Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
aka ce mahaifiyar Inna 'yar bori ce "
"In ji uban wa? Ƙarya ne bayar da magani kawai tayi"
Ummi ta yi murmushi, ta ce "Nana ƙaraso magana zamu yi"
Nana ta so wucewa ɗaki, ta kwanta, duk da ta yi murnar zuwan Ummi gidan, amma soki burutsun da Baba ya fara ya sanya duk ta ji komai yayi mata zafi. To idan ubanta mahaifi ya gaza da larurarta ina ga miji, da za su haɗu rana tsaka su yi aure?" Ta zauna a hankali, tana jin yadda ƙafafuwan nata suke yi mata zugi.
"Yaya magungunan da muka karɓo a wurin mutumin nan, kin yi su kuwa?"
Nana ta jinjina kai alamar eh.
"To yaya ki ka ji, akwai sauƙi?"
Da ƙyar Nana ta ce "Eh akwai"
Baba ya ce "Ina fa wani sauƙi, babu sauƙi ko kaɗan sai wurin Allah. Nan na ɗaukko malamin nan na almajiran gangare, yayi mata ruƙiyya wai aljanun suka ƙi magana, ba ki ga dukan da ta ci ba, sai da ta ba ni tausayi amma jiya i yau. Shiyasa duk na damu na aurar da ita, ko na huta. Ai ni wannan zancen da ki ka zo mini da shi, ba ƙaramin daɗi yayi mini ba, Allah ya tabattar da alkhairi tun da shi wancan yaƙi cewa komai".
Cikin mamaki da rashin fahimta, Nana ta ce "Wane zancen ne?"
Ayshercool
08081012143
BUZU
AISHA ADAM (Ayshercool)
Arewabooks Ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724
YOTA 002
BRIGHT PENS 3rd batch
P6
Ummi ta yi murmushi, ta tura wa Nana wata leda gabanta. Nana ta kalli ledar, daga saman ledar take iya hango sabulun wanka da man shafawa.
"Saleh ne ya aiko ni, tun ranar da ki ka je gidana, yake bibiyata shi fa son ki yake yi, auren ki zai yi" take Nana gabanta ya faɗi, damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta ta ce "Anty Ummi, Saleh kuma?"
Baba ya ce "Shi fa, ƙanin mijin Ummi ba yaron kirki"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "To Baba Auwwal ɗin fa, da ka ce masa ya turo?"
Sai Baba ya hau faɗa ya ce "To ina na ganshi? Tun da na ce ya fito ɗin ya fito? Da a bawa bare ke, ba gara shi ba, tun da ya san larurar ki, idan aka yi auren ba ruwanmu da kayan ɗaki, ya ɗauke ki ya tafi da ke can Ikkon, wurin neman kuɗinsa ba, ɗaki ɗaya ya ishe ku kafin Allah ya yassare masa ku tara zuriya ba. Nana wannan iskokan duk aure ki ke buƙata da kin yi shikenan za su daina damun ki".
Har Nana za ta yi shiru, amma ta kasa ta ce "Baba to idan iyayen malam Auwal ɗin suka turo fa?"
Ummi ta ce "Nana wai ƙanin mijin nawa ne ba kya so ko kuwa?"
Gaddafi da yake gefe, tun da ake maganar bai ce uffan ba, ya na ta faman gyara wata radio ya ce "Ai dama ke Ummi ke ce ki ke tausayin yarinyar nan, ita ba tausayin kanta take yi ba"
Nana ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ya ma za ayi Ummi ta yi mata haka, ta ce zata haɗa ta da wani Saleh, mutumin da ba nutsuwa ce da shi ba, ga shaye-shaye da yake yi, askin da yake kansa kaɗai ya isa ya bayyana maka, abin da yake aikatawa a Lagos ɗin.
Ummi ta taɓa ta ta ce "Nana kin yi shiru"
"To me zan ce, Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi"
Baba ya amsa da Amin.
Nana ta miƙe ta nufi ɗakinsu, zuciyarta babu daɗi, addu'a take yi da fatan, Ubangiji Allah ya sa Auwal ya fito, amma Saleh kam, ba ta tunanin ko me za ayi mata, zata iya aurensa. Dan ko Suleiman da aka fasa aurensu ya fi dama dama a kan Saleh.
Ji tayi jiri yana ɗibar ta, dan haka ta samu wuri ta kwanta, ta din ga yi wa Allah kirari, tana magiyar Allah ya daidaita ta da Auwwal ya fito ya turo iyayensa.
Ummi ta leƙo tayi mata sallama, amma ta ganta a kwance, ta ce "Nana bacci da yammacin nan, ni dai na tafi, in sha Allah zai zo ku gaisa". Nana na jin Ummi, amma tayi banza da ita. Shikenan dan ana so ka yi aure, sai a ace ka auri mutumin banza.
Ranar dai haka ta ƙarasa wunin ranar sukuku, dare ma yayi bacci ya ƙaurace wa idanunta, sai wani azababben ciwon kai da ya kama ta.
A hankali ta din ga juyi a kan shimfiɗarta, amma babu bacci babu alamarsa, sai wannan ciwon kan, da take jin tamkar ana sara mata kan da gatari.
A hankali kuma ta din ga jin, tamkar ana ɗaɗɗaureta da sarƙa, ambaton Allah take ƙoƙarin yi, amma ta kasa sai a zuciyarta.
Ta saka hannun tana laluben hularta, domin ta saka a bakinta ta toshe, kar ta yi ihu cikin dare, ta hana mutane bacci.
Ji ta yi an kira sunanta a tsakar gida, duk da ba ta san muryar ba, amma ta amsa a wahale.
Jin an ci gaba da kiran sunanta, ya sanya ta yinƙura da ƙyar ta tashi, kanta babu ɗankwali, ta fito tsakar gida neman mai kiranta.
Kallon tsakar gidan tayi, taga duhun ya ninka na dare, ba ta iya gane komai a tsakar gidan. Ta juya don ta koma cikin ɗaki, amma ta rasa hanya, saboda duhu ba ta ganin komai.
Ji ta yi an ci gaba da kiran sunan ta, kawai ta hau tinkarar wurin da take jin ana kiranta.
Gaddafi yana shagonsa a ƙofar gida, ya ji an buɗe gida, ya duba agogon wayarsa, ƙarfe biyu saura mintuna tara na dare.
Tashi yayi ya leƙo, ya ga Nana ta fito, daga ita sai zani da vest kanta ko ɗan kwali babu.
Sai da ya bari ta yi nisa, sannan ya fito ya bi bayanta, a zaton sa ko wani yawon banzan take, sai dai ga mamakinsa kawai tafiya take yi.
Ganin tafiyar ta ƙi ƙarewa ya sanya ya ce "Ke dan ubanki ina za ki je a tsohon daren nan?" can kamar a wata duniyar, haka take jiyo muryarsa. Ba ta tsaya ba, kuma ba ta yi magana ba, ta cigaba da tafiya.
Danƙo hannunta yayi, ya din ga jan ta har zuwa gida, sai dai ba ta yi masa musu ba, bin sa kawai take yi, dan ta kasa tantance bacci take yi, ko kuma a zahiri ne.
A tsakar gida ya hankaɗa ta, ta faɗi ƙasa, cikin ɗaga murya, yake tambayarta gidan uban wa za ta a wannan daren.
Shiru tayi, ta ci gaba da laluben hanya tana ƙoƙarin tashi. Ya saka ƙafa ya hankaɗa ta ta sake bajewa a wurin. Wata 'yar ƙaramar ƙara ta saki, ta sake yinƙurawa za ta fita, wannan karon da azama ta yinƙura, sai dai tamkar ya samu namiji ɗan uwansa ya sake janyota yayi jifa da ita.
A wannan karon, ba ta ji muryar komai, sai dai zafin buguwar da take yi.
Baba ne ya fito daga ɗaki, yana tambayar Gaddafi ko lafiya.
"Wannan mahaukaciyar yarinyar ce, ta buɗe gida ta fita a haka, na bi bayanta na kamo ta".
Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni Wallahi lamarin nan na Nana ya ishe ni, kula Gaddafi za ta sake fita". Baba yayi maganar yana nuna masa Nana, da ta kwaso da gudu za ta nufi hanyar fita.
Ƙafa Gaddafi ya saka mata, ta faɗi a wurin, amma cikin ƙarfin hali, ta sake tashi.
Fizgo ta ya sake yi, ya wanka mata mari har sau biyu. Amma ko gezau ba ta yi ba.
Baba ya ce "Gaddafi daina dukanta, ba fa ta hayyacinta, ba ta san me ka ke yi ba"
"Wallahi ƙarya take yi, iskanci ne kawai, buɗe idonki ki kalle ni" dan sai a lokacin ya lura duk abin nan idanunta a rufe suke.
"Gaddafi tofa mata abin da ya sauwwaƙa, ni tsorona kar ta fita tayi wani wurin ba a sani ba"
"Ni me na iya da zan tofa mata?"
Baba ya ce "Jeka kawai, bari na zauna na ga jikinta ya saki, kar ta sake fita. Dan Allah ko da bacci zai ɗauke ni, idan ka ji motsinta ta buɗe gidan, ka riƙota"
"A'a wallahi ban yi alkawari ba, bacci zan yi"
Baba ya ciro zanin mama da yake kan igiya, ya rufawa Nana da take baje a wurin kamar abin banza.
*****
Washegari da safe, Nana sai haƙura ta yi da zuwa makaranta, saboda yadda jikinta yake yi mata ciwo, dan har targaɗe ta yi a hannu. Da safe Jamila take gaya mata abin da ya faru.
Shiru Nana tayi ba ta iya cewa komai ba, ita kanta dan babu yadda za ta yi da ƙaddararta ne.
Ƙugin da cikinta yake yi na yunwa bai dameta ba, ta nemi wuri kawai ta kwanta tana goge hawaye a ɓoye.
*****
Fuskarta babu annuri take kallon mutumin, kamar ta fasa ihu ta ce "Wai kana nufin babu abin da ya sauya kenan?"
"Ƙwarai kuwa, komai yana nan yadda yake"
Ta sake tsuke fuska ta ce "Kuma kai babu wani abu da zaka iya yi a kai, gaskiya ba zan iya zuba ido, duk aikin da na yi tuƙuru, kuma ace ba zan mori wahalata ba, ba fa zai yiwu na zama a ƙarƙashin maƙiyana ba"
Yayi murmushi ya ce "Bar ganin mu na kauce hanya, akwai abin da bamu isa mu yi wani abu a kai ba, ko kuma mu canza ba, ke za ki yi duk iya ƙoƙarin da za ki yi, sai mu ga ta ɓangarenmu me za mu iya yi. Amma taurarinta su na da haske sosai, duk wanda ya raɓe ta, za ta iya haska na su tauraron"
Guntun tsaki matar ta ja, ta ce "Ka ga duba mini wani abun, ka bar maganar nan kawai"
Can gida babu wanda ya matsa Nana ta fito ta yi aikin gida, ita ma kuma ba ta yi ba. Sai dai abin da ya ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta ji Baba su na magana da Mama da Gaddafi ba, wai akwai wani mai magani a tsanyawa, idan aljanu suka gagara, har kwantar da mutane yake yi, a tafi a bar shi, sai ya warke ya sallame shi. Babu tunanin komai ta ji Baba ya amince, za a kaita. Rasa abin yi ya sanyata fashewa da kuka.
Sallamar Jamila ce ta sanya ta goge hawayenta.
"Nana ya jikin?"
"Da sauƙi" ta amsa a hankali.
"Ungo wannan naki ne" tayi maganar tana miƙa mata leda.
Ba ta karɓa ba ta ce "Mene ne wannan?"
Jamila ta gyara zama ta ce "Kin tuna ranar da ki ka je kira na, a gidan maman khairat" Nana ta jinjina kai, ba tare da ta yi magana ba.
"Kin tuna matar nan da ki ka gaisar a falo"
"Na tuna"
"To ita ce ta ce a baki, atamfa ce da turaruka, kin san 'yar kasuwa ce"
"Meyasa za ta bani, ta sanni ne?"
Jamila ta ce "A'a ranar da ki ka je ne, ta ga duk kin rikice da kuka gaisa, bayan kin tafi ta tambaye ni ko ta yi miki wani abin ne; na ce mata a'a baki da lafiya ne, shi ne ki ka bata tausayi".
Ita dai Nana ta yi ƙuri da ido, tana kallon Jamila. "Nana ki karɓa mana, ba a mayar da hannun kyauta baya" ta saka hannu ta karɓa ta ce "To na gode sosai" ba dan ta so ta karɓa ɗin ba, ita abubuwan da suka dame ta a yanzu, sun hanata jin daɗin komai na duniya yanzu. Ji take yi tamkar ta kashe kanta ta huta kawai.
Kullum cikin addu'a take, babu dare, babu rana, akan Ubangiji Allah ya bata lafiya, sai dai haryanzu Allah bai karɓa mata ba. Wasu lokutan har shagala take da roƙo lahirarta, saboda yadda take fatan lafiya ido rufe, sai dai idan ta tuna ta yi ta istigfari.
*****
Ranar laraba, ta shirya ta tafi makarantar da take koyarwa, sai dai zuwanta ke da wuya, aka sanar mata da director yana son ganinta.
Ta san a rina, dan haka ta tsananta addu'a, ta nufi ofishin nasa.
Ta tarar da shi tare da wani babban mutum, zaune kirim a kan kujera. Ta gaida mutumin ba tare da ta kalle shi ba, ba kuma ta jira ya amsa ba, ta gaida director.
Ɗan ƙaramin yaron da yake zaune a jikin mutumin, ya saukko daga jikinsa, cikin gwarancin yara, ya nufo Nana yana faɗin "Anti Nana" ɗagowa ta yi tana murmushi, dan gaba ɗaya da ta shigo, hankalinta ba a jikinta yake ba, dan haka ba ta lura da yaron ba ma. Ta buɗe hannayenta ta rungume shi.
Director ya ce "Kin ga wannan shaƙuwar taki, da yaran nan ne, ya sanya haryanzu ban sallame ki ba daga makarantar nan. Babu wadda take iya ɗaukar rigimarsu kamar ki, amma ki na ta wasa da damarki. Kwata-kwata yaushe aka dawo makarantar da har za ki yi fashin kwana biyu, ba tare da kin sanar da hukumar makaranta ba?"
Cikin nutsuwarta da kamala ta ce "Dan Allah sir ka yi haƙuri, ba ni da lafiya ne, ba a son raina na yi fashi ba"
A ƙule ya ce "Wai wace irin rashin lafiya ce haka, da kullum ba ki da lafiya, idan ba zaki iya ba, ki ajiye aikin mana dole ne?"
Mutumin da yake zaune ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ayi mata uzuri musamman duba da yaranmu suke ƙaunarta. Ka ga ba zuwa makarantar nan nake yi ba, na fi shekara rabon da na zo, amma na san Anty Nana a bakin Muhsin, duk abin da yake yi, idan aka ce za a gaya mata sai ya daina. Ina nema mata afuwa dan Allah"
Director ya ce "Alhaji ba zaka gane ciwon kan da yarinyar nan take bamu ba. She's very hardworking lady, yarinya ce mai ƙoƙari da juriya, amma wannan fashin nata, kullum cikin ciwo shi ne yake ɓata mini rai wallahi"
Mutumin ya kalli Nana ya ce "Anty mene ne rashin lafiyar taki ne?" Nana tayi shiru ta rasa abin cewa. Bai damu ya sake tambayarta ba ya ce "Kuma ki na zuwa asibiti?" Ta jinjina kai alamar eh.
"Allah ya sarki, to Allah ya baki lafiya yanzu dai ki tashi ki je, na roƙa miki afuwa " Nana ta sake risunawa cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Director ya ce "Tashi ki tafi" ta tashi jiki a sanyaye, hannunta riƙw da na Muhsin, da bakinsa yaƙi rufuwa yana ɗagawa babansa hannu.
Duk da ranta ba ya son faɗan da ake yi mata, yanzun ma ba ta ji daɗin faɗan ba, amma da tuna laifinta ne, haka nan ta haƙura, ta danne damuwarta ta shiga cikin ɗalibanta, tare da ƙoƙarin samarwa kanta nishaɗi da nutsuwa tare da yaran.
Amma sai ya zamana yaƙe kawai take yi, ƙasan zuciyarta tamkar ta fasa ihu, ga batun kaita gidan mai magani, duk da ba a kuma zancen ba, ga kuma maganar Saleh, ga malam Auwal ya juya mata baya baki ɗaya.
Da ta dawo daga makaranta, ta yi sa'a, ta tarar da wata guntuwar shinkafa, an ajiye mata, sai dai ko maggi babu, ta barbaɗa gishiri, ta ci ta tafi islamiyya.
Duk da ta san tayi sammako da yawa, hakan bai dame ta ba, saboda zaman gidan na su ne ba ta so, bata ƙaunar duk wani abu da zai ƙara dagula mata lissafi.
Kamar yadda ta saba, ta share duk wuraren da taga zata iya sharewa, ta shiga wurin ajiye tabarmi, ta hangi Auwal a cikin ofishin malamai, yana duba wasu litattafai. Ɗauke kanta ta yi, kamar ba ta ganshi ba, ta shiga ta ɗaukko tabarmar 'yan ajinsu, ta fito.
Ba ta sanya ran zai kula ta ba, dan sati guda kenan, ko gaishe shi ta yi, sama-sama yake amsawa.
"Nana" ya kira sunanta ba tare da tayi tsammanin haka ba, ta waiwaya tare da tunanin ko ba shi ba ne ya kirata. Amma ta ga yana kallonta, tabbacin shi ne yake kiranta. Sharewa tayi, ta fice ta tafi ajinsu.
Tana tsaka da shimfiɗar tabarmin ya shigo ajin, ya ce "Nana, ki na ji ina kiran ki ki ka yi share ni, Yaushe ki ka zama haka?" Ta miƙe sosai tana kallonsa, ta haɗiye wani abu mai ɗaci da ya tsaya mata a maƙogwaronta.
"Me yasa ba ka yi wa baba bayani ba, kuma ka hanani na yi masa; cewar kai malamina ne ba wanda yake so na da aure ba? Dama ka ce tausayina ka ke ji, ni kuma kasancewar wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa kamawa zai yi, na kawar da tunanin komai, na fara sonka ina tunanin ko yaya zan samu afuwa. Amma sai halayenka suka sha banban da abin da ka ke koya mana. Ina ma baka ce ana so na ba, na ci gaba da kallonka a matsayin malamina mai tausayina.
Jiki a sanyaye cike da borin kunya ya ce "Ki yi haƙuri Nana, na san ban kyauta miki ba, babu yadda zan yi ne, matsala aka samu, na rasa ta yadda zan yi miki bayani. Ina ta ƙoƙarin shawo kan matsalar ne, amma ban ce ina sonki dan na yaudareki ba, ko na yi wa mahaifinki wasa da hankali ba".
Shiru ta yi masa, ta ci gaba da gyara tabarmin, dan ba ta ma san meyakamata ta sake ce masa ba.
"Nana, ki ɗan bani lokaci kaɗan, ina daf da shawo kan matsalar"
"Tom" ta faɗa a taƙaice, ba tare da ta ko kalle shi ba. Bai taɓa zaton Nana tana fushi har haka ba.
Ya kalli yadda take ta jan tabarmin, ba tare da wani dalili ba, ya durƙusa a kusa da ita ya ce "Kalli ki ga" ta ɗaga kai ta kalle shi.
"Tabarmar ta shimfiɗu haka, ba ita ta yi miki laifin ba, ni ne amma ki yi haƙuri"
Ta kalle shi da idanunta, masu kama da za ta yi kuka, har za ta yi magana, sai kuma ta haɗiye ta fasa.
"Kin haƙura?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa shi ma.
Murmushi ta yi, ba tare da ta shiryawa hakan ba.
Shi ma murmushin yayi mata ya ce "Barakallahu fik, ki ci gaba da yi mana addu'a, in sha Allah komai zai daidaita amaryata".
Sunkuyar da kai ta yi, bakinta ya kasa rufuwa saboda murmushi.
"Ya jikinki, ina fatan ki na kula da duk adduo'in da nake baki"
Ta jinjina kai ta ce "Eh, ina yi"
"Yauwwa ki ci gaba da kula, Ubangiji Allah ya baki ingantacciyar lafiya"
"Amin na gode sosai" ya fice bar ajin.
A hankali ta ji zuciyarta ta yi sanyi, daga zunzurutun damuwar da take ciki.
Aka yi karatun Alqur'ani da ita lafiya ƙalau,