BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   63 / 64

186K to 189K   out of 190K words

na hagu, ta fara iƙama, sai dai ta kakare, bayan shaƙar da ya yi wa wuyanta.

Ya miƙe ya danne ta a kan katifar, ta kasa addu'a, ta fara kiciniyar ƙwacewa, cike da tsoron kar ta yi wani abu, da zai sanya mutanen gidan su ji, su zo su tarar da su a wannan yanayin. Gaba ɗaya ya rikiɗe mata, zuwa wannan tsohon cikin mummunar siffa, har dogon farin gemun sa, yana taɓa fuskarta, ga numfashinta tana jin zai bar gangar jikinta.

A kan wani tsauni ta ganta, ta yinƙura da ƙyar, ta ja jikinta saboda azabar sanyin da take ji. Wuyanta sai raɗaɗi da zafin shaƙar da ya yi mata, ne yake damunta.
Babu tsammani ta ga tsohon nan, a tsaye yana kallon ta.

"A'uzubikalimatillahi tammat" ta furta tana ja da baya. Ya ɗan ja da baya, yana ci gaba da kallon ta.

"Me na yi maka ne? Laifin me na yi maka da na cancanci haka?"

"Ba ki yi mini laifin komai ba, hasali ma waɗanda suka yi mini laifin, ba sa Duniya amma ba zan taɓa hucewa ba, sai na hukunta su ta hanyar tarwatsa zuriyar su, da gadar da azaba da wahala ga duk wanda ya fito daga cikin zuriyar su. Na zaɓi na azabtar da ke fiye da kowa, saboda hakan ne zai sanya na ƙuntatawa Ƙaisar, da ya fifita bil'adam a kaina. Zan ci gaba da addabawa rayuwar ki, sai na sabauta ku a ƙarshe na sanya mijinki ya yi ajalinki. Ban taɓa alfahari da yi wa biladama wani aiki ba, kamar aikin da na yi a kan Buzun nan saboda a dalilinsa ya sake sada ni da abokan gaba na, kuma ba zan gushe ba sai na ɗauki mummunar fansar da sai na bar muku mummunan tabo a zuriyar ku"

"To idan mu zuriyarmu sun yi maka laifi, shi kuma mijina me ya yi maka?"

Ya tako ya ƙaraso gaban Nana ya durƙusa, ta din ga ƙoƙarin yin addu'a, amma ta kasa. Ya buɗe bakinsa, tana iya hango cikin bakinsa, yadda wani irin baƙin hayaƙi, ke ƙoƙarin fitowa daga bakin nasa, sai dai kan ya yi wani abu, ta ga ya ɓace.

Ta motsa a hankali ta kalli Sayyid a can gefe, ya takure yana bacci. Ta matsa ku sa da shi, ta ji jikinsa ya saki babu zazzaɓin. Sai dai wani irin bacci yake yi,rabin idonsa a buɗe, ƙwayar idanunsa baƙar ta ɗauke sai farar. Ga alamar yana numfashi. Ta ɗauki bargo ta lulluɓe shi. Ta kunna karatun Alkur'ani a waya ta ajiye a gefe.

Ta ja ta zauna ta yi shiru, abin duniya ya ishe ta, sai kuma ta koma tunani kamar yanzu ta yi rauni a ibada, shaiɗan ya yi galaba a kanta, kan cewar idan ta yi addu'a wahala ta fi tsananta a gare ta. Domin hatta addu'a kwanciya bacci, ranar da ba ta yi ba, sai ta kwanta ta tashi lafiya ƙalau, ba mafarkai babu ciwon ƙafa ko baya, ko ma jikin baki ɗaya. Azkar ma ba ko yaushe take iya yi safe da yamma ba.

Ta yinƙura ta tashi, ta je ta ɗauro alwala, ta zo ta sake haska shi, ta ga bacci yake yi, ta nemi guri ta kwanta, ta ɗora hannunta a goshinsa, tana karanto addu'oin kwanciya bacci.

*****

Jamila na miƙe a kan katafaren gadon, ga chips a gaban ta, ga kakkauran shayi, hannunta riƙe da zuƙeƙiyar wayarta.

Abba ne ɗan gidan Hajiya Sa'a, yake yi mata magana ta what's app. "Ƙanwata, shi ne tun da ku ka sauka, ba ki neme ni ba ko?"

"Ba haka ba ne, ba ni da data ne"

"Kuma ba ki gaya mini ba, bari na saka miki. Ina Mummy?"

"Ta fita"

"Wai ina ku ka je ne a Abujan?"

Jamila ta yi masa reply da "Ban san sunan gurin ba, wani gida ne dai mai kyau sosai"

"Ok, to dan Allah ki kula da kan ki sosai da sosai, Allah ya bayar da nasarar abin da aka je nema, na ji ta ce taron kasuwanci ne ko?"

"Wallahi dai ban sani ba tukuna"

"Haka ta ce mini ni, ta tafi da ke ku ka bar ni a gida, ai shikenan" har za ta rufe data ta ga 10gb na data. Sai ta washe baki ta ce "Har 10gb na gode sosai da sosai"

Abba ya ce "Babu godiya tsakanin, Yaya da ƙanwarsa, ki kwanta da wuri ki yi bacci. Ki yi addu'a kuma, sai da safe"

"To yayana na gode sosai da sosai" suka yi sallama, ta rufe laste seen ɗin ta da online, ta tafi kallon videos a tiktok.

Hajiya Amina ce ta shigo ɗakin, ta ce "Jamila ba ki yi bacci ba?"

"Eh Mummy, kin dawo?"

"Eh zan sake zuwa wani gurin ne, babu lallai na dawo da wuri, za mu yi meeting, ki yi kwanciyar ki"

"To shikenan, sai kin dawo"

"Yauwwa amma ba kya buƙatar wani abu, ko jin yunwa ko?"

Ta ce "A'a a ƙoshe nake"

"To sai na dawo" Hajiya Sa'a ta fice, ta rufe wa Jamila ƙofar.

****

Nasiru tun ranar da ya je gidan Ummi, su Nana suka tashi, ya koma gida ya ba wa Baba labari. Baba ya ce "To shikenan ma, ta kwana gidan sauƙi, tun da sun samu mafita.
Ni na san babu yadda za'a yi ma a kore su haka kurum, dan mijinta ba shi da lafiya akwai dai abin da suka aikata.

"Dama wasu Buzaye abin yarda ne, kalli kayan da suka kawo mata fa, Allah ka dai ya san mugun abin da suke aikatawa, har aka kama su. Kai Nasiru to ya gidan da suka koma yake?" Cewar Mama cike da son jin ƙwaƙwaf.

Nasiru na tauna rake ya ce "Normal dai gida ne, amma da wasu a gidan, wancan gidan da suka baro ya fi. Ɗakinsu ya fi kyau da girma, banɗakin har da famfo ga wuta, wannan kuwa gaskiya bai yi kyau ba"

Ta sake cewa "Kuma da gaske mijin nata ba shi da lafiya?"

Ya ɗaga kai ya ce "Kai, sosai yana daurewa ne kawai, idan ya yi magana haki yake yi fa, wannan karon na ga ya yi magana sosai. Da an yi abu sai ya ce mata Rayuwata, ki yi a hankali ki zauna ki huta"

Sai ta sake zabura ta ce "Au rayuwata yake ce mata"

"Kai Mama dan Allah ki rabu da ni, haba wannan tambayoyin kamar a kabari"

"Kai a gidan uban wa ka san kabarin, sai ka yi saɓo tukuna" ya yi mata shiru, ya tashi ya ɗauki rakensa da yake sayarwa a ƙofar gida, da wuƙa ya fice.

*****
Tun da garin Allah ya waye, Nana take tashin sa, amma ya ƙi tashi, irin wannan baccin da ta farka ta ga yana yi dai shi yake yi.
Gaba ɗaya ta tsorata, ga dai numfashi yana yi, idan ta taɓa zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi jefi-jefi.
Ta saka shi a gaba, ta ma rasa abin da ya kamata ta yi. Ummi takira ta a waya, ta tambaye ta babu matsala babu wani abu da take buƙata, ta ce mata eh.
Har sha biyu na rana Nana ta rasa abin yi, ta kunna karatun Alƙur'ani a wayarta, ta ajiye masa sai dai bai fi mintuna talatin ba wayar ta ɗauke. Ji ta yi ana bubbuga ƙofar ɗakin nasu. Ta yinƙura ta tashi ta saka hijjabi, ta je ta buɗe.

Sajida ta gani a tsaye, ta ɗan saki fuskarta su ka gaisa. Sajida ta ce "Mun ji shiru ne, ko ƙofa ba ku buɗe ba, shi ne na ce bari na ƙwanƙwasa ko lafiya?"

Nana ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, ba ma jin daɗi ne daga ni har shi, shi yasa ba mu fito ba, amma lafiya ƙalau muke"

"Ok Allah sarki, ko dai amarya ce ne, haryanzu ba a gama cin amarci ba?" Ta yi maganar tana kallon Nana.

Nana kawai ta yi murmushi, ta koma ɗakin, ta buɗe ƙofar ta saki labule. Dama ta gyara komai a ɗakin. Ta dafa shayi da habbatussauda, da citt, kanumfari, kimba, na'ana'a kamar yadda yake dafawa, ta zuba a flask ta rasa me za ta dafa, dan ba ta son cin komai.

Tana nan zaune, sai ga 'yar gidan Ummi ta zo, Islam. Ta kawo wa Nana faten doya da wake, ya sha alayyahu. Ƙamshin attaruhun da ya daki hancin Nana, sai da ta haɗiye yawu. Ta ba wa yarinyar wayarta, ta miƙa mata caji.

Ta ɗan zuba abincin tana ci, ta zuba masa ido, tana tunanin ko Asibiti za ta nemo mota su tafi, amma kuma sai ta tuna abin da ya yi jiya ba shi da alaƙa da ciwon Asibiti.
Tana ta tunanin mene ne mafita, kuma ba ta son waɗannan maganannun matan, suk san halin da suke ciki ita da mijinta.
Tana nan zaune tana bin sa da kallo, ta jiyo hirar Sajida da Barira, da wasu maƙwabta. Barira ta ce "Sajida, jiya da daddare, kin ji kamar ana nishi cikin dare?"

Sajida ta ce "Wani irin nishi kuma? Ni ban ji ba"

"Wallahi nishi, kamar ana kokowa kamar wani gurnani, ga Amiru ya yi bacci, na din ga jin tsoro na kasa bacci, na ce ko gamo na yi da aljanu"

"Ba wasu aljanu, ba wani aljani da yake razana mutum, da wani sauti ko wani abu, duk ƙaryar banza ce"

"Kai ni dai na tsorata, kuma daga nan haka na din ga jiyo sautin, wajen nan" ta yi maganar tana nuna ɗakin Nana.

Sajida ta yi magana ƙasa-ƙasa, Nana ba ta ji me su ka ce, sai ji ta yi sun tuntsure da dariya. Ta yi ajiyar zuciya, ta fara tunanin ko dai wani gidan za su kama, ta san idan suka ci gaba da zama a gidan nan, asirin su na iya tonuwa, wanda ba za ta so hakan ba.

Babu tsammani ta ga ya tashi zaune, ta tashi da sauri ta nufe shi cikin kulawa ta ce "Sannu Sayyid, ka tashi?" Shiru ya yi yana bin ta da kallo, tamkar ya ga wata baƙuwar halitta daban.

"Sannu ya jikin naka?" Yanzun ma bai yi magana ba, ya ci gaba da bin ta da ido. Ta yi ta magana ya yi shiru, tamkar kurma. Can kuma ya tashi ya shiga banɗaki ya fito ya nemi guri ya zauna.

"Sayyid, za ka yi sallolin da ba ka yi ba, Asuba da kuma Azahar, duk ba ka yi ba" ya yi mata shiru, ya kawar da kansa gefe. Ta tsiyayo ruwan shayi a kofi, ta zo gabansa da cokali ta zauna ta ce "To ɗan sha tea ɗin, sai ka ci abinci ka yi sallar" ya kawar da kansa ya yi mata shiru. Ta ƙara matsawa kusa da shi, kawai ya hamɓare kofin ruwan zafin ya kware mata, a wuyanta zuwa jikinta. Wata irin zabura ta yi, ta ja da baya tana tsuma, saboda yadda zafin ya ratsa fatarta. Ko kallon inda take bai yi ba, ya ja gefe ya ci gaba da huci.

Ranta ya yi mummunan ɓaci, amma ta kalli fuskarsa, ta tabattar da yana hayyacinsa, babu yadda za a yi ya yi mata haka, dan haka ta yi shiru ba ta ce komai ba, ta tashi ta cire kayan, ta saka wasu.

Haka suka wuni a ɗakin, bai yi salla ba, bai ci abinci ba, kuma bai yi magana ba.
Ana yin sallar magariba, ya haura kan katifa ya kwanta.
A jikin mudubi ta tsaya, tana haska ƙirjinta, yadda inda ruwan zafin ya zuba a ƙirjinta, ya ɗuri ruwa.
Ta hasaka kan katifar, ta ga ya ci gaba da wannan baccin, mai rabin idonsa a buɗe, ta nemi guri a ƙasa lungun wardrobe ta kwanta. Sai dai yau ta kwanta cike da fargaba da kuma zullumin abin da zai faru, kar ta je ya sake shaƙe ta.
Sam ta kasa bacci, da ta fara sai ta razana ta buɗe idonta, dama a kunne ta bar fitila ba ta kashe ta ba.

****
Shukura ce tare da Sagir a zaune a cikin mota, ta zuba wa ƙofar gate ɗin Asibitin ido. Ya ce "Ya dai? Ki shiga ki fito ina nan ina jiran ki"

"Wallahi haka kurum gabana yake faɗuwa, ko hanyar Asibitin nan ba na son na ni an faɗi sunan ta"

"Shukura duk saboda da ɗan ki ya rasu, ban taɓa ganin mutum mara tawakkalli kamar ke ba"

"Ba haka ba ne, wallahi yanzu ma ban da Mummy ta matsa, ba zan zo ba, bari na je na dawo"

Sagir ya ce "Tom ki yi masa sannu, ni na zo na duba shi dama" ta jinjina kai ta fice daga motar.

Tana shiga cikin Asibitin, ta din ga jin kamar a lokacin ne, za a yi mata aiki a cire ɗan cikinta, wata irin fargaba da yanayi mara daɗi ta din ga ji a jikinta.

Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta, jiki babu ƙwari ta nufi ɗakin da Hajiya Amina ta kwatanta mata. Sai da ta yi knocking sannan ta tura ƙofar ta shiga. Fadila na zaune a gefen gadon kusa da Alhaji Fatuhu, ga cikinta ya yi wani irin girma, tamkar tana yinƙurawa ɗa zai faɗo. Sai dai gaban Shukura ya yi mummunar faɗuwa, ganin yadda Alhaji Fatuhu ya koma. Dogon mutum mai jiki, mai hasken fata, ya koma baƙi ƙirin ya yi wata irin mahaukaciyar rama, jikinsa tamkar fata kawai aka yafa wa ƙashi. Ta ji kanta ya sara, wani irin abu ya soki zuciyarta. Wani irin wari ɗakin yake yi, tamkar na mushe, ga shi dai babu ƙazanta a jikinsa, ga ɗakin a share a goge yana ƙamshin turaren wuta, amma ita warin mushe ta din ga ji, da ba ta san daga ina yake fitowa ba

Fadila tana yi mata sannu da zuwa, amma ba ta kula ba, ta ƙarasa kan gadon, ta zaune. Yana daga zaune, ya kalle ta ya yi murmushi tamkar mai raɗa ya ce "Shukura"

"Daddy, haka jikinka ya koma?" Ta yi maganar cikin matsanancin tashin hankali, da tuni hawaye ya wanke mata fuska.

Ya ce "Alhamdillah, ai na ji sauƙi ko Maman Muhsin?" Fadila ta jinjina kai hawaye na zubo wa daga idonta ita ma.

"An ce mini kin haihu ɗan ya rasu, ban zo na duba ki ba, na haɗu da wannan larurar"

Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri ban zo na duba ka a kan lokaci ba. Ban zaci abin ya kai har haka ba"

Ya yi murmushi yana jinjina kai, aka turo ƙofar ɗakin,gaba ɗaya suka waiwaya Doctor Sharif ne ya shigo, tare da wata nurse.

Yana ganin Shukura ya yi murmushi ya ce "Hajjaju kwana da yawa, ni da na yi zaton zuwa yanzu ma, kin dawo mana awo? Ya gida ya mai gidan?"

"Lafiya kalau" daga haka ta ja baki ta tsuke. Sai da ya sha jinin jikinsa, da irin amsawar da ta yi masa.

Ya kalli Fadila ya ce "Uwar biyu, ya mai jikin?"

Fadila ta ce "Alhamdillah mun gode Allah"

"Ma sha Allah. Na ce ki je a duba ki, idan inducing ɗin ki za a yi, idan ma tiyata ya kamata a yi miki to. Amma kin ƙi"

"Kar ki soma yarda, a kashe miki ɗa, gara ki je wani Asibitin" tsit suka yi baki ɗaya, suka waiwayo su na kallon ta.

Jikinsa ne ya yi wani irin sanyi, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa. Cikin damuwa ya ce "A kashe mata ɗa kuma Shukura"

"Nawa ba a hannunku ya rasu ba?"

"Kuma ai ba kya ce za a kashe mata ɗa ba, nakin ma, Allah ne ya kawo ajalinsa"

Shukura ta ce "Ba zan dai sake zuwa Asibitin nan na haihu ba. Daddy Allah ya ƙara afuwa. Maman Muhsin sai anjima Allah ya raba lafiya"

Fadila ta ce "Amin, mun gode sosai da sosai Shukura, ki gaida gida. Mummy ma an ce ta tafi Umara ko?"

"Eh wallahi. Allah ya raba lafiya" har Shukura ta fice, jikin Doctor Sharif tsuma yake yi, amma ya dake tare da ɓoye hakan.

*****

Jamila na tsaka da bacci, ta ji ana tashin ta. Ta buɗe idonta ta ga Hajiya Sa'a a tsaye amma fitilar ɗakin a kashe.

"Hajiya lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau, tashi ki saka wannan rigar mu tafi"

Cikin mamaki ta ce "Ina?"

"Ki saka sai mu je ki gani. Ki cire komai na jikinki ki saka ta"

Bakinta fal tambayoyi, amma babu damar yi. A duhun ta karɓi rigar ta saka, kanta babu ko ɗan kwali, Hajiya Sa'a ta kama hannunta suka fice. Sun yi doguwar tafiya sosai, su na ratsa guri-guri, sai dai duk a cikin duhu ne. Jamila ba ta san ina suke bi ba, da kuma inda za su je ba.

Aka buɗe musu wata ƙofa suka shiga, ta ja ta tsaya. Yanayin gurin babba ne yana da girma sosai. Sai dai da mutane a ciki, galibinsu maza ne. An kunna kyandira a gurin. A haka ta lura kayan jikinsu jajaye ne da baƙaƙe.
Sun kewaye wata ƙatuwar tukunya a tsakiyar ɗakin, fuskokin su a rurrufe.
Hajiya Sa'a ta ja ta suka samu guri suka zauna.
Wani irin gurnani mutanen ɗakin suke yi, su na wasu irin maganganun da ba ta fahimtar abin da suke faɗa. Da alama ɗaya daga cikin su ne yake jagorantar abin da suke yi, mai kama da ibadar bautar wani abin.

"Mun yi baƙuwa a gurin nan" cewar mutumin da yake zagaye tukunyar, yana faɗar abin da yake faɗa suna yi masa amshi.

Hajiya Sa'a ta ce "Eh, baƙuwar mu ce, da na sanar da zuwan ta wannan bugiren"

"Ita ce aka kasa samo jinin 'yar uwatta, uwar gijiyar uban duƙusa?"

"Eh ita ce"

"Mu na yi mata maraba da zuwa ƙungiya, za ta samu abin da take so. Idan duniya ce kun same ta kun gama. Babu wani abu da zai gagare ku. Can kuma wannan matsalar ku ce, ku neme ta ku rasa nan, ko ku nemi nan can kuma sai abin da hali ya yi. Mu na yi wa wanda ba su bayar da sadaukarwar su ta wannan shekarar ba, idan lokaci ya yi za su ga abin da ba su zata ba. Wanda suka riga su ka yi, mu na taya su murna da ƙara tabattar musu sun samu duniya, su taka wanda suka so, babu mai ganin bayansu, masu neman ɗaukaka za su samu, masu neman ilimi za su dace. Masu neman kuɗi sun samu, haka ma masu neman madafun iko. Mu na sake jaddada muku dokokin ƙungiyarmu, babu fita bayan an shiga. Babu tona asirin ƙungiya. Duk wanda ƙungiya ta buƙata za ka bayar, babu jayayya babu musu. Akasin haka jininka ya zama mallakin dodon ƙungiya".

"Mun yarda, mun yi mubayi'a, mun bi dodon ƙungiya, mun bi sarkin ƙungiya, ranmu da jukkunanmu fansa ne a

63 / 64