BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   40 / 64

117K to 120K   out of 190K words

haɗa ruwan ta shiga wanka, sai dai bayan ta shiga banɗakin, ta ji ruwan ya yi mata zafi sosai, maimakon ta kunna famfo, ta ƙara sirkawa, sai ta jingina da bango tana jiran ya huce. Shiru ta yi tana ta tunani daban-daban a zuciyarta.

Ɓangaren buzu bayan ya dawo ɗakin, ye nemi Nana ya rasa, ya ga littafin sa a kan mudubi. Ya ɗan yi jimm ko zai ji motsinta amma shiru.
Kusan mintuna goma bai ji ko zubar ruwan famfo ba, balle ya yi tunanin tana banɗaki.

Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi, kamar yadda ya tashi ɗazu, da ya dawo ya tarar ba ta nan ashe tana cikin gidan nan ba ta gaya masa ba.

Kasa jurewa ya yi ya nufi banɗakin kawai ya buɗe ƙofar.

Zabura Nana ta yi, ta saki ƙara, domin ƙoƙarin cire zanin jikinta take yi ta yi wanka.

Cak ya tsaya yana kallonta, ta saka hannu ta riƙe zanin da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta kare ƙirjinta da shi.

Sannu a hankali take jin sanyi, ƙirjinta kuma ya fara bugawa.

Ta sake ɗaga ido, suka haɗa ido, ko a jikinsa ya ci gaba da tsare ta da ido. Ta yinƙura da niyyar magana, amma ta ji ta kasa furta komai, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

A hankali ta ji ya rufe ƙofar toilet ɗin, wata irin ajiyar zuciya ta yi, jiki a sanyaye ta yi wanka, sai dai ta kasa fitowa saboda kunya.
Da kyar ta iya fitowa, amma ta ga baya ɗakin, cikin hanzari take shiri, domin kwanta, kafin ya sake shigowa.

Gari sai walƙiya ake yi, da wata irin tsawa hadari yana tasowa.

Tana gama zura rigar ta ya shigo, bai ce komai ba, ya rufe taga sai dai yana juyowa gaba ɗaya kamaninsa sun sauya, ya koma wannan tsohon.

Kallon kallo suka yi da ita, ta tsaya tana yi masa wani irin kallo, mai cike da tsoro da razani, a take fitilar ɗakin ta ɗauke, ɗakin ya gauraye da wani irin matsanancin duhu, ƙofa da tagar ɗakin su ka din ga bugawa da ƙarfin gaske.
Wata irin walƙiyya ta haska ɗakin, ta ganshi sanye cikin wannan fararen kayan da take ganinsa da su, hannunsa riƙe da sandar sa, idanunsa baƙi ƙirin wani baƙin hayaƙi na fitowa daga cikin su.

Ya hangame bakinsa, ya fara fito da wuta.

"Allahumma ajirni fil musibati, wa aklifni kharin min ha" ta yi maganar tana sanya hannunta, ta ɗora a kanta.

"Meyafaru?" Ta ji muryarsa. Ta buɗe idonta ta kalle shi a hankali. Fuskarsa ɗauke da damuwa yake tambayarta. Da sauri ta ja da baya tana girgiza masa kai.

"Kar ka sake zuwa kusa da ni, ka yi mini duk abin da za ka yi mini, na gaji me na yi maka ne?" Ta yi maganar cikin kuka.

Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan kururwar.

Ya taka ya ƙara matsawa kusa da ita, amma ta din ga ja da baya, tana maimaita "kar ka matso kusa da ni, ba na buƙatar ka, kar ka zo inda nake".

"Kalli ni mutum ne ba abin tsoro ba, babu abin da na yi miki, le regard kalli" ya yi maganar yana nuna mata hannunsa domin ta taɓa ta tabattar.

Cikin fita hayyaci Nana ta ce "Ka fita ba na son ganinka, ba za ka haukata ni a banza ba, ka fita ba na son ganin ka" ta yi maganar jikinta na tsuma da karkarwa. Cikin sauri ya nufi ƙofar fita yana waiwayen ta.

Yana fita ta silale ta faɗi a gurin.

Fitar sa ke da wuya, ruwan sama mai ƙarfin gaske ya sauka.

****

Dare ya tsala, Fadila na zaune bacci ya gagari idonta, ta kalli kusa da ita, mijinta Sagir yana ta baccinsa hankali a kwance, ita kuwa duk dare fargabar kwanciya bacci take yi, saboda miyagun mafarke-mafarken da take yi. Tun Sagir na damuwa har ya gaji ya rabu da ita.
Ta yi niyyar yin alwala ta yi nafila ko raka'a biyu ce, amma kasala ta danne ta, ga wani irin tsoro da take ji.
Dama ko normal sallar farilla a zaune take yin ta, saboda yadda cikin ya tsufa sosai da sosai ga shi da girma. Ga exams tana facing, ba ta iya karatun sam.
Ta dafe goshinta tana wani irin gumi, duk da sanyin A.C da ya sanyaya ɗakin.

Tana jiyo surutan Haidar a cikin bacci, yana ta kiran sunan Nana.

Kawai ta zuba uban tagumi hannu bibbiyu ba tare da sanin abin yi ba.

****

Ko da Nana ta buɗe idanunta, da hasken fitilar ƙwan ɗakin, ta fara karo.

Ta juyo da kanta, da ya yi mata nauyi tamkar zai tarwatse, kawai ta hange shi a bakin ƙofar banɗaki, yana ta sanɗa yana cire kayan jikinsa a hankali, da suke ta ɗigar da ruwa, jikinsa yana ta wata irin karkarwa. Aka yi walƙiya ta hangi yadda ruwa yake zuba ta taga. A take ta tuna abin da ya faru, da azama ta tashi zaune, ta yinƙura ta tashi, ta nufe shi. Sai a lokacin ya farga da ta tashi. Sai da ya tsorata ya tsaya cak, yana tsoron kar ta sake rikicewa ta ce ba ta son ganinsa.

"Me yasa ka fita ruwa ya dake ka har haka? Subhanallah" ta yi maganar tana karɓar rigar hannunsa. Babban abin da ya tsorata ta, bai wuce yadda jikinsa yake karkarwa ba, haƙoransa suke haɗuwa da juna, su na bayar da wani irin sauti.
Ta buɗe wardrobe ta ɗaukko zaninta, ta fara goge masa ruwan jikinsa. Cikin damuwa ta ce "Me yasa ka tsaya ruwa ya dake ka haka?" Kawai ya kalle ta.

Ta ajiye zanin, ta ɗaukko flask ɗin da ta zuba ruwan zafi, ta shiga banɗakin ta zuba a bokiti, ta haɗa masa ruwa mai zafi.

"Ka shiga ka yi wanka da shi, za ka rage jin sanyin" bai musa ba ya shiga banɗakin, ta ɗauko wando ta rataye masa a jikin ƙofar, ta rufe masa ƙofar.

Ta ɗaukko bargonta, ta ajiye a kan katifar, ta duba kayanta, ta samo man zafi ta ajiye. Ta tsaya tana jiransa. Ba a jima ba ya fito, sai dai jikinsa na ta ci gaba da tsuma, yana karkarwa.

Mamaki take yi, yadda dukan ruwa ya saka shi haka, ita ba ta san adadin dukan da ruwa ya yi mata ba, ko ciwon kai bai taɓa saka ta ba.

Ta ɗaukko riga, ta miƙa masa, amma ya ture ta, ya nufi gurin da yake kwanciya.

Ta riƙo hannunsa ta ce "Zauna a nan" ta nuna masa gefen katifar. Ya zauna a hankali yana rintse idanunsa.

Ta ɗauki man zafi tana shafa masa a jikinsa, sai dai jikinsa ya ɗauki zafi rauuu.

"In baka rigar ka saka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Ta gyara masa fulo ta ce "To kwanta" ya ja jikinsa a hankali ya kwanta, ta lulluɓe shi da bargo.

Ta yi shiru cikin matsananciyar damuwa, ita kanta ba ta san ya aka yi yau ta gigice har haka ba. Ba ta san yadda aka yi ta rasa nutsuwar ta har hankalinta ya gushe ba, duk da abubuwa irin haka na faruwa da ita, wasu lokutan kuma ta na iya sarrafa kanta.

Ji ta yi yana wani irin nishi, jikinsa tamkar ana girgiza shi. Ta ɗaga bargon cikin damuwa, ta ga yana jijjiga.

Ta rikice ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, tsoro ka ke bani ne, ba ina nufin ka fita ruwa ya dake ba ne ba."

Tana kuka ta ɗaukko ɗan kwalinta, ta jiƙo shi da ruwa, ta ci gaba shafa masa. Amma ta ga leɓensa har ya fashe saboda karkarwa. Ta kalli gari yadda ake ta lafta ruwa, balle ta ce a taimaka mata a kai shi asibiti.

Ya yi mata alama da hannunsa ta matsa kusa da shi, ta matsa sosai a hankali ya ce "Zafi, ana ƙona ni, ƙonewa nake yi"

Cikin kuka ta ce "A'a babu wanda yake ƙona ka, zazzaɓi ne ka yi haƙuri"

"A'a, ƙona ni ake yi, sanyi nake so"

Cikin rashin fahimta ta ce "Sanyi kuma?"

"Eh, saboda ƙonewa nake yi yanzu" yayi maganar haƙoransa na ƙara karo da juna.

Cikin damuwa ta ce "To mu koma bakin ƙofar ɗakin?"

Ya girgiza kai ya ce "Sanyin da ki ke ji nake so"

"Sanyin da nake ji kuma? Ai ba na jin sanyi"

"A'a ki na ji, ki taimaka mini dan Allah, sanyin da ki ke ji nake so"

"To ta yaya zan baka?"

"Jikinki za ki bani, shi nake buƙata ko zan daina jin zafin wutar nan" duk da jikinsa yana rawa, amma tana fahimtar abin da yake faɗa.

"To ai ni ban san ta yaya zan baka ba"
Ta yi maganar a sanyaye dan ba ta san ya yake nufi ba.

"Kin yarda za ki bani?" Ya yi maganar yana buɗe idonsa da suka kaɗa su ka yi jawur ya kalle ta.

Ta jinjina masa kai alamar eh, cikin tsoro dan ba ta san ya yake nufi ba.

Ya buɗe mata cikin bargon, ya saka hannunsa ɗaya ya janyo ta, ya mayar da bargon ya rufe., ya mirgina ta gefensa ya saka hannayensa ya ƙanƙame ta.

"Wash Allah! Zafi zan ƙone" ta yi maganar a gigice, saboda wani irin zafi da yake fitowa daga jikinsa, yana ratsa fatarta, duk da akwai rigar bacci a jikinta.

Ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta kasa, saboda ya danne ta, ta kowane ɓangare.

"Yi hakuri, ba za ki ƙone ba, za ki daina ji"

Nana ta fashe da kuka tana girgiza kanta, shi da zafin yake fitowa daga jikinsa ya yake ji kenan?.

A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa bayanta, yana sauke numfashi a wahale. Cike da ƙarfin hali yake cewa "Yi haƙuri, na san ba zaki ƙone ba, nikaɗai nake ƙonewa" ya din ga hura mata iska a kunnenta.
A hankali ta daina jin zafin, temperature jikinsa, ta fara komawa normal, ta ji ya daina wannan tsumar,  numfashin ma da yake ta saukewa ya daina. Sai ta ɗan zabura a rikice ta ɗago, ta kai hannu hancinsa. Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ban mutu ba, ina numfashi" ajiyar zuciya ta sauke tare da gode wa Allah ganin yana raye ya kuma dawo daidai.

"Sannu ka daina jin zafi?" Ya jinjina kai alamar eh.

"Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, tsorata ni ka ke yi ne, ba ina sane na yi maka ba"

"Ni ma ki na tsorata ni wasu lokutan"

Cikin mamaki ta ce "Ta yaya?"

"An gama ruwan ko?" Ya yi maganar yana basar da wadda ya yi.

"Eh an daina, amma dama ka na doguwar magana haka sosai?"

"Eh"

"Amma na yi ta magana ɗazu ka ƙyale ni" ta yi maganar da shagwaɓar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba.

Dariya ta ji yana yi, ya ƙara riƙe ta gam.

"Yanzu wai da gaske ba ka iya tuna komai game da kan ka?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Haka ne, ina iya tuna abubuwa na yau da kullum, wasu lokutan kuma ba na iya tuna komai ma. Tun da farka a cikin wannan duniyar da nake jin ta tamkar mafarki, nake iya ƙoƙarina na tuna waye ni, saboda na fuskanci babu wanda yake rayuwa shikaɗai kowa yana da ahali. Amma a duk lokacin da na yi ƙoƙarin hakan, na takura ƙwaƙwalwata, sai na ji wani duhu ya ƙara ninkuwa a cikin kaina, na ji kamar kan zai tarwatse. Kuma a ƙarshe sai na yi rashin lafiya, ko dai na ji wannan zafin tamkar ana babbaka mini wuta, ko kuma na sake manta wasu muhimman abubuwan. Amma yanzu ke ce ahalina"

"Kenan ba dalilin dukan ruwan nan ne ya saka jijjiga ba?"

"Ba zan iya ganewa ba, abubuwan suke saka ni hakan da yawa"

Nana ta ce "To ni dai ka yi haƙuri dan Allah, ka yafe mini na gaya maka ba ni da cikakkiyar lafiya ba da son raina  ba" ta yi maganar cike da jin daɗin, yadda suke hira yau sosai har haka.

Ya yi shiru, yana ƙoƙarin karkata ga wani abin daban.

"To bari na tashi, tun da ka koma daidai"

"A'a ban koma ba"

Ƙirjinta ne ya fara bugawa cikin matsanancin tsoro, za ta yi magana muryarta ta din ga rawa.

"Dan Allah" shi ne kawai abin da ya iya fitowa daga bakinta.

"Shhhhhh"

Wutar ɗakin ta ɗauke gaba ɗaya, duhu ya mamaye ko ina, sai ƙamshin turaren da ta ji a wancan ɗakin da ta yi mafarki da shi, ya ziyarci hancinta. Gaba ɗaya sai ƙwaƙwalwarta ta juye, ta rikice. Yau ma mafarkin ne? Ko kuma zahiri ne? Nan ta shiga dambarwa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tantance, sai dai haƙar ta, ba ta cimma ruwa ba.

Ayshercool
08081012143.


35

Nana ta motsa, ta ji taushin katifar da suke kai, ta fi ta ɗakinsu. Ga ƙamshin turaren da ya sauya, ya sanya Nana sakankancewa a kan a wannan karon ma, irin wancan mafarkin ne.
Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, a wannan karon ma ta kasa sarrafa kanta da nutsuwar ta.

Sai dai a wannan karon al'amarin ya banbanta da na farko.

"Kai ka rabu da ni" Ta faɗa da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture shi.

"A'a" ya faɗa ƙasa-ƙasa.

Tabbas ba mafarki ba ne ba, bayan Buzun mijin nata ya dangana da ita, wani bugire mai girman gaske, bugiren da ba ta taɓa kawo faruwar sa a tsakanin su ba. Ita a tunaninta tun da ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa ba ya jin komai, hakan ne ya sanya take yawonta ma babu hijjabi a ɗakin, sai ta ga ya dame ta da kallo, ta rufe jikinta.

Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka ƙyale ni"

"je suis désolé (ki yi haƙuri)" ya yi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa.

Bayan wani lokaci da Nana ba ta iya tantance adadinsa ba, domin ta daɗe da daina gane komai.

"Ma femme. (Matata)" Ya yi maganar yana ɗan murza ya tsunta. Ta buɗe idonta da ya yi jawur, da ƙyar tana kallon sa.

A wannan karon fitilar ɗakin a kunne take. Sai dai fatarsa ta yi jawur.

Ta sunkuyar da kanta daga kallonsa.

Ya saka hannu ya share hawayen da ke fuskarta, sai dai kuma ya kasa magana.

Ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta, ya kamo hannunta ma ya sumbata. Ta lumshe idanunta tana numfashi a hankali.

"Merci (Na gode)" shiru ta yi tana ƙara sunkuyar da kanta.

Ya saka hannunsa ya ɗago fuskarta, amma ta lumshe idanunta, ta ƙi buɗewa.

"Kalle ni mana"

Kwaɓe baki ta yi, ta ci gaba da kuka. Ya saki murmushi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce "A yi haƙuri"

Ya ci gaba da wasa da yatsun hannunta, daga baya ya tashi a hankali yana kallonta, sai dai ya rasa abin gaba ɗaya.

Nana ta yinƙura da ƙyar, ta tashi zaune, ta ja bargon ta rufe jikinta.

Su na haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa, fuskarta a haɗe, hawaye na biyo fuskarta.

"Yi haƙuri" ya yi maganar yana kallon ta.

Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshsheƙa.

Shafa bayanta ya ci gaba da yi, cikin sigar rarrashi, amma ta maze ta din ga kuka.

Ya ce "Ki yi shiru"

Ba ta kula shi ba, ta janyo rigarta, ta saka ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta nufi gas ɗin ta.

Ta dafa ruwa ta shiga banɗaki, ta jima sannan ta fito, a ƙofar banɗakin ta tarar da shi a tsaye.

Sai da ta ɗan tsorata, ta na ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, ya ce "Ni fa?" Ta kalle shi.

Ya ce "Zan yi wanka"

Ta ba shi hanyar shiga banɗakin, ya kalli hanyar ya ce "Ruwan sanyi? A a ina jin sanyi"

"Bari na dafa" ya koma gefe ya zauna, ta ɗora masa ruwan, ta kalli agogon ɗakin, huɗu da rabi, ta san idan ta kwanta yanzu ba bu lallai ta samu sallar asuba.

Ta shimfiɗa sallaya, ta ajiye wayarta a kai, ta ajiye hijjabinta.

Yana gefenta, sai bin ta yake yi da ido.

Ta kai ruwan banɗaki, ta na haɗa masa, sai a yanzu ta tuna lokacin da ya ce mata zai yi wanka, ashe ruwan sanyi ne ba ya so.

Ta kashe famfon kenan, ta yinƙura ya shigo banɗakin. Ta tashi tsaye tsam tana rarraba ido.

Ya mayar da ƙofar ya rufe, ta ɗago da sauri ta ce "Amm ga ruwan nan, idan zafin bai yi ba, sai ka kunna famfo ka ƙara sirkawa".

"Na kasa tuna yadda ake wankan, sai kin tuna mini"

"A'a wallahi nima ban iya ba" ta yi maganar idanunta a waje dan tsoro.

"Amma ke ki ka yi? Ko wankan kwanciya bacci ki ka yi?"

Gaba ɗaya mamaki ya cika Nana, mutumin da magana take yi masa wahala, shi ne ya ritsa ta da wannan maganganun kamar ana karanta masa.

"Dan Allah ka yi haƙuri, ni ban iya ba"

"Astagfirullah ba kyau ƙarya" ya yi maganar yana taɓa ruwan.

*****

Doctor Sharif ne da wani likita a kan Shukura, su na gwada bp ɗin ta. Duk ta kumbura sosai da sosai.

Jininta ya hau sosai da sosai, ba zai yiwu a yi mata tiyata a wannan ƙadamin a cire jaririn ba, saboda hawan da jininta ya yi. Ga shi lokacin haihuwar ta bai yi ba.

Sakamakon da ya fito daga lab kuma, still ya nuna jininta ya yi ƙasa.

Doctor Sharif ya fito cikin damuwa, ya dubi Hajiya Amina da Yusuf, da kuma mijinta Sagir ya ce "Wai me yake damun Shukura har haka. Normal teses ɗin suke tuk daga farkon cikin nata, amma lokaci ɗaya a ce jininta ya yi wannan mugun hawan ta kumbura har haka?"

Sagir ya ce "Wallahi doctor na rasa gane kan ta, tun bai fi kwana uku da dawowa ta ba, duk ta canza. Ba ta cin abinci, bacci ma ba ta iya yi. Kullum na farka cikin dare tana zaune, na yi, na yi na tambaye ta mene ne,ta ce mini ba komai, Mummy ai har ke na gaya wa ko za ki tambayeta abin da yake damun ta.

Hajiya Amina ta ce "Rigima ce kawai irin ta Shukura, duk ta ɗaga hankalinta, wai tana ji a jikinta wannan cikin mutuwa za ta yi. Ina ta rarrashinta ina ba ta haƙuri, amma ta addabi kanta kuma wallahi farkon cikin duk ba haka ta yi ba."

Cikin damuwa Yusuf ya ce "Yanzu doctor mene ne abin yi?"

"Zamu ajiye ta a nan, a samu jinin ya sauka, idan babu matsala za a iya barin cikin ya cika watannin haihuwar fine, idan kuma akwai matsala za a tiyata a cire cikin"

Hajiya Amina ta ce "Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi"

Doctor ya amsa da "Amin, dan Allah a kula, hajiya ke kaɗai za ki zauna a gurin ta, babu 'yan dubiya Please, kar a bari kowa ya je inda take, yanzu dai ta samu bacci Alhamdilillah"

"To shikenan in sha Allah, za a

40 / 64