BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   4 / 64

9K to 12K   out of 190K words

amsa mata.

"Nasiru wai ba kowa a gidan ne, dan Allah ku buɗe mini ƙofa, ban yi salla ba"

Nasiru ne ya leƙo daga soro, ta jiyo muryar Mama daga ɗaki tana faɗin "Kai Nasiru ba ka na leƙowa ba, wallahi ka buɗe mata sai na ci ubanka"

Nasiru ya ce "Mama wallahi ta dawo daidai, ba ki ji tana maganarta normal ba"

"Wallahi ba zaka buɗe ta tana wannan tamɓmelen ba"

A raunane Nana ta ce "Dan Allah mama salla zan yi fa" banza ta yi mata, Nana ta gaji ta koma ta nemi wuri ta zauna, ta na tuna mafarkin da ta yi.

Sallamar baba ta ji a tsakar gida, da alama shi da wasu ne, saboda ba muryarsa kawai ta ji ba.

"Ga ɗakin nan malam, wallahi bamu yi bacci ba, daga mu har maƙwabata, kwana ta yi tana iface-iface, dan kawai na yi mata faɗa kafin ta kwanta, da 'yan shekarun nan, abin nata ya lafa, amma kwanan nan, abin ya dawo tuburan dan kwananta biyu ma, bamu san in da ta tafi ba"

"Kar ka damu, in sha Allah koma menene a jikinta, yau sai ya fita"

Ita dai Nana ta zubawa ƙofa ido, tana jiran abin da zai faru.

Aka buɗe ƙofar, ta ga Baba da wani malamin makarantar allo, da garadan almajirai mutum uku, da wata irin zabgegiyar bulala a hannun malamin, ba shiri ta miƙe tsaye tana zazzare ido ta fara ja da baya.

Malamin ya kalli Nana ya ce "Zaka gane kurenka munafuki, yau sai ka fita daga jikinta, ya tunkaro Nana da wannan zabgegiyar bulala.

A gigice ta ce "Baba, dan Allah lafiyata ƙalau dan Allah kar ka bari ya dake ni, wallahi ni ba aljani ba ce."

Ayshercool
08081012143
BUZU

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)


P4



Baba ya tsaya daga bakin ƙofa, yana leƙowa.

Kuka Nana ta fara yi, tana "Dan Allah kar ka dake ni, wallahi  a hayyacina nake nice"

"Ƙarya ka ke yi, babu irin aljanin da ban yi karo da shi ba, duk wani siddabarunku na sani" yayi maganar yana riƙe kan Nana, ya fara tofa mata ayoyin Alkur'ani.

Nana ta rasa me yakamata ta yi, ita dai ta san a hayyacinta take, ba ta da zaɓin da ya wuce, ta nutsu ta yi shiru, kar ta yi wani abu, ace aljanin ne. Sai dai jikinta yana ta tsuma, dan tsoron kar malam ya dake ta da bulalar nan.
Sai dai ba ta tsira ba, babu tsammani ya zuba mata bulalar nan a jikinta, sai da ta gantsare ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta zube a ƙasa ta gigice. Yana karanta mata Alqur'ani ya ƙara zuba mata bulalar nan tamkar ta dukan doki.

Ta yinƙura zata gudu, gardi ɗaya ya danƙo ta yayi ciki da ita, suka kewaye ta su na yi mata karatu, malam yana zuba mata bulala yana cewa "Zaka yi magana ko ba zaka yi ba?"

Cikin kuka da ƙaraji ta ce "Ni ba aljani ba ce ba, nice a hayyacina nake, Baba dan Allah ka taimake ni ka ce ya daina duka na" sai jikin Baba yayi sanyi ya ce "Malam ɗayyabu, ba za ayi karatun nan babu duka ba, na ga kamar ita ake duka"

Malam ɗayyabu ya ce "A'a kar ka damu, ka yi haƙuri ka je ka jira mu a waje, ai wannan aikina ne, ba ita ake duka ba, ka jira mu mu gama" ganin Baba zai tafi ya bar ta a cikin maza daga ita sai su, ya sanya ta ƙara fashewa da kuka, ga raɗaɗin bulala da fatarta take yi.

Tana ji tana gani, malam ya saka almajiransa, suka rirriƙe ta, suna yi mata karatu, malam yana shafa mata man gelo a fuska, yana zuba mata wani ruwa a jikinta, ga kuma bulalar da yake ta zuba mata tana ihu. Babban abin da ya ɗaga mata hankali, bai wuce yadda a wayance ɗaya daga cikin yaran malam, yake goga mata jikinsa yana naniƙar ta ba, kuma yana sane.

Tun tana kuka muryar ta na fita, sai da ta yi laƙwas ta kasa motsi gaba ɗaya, kukan ma ta kasa sai ajiyar zuciya da take saukewa, ji take da da makami a kusa da ita, sai ta illata wanda yayi mata rashin ɗa'ar nan, sai ta daina jin zafin bulalar, sai na baƙin cikin tozartar da ta yi.
A banza wanda ba muharramanta ba sun daddaneta, babu ladduban ruƙiyya babu komai.

Malam Ɗayyabu ya ce "Ina ga aljanin ya tafi, duk na ga gardamamme ne, bai yi magana ba, amma ya kau. Ku tashi muje zan bawa babanta magungunan da zata din ga yi"

Nana tana daga kwance tana ji suka fita, hannayenta da suka banƙare suka riƙe kamar ba a jikinta suke ba, ga fatarta kamar an sakata a cikin wuta saboda raɗaɗi.

Ta jima a kwance tana numfarfashi, daga baya ta ja jikinta a hankali, ta fita tsakar gida ta yi alwala, ta idar kenan Baba ya shigo da ƙullin baƙar leda a hannunsa, ya ce "Kin farfaɗo kenan?" Ta ɗaga kai ta kalli Baba, ta mayar da kanta ta sunkuyar, wani mugun haushin Baban ya kamata, ba ta ce masa uffan ba, ta shiga ɗakinsu.

Tana kallon suwaiba tana raɓe raɓe, za ta shigo ɗakin, ba ta kula ta ba ta tayar da salla. Da ƙyar ta yi sallar, ga yunwa ga zafin duka.

Ta zame rigar jikinta, tana haska jikin nata da mudubi, wani wurin har jini ne ya fita, ita kanta ta san ba ƙaramin dakuwa ta yi ba, a take wasu hawayen suka ci gaba da zubo mata. Hankalinta ya kai kan raunin da yake wuyanta, ta shafa wurin ta yi shiru tana tuna mafarkinta da tayi jiya.

Jamila ta shigo ɗakin da sallama, Nana ta amsa a hankali. Cikin tausayawa ta ce "Sannu Nana, subhnallah haka duk suka ji miki ciwo?" Tayi maganar cikin tausayawa, ganin yadda fatarta tayi ruɗu-ruɗu.

Ga buredi da ƙosai ki samu ki karya. Sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta karɓa ta ce "Na gode sosai"

Tuni masu aiki suka fara aikin gyaran gidan su Nana.

Jamila na shirin fita, mama ta tsare ta a ɗaki ta ce "Ke magana nake son mu yi da ke"

"To mama, ina jinki"

"Gidan maman khairat ɗin za ki tafi?"

Jamila ta jinjina kai ta ce "Eh mana, idan ban je ba me zamu samu mu ci?"

Mama ta gyara zamanta ta ce "Zuwa la'asar ki dawo, kin san ba a bori da sanyin jiki, duk da tana yi miki alheri, matar nan tana ƙaunar ki, amma dole mu bi ta wurin malamai, a ƙara yi mana aiki a kanta, yadda zata ƙara sakar mana hannu, ai ni tarewar matar nan alkhairi ne a gare mu" Jamila ta ce "To mama, duk yadda ki ka ce, amma duk da haka ai tana yi mini ƙoƙari sosai fa, kalli abubuwan da take yi mana"

"Ke dalla can ba a zama haka, idan ta kama mijinta ma, ba sai a shiga a fita, ayi wadda za ayi ba"

Jamila ta ce "Ahh haba mama, banda auren mijinta, butulci kenan ai"

"To na ji, ita ɗin dai a ƙara mallake mana ita, ta ƙara sakar mana hannu, daga ita har mijin nata"

Jamila ta gyara zaman gyalenta, ta ce "Shikenan, sai na dawo"

"To Allah ya tsare yarinyar kirki, duk abin da ki ka ci dai ki tuna da ni, Allah ya yi albarka"

"Amin" Jamila ta amsa ta nufi hanyar ficewa.

Haka Suwaiba ma ta shirya, tana ta baza ƙamshi, cikin matsatsun kaya ta fice.

Nana ta ɗan girgiza kai, su waɗanda suke shigar banza, su wuni jin kaɗe-kaɗe, ba Qur'ani ba azkar, aljanu ba su bi su sun takura musu ba, sai ita da take ƙoƙarin killace jikinta da ƙoƙarin yin addu'oi. Saurin katse tunanin ta yi, ta fara istigfari.

Ta lallaɓa jikinta ta fita tsakar gida, ta fara kaye-kaye, ta tattara kwanukan wanke-wanke, ta koma gefe dan ta wanke. Dan bayan da larurar nan ta waiwayota a 'yan kwanakin nan, su na tsoron taɓa ta, da akan wanke-wanke sai a ci mata mutunci, har ma a haɗata da Baba ya yi mata nasa cin zarafin.
Kafin yamma tuni an gama da gyaran katangar gidan su Nana, har ma an ci ƙarfin aikin, gyaran masan gidan da na rijiya, mama sai alfahari take tana hura hancin albarkacin 'yarta aka ci, aka yi wannan gyaran, dan da ta malalacin mai gidan ne, sai dai a zauna a haka.

*****
"Wata guda kenan, haryanzu shiru babu wani labari, an yi addu'ar, an yi duk abin da yakamata, amma haryanzu babu wani ƙwaƙwƙwaran labari a kan ina ya tafi. Kuma babu wata shaida ko alama, ko saƙo da zai bayar da damar gano in da yake. Amma kai a naka binciken me ka gano?"

Mutumin ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ni abin da na gani, ya yi nesa da gida sosai ma, yana kudu da nahiyar nan ma"

Matar ta dubi mutumin cikin rashin fahimta ta ce "Me ka ke nufi?"

"Ina nufin, koma a ina yake ya riga yayi nesa da gida sosai da sosai"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu mene ne abin yi? Ina mamakin dalilin da zai sanya, ya yi wannan shirmen, kawai ya tafi ya bar gida ba sanarwa ba komai?"

Mutumin ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Allah masani"

"To kai yanzu mene ne abin yi, dole dole ana buƙatar sa a gida, a wannan ƙadamin da ake ciki, banda tsabar wulaƙanci da baƙin ciki, kawai sai ya kama ya bar gida? Kawai ayi masa kiranye ko gidan uban wa ya je ya dawo"

Da sauri ya ce "A'a, na so na bayar da wannan shawarar, amma na duba na ga akwai matsala idan aka yi masa kiranye za a samu matsala, idan bai dawo ba zai yi hauka tuburan, abin da yafi dai ayi tunanin wata mafitar"

Tayi shiru tana tunani, daga bisani ta numfasa ta ce "Shikenan babu laifi, zaka iya tafiya " ya jinjina kai ya tashi ya fice.

*****

Tun da Baba ya yarfa Nana, a wurin malam Auwal, take matuƙar jin nauyinsa, shi kuwa har cikin zuciyarsa ya ji ya aminta da abin da baba ya faɗa.

Yana zaune a ofishin malamai, yana marking wani assignment da ya bayar, ya hango Nana ta shigo makaranta a makare, ya zuba ido ya ga wani mataki malam Nura zai ɗauka.
Ya tattara hankalinsa a kansu, baya son a daki Nana, duk da ya san duk makarantar babu wanda bai san matsalarta ba. Tayi wiƙi wiƙi da ido, tana tsoron kar malam Nura ya daketa.

Cikin ikon Allah, sai bai daketa ba, ya sanya ta ɗebo ruwa a rijiya ta zuzzuba a butocin alwala.

Yayi ajiyar zuciya, ya ci gaba da makin ɗin sa, kawai zuciyarsa ta raya masa, idan kuma wani abu ya sameta a gaban rijiyar fa? Ba shiri ya tashi da hanzari ya tafi.
Tana gaban rijiyar tana jan ruwa, yayi gyaran murya.

Tana waiwayawa, ta ganshi, risunawa tayi tana gaishe shi, bai amsa ba, ya ƙarasa ya ce "Bani gugan ki tafi aji" ta zaro ido ta ce "Ya sayyadi Nura ne ya....

"Ni kuma na ce ki kawo ki taf...

A ɗan raunane ta ce "Ya sa...

Auwal ya ce "Za ki bani, ko sai na jefa ki a rijiyar" murmushi ta yi, tana kallon rijiyar ta ce "To bari na janyo gugan" tayo maganar tana janyo gugan daga rijiya.

Ta juye ruwan, ta ajiye zata tafi ya ce "Nana" ta tsaya cak ta ce "Na'am" ya ce "Ya jikinki kuwa?"

Take annurin fuskarta ya ɗauke, ta ce "Na ji sauƙi"

Auwal ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya ɗorar da lafiya, ki ci gaba da addu'a da azkar ɗinki" ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah"

"Amm goge wannan abin na bakinki, sai ki tafi aji" kallonsa tayi, man leɓe ne kawai a bakinta, ba jambaki ba, shi aka hana sakawa.

Ba tayi musu ba, ta goge. "Maza jeki, anjima zan zo gida in sha Allah" ji ta yi gabanta ya faɗi, amma ta kasa magana, ta ja ƙafafuwanta a hankali ta tafi aji.

Auwal su na gaban su Nana sosai, lokacin da take yarinya sosai suka yi sauka, bayan sun yi sauka ya ci gaba da koyarwa, ko da ya tafi karatu ya dawo, ya ɗora da koyarwar a islamiyyar.

Tunani take yi, kar dai malam Auwal, da gaske ya yadda da abin da Baba ya gaya masa.

Ganin yau tana cikin hayyacinta, ya sanya 'yan ajinsu, suka sake da ita, tare suka zauna da ƙawarta Amira, a wuri ɗaya suka ɗauki karatu.

Amira ta so tambayar Nana, ina ta tafi aka yi ta nemanta, amma ta fasa, saboda kar ta tsokanota ta burkice.

Duk damuwar da Nana take ciki, da zarar ta fito makaranta, aka yi karatu, ta haɗu da ƙawayenta, sai damuwar ta ragu, sai ta kamo hanyar gida tukuna. Sai dai tana jin babu daɗi yadda wasu lokutan ƙawayen nata, suke gudunta, saboda larurarta.

*****

"Yanzu kai Habu yaya zamu yi da wannan mutumin, kana ganin mutum kamar katako, baya gane komai, ni anya ma ba hauka ne yake damunsa ba?"

Habu ya ce "Ashsha! Na gaya maka ɗan uwana ne, ba shi da cikakkiyar lafiya ne, magani nake nema masa, da ya warke shikenan"

"Ikon Allah, Allah ya bashi lafiya, ga mutum har mutum a haka, amma ba ya gane komai, Allah ya bashi lafiya"

Habu ya amsa da Amin, tare da kallon wurin da wanda suke maganar a kansa yake.

Yana ta wasa da zobunan hannunsa, manya manyan azurfa, da kuma tagulla.

A hankali ya saka hannunsa ya ɗago layar da take wuyansa, wadda ta sauka a cikinsa. Ya zuba mata ido yana jujjuyata. Cikin hanzari Habu ya matsa kusa da shi, ya ce "Ka gane mene ne wannan ɗin?" Ya ɗaga manyan idanunsa ya kalli Habu, amma bai yi magana ba.

"To ka tuna wani abu ne? Waye ya baka ita?" Bai yi magana ba, ya tattare ta, ya zura ta a cikin rigarsa, ya kawar da kansa gefe daga kallon in da Habu yake.

Habu yayi ajiyar zuciya, ƙasan zuciyar sa, yana fatan Allah ya taƙaita wannan al'amari, kamar kullum ƙara rikicewa yake yi, yanzu ba ya magana sai dole, kuma maganar ma galibi shirme ce kawai.

*****

Abin da Baba yayi, tamkar ya share wa Auwal hanya wurin bayyana wa Nana abin da yake zuciyarsa game da ita, sai dai jikinta yayi matuƙar sanyi, da ya ce mata ya daɗe yana tausayinta, hakan ya sanya take tambayar kanta anya so ne? Ko dai tausayin ne kawai, duk da ya daɗe yana nuna mata alamun so. Gefe ga tsoro da fargabar abin da zai biyo baya yana damunta, dan kullum ta kwanta sai ta yi mummunan mafarki a kan malam Auwal, abubuwa na tashin hankali sun faru da shi.

Ajiyar zuciya tayi, bayan kwashe dogon lokaci malam Auwal, na ta yi mata bayani, ba tare da ta ce "Uffan ba"

"Nana" ya kira sunanta a hankali.

"Na'am" ta amsa tana sake sunkuyar da kanta ƙasa.

Ya ɗan marairaice ya ce "Ina ta zuba nikaɗai, ki ce wani abu mana"

Har yanzun dai ba ta yi magana ba, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji, banbarakwai take jin abin, wai yau malaminta ne kuma yake sonta, yake ta tsarata da kalamai na soyayya.
Jin taƙi magana, ya sanya ya canza akalar hirar, zuwa ta karatu sai a lokacin ta saki jiki, tana amsa masa.

Bai wani daɗe ba, ya ce "Bari na tafi, tun da dai ba za a kula ni ba, amma ki sani duk lokacin da na zo wurinki, a matsayin Muhammad Auwal na zo, ba ya sayyadinki ba" murmushi ta yi, ta cigaba da sunkuyar da kai.

"Ungo saka mini lambar wayarki"

Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ni da waya"

"Haba dai? Ke haryanzu baki girma ba kenan, to shikkenan za'a nemo waya in sha Allah, ki gaida Baba, ki sanar masa ina nan tafe, za a zo ayi magana in sha Allah" shiru Nana tayi, ba ta yi murna ba, ba ta ji haushi ba, dan ita ba ma ta tantance tana son sa ko a a ba, ita dai ta san ba dan tana jin tsoron abin da ka iya faruwa ba, da ta so ya aureta, tana matuƙar ƙaunar muryar malam Auwal mussaman idan yana karatun Alqur'ani.

"Sai da safe, ki shiga gida, ki yi ta addu'a, idan kin yi azkar ɗin kwanciya bacci, ki yi ta nanata *Wa hifzan min kulli shaɗanin marid*"

A hankali ta ce "In sha Allah, na gode sosai"

Ya ce "Yauwwa ungo wann, kya sai farar ƙasa, dan naga yadda ki ke shanta a makaranta"  yayi maganar yana miƙa mata kuɗi.

Ta ɗan kalle shi ta ce "Ya sayyadi ni ɗin?"

"Au ƙarya na yi? Ba kya sha ne?"

"Ina sha amma kaɗan" ta faɗa tana mamakin yadda saka mata idon da yake yi, har ya gane tana shan farar ƙasa.

"Karɓi mana" yayi maganar yana sake miƙa mata.

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka bar shi, na gode"

Haɗe rai yayi ya ce "Bana son jayayya, karɓi" jikinta na ɗan rawa ta haɗa hannayenta biyu, ta risuna ta karɓa ta ce "Na gode sosai, Allah ya ƙara buɗi"

"Amin, shiga gida ina kallon ki" ta juya ta shiga gida, sannan ya juya ya tafi.

ta juya a hankali ta shiga cikin gida tana murmushi.
Abin har mamaki yake bata, wai ya sayyadi Auwal ne yake sonta, ganin abin take kamar almara.
Duk da damuwar, abin da take fargabar faruwarsa, na ci gaba da addabar zuciyarta, amma wani sashin na zuciyarta, na kwantar mata da hankali, saboda a ganinta malam Auwal masanin addini ne, mai riƙo da addini dan haka babu abin da zai faru da shi.

Tana sallama Baba ya tsare ta, ya ce "Yauwwa dama ke nake jira, tuntuni"

Ta tsaya, tana sauraron abun da Baba zai ce.

"Yaya maganar turowar? Ni fa ba na son a tsaya a ɓata lokaci a waje ana shashancin nan, ya kawo abin da Allah ya sa yake da shi, a ɗaura auren nan ki tafi, ko a rage mini wata wahalar" A yanzu dai Nana ba zata iya tuna, rabon da Baba ya mora mata wani abu ba, amma da an motsa sai ya yi ta mitar wahala ta yi masa yawa.

Ta numfasa ta ce "Ya ce na ce maka, ka yi haƙuri, yana kan tattaunawa da magabatansa ne, in sha Allah za su zo"

"Yauwwa ya dai fi. Na ce babu abin da ya baki ne? ƙanen ki sai kuka suke yi, sun ci abinci amma ba su ƙoshi ba, dama wanda Jamila ta zo da shi ne, suka

4 / 64