Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
nake yi wa kashedi, kar wanda ya sake gangancin danganta ni da zina, amma idan kun ƙi ji ba za ku ƙi gani ba"
Ta nufi banɗaki, tana jin Yaya Atine tana kiran ta, amma ta yi mata banza, ta shiga ta yi alwala ta koma ɗaki ta tayar da sallar azahar. Tana zaune a bigiren da ta yi salla, ta kasa addu'a ko lazumin ta kasa, haka zalika ta kasa kukan ma, ta rasa me ma za ta ce. Kawai ta haɗa kanta da gwiwarta ta yi shiru. Har yanzu ji take tamkar kawai barazana ake yi mata, amma ba da gaske ne wai an yi mata aure ba.
Ga yunwa tana ji, ga jikinta a mace babu ƙwari, ga damuwa gaba ɗaya ji take kamar ma ba ita ba ce ba.
Can ɓangaren Hajiya Amina kasa zaune ta yi ta kasa tsaye, ta din ga mita tana faɗa, har da cewa sai ta kai Baban Nana Human rights.
Shukura ta ce "Mummy ki na da ɗorawa kai, mutumin ya yi wa 'yar sa aure, kuma ki ce za ki kai shi human rights?"
"To Shukura na rasa abun da zan yi zuciyata ta yi mini sanyi ne, gaba ɗaya tausayin yarinyar nake ji. Ba na tunanin an tsaya an ji ta bakin ta. Ke ba kya gurin lokacin da aka kira ni, aka ce an ganta a ɗakin masu gadi. Gaba ɗaya ba ta hayyacinta, ba ki ga a yadda aka fito da ita ba. Kuma shi ma a buzayen wannan wanda ba ya maganar ne fa, har aka yi ta balahirar nan aka gama bai yi magana ba. Ke wait kamar fa yarinyar nan ita ma tana da mental issues"
Shukura ta ce "Au ke sai yanzu ki ka gane? Ni na daɗe da fuskantar hakan, shi yasa wasu lokutan ba na sakewa da ita, ko na ganta da Haidar"
Cike da damuwa ta sake cewa kuma babanta ya san mutumin da ya aura matan, yana da mental issues?"
"Mummy ina zan sani ina nan?"
"Oh my God" Mummy ta faɗa tana zama.
Ta ci gaba da cewa "Wannan mutanen da ba sa iya zama guri ɗaya, yanzu suna nan anjima su na can, yanzu haka za su yi ta yawo da ita, ko kuma can ƙasar ta su zai kaita oho. Dan Allah Shukura, ki ɗan haɗo ɗan abin da ya sauwwaƙa mu haɗa a kai mata, ko ma mene ne ya same ta, duk a dalilin mu ne"
Shukura ta ce "A'a ba a dalilinmu ba ne, ki daina ɗora mana laifi Mummy, zan haɗa abin da ya samu, ni yadda za mu yi da Haidar kawai nake ji wallahi, dan yadda yake ƙaunar ta ba ya ƙaunata haka. Inda Allah zai taimake ni babansa cikin satin nan zai dawo, da ban san yadda zan yi ba"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Ina jin sa fa tun safe yake bin Jummai, yana ce mata ina Anty. Tana tsokanarsa tana cewa antynta ce ba ta sa ba, har da kukansa ya zo yana gaya mini, in cewa Jummai Anty Nanansa ce ba ta ta ba"
"Ai sun shaƙu sosai ne, zan ga abin da zan yi a kai". Shukura ta yi maganar tana ɗaukar remote.
****
Cikin ƙanƙanin lokaci labarin aure Nana, ya karaɗe dangi da unguwa baki ɗaya, Mama na ta nanata ai cikin dare aka ɗaura auren a gidan mai unguwa, jin hakan ya sanya sai mutane su tambayi ba'asin dalilin yin hakan, saboda ba abu ne da aka saba da shi ba, mussaman auren budurwa, a ce an ɗaura shi cikin dare kamar yaƙi.
Sai Mama ta ce "Hmm ku dai a yi sha'ani, labarin ne babu daɗin ji"
Yaya Atine ce ta bi Nana da kwanon abinci har ɗaki ta tsaya a kanta ta ce "Ki tashi ki saka wani abu a cikin ki, kina ta kwanciya kin wuni ba ki ci komai ba" Nana ta yi mata banza ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi ba.
A hasale Yaya Atine ta ce "Shikkenan kin yi wa kanki" Nasiru kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, idan ya fita ya zagaya sai ya dawo ya leƙa Nana, har aka yi sallar magariba salla ce kawai take fito da Nana, babu wanda ta tankawa a gidan.
Saura ƙiris Alhaji Zailani ya furzo abincin da yake ci, bayan da Hajiya Amina ta kammala yi masa bayanin abin da ya faru. Ji ya yi tamkar ta zuba masa wuta a zuciyarsa. Wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa. A zuciyarsa ya ce amma wannan an yi la'anannen tsoho, mu gama yarjejeniyar zai ba ni aurenta burina na daf da cika, kawai sai ya aurawa wani, saboda hauka. A fili kuwa cikin ƙwarewa da iya duniyanci, ya nuna halin ko in kula ya ce Allah ya kyauta. Bayan ya kammala cin abinci ya cewa Hajiya Amina ta zauna a sashenta kawai, zai ɗan fita.
"Amma na ga yaushe ka dawo, da har zaka sake fita koma mene ne ka bari sai da safe mana?"
"Yaushe ki ka fara kafa mini dokoki a gidana?" Yayi maganar yana tsare ga ido, babu shiri ta ce "Allah ya baka haƙuri"
Kamar zai haukace, haka ya ɗauki mota ya fita, yana tafe yana ta ɗure-ɗuren ashariya a cikin mota, yana zage-zage.
Gidan malam Gambo ya nufa, gurin sha ɗaya na dare, haka ya kira shi a waya ya fito.
"Alhajin Allah, lafiya kuwa ka zo a daren nan, ba yau ka dawo daga tafiya ba?"
Cikin damuwa ya ce "Babu lafiya, dan kuwa an yanka ta tashi"
"Too ikon Allah, me ya faru?"
"Yarinyar nan, da za a ɗaura mana aure, babanta ya yarda zai bani aurenta, ina murna muradina zai cika, kawai yau na dawo na tarar wai ya aurawa ɗaya daga masu gadin gidana, saboda an ganta a ɗakinsu, wai ko yana zarginta ne oho masa, ni ko inda yake ban je ba, dan Allah meye abin yi? Ni fa ina iya saka a kashe ko ma uban wa aka aura mata, muddin muradina zai cika"
Malam Gambo ya girgiza kai ya ce "A'a kar ka ja da zafi, amma tabbas aiki ya koma baya sosai. Ka bi komai a hankali kar ka yi garaje asirinka ya tonu. Ko da auren ko babu, muddin ka yi abin da na ce, buƙata za ta biya. Amma ka san ba ta yarda da kai ba ta da aure ba, babu lallai ta yarda da kai yanzu. Amma dai ka san abin yi ko kuma ku daidaita da wanda aka aura mata ɗin, ka biya shi ya sake ta."
Ya shafi tumbinsa ya ce "Ni ina ma na san wanda aka aura mata a cikin nasu, shikenan dai sai ka ji ni. Amma tsaya wai babu wani abu da za ka yi mini da zai sanya yarinyar nan ta yarda?"
Malam Gambo ya girgiza kai ya ce "Da da akwai, kafin ka tambaya ma zan gaya maka"
Ya jinjina kai ya ce "Haka ne" ya juya ya nufi motarsa cikin matsananciyar damuwa.
Wayewar gari, Nana ta tashi da wani irin azababben zazzaɓi, ta din ga jin tamkar ana ɓalla ƙasusuwanta, ta din ga tamkar an yage mata fata an cilla ta a cikin ƙanƙara, saboda azababben sanyin da take ji. Ko idanunta ba ta iya buɗewa.
Nasiru dai bai gaza ba, ya zo yana tashin Nana, a kan ta tashi ta ci Abinci. A galabaice ta ce "Nasiru ka ƙyale ni ba zan ci ba, mutuwa zan yi na gaya maka"
"A'a dan Allah ki daina faɗar haka, ba za ki mutu ba Nana, dan Allah ko shayin ki sha"
"Kai ma jarababbe ɗan neman suna, ka ƙyale ta mana" Suwaiba ta yi masa maganar cikin tsawa.
Bai kula ta ba ya je ya samu Baba ya gaya masa Nana ba ta da lafiya, amma Baba ya yi mursisi ya ce idan ta yi mushe, a yi masa magana ya yi mata sutura. Sosai Baba yake jin takaicin abin da Nana ta yi, wanda da tuni yana nan yana murna zai zama sirikin attajiri.
Ya gama magana da Nasiru, sai ga motar Alhaji Zailani. Jiki na rawa Baba ya nufi motar, tun kan ya gama parking ɗin.
Kallo ɗaya ya yi wa fuskar Alhaji Zailani ya sha jinin jikinsa. Ya sauke gilashin motar ya dubi Baba cike da takaici ya ce "Yanzu abin da ka yi mini ka kyauta a matsayin ka na dattijo?
Cikin kame-kame Baba ya ce "Wallahi Alhaji ban yi hakan domin saɓa magana ta ba, babu yadda na iya ne, kuma da kunya a ce babban mutum kamar ka, ba zan iya cin amanar ka ba ne, shiyasa na hukunta ta dai-dai da abin da ta aikata. A ce ka na neman aurenta amma a ganta a wani guri da wanda yake ƙarƙshin ka, ai girman ka ya wuce haka, wallahi ba dan na ci amana na yi hakan ba, ya zama tamkar hukunci ne a gare ta" gaba ɗaya sai jikin Alhaji Zailani ya yi sanyi da wannan shiryayyun kalmomin na Baba.
"Amma an tabattar da abin da ake zargin nata ne? An kama su ne?"
"Eh to, ba na ce ba, nemanta aka yi aka rasa, aka gano ta a sume a ɗakin masu gadi dai" Alhaji Zailani ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce "Shikenan na gode"
Baba ya ci gaba da ba shi haƙuri, bai saurari Baba ba, kawai ya ja motarsa ya tafi.
Alhaji Zailani ya tara su Habu a harabar gidansa, yana ta bala'i a kan abin da aka ce masa ya faru a gidan, a kan ba zai lamunci haka ba, a din ga yi masa rashin ɗa'a a gida, idan ba su yi wasa ba duk sai ya kore su.
Yana zaune a cikin ɗaki, yake jiyo baloƙoƙon da Alhaji Zailani yake yi, Sulei sai ba shi haƙuri yake yi.
"A cikin ku, waye ne a kama tare da yarinyar?"
Sule ya ce "Wallahi Alhaji ba wani abu suka yi ba, hasali ma shi ba shi da cikakkiyar lafiya ƙwaƙwalwa, yanzu haka yana bacci ne, wallahi ba wani abin suke yi ba, ko Habou?" Habu kawai ya jinjina kai.
"Lallai ina son ganinsa, ba hauka ba ko a turu yake" suka jinjina masa kai.
A hankali ya yinƙura ya tashi, ya nufi bakin taga, ya hango Alhaji Zailani ya nufi cikin gidan, yana baza jallabiya. Ya ɗan murza zobe hannunsa tare da jinjina kai, ya koma ya samu guri ya zauna.
Sai da Baba ya ga Nana na neman mutuwa, sannan ya yadda a kaita Asibiti, ba ta ci ba ta sha, daba ɗaya ta zuge ta yi wuri-wuri, ko iya tsayuwa ba ta yi saboda jiri, ba ta iya gane komai.
Tana kwance ana saka mata ruwa, ta ganta a libraryn Ƙaisar, ga hannunta ɗauke da ruwa. Yana zaune ya na rubutu.
"Sannu ko" yayi maganar ba tare da ya kalle ta ba.
"Idan ma kin kashe kanki, ƙaddara ta riga fata, dole ki tashi ki ƙwarara jikinki, ki ci abinci ki ware. Ko dai mu yi gaba da gaba da ƙalubalen da yake tunkaro mu, ko kuma ki amince na ɗauke ki baki ɗaya, idan ba haka ba ba zan iya cewa ga abin da zai faru ba"
Nana ta ɗaga ido ta kalli inda yake zaune, ta yi masa shiru ba ta ce masa komai ba.
Ya miƙe tsam ya rufe littafin, ya miƙa hannunsa can saman wani guri, ya ɗaukko wata kwalba, ya zo gabanta ya zauna, ya ƙura mata ido, take ta ji tamkar an zare mata kuzarinta.
Ya watsa mata wani koren abu a fuska, babu shiri Nana ta yinƙura ta tashi zaune tana tari.
Ummi ta gani a ɗakin da take a asibiti.
"Zan sha ruwa" Nana furta a wahale. Aka kawo mata ruwa, ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta. Sai da Nana ta kwana a asibiti sannan aka sallame ta, wata irin azababbiyar yunwa da ta sako ta gaba, haka ta din ga cin abinci.
Sun koma gida babu daɗewa sai ga Hajiya Amina, tare da Haidar. Yana ganin Nana ya je ya maƙalƙale mata yana murna. Ita kanta Nana ta yi murnar ganin Hajiya Amina da Haidar.
"Nana, duk da ni ba na zargin ki, kuma ba zan takura miki da tambayar jin abin da ya faru ba, amma ki yi haƙuri da abin da ya faru, amma idan ba kya son auren nan ki yi mini magana, a shigar da ƙara a hukumance a raba auren, kalli duk yadda ki ka rame"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Na gode sosai da sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi ina fatan Allah ya sanya haka shi ne mafi alkhairi, ni ba auren ne damuwata ba, zargin da ake yi mini.. ta kasa ci gaba saboda yadda kuka ya ƙwace mata.
Ta dafa bayan Nana ta din ga rarrashinta. Kaya ta kawowa Nana, har da bedsheets sabo da tsofaffi amma masu kyau, ga 'yan kayan kitchen da ta kawo mata, da Shukura ta bayar a kawo mata. Ta yi ta godiya, ta tashi za ta tafi, Nana ta ce za ta raka ta, ta ce "A'a ai ke yanzu matar aure ce, ki yi zaman ki Allah ya sanya alkhairi" ta ƙarasa maganar tana danƙawa Nana kuɗi a hannu.
Maƙwabta na ta zuwa Allah ya sanya alkhairi, da biyu domin su ga halin da Nana take ciki, har da 'yan islamiyyar su, da tun da ta bar makarantar babu wanda ya bibiye ta, balle a ji dalilin daina zuwan ta.
Baba sai kaiwa yake yi, yana komowa yana nanatawa Nana ta haɗa kayanta cif, ta fara shiri. Yanayin yadda take ganin duniya ta juya mata baya, ta ji ina ma ba a haife ta ba, kuma duk wannan abin babu wanda ya kira mahaifiyarta ya gaya mata halin da ake ciki. To me ye ma amfanin gaya mata, tun da ba wani abin za ta amfana miki ba, kuma kin san ba zuwa za ta yi ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita.
Da daddare gari ya yi tsit, Nana tana ta juyayi da tunanin wa ma aka aura mata a cikin buzayen, tun da su na da yawa.
Babu tsammanni bacci ya yi awon gaba da ita, sai dai ta din ga jin ta tamkar a zahiri ba mafarki ba. Da wata irin murya mara daɗin ji, cikin maɗaukakin sauti mai matuƙar razani da kiɗima zuciya ake yi mata magana.
"Ko kin san wa ki ka aura? Mutumin da shi kansa bai tantance waye shi ba, bai san mene ne jinsa ba, mutum ne shi ko aljan. Rayuwa da shi na iya sadar da ke da ajalin ki. Lokaci ya yi da za ki biya abin da kakannin ki suka aikata, da kuma abin da ya faru a silar ki ke ce tabbas ke za ki biya wannan bashin. Ki tsira da ranki ki bar gida, ki yi nesa da gida, ko kuma ki fuskanci rayuwa mafi muni da hatsari" A gigice Nana ta tashi, ta fita tsakar gida da gudu tana haki, jan burki ta yi duk da zuciyarta na raya mata ta zare sakata ta ruga da gudu. Wani irin zafi take ji da matsanancin tashin hankali, ji take kawai ta buɗe ƙofa ta fita shi ne za ta samu nutsuwa.
Juyawa ta yi da nufin ta fice ta bar gidan, amma ta ji kamar ta na ƙwaƙƙwaran motsi, zuciyarta za ta yi bindiga saboda bugun da take yi.
"Ki na ƙara ɗaga ƙafarki, zuciyar ki za ta tsaya da aiki. Sai da na gaya miki, babu irin kashedin da ban yi miki ba, ki ka yi kunnen uwar shegu da ni, wallahi da kin sake kin buɗe ƙofa kin fita, haukacewa za ki yi. Yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya" A wannan karon ta gane muryar ƙaisar ce, amma ta farkon ba ta san muryar waye ba.
Zumbur ta tashi zaune, tana kallon ɗakinsu, a iya saninta dare ne ta kwanta tana bacci, amma yanzu ta ga azahar ce.
Yaya Atine ta shigo ɗakin tana faɗin "Kin gama shure-shuren da ihun, kin ga dama kin tashi kenan? Wallahi tun wuri ki ajiye wannan haukan aljanun naki, ki kama kanki, ba kowa ne zai zauna kina masa wannan shirmen banzar ba, idan kin ga dama ki tashi ki wuce ki yi wanka ki zo ki ci abinci" Nana ba ta motsa ba, tana tunanin ko ta yi sallar asuba?.
Ummi ta shigo ɗakin da jaka fuskarta ɗauke da mamaki ta ce "Nana" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta.
"Kin ga yanzu daga fita ta, na haɗu da wasu buzaye, wai 'yan uwan mijin ki ne, suka ba ni wannan kayan wai a ba ki, sun ce , a ce ki yi haƙuri abin ya zo babu shiri, kuma ba su da isassun kuɗi. Kin ga dubu hamsin, wai a baki ki yi wani abin ga kuma kaya"
Yaya Atine ta waro ido ta ce "Buzayen?"
"Wallahi kuwa"
"Kirawo Rabi maza a yi a gabanta" aka kirawo Mama, aka buɗe zip ɗin jakar.
Danƙareriyar shadda bazin ce a farko, fara ƙal an yi mata aiki irin na buzaye, har da awarwaraye da ɗan kunne, da sarƙa.
Kaya dai Atamfa set biyar, sai takalma guda biyu da turare har da na wuta.
Ummi ta ce "To ke Nana ki na ta wani buntsire-buntsire da alama wannan za su kula da ke. Kalli a yadda aka yi auren fa, amma har suka yi miki wannan kayan haka." Ita kanta Mama abin ya ba ta mamaki ya tsaye mata a rai ta za ta Nana za ta tozarta fiye da haka.
Ummi ta ce sai An yi wa Nana gyaran jiki an yi mata lalle da gyaran gashi, tun da har sun ƙoƙarta sun kawo wannan kayan.
Da aka gaya wa Baba nuna wa ya yi ko a jikinsa, duk da cikin ransa ya ji daɗin kayan da suka kawo mata, damuwarsa kar ma a fara yi masa zancen kayan ɗaki. Dan sadakin ma naira dubu hamsin ya ware zai ba ta.
****
A tsanake yake ƙare masa kallo, tun daga kansa, har zuwa kan yatsunsa da suke ɗauke da manyan zobunan azurfa. Duk da fuskarsa a rufe take, sai idanunsa kawai ake iya gani, yatsun hannunsa su ka fallasa asirin kalar farar fatarsa.
"Ko za ka sauke rawanin naka mu yi magana?" A hankali ya juya ƙwayar idonsa, yana kallonsa amma bai yi magana ba.
"Magana nake, ka sauke rawanin fuskarka mu yi