BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   38 / 64

111K to 114K   out of 190K words

hankali, fuskarta duk busasshen hawaye.

Cikin damuwa ya ce "Amarya, meya faru ne? Ya kira ni hankali a tashe ya ce kina kuka, ko wani abin ya yi miki ne da ba kya so?" Ta ɗaga kai ta kalle shi, sai kuma ta ji tausayin sa ya kama ta, daga shi har Habun.

Ta ce "Ba abin da ya yi mini fa"

Habu ya ce "Kar ki ji komai, gaya mini idan wani abun ya yi miki ma?"

"Bai yi mini komai ba"

"Subhnallah, amma hankalinsa ya tashi sosai da sosai fa ya kira ni ya gaya mini, ki na kuka bai san meyafaru ba. Ko ba kya son sa ne?"

Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, aikuwa ya tsare ta da ido, da alama jiran amsar sa take yi. Ta kawar da kanta gefe tana murguɗa baki.

Habu ya yi shiru yana murmushi, buzu ya miƙa mata kofin shayin, ta karɓa, sai dai ta tuna wancan karon da ya ba ta abu ta sha, hankalinta gushewa ya yi, dan haka ta ci gaba da riƙe kofin a hannunta.

Ganin babu wata matsala ya sanya Habu ya ce "To ni bari na tafi, amma dan Allah a daina yi masa rigima, ni bari na tafi"

Suka yi magana da french, Habu ya yi musu sallama, ya tafi.

Yana tafe a hanya, hana murmushi yana yi musu fatan alkhairi, domin ya ji daɗin yadda ya gan su.

"To kai ma ka ci ƙosan mana" ta yi magana tana ɗaukkowa ta miƙa masa.

Ya saka hannu ya karɓa, ya saka a bakinsa.

Nana ta numfasa ta ce "Daga yanzu idan ina yin kuka, ko bani da lafiya, ka daina gaya musu, ka ga an saka shi yana ta zuwa, kuma da nisa daga can zuwa nan"

Ya dube ta ya ce "To ki daina"

"To, amma dama wai ka na magana haka, amma sai ka din ga yi mini shiru? Ba na jin daɗin hakan gaskiya" ya ɗan yi murmushi ya ce "Ɗaukewa take yi"

"Me?"

"Maganar " ya bata amsa.

Cikin mamaki ta ce "To ta yaya maganar mutum take ɗaukewa, kamar wutar nepa?"

Ya ce "Ban sani ba, wataran ma yaren naku, ɗaukewa yake yi, na manta duka"

Kawai ta ɗauki kalaman nasa, a matsayin zolaya, sai ma suka bata dariya.

"To ni dai ka gaya mini sunanka"

"Buzu".

Ta ce "Ai Buzu ba suna bane ba, sunanka na gaskiya"

"Shi na faɗa"

"To ai Buzu ba suna ba ne ba, kamar sunan ƙabila ne"

Horn ɗin mota suka ji, a bakin gate, dan haka ya tashi ya fita ya je ya buɗe, bayan ya buɗe, ya ƙi dawowa ɗakin ya yi zamansa a waje.

Sai bayan sallar isha'i ya dawo, ya ci abinci ya nemi guri ya ɗaukko wayarta, ya kunna film ɗin Indiya fassarar hausa yana kallo.

Ta ƙura masa ido, duba yadda ya tattara nutsuwar sa a kan screen ɗin wayar.

"Wai zuwa yaushe za ka bani wayata ne? Ina son kiran su Anty Ummi, tun da suka tafi ban kira na ji yaya suka je gida ba" ya yi mata shiru, ya ci gaba da kallon.

Zaman shirun ya dame ta, ga wayarta a hannunsa, ga babu abokin hira. Ta kwanta bacci da wuri ko za ta yi bacci, amma ta kasa.

Da ƙyar bacci ya ɗauke ta.

Daf da kiran sallar asuba ta tashi, ta shiga banɗaki ta duba, ta ga ta samu tsarki, ta yi wanka ta yi alwala ta fito. Ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ɗakin, ba ya cikin ɗakin. Duk da wasu lokutan idan ta kwanta bacci ba ta iya tantance mafarki ko kuma zahiri, amma ba ta tunanin da idonta ta taɓa ganin ya kwana ɗakin. Ko dai ya kwanta a farkon dare, tsakiyar dare ta neme shi ta rasa, ko farkon dare baya nan, cikin dare ta ganshi kafin asuba ta neme shi ta rasa.

Har ta doshi ƙofar ɗakin, da niyyar ta ɗaga labule ta duba, ta gani ko yana waje, amma ta fasa da tuna abin da ta gani a wancan karon. Babu tsammani iska ta kaɗa labulen, ta hango shi a kan benci a kwance ya takure, yana bacci.
Sai ta ji tausayin da ya kama ta.

Ta tayar da salla, ta yi nafila raka'a biyu, ta zauna ta din ga istigfari da salatin annabi Sallallahu alaihi Wasallam.
Bayan ta gama ta ɗaga hannayenta ta din ga tasbihi duk wanda ya zo bakinta yi take yi. La'ilahaillalahul azimul halim
La'ilahaillalahul jalilul jabbar
La'ilahaillalahul kabirul mut'al
La'ilahaillalahu muɗɗali'i sittar
La'ilahaillalahul khaliƙul laili wa nahar.
Allahu Allahu rabbi, la ushriku bi hi shai'an.
Allahumma inni as'aluka bi anni, ashhadu annaka antal ahadussamadu lazi lam yalid wa lam yulad, wa lam yakun lahu kufwan ahad.
Sai da ta gama tasbihin kaf, sai kuma ta rasa abin da za ta roƙa. Ta sauke hannunta a hankali ta yi shiru, kawai daga bisani ta rufe da sayyidul istigfar, dai-dai lokacin an kira sallar asuba.

Ƙarar zubar ruwan famfo ta ji, ta dake ta je ta leƙa, ta hango shi a durƙushe yana alwala. Ya idar ya zare sakatar gate ya fice.

"Abin mamaki, mutum mai taɓin hankali ya san salla, ya san addini anma kuma a ce ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa anya kuwa?" Ta tambayi kanta.
"Zan ci gaba da tunzura ka, da ƙoƙarin ƙure haƙurinka, har sai na tantance ainihin jinsin ka, sai na gano ko kai waye!" Ji ta yi an bushe da dariya mara daɗin ji, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sautin.

AYSHERCOOL
08081012143
Page 33

Ƙoƙarin dai-daita nutsuwarta ta yi, ta tattara hankalinta guri guda.
Ta fara jin sanyi yana ratsa ta, ta din ga nanata Innalillahi wa innalillahi raji'un. Sai kuma ɗif tamkar an yi ruwa an ɗauke, ta daina jin sautin dariyar.
Ta tafi banɗaki, ta sake yin alwala, ta zo ta yi raka'atanul fajari, sannan ta yi sallar asuba.

Ta zauna a kan daddumar, tana kallon wardrobe, tana son ta je ta ɗaukko Alqur'ani, amma ta kasa tashi.
Ta yi ƙoƙarin yin karatun Alqur'anin da ka, ta karanta abin da ta sani, amma ta ji tamkar an tattare komai daga cikin kanta an kwashe bar mata fanko.

Ba ta san me ya ci gaba da wakana ba, ta ji an taɓa hannunta. Ta buɗe idonta ta ɗaga kanta ta kalle shi. Ta ganta zaune a kan daddumar, sai dai gari ya yi haske sosai, da alama takwas ma ta wuce.

Ya nuna mata ledar hannunsa ya ce "A zo a karya, ga abinci" ƙamshin soyayyen ƙosan ya daki hancin Nana yawunta ya tsinke. Duk son ta da ƙosai ta girgiza masa kai.

Ya ce "Me yasa?"

"Azumi na ɗauka"

"Da izinin wa?" da fari shirin tashi take yi, babu shiri ta koma ta zauna, tana bin sa da ido. Mamaki take yi har ya san sai da izninsa za ta yi azumi?.

Ya kamo hannunta, ya juyo cikin tafukan hannun ya ce "Kalli, kin zubar da jini sosai, ta ya ya za ki ɗauki azumi? Ki ci abinci"

Ta noƙe kafaɗarta ta ce "Ni ba zan karya ba, na riga na yi niyya, ka bari daga wannan idan zan kuma yi zan gaya maka in sha Allah"

A fuskarsa ta ga alamar ya ji haushi, saboda yadda y tsuke fuskar, kawai ya gyaɗa kai ya ce "sai ki yi na gani" ya tashi daga gabanta. Ta bi bayansa da kallo, yana tashi ita ma ta tashi, ta haye katifarta saboda bacci kanta har wani nauyi ya yi mata.

*****

Jamila fatar jikinta, ta warke, amma da ƙyar take tafiya tamkar tsohuwa. Hatta banɗaki sai an kai ta, komai a duƙe take yin sa.

Babu shiri Mama ta ɗauki Jamila, ta kira ƙanwarta ta raka ta zuwa gurin wani mai magani, tana ta bala'in daga zuwa gidan Nana wannan masifar ta afka mata. Ta din ga faɗan ba yadda ba ta yi da su ba, a kan kar su je gidan Nanan, tun da dai alkhairi babya bibiyar ta, amma suka nace su ka tafi.

Ko da suka je gurin mai maganin, ya ƙare wa Jamila kallo ya ce "Gaskiya wannan ya fi ƙarfina, sai dai na nemo Ibrahima wakilin rafi, ya duba ta. Idan da wani abu ma duk zai yi muku bayani"

Mama ta ce "Waye hakan? Kuma a ina yake?"

Ya ce "Kar ki damu, yanzu za ki gani, ba a nesa yake ba, yana nan kusa"

Mama ta ce "To madalla, mun gode sosai da sosai "

Mutumin ya tashi, ya din ga tattara shirgi a ɗakin, da tsummokara ya cika gurin da su, kamar ɗakin mahaukaci. Sannan ya buɗe wasu manyan randuna a shaƙe da ruwa, ya barbaɗa wani magani a ciki. Ya buɗa wata jaka, ya kwaso wasu tarkace, ya ɗaura wani guru a damtsensa, sannan ya saka yaronsa ya kawo masa, garwashi a cikin kasko, ya turare ɗakin da wani irin hayaƙi mai warin gaske, sannan ya nemi guri ya zauna a tsakiyar shirgin nan da ya baje.

Ya sunkuyar da kansa, ya din ga karanto wasu abubuwa da ba a iya gane me yake cewa, saboda ba yaren hausa ba ne, yana yi yana kaɗa kansa.
Can bayan wani lokaci ya ɗago kansa a hankali.

Gaba ɗaya kamaninsa sun sauya, fuskarsa duk ta wani tattare tamkar tsoho, jikinsa kuma sai karkarwa yake yi, kamaninsa sun canza.
Ba Mama ba hatta Jamila, a tsaroce suka ja da baya, su na rarraba ido.

Ya ƙure Jamila da ido sannan ya ce "Wannan ai wani aljani ne yake jinya a jikinta" Ba Jamila hatta Mama cikin bala'in kiɗima da tashin hankali, ta kalli mai maganin ta ce "Aljani yake jinya a jikinta kuma, na shiga uku na lalace, ta yaya?"

"A'a ba ki shiga uku ba, uban duƙusa su ka yi wa laifi da alama, ya hukunta su ne, su duka daga ita har shi a haka"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wa kenan?"

"Wani aljani ne shi ma"

Cikin damuwa ta ce "Ya za a yi Jamila ta ga aljani ta yi masa wani laifi?"

"To wannan kuma wani abu ne daban, ba na son dai yin doguwar magana, balle dogon jawabi, amma idan ta nutsa ita ta san ta yi laifin. Yanzu dai zan baku magani, na sha da shafawa, sai kuma wanda za ta din ga sheƙa kafin ta kwanta bacci.
Daga nan sai kuma a samu ƙosai mai zafi, a yi sadakarsa bayan la'asar. Amma iya ƙanan yara wanda ba su kai shekaru goma ba, su za a bawa. Za ta miƙe gaba ɗaya, ta warke. Sai kuma a nemi saurayin zakara, a yanka a fige shi a sulala, da almuru idan an gama rabawa yaran ƙosan, a tona rami a binne zakaran. Zai bar jikinta ya yi jinya a wani guri. Wanda kuma su ka ba ta aikin. ta yi musu su za su ɗauki ragamar ba wa uban duƙusa haƙuri. Ni ba ma shi nake ji ba, an riga an nakasta aljanin har abada. Ya ƙone sosai daga feshin wutar da aka yi masa. Wata ƙila ya yafe mata gaba ɗaya, wataƙila kuma shi ma ya ce sai ya rama, duk da babu lallai ya samu damar hakan ƙungiya ba za ta ba shi wannan damar ba"

Cikin tashin hankali ta ce "Ni fa duk ban fahimta ba, ka na maganar ƙungiya, bayar da haƙuri, duk me ya kawo wannan zancen?"

Ya ce "Ki bar shi a haka kawai yadda na gaya miki "

Cikin damuwa "Ni dai malam ka taimake ni dan Allah, ka da yarinyar nan ta nakasa ita ma. Yayarta ta nan haka take ta fama da aljanun nan, da ƙyar ta yi aure tamkar za ta haukace, daga zuwa gidanta ta gamu da wannan masifar"

"Kar ki damu, ba wani abu" Ya ɗaga hannunsa sama, ya dunƙule ya watsowa Mama wani ƙulli guda uku, ya ce "A je a yi mata wanka da shi, za ta ware, na baƙar takarda shi ne na shan, sai na shaƙar"

Bayan ya basu maganin ya sallame su.

****

Haɗuwa da kuma ƙasaitar ɗakin, ya sanya Nana sakin baki tana ƙarewa ɗakin kallo, tare da tunanin yau kuma a ina take?.
Sai dai yanayin adon da aka yi wa ɗakin, ba wai ado ne irin na wannan zamanin da muke ciki ba. Ta ɗaga kai ta kalli rufin ɗakin, sai dai ga mamakinta, sai ta kasa tantance wani irin rufi ne, gini ne dogo mai matuƙar tsawon gaske. Sai da ta kalli wani sashi na jikin ɗakin, sai ta ga ya yi kama da cikin dutse,, ba wai gini ne na bulo ko ƙasa ba.
Wani irin ƙamshi ya karaɗe ilahirin ɗakin, amma shi ma ƙamshin sai ta ji bai dace da wannan zamanin ba.
A hankali ta kalli gadon da take kai a zane, ta shafa saman gadon, wani irin laushi na ban mamaki, bayanta ga fululluka a ajiye. Jin motsi ya sanya ta zabura ta waiwaya zuwa inda take jin motsin. Sai a yanzu ta hango wani sashi da ta sani a gurin. Gurin da ta gan ta jiya tana taje masa gashin kansa ne. Gadon ya tunkaro da kofin shayi a hannunsa yana takawa a hankali, jikinsa sanye da wata doguwar riga fara ƙal.
Sai da ya zo gaban gadon sannan ya ajiye kofin a gefe, ya taka wani abu ya hawo gadon.
Kallonta yake yi yana wani irin murmushi mai ƙayatarwa, ya sumbaci bakinta ya ce "que se passe-t-il?"

"Ban iya ba" ta bashi amsa tana kallonsa ta ƙasan idonta.

Ya yi dariya yana rungume ta a jikinsa ya ce "Me ya faru na ce" ya yi maganar yana shafa gefen fuskarta.

Ta ɗan tura baki ta ce "Ni sanyi nake ji" ta yi maganar kamar za ta yi masa kuka.

Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ai ina kusa da ke, kwantar da hankalinki yanzu zan ba ki ɗumin da ya dace da yanayin jikinki, wanda ba zai cutar mini da une ame(Soul/ruhinki ba). Ni ma ki bani wanda ya dace da ni, ni sanyin nake buƙata". Ya yi maganar yana rungumeta a jikinsa, cike da shauƙi.

Tamkar almara haka Nana take ganin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ta da shi, Kasa saita kanta ta yi a dalilin yadda jikinta yake wata irin tsumar da tun da aka haife ta, ko a duniyarta ta zahiri ba ta taɓa tsintar kanta a makamancin wannan yanayin ba. Ita duk yadda take tsintar kanta a mabanbantan yanayi, da gurare ba ta taɓa mafarki makamancin wannan a rayuwarta ba. Ga shi ya fi kama da zahiri ba mafarki ba.
Amma duk da haka, ta bar wa zuciyarta mafarki ne, babu tunanin komai take biye masa, tamkar masoyan da suka shafe tsawon lokaci, cikin matsananciyar soyayya da ƙaunar juna.
Bayan wani lokaci a hankali ya buɗe idonsa, ya ƙura mata ido idanunta a lumshe. Ta buɗe nata suka yi ido huɗu.
Ta ɗan zaro masa ido, tare da murguɗa masa baki ta ce "Meye?"

Ya yi murmushi ya ce "Komai ma, je suis heureux (Ina cikin farin ciki) na samu farin ciki amma ba cancan ba saura sex... Hannu ta saka ta toshe masa baki tana hararsa. "Kai ba ka jin kunya ne? Ka ke faɗar irin wannan maganat?"
Dariya ya yi, yana ƙoƙarin cizon hannun nata. Ya ce "Yanzu ma ai ba mu ji kunyar ba, tun da...
Ba ta bari ya ƙarasa ba, ta yinƙura ta kama kafaɗarsa, za ta cije shi, ya mirgina ta yana dariya.

"Haryanzu ka ƙi ka gaya mini sunanka" ta yi maganar tana lumshe idonta

"Ƙasair" ya furta a taƙaice.

"Ƙaisar kuma?" Ta furta a zahiri bayan da ta buɗe ido, ta ga yadda take ƙanƙame da pillow.

Juyowa ya yi daga inda yake zaune, da wani ɗan ƙaramin littafi a hannunsa, suka yi ido huɗu. Kawai ya yi wani irin murmushi yana ɗan kaɗa kai ya ci gaba da kallon ɗan ƙaramin littafin.

Ta tashi tana ƙarewa kanta kallo, tana jin abin da ya faru a tsakanin su a jikinta, dan hatta ƙamshin turaren da yake yi, shi take ji haryanzu.
Ita dai ba gwanar nannauyan bacci ba, balle ta ce ko abin ya faru a zahiri tana bacci. Ko da tana gurin ƙaisar da an taɓa ta take tashi. Wasu lokutan ko tsayuwa aka yi a kanta, sai ta farka.
Sai dai ba ta gama razana ba, sai da ta ji ta ba a daidai ba gaba ɗaya. Da sauri ta tashi ta tafi banɗaki, cikin damuwa. Sai dai ko da ta duba, ta sha mamakin abin da ta tarar. Abin da ya faru a mafarki ta gan shi a zahiri, azumin ya karye ɗungurungum, kamar yadda ya gaya mata.

Ta jingina da bangon banɗakin, al'amuran sun fara ba ta tsoro, ta yaya mutum zai biyo ta cikin mafarki, har ya aiwatar da abin da ya ce? Yaya aka yi ta iya biye masa haka, babu kunya babu jin nauyin sa, duk al'amarin baƙi ne a gare ta, kuma ta farka sun haɗa ido yana murmushi, kamar dai ya san abin da ya faru.
Maganganun Ƙaisar su na ta ƙara tabatta ba ta tunanin ɗan Adam ne Buzun nan. Jiki a matuƙar sanyaye, ta yi wanka.

Ko da ta fito ba ya ɗakin, ba ta ko yi yinƙurin gyaran ɗakin ba, ta zauna zaman jiransa.

*****

Mama ce take zaune a ɗaki, tana ba wa Suwaiba labarin yadda aka yi a gurin malamin nan.

"Ni anya ma kuwa Suwaiba, idan Jamila ta warke, ba gurinsa za mu koma ba, ya haɗa muku maganin farin jini, tun da wannan karon na ga kamar maganin malam Ɗayyabu bai yi ba".

Suwaiba ta ce "To mama, a bari dai a fara ganin yanayin jikin nata, amma na yi mamaki da aka ce wai aljani ta yi wa laifi. Ni na fara zargin Nana wallahi".

"Ai idan na faɗa wasu lokutan haushi ku ke ji, a zo a sayo mini waken da zan soya a yi sadakar nan, anjima kaɗan na je na sayo zakaran nan. Kar rana ta take an ce ƙosan da zafinsa ake so a bayar"

Nasiru ya ce "Mama shi ƙosan ne zai ba ta lafiya? Allah kawai za..

"Rufe mini baki kafin na ragargaje ka a gurin, dama yadda ka ke shishshige mata kafin ta tafi, duk ka ko yi miyagun halayen ta".

****
Nana ko karyawa ba ta yi ba, ba kuma ta da niyyar ɗora komai, ta zauna zaman jiran dawowar sa.

Ba a yi mintuna talatin ba ya shigo, hannunsa riƙe da ledar buredi.

Ya ajiye mata a gabanta, bai yi magana ba zai juya, ta riƙo rigarsa ta tashi tsaye.

"Ina son na san waye kai? Me na aura? Na kasa fahimtar abubuwan da suke faruwa ka yi mini bayani" ta yi maganar numfashinta na fita

38 / 64