Hatta kayan wankan yaron an jere su a cikin toilet, kayan alatun rayuwa dai babu wanda babu a ɗakin nan. Ta gama nuna mata suka koma falo, ta ce a kawo wa Nana Haidar.
Jummai ta shigo tare da Haidar, hannunsa riƙe da feeder, cike da shayi yana sha.
Shukura ta kalli Jummai, ta ce "Yauwwa Jummai ba ta shi, Haidar ga new Nanny ɗin ka" shiru ya yi yana kallon Nana.
Nana ta yi masa murmushi, tare da miƙa masa hannunta, amma ya noƙe a kusa da Jummai.
Nana tana kamo hannunsa, ya daddage ya saka wani irin ihu, da sai da Nanan ta tsorata.
"Ke ɗauke shi, ki tafi da shi ki rarrashe shi, ba na son wannan shegen kukan da yake yi"
Nana ta ɗauke shi, ya din ga zunduma ihu, yana buga mata feeder hannun shi, yana zillo yana ƙoƙarin sauka daga jikinta, yana miƙawa Shukura hannu.
Cikin tsawa Shukura ta ce "Ki tafi da shi, ki rarrashe shi, ki fara aikin ki"
Nana ta nufi ɗakin da Shukura ta nuna mata, ta ce nasa ne. Ta ci gaba da ƙoƙarin rarrashin sa, amma abu ya ci tura. Duk son Nana da yara, sai da ta ƙulu da iskancin da yaron nan yake yi mata.
Ta zuba masa ido, ya yi iya yin sa, ya