BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   33 / 64

96K to 99K   out of 190K words

a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an shaƙe ni, da ƙyar nake numfashi"

Malam Gambo ya yi shiru ya ce "Kuma ka tabattar ba ka yi maganar da shi a zahiri ba?"

"Wallahi na kasa tunawa"

"Hakan na nufin da akwai matsala kenan, ka ɗan bani lokaci zan yi bincike"

Cikin damuwa ya ce "Zuwa yaushe kenan? Ni fa duk abin da za ayi sai dai a yi, fatana kawai burina ya cika"

"Kar ka manta burin naka ba ɗaya bane ba, kar ka manta bayan burinka na son haska taurarinka, na mallakar dukiya mai tarin yawa da kujerar siyasa, akwai burinka na son kawar da babban amininka, idan ka yi wasa za mu yi jifar gafiyan ɓaidu, dole ka tattara hankalinka a kowane ɓangare, muddin ba ka durƙusar da shi ba, taurarinka ko sun haska ba za ka taɓa shan gabansa ba, dan haka ka kula da kyau"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce"Na fahimta, shi ma ba mantawa na yi da nasa ɓangaren ba, shi ma na shirya komai, amma ina sauraren ka abin da binciken naka ya baka sai ka sanar da ni. Dan ko ya kama na zubar da jininsa ne zan yi domin na samu cikar muradina"

"Ka dai dakata, zuwa lokacin da zaka ji daga gare ni tukuna"

Da ƙyar ya lallaɓa Alhaji Zailani ya kwantar masa da hankali.

*****

Cikin tsananin tsoro da razani Jamila take kallon hajiya Sa'a, jikinta na wata irin tsuma cikin faragaba da tashin hankali. Yawun da za ta haɗiye ma ya gagare ta, saboda tsoron da ya mamaye ta.

"Jamila, na gaya miki sirrinmu, idan kin ga dama ki yi shiru da bakin ki, ki tara arziki ki bar shi, idan kuma kin so ki fallasa, ba ki da hujjar kare kanki, kuma sai na ƙarar da zuriyar ku, ta hanyar bayar da jinin ku ɗaya bayan ɗaya.
Abin farko da nake buƙata ki taimaka mini, shi ne mu na buƙatar jinin yayar ki Nana, a baya na sha baki abu ki bata, ba tare da kin san dalilin hakan ba, to yanzu na gaya miki abin da nake so. Dan haka za ki taimake mu muma"

Jamila na jan numfashi da kyar cikin rauni ta ce "Amma ba za ta mutu ba?"

Safiyya ta ce "Ke ina ruwan ki da zata mutu ko ta rayu, idan aka so har babanki za a iya nema ki bayar, to dan dai wannan da ba uwarku ɗaya ba"

Hajiya sa'a ta ɗaga mata hannu ta ce "ƙyale ta, dole za ta ji banbarakwai abin, ina ga sai dai mu sanya ta a wani ɓangaren, tana da tsoro sosai da sosai. Yanzu dai ki fara yi mana wannan aikin tukuna"

Jamila cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Hajiya a canza mini wani, tausayinta nake ji" har maman khairat ta hasala za ta yi kan Jamila da masifa, hajiya Sa'a ta ɗaga mata hannu. Ta dubi Jamila ta ce "Ba fa kashe ta za a yi ba, ɗan kaɗan muke son jinin nata"

"To ai ta yi aure, babanmu ya aura mata wani buzu" ta yi maganar hawaye na cika mata idanu.

"Eh na san ta yi auren, na ga duk kin tsorata kin damu, bari na kawo miki lemo ki sha" ta tashi ta ƙiftawa maman khairat ido, ta fice daga ɗakin.

Ba a jima ba ta dawo da lemo a cikin glass cup, ta miƙa wa Jamila. Jin sa da sanyi, ya sanya ta karɓa kai tsaye ta fara sha. Sai dai tun kafin ta gama shan lemon, jiri ya fara ɗibar ta.

Maman khairat ta karɓe kofin lemon, Jamila kuma ta silale, cikin fita hayyaci.

Suka sassaki labulaye, suka kashe fitila, duhu ya mamaye ɗakin, ta kunna kyandira, ta bawa maman khairat ta riƙe mata, ta ɗaukko wata jakar fata ta zazzageta.

Wani irin tarkace ya zubo daga ciki, tare da layoyi, ta cire wa Jamila kayan jikinta, ta din ga sha mata wani irin mai jawur da shi. Bayan ta gama ta ɗaukko wata allura a cikin wata laya, ta sokawa Jamila a wuyanta. Aikuwa ta zabura jikinta ya yi wata irin girgiza. Ta juya bayanta ta kuma soka mata a ƙeyar ta. Nan ma jikin nata ya sake girgiza.
Ta sake saita ƙahon zuciyar ta, ta sake soka mata. Jikinta ya din ga tsuma ba tare da ta tsaya ba. Hajiya sa'a ta din ga karanto wasu abubuwa cikin wani irin yare, jikin Jamila na ci gaba da rawa tamkar ana girgiza ta.
Ta kama hannunta, ta saka mata wasu awarwaraye, sannan ta kawo wani bargo ta rufe ta da shi.

****

Tamkar mujiya haka Nana take zaune a ɗakin nan, duk abin duniya ya ishe ta, yamma tana yi ya ɗauki radiyo ya fice ya bar ta a ɗakin ita kaɗai.

Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su.
Ɗan kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daɗi sosai da sosai.
Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata wannan abin. Ta haɗa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe.

Ta janyo jakar kayanta, ta buɗe wardrobe ɗin, ta ga ɓangare ɗaya shaƙe da kayansa, sai da abin ya bawa Nana mamaki.
Ɓangare ɗaya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ta daɗe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ƙarewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ƙarshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a kai ga ɗinkawa ba.
Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe ɗin.
Drower ƙasan wardrobe ɗin kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad ɗin ta. Ta gyara kan katifar ta ɗame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ƙatuwar katifa.

Wani murmushin ne ya sake suɓuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta.

Ba ta san lokacin da ta ƙwala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba.
Kuma kasancewar ta ƙure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faɗa kan katifar.

Taku ɗaya ya ƙara, ya tsaya a kanta yana kallonta.

Ayshercool
08081012143

29

Ƙara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa.

Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi zaune tana kallon wayar, gaba ɗaya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta.

Ta bi wayar da kallo, ta kasa taɓa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta ɗan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta ɗauki wayar ta duba ta ga a kashe take, sai ƙamshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya.

Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke.

Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ƙofar ɗakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta yi mata maraba, ta shimfiɗa mata sallaya ta zauna.

Bayan sun gaisa Nana ta ce "Ban gane ki ba"

"Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa"

Nana ta ce "Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo"

Matar ta ce "Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ai ban san da mutane a gidan ba"

Haula ta ce "Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo."

Zuwan Haulat sai ya ɗebe wa Nana kewa, su ka yi ta hira.

Sun daɗe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ƙofar ɗakin ta ce "Idan na fara fita, nima zan kawo miki ziyara"

"To shikenan, ai a nan baya muke"

Nana ta ce "Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?"

Haula ta ce "Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin"

"Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida"

Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin ɗan ƙaramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ƙoshi ba.
Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa.
Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai ɗaga kai ya kalle ta ba, ta fita.

Sai da Nana ta ji babu daɗi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi magana ba kurma bane ba, tsagwaron wulaƙanci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru.

Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne.

Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake ɗaukar kwanon da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai.
Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun zuciyar, sai dai sanyi da take ji.

Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take ɗan dannawa, sai da ta saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa.
Ya rage kayan jikinsa, ya ɗauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga ɗakin.
Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banɗaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta shirya ta kwanta.

A iya saninta, wayarta take ɗan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta.

"Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?"

"Meye haka wai?"

"A ina?"

"Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?"

Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?"

A ƙule Nana ta ce "Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum ɗin ne ko akasin haka"

Ƙaisar ya ce "Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata ki tsaya kar allura ta tono garma"

"Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa"

Kawai ƙaisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce "Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa ba, ni ba jinnil ashiƙ bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne ba su yi mini ba, duk da wannan ma da na farga da wuri sai na ruguza shi, sai dai idan na matsa za ki iya rasa rayuwar ki baki ɗaya, shi yasa na ƙyale"

Nana ta ce "Saboda me?"

"Kawai" ya bata amsa.

"Amma wai da gaske aljani yana auren mutum?"

"Eh"

"To ku ina naku matan ku ke auren na mutum?"

Ya ce "To ai ni ba aljanin soyayya ba ne ba da za ki tambaye ni."

Nana ta ce "Amma ka hana ni aure? Me yasa ka saka Saleh ciwon ciki?"

"Ke ko duk matan bil'adama sun ƙare zan auri masifaffiya ne mai azabar taurin kai kamar ke ne?"

"Eh abin nan ne, da ake cewa makaho ga ido, ya ce wari yake, na fi ƙarfin ka ne kawai"

Ya ce "Ko?"

"Eh mana, dan Allah ka gaya mini ya ake yi ku ke auren bil adama"

"Ni ma ban sani ba, sai dai zan baki wani littafi ki karanta, soyayyar Aljani Ridwan, da bil adama" Nana ta zabura ta ce "Dan Allah, ya sarkin baka, a wane hali yake yanzu? Kuma ni ba littafin soyayya nake so ba, wannan littafin na Jaddul jinn nake so ka bani na ƙarasa karantawa"

"Ba zan bayar ba, kuma ba wannan ne ya sanya na kira ki ba, duba jikin mudubi, ki zo ki gaya mini abin da ki ka gani"

Nana ta ce "Wallahi ba zan kalla ba, masifa da bala'i kawai ka ke nuna mini a cikin mudubin nan, Allah ya sa ya tarwatse...

"Wallahi sai kin kalla, wataƙila zuciyar ki ta saduda, ki yi abin da ya dace"

Kawai ta ganta a gaban mudubin, Jamila ta gani a kwance tsirara, Hajiya Sa'a na ta tsira mata allurar nan. Tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta ta ce "Dan Allah me take yi mata? Jamila ce fa"

"Ƙwarai ita ce, Matar ta umarceta ta kawo mata jininki, ta ce ba za ta iya ba, shi ne ta bi ta bayan gida, yanzu haka ta gama mallake ta, duk abin da ta ce ta yi shi za ta din ga yi, ba za ta taɓa kaucewa maganar ta ba"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu ya zan yi, kar ta cutar da Jamila, shiyasa ni tun farko ba na son yawon maƙwabtan nan da take yi. Wannan matar ba ita ta bayar da Muhsin ba?"

Ƙaisar ya ce "ƙwarai ita ce, kuma ba wannan ba, bayan cin moriyar ganga, yada ƙwauron ta za ta yi. Ba wannan ba bayan ɗalibin ki da ki ka rasa, babansa ma an sako shi gaba, wataƙila nan kusa ko nesa kaɗan ya bi ɗan nasa".

"A'a ba gaskiya ba ne ba Ƙaisar, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba"

"Dama ai ba gaya miki nake yi domin ki yadda ba"

Ta ɗan yi shiru cikin jimami da tashin hankali, ta ce "Yanzu meye abin yi, ba na son Jamila ta faɗa ga halaka" ta yi magana cikin kuka.

"Kin fi ni sanin abin yi ai Nana Asma'u"

"A'a ban da wannan, wannan ba mafita ba ce ba, na gaya maka ba zan yi wannan ba"

Ya ce "To shikenan, sai ki zura ido mutane na cutuwa alhalin ki na da yadda za ki yi, ki taimaka musu"

"A'a ƙasair" kawai ta ga tamkar ya wurgota waje.

Ihu ta saka ganin tana faɗowa daga sama, za ta faɗa cikin ruwa. A razane ta tashi tana faɗin "Ya Allah" ta dafe saitin zuciyarta tana haki.

Ita kaɗai ce a cikin ɗakin, ta janyo wayarta ta duba lokaci, ta ga uku da rabi na dare. Ta yi shiru domin tuna abin da ya razanata daga baccin, amma ta kasa, kawai faɗowarta daga dogon tsaunin da libararyn Ƙaisar zuwa ƙasan ruwa ta iya tunawa.

Ta kalli ɗakin, fitila a kunne, amma ba ya ciki.

Ta tashi a hankali, ta nufi ƙofar ɗakin, ta leƙa harabar gidan.

Yana kwance a kan benci, yana bacci ya tada kansa da hannunsa. Gabansa ɗan murhun dafa shayinsa ya mutu, ga butar shayin da kofinsa.

Wasi-wasi ta shiga yi, a kan ko tashin sa za ta yi. Wutar gurin ce ta ɗauke gaba ɗaya, gurin ya gauraye da duhu, aka yi wata irin walƙiya mai hasken gaske, kawai ta ga wannan tsohon a tsaye a kansa.
Tamkar an dasa ta, ta kasa motsi ta kasa gaba ta kasa baya, aka sake walƙiyar nan, ta sake ganin tsohon nan a tsaye a kansa, sai dai wannan karon ya feso wani irin tartsatsin wuta da ya tilasta mata yin baya cikin matsanancin tsoro.

A hankali ta buɗe idonta, kawai ta ganshi a tsaye yana kallonta, kamar taɓaɓiyya haka ta zura da gudu, ta koma kan katifa ta kifa kanta tana haki, saboda tsoro da razani. Maganganun Ƙaisar suna nema su fara zama gaskiya a kan mutumin nan. Tabbas ta fara tantamar kasancewar sa mutum. Duk da ta san ba ta da cikakkiyar lafiya ƙaisar ya saba tsorata ta, amma ya za a yi a ce mutumin da ta hango yana bacci, cikin abin da bai fi ƙifta ido sau biyu ba, ta gan shi a gabanta.
A ɓangaren sa shi ma mamaki yake yi, me take yi a tsaye a bayan labule a wannan tsohon dare haka?.

*****
Hajiya Sa'a ce take kallon Jamila, tana wani irin mugun murmushi ta ce "To jamsy me ki ka ce yanzu?"

Jamila ta ce "Ta yaya zan samo miki jinin nata?"

"Yauwwa Jamila, ba wani abu ne mai wahala ba, magani zan baki a abinci, ki kai mata ta ci, sai kuma abin da za ki ajiye mata a ɗaki"

Jamila ta ce "To shikenan, babu damuwa an gama"

"Kin tabattar za ki iya?"

"Eh mana, me zai hana?"

Hajiya Sa'a da Maman Khairat suka kalli juna, suka sheƙe da dariya, Hajiya Sa'a ta ce "Yauwwa jamcy, zan gaya miki duk yadda za a yi " Jamila ta gama wuninta a gidan, sannan ta tafi gida. Sai dai gaba ɗaya ta din ga jin ta wani iri, tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita.

****
Tamkar bakin mama ya taɓo ƙeyarta, haka take washe baki, a gaban malaminta. Ta ce "Anya ka taɓa yi mini aiki mai zafin wannan? Komai ya tafi yadda ake so, wallahi yadda na tsara masa komai

33 / 64