Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
kiyaye"
Kiran Alhaji Zailani ne ya shigo wayarsa, dan haka ya bar gurin ya yi gaba ya ɗaga.
"Sharif"
"Na'am ranka ya daɗe"
"Yaya ake ciki, Amina ta gaya mini su na asibitin ku Shukura babu lafiya, haihuwar ce ko yaya?"
"A'a tukuna dai ranka ya daɗe, jininta ya yi hawan da ba zai yiwu mu yi tiyata yanzu ba, mu na dai ƙoƙarin dai-daita jinin nata ne".
"To ko ma dai mene ne, kar ka manta da maganar mu"
"Ban manta ba, ina sane ranka ya daɗe"
"Yauwwa ya yi" ya katse wayar.
*****
Jamila ce zaune fuskarta duk hawaye, a gaban Hajiya Sa'a. Hajiya sa'a ta riƙo hannunta ta ce "Kar ki damu Jamila, na san kin yi iya ƙoƙarin ki, za mu canza fasalin aikin namu, Sannan za ki samu lafiya za ki warke gaba ɗaya ma"
Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.
"Akwai wata tafiya da nake son na yi Abuja, idan babu damuwa ina son za ki raka ni, amma sammako za mu yi, mu je mu dawo?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Mama za ta bar ni, Baba ne babu lallai ya yadda, amma na san za ta saka baki ya bar ni, zan ma iya tahowa bai sani ba"
"Yauwwa Jamsy, kar ki damu ki kwantar da hankalinki, in dai mu na tare, kuma za ki din ga yi mini biyayya babu abin da ba zan yi miki ba, kin ji yarinyar kirki?" Jamila ta jinjina kai tana ɗan sakin fuskarta.
Ta numfasa ta ce "Hajiya bari na je gida"
"Ban ce ki daina ce mini Hajiya ba?"
"Yi haƙuri Mummy"
"Good, sai kin dawo yarinyar kirki, ki gaida gida, zan saka miki kuɗin, kayan kwalliya a account ɗin ki"
Ta saki murmushi ta ce "Tom Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Ta juya ta bar falon, tana jin wani irin nishaɗi, duk da wata irin fargaba na ratsa ta, daga ƙarƙashin zuciyarta, da ba ta san ta mece ce ba.
Karo ta yi da wani matashin saurayi, yana ƙoƙarin shiga gidan.
"Sannu ina wuni?"
"Lafiya ƙalau ya ki ke?"
"Lafiya ƙalau" ta amsa tana niyyar raɓa shi ta wuce.
"Gurin Mummy ki ka zo ne?"
Jamila ta ce "Eh gurinta na zo"
Ya ce "Ok shikenan, ki gaida gida"
"Gida zai ji na gode sosai da sosai" ta nufi gate ɗin ta fice.
****
Da ƙyar Nana ta iya sallar asuba, saboda gajiya ga bacci da take ji, da ta idar da sallar ma, a kan sallaya ta jingina tana gyangyaɗi ta kasa azkar ɗin.
Hannunta ya ɗan shafa, ta buɗe idonta da kyar ta kalle shi.
"Bacci ne?" Ta ɗaga masa tana lumshe idonta.
Ya kama hannunta, ya ɗaga ta tsaye, ya ja ta zuwa kan katifa. Ta tsaya tana ƙoƙarin cire hijjabin, ya ƙarasa cire mata ta kwanta. Ta hau katifa ta buɗe bargo ta kwanta, kawai ta ji shi ma ya bankaɗo bargon ya shigo. Zumbur ta tashi zaune tana kallon sa. A ranta ta ce "Lallai ji mutum da samun guri" za ta yi magana ta fasa ta tsaya tana kallon sa.
Shi kuwa ya yi kwanciyarsa, ya lumshe idanunsa, ya bar ta a zaune tana hamma. Sai da bacci ya ci ƙarfinta sannan ta kwanta. Sai da ya ji ta kwanta sannan ya buɗe idonsa. Ya juya sosai yana kallonta.
Zai iya cewa tun da ya tsinci kansa a cikin wannan duniyar da yake a yanzu, wadda yake kamantawa da duniyar mafarki, bai taɓa tsintar kansa cikin nishaɗi da farincikin yau ba.
Ya kasance cikin damuwa, da tsananin ɓacin ran rashin sanin waye shi, daga ina yake? Ina zai dosa? Rashin sanin amsoshin nan, na dugunzuma hankalinsa da haifar da wani irin nauyi a ƙirjinsa, wani irin duhu ya mamaye shi, bai taɓa jin daɗin komai, ko farinciki da komai ba. Duk da dai-dai gwargwado Habu da sauran wanda suke tare su na ƙoƙari a kansa, amma sam babu abin da yake raguwa na duhu da damuwa a tare da shi. Sai bayan da ya fara kasancewa da Nana a ɗaki guda.
Ganin gilmawarta kawai, yana kallon ta, yana jin daɗi. Ya kan ji kamar ya yi mata magana amma sai ya kasa, ya rasa mai zai ce mata. A wannan duniyar da ya yi wa laƙabi da duniyar mafarki, ya ga mutane na bawa ahali muhimmanci, amma shi ba shi da su, kuma ba a duba rashin ahalin nasa ba, aka aura mata shi, hakan ya kan saka ya ji tausayinta.
Yanzu a wannan duniyar yana kallon Nana a matsayin ahalinsa. Duk da ba ya son hayaniya, amma muryarta mai sanyi da daɗin sauraro, ba kamar su Habu ba, sai yana cikin damuwa ko rashin lafiya, ya din ga jin muryoyin su a sama kamar kwarankwatsa ba.
Ya kan ji babu daɗi idan ya ji ta shiru, yana matuƙar son ya ga tana kallon sa, idan su ka haɗa ido ta murguɗa baki tana magana ƙasa-ƙasa, komai na ta a sanyaye.
Ya ƙura mata ido, yadda ta yi nisa a baccinta, ya sumbaci goshinta, ya mayar da bakinsa wuyanta ya sumbata. Ta buɗe ido ta juyo ta kalle shi, idanun na ƙoƙarin sake rufewa. Ya kwantar da kanta a kan ƙirjinsa. Ba ta yi musu ba, sai ma jikinta da ya saki. Murmushi ya yi jin yadda numfashinta yake shiga nasa, ya ji tamkar su dauwwama a haka saboda yadda yanayin ya yi masa daɗi.
"Ke ce Ahalina"
Nana ce ta raɓe a gefen ƙofa, tana hango ƙaisar yana rubutu, sai dai wannan karon ba a cikin Library bane ba, gurin da yake haɗa magunguna ne. Ga tarkacen kwalaban magunguna ko ina a cikin gurin.
"Ya dai?" Ya tambaye ta.
"Ba komai" ta faɗa a hankali, tana sinne kai.
Ya ce "Na ga kwana biyu kina nema na, ba mu haɗu ba, akwai matsala ne, ko kina buƙatar wani abin ne?" Ta girgiza kai tana sinnewa.
"Wai meyafaru ne na ga kin canza yau gaba ɗaya, kamar ba ke ba? Kin wani nutsu" Still taa yi shiru tana ƙifta ido.
Kawai ta ji ya bushe da wata iriyar dariya, da sai da ta tsorata ta ɗan ja da baya, saboda yadda sautin dariyar ya karaɗe ilahirin gurin.
Ya tsagaita da dariyar ya ce "Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki ban ga komai ba, ba abun da na ganu" ta yi tsuru -tsuru amma ta kasa magana.
Ya ce "Ki maze fa kamar babu abin da ya faru, babu abin da na gani, ai ku na cikin duhu, kuma duk da haka ma, lamari ne mai girman gaske da bai dace na ga ƙwaƙwaf ba. Sai na yi gaba abuna" ya yi maganar yana tashi tsaye.
Ya nufi gurin wasu kwalabe, yana duddubawa "Ki saki ranki fa, sai dai ban sani ba ko kin gano sakamakon binciken naki, na mutum ne ko kuma aljani da ki ka iya amincewa wani abu ya faru tsakanin ku. Abin da mamaki yadda jikin ɗan Adam yake iya ɗaukar zafi kamar an saka shi a cikin wuta, kuma bai mutu ba. Kodayake ai haryanzu ban tabattar ba ko wani abun ya faru ba, tun da a cikin duhu ne, amma tsaya a tsakanin ke da shi waye ya kashe muku fitilar ne? Ko ita ta kashe kanta?" Ya sake bushewa da dariya, ya yi wata irin hajijiya, guguwa ta tashi, ta cikin guguwar muryasa ke tashi ya ce "Kamar dai yadda na gaya miki ne, ban ga komai ba ki daina sinne kai" guguwar ta yi waje ta daina jin muryarsa.
Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta din ga jin tamkar wadda ta aikata saɓo.
Ba saɓo ki aikata ba Nana, makomar ki ki ke tunani. Wata zuciyar ta tunatar da ita. Tabbas zancen rashin sanin waye shi, yana damun zuciyarta. Amma ita ma mutum ce ba gini ba, ta yaya za ta iya tsallake dabaibayin da ya yi mata a daren.
Idaonta ya sauka a kan tarin litattafan da suke gurin da ya zauna, da hanzari ta tashi ta tafi ta hau caje litattafan. Bisa tsananin sa'a ta ci karo da littafin da take ta ƙuzun son jin ci gaban sa.
Da hanzari ta buɗe, sai dai tana buɗewa kawai ya kai ta daidai gurin da ta tsaya.
Ta nutsu ta ajiyar zuciya ta fara karantawa.
Lanti ta yi alwashin ko tilon 'yar ta, za ta rasu ba za ta taɓa kai wa sarkin aska yarinyarta ba ya bata magani. Mijinta ya rarrashe ta a kan ta yi haƙuri, su kai yarinyar ko za a dace da maganin.
Cikin damuwa ta ce "Duk da yarinyar nan ce kaɗai nake da ita a yanzu, ba kuma ni da tabbacin sake samun wani ɗan, amma gara na rasa ta da na je gurin maƙiyina nema mata magani, ni na san abin yi, ka bar ni kawai"
Lanti ta shirya, ta ɗauki yarinyarta, ta tafi garin da aka ɗaukko bokan da ya yi wa sarkin aska girka.
Ko da ta je garin ta iske ya tsufa sosai, ga rashin lafiya yana ta fama da ita.
Ta gaya masa abin da yake tafe da ita.
Ta ce "Ka ga halin da yarinyata take ciki nan, ni kuma ba zan iya kai wa sarkin aska ita ba ya bani magani, saboda a duniya ba ni da maƙiyin da ya fi shi yanzu a duniya. Kuma ina son na dakatar da zaluncin da yake yi wa mutanen ƙauyenmu, da sunan Aljanu ne suke saka shi"
Ya yi shiru sannan ya ce "Ni kaina na yi dana sanin girkar da na yi wa sarkin aska, kafin ke wasu da dama sun zo a kan haka, ciki har da mai garin ku, su na neman mafita. Sai dai hatta ni kaina yanzu sarkin aska ya fi ƙarfina, da na san haka ne da ban yi masa girkar nan ba".
Cikin damuwa ta ce "Yanzu mene ne abin yi?"
Ya ce "Babu wani abu da zan iya, sai dai ki koma gurin kakanki, mahaifin sarkin baka, ki ce masa ni na turo ki, ni boka Giyaz"
"Kakana kuma? Kakana ne yake da yadda za a yi da Sarkin Aska?"
"Ke dai ki je ki same shi, ki ce masa ni na aiko ki"
Ta jinjina kai ta ce "To shikenan" ya bata magani, bayan kwanaki uku, ta koma garinsu.
Kai tsaye gurin kakanta ta fara zuwa, bayan sun gaisa ya yi mata sannu da zuwa.
"An aiko ni gurinka"
Ya ce "Tun kafin ki dawo aka aiko mini da 'yan aike, suka sanar da ni zuwan mi"
Cikin mamaki ta ce "Su wa kenan?"
Ya yi murmushi ya ce "lokacin da aka zo da ni garin nan, ina ɗan ƙarami sosai da sosai na san wasu daga cikin gwagwarmaya da dambarwa da aka din ga yi da aljanu kafin mu samu zaman lafiya. Sai dai alƙawarin aljani ba shi da tabbas, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da muka yi, sun ƙi yarda mu zauna lafiya, su na kawo mana farmaki, lokaci zuwa lokaci. Yanzu dai ki na da burin kawo ƙarshen sarkin baka, kuma kina burin ganin 'yar ki ta warke gaba ɗaya, abu ɗaya za ki yi sai dai abin da wahala"
Cikin zaƙuwa ta ce "Ka gaya mini, ko mene ne zan yi, muddin burina zai cika"
"Burinki zai cika, amma sai dai ki amince a yi miki girkar aljanu, ya zamana ke ma ki na da aljanun da ki ke iya sarrafawa, sannan za ki iya ja da shi, har ma garin nan ya zauna lafiya. Amma sai dai ki samu masu ƙarfi da za su iya jayayya da na Sarkin Aska."
Ta numfasa ta ce "Kakana na amince ka yi mini girkar aljanu, dole na kawo ƙarshen sarkin aska a garin nan"
"Lanti, ki je ki ya shawara tukuna. Girkar Aljanu ba hukunci ne da zaka yanke kai tsaye ba tare da cikakken shiri, da nazari ba"
Ta tari numfashin sa da cewa "Ba na buƙatar yin shawara, na gama yanke hukunci na amince a yi mini girkar Aljanu"
Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi za ki je sai nan da sati biyu, zan haɗa tsumin da za a yi miki amfani da shi, gurin yin aikin zan shafe kwanaki ina aiki a kai, domin yi miki girkar. Sai dai ina son ja bakinki, ki yi shiru har zuwa lokacin da za a yi aikin"
"To kakana, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai kai, amma ya aka yi ka iya wannan abubuwan haka?"
Yayi murmushi ya ce "Kamar yadda na gaya miki, tun ina yaro aka zo da ni garin nan, lokacin ana kan ganiyar rashin zaman lafiya da ainihin aljanun da suke zaune a garin nan. Bayan na ɗan tasa na fara yawon farauta, a nan na yi karo da wani matashin saurayin, sa'ana muke shiga tare da shi daji, gurin yin farauta sai dai ya fi ni rashin ji. Shi ne ya koya mini farauta, da siddabaru kala-kala da hatsabibanci, ban san gidan su ba, kullum a hanya muke haɗuwa mu tafi Daji. Sai daga bisani na fahimci ba mutum ba ne ba. Aljani ne yake shiga jikinsa, muke wannan abotar, shi ne ya koya mini harkokin farauta da magunguna har mahaifinki ya gada. Kuma ba kowa ba ne face wannan bokan da aka kawo shi garin nan ya yi wa sarkin aska girka, wanda ki ka je gurinsa yanzu. Jikinsa aljanin yake shiga, kuma shi ya haɗa mu abota da boka Giyaz."
Lanti ta jinjina kai cike da mamaki, dan duk labaran da yake ba ta, bai taɓa ba ta wannan labarin ba.
Ta koma gida ta yi shiru da bakinta, ko mijinta ba ta sanarwa ba.
Kakan Lanti ya shirya ya tafi daji, ya shafe makonni biyu, yana tattara saiwowayi, sassaƙe da kuma sassan jikin dabbobin da yake buƙata gurin yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu.
"Dattijo ka yi a hankali, za ka yi mini ɓarna fa" kakan Lanti ya ɗago tare da faɗin muryar wa nake ji haka, rai kan ga rai Uban duƙusa?"
"Ƙwarai kuwa, na zata ka mutu ai"
Kakan Lanti ya bushe da dariya ya ce "Ban mutu ba tukuna, ina nan raye ina ka tafi tsawon wannan lokacin haka? Kuma a ina ka samo gangar jikin da ka shiga haka ka zo mini?"
Kyakyawan farin matashin da yake tsaye a gaban kakan Lanti yayi murmushi ya ce "Labarin dogo ne, na yi balaguro ne zuwa gabashin duniya, na samo labarai daban-daban da zan rubuta"
"Yanzu neman labarin ne, kusan shekaru hamsin babu amonka"
"Shekaru hamsin mu a gurinmu ai babu yawa. Bani labari na ga gari ya zama alƙarya abubuwa sun canza sosai da sosai. Saukata kenan da kai na fara karo na ce bari na bayyana na kwashi gaisuwa"
"Tuba nake uban gidana, ai ni yakamata na zo kwasar gaisuwa." Nan kakan Lanti ya bawa uban duƙusa labarin abin da ya faru.
Cikin damuwa ya kalli kakan Lanti ya ce "Yanzu duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, sai da aka saɓa ta? Waye ya yi wa sarkin askar girka?"
"Giyaz ne, mutane sai wahala suke yi a garin nan, saboda abin da sarkin aska yake yi. Ya sadaukarwa wasu daga ahalinku jini, ya mayar da su baƙaƙen aljanu da sunan zai taimaka musu gurin ɗaukar fansar abin da mutanen garin nan suka yi muku"
Matashin ya shafi fuskarsa cikin damuwa, ya ce "Yanzu wa za ka yi wa girkar?"
"Jikata ce, da nake kyautata zaton sarkin aska ne ya kashe babanta, saboda yana bayar da magani"
Uban duƙusa ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne, shikenan zan je gida, zan huta kafin ranar da za ka yi mata girkar, amma ka tabattar za ta iya ɗauka? Ka san idan aka samu akasi, za ta iya haukacewa fa"
"Za ta iya, tana da juriya, kuma tana fatan ɗaukar fansar abin da aka yi wa mahaifinta"
"To shikenan, zan sake dawowa"
"To shikenan ubangidana, ina godiya da wannan ziyara ta bazata" suka yi sallama.
Kakan Lanti ya koma gida, ya shiga wani ɗaki a cikin gidansa, ya haƙa rami ya saka wata randa. Ya kawo saiwoyin da ya zo da su ya zuba a ciki, ya kawo tarkacen magunguna kala-kala ya zuba a ciki. Ya kawo ƙasusuwa da wasu sassa na jikin dabbobin daji, a zuba a ciki. Ya kawo turare ɗan goma, da farin goro duk ya zuba a ciki ya rufe randar, sannan ya mayar da ƙasar ya binne.
Sai da aka kwana biyu, daren na uku da zai buɗe randar, wanda saura kwana biyu ya yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu. Yana cikin bacci, ya ji wata irin ƙara, sanyi yana ratsa shi, ya tashi da nufin neman abin rufa, amma ya gan shi a tsakiyar daji, gurin da suka haɗu da uban duƙusa.
Cikin mamaki ya ce "Ubangidana lafiya aka kira ni a wannan daren haka? Idan na yi laifi ne ina neman afuwa" uban duƙusa ya fito daga bayan bishiyoyi ya ƙaraso gaban tsohon nan ya ce "Ba ka aikata mini wani laifi ba abokina, Ina mai baƙin cikin sanar da kai mutuwar Giyaz"
"Wayyo, Giyaz ya mutu?"
"Ƙwarai Giyaz ya mutu, sannan na yi baƙin cikin abin da na zo na riska, galibin 'yan uwana, sun koma baƙaƙen aljanu, kuma sarkin aska yana sarrafa su ta mummunar hanyar da ba ta dace ba. Su na sanya muku miyagun cututtuka. Tabbas idan ku ka yi sake sai sun shafe tarihin mutanen garin nan. Ban ji daɗin yadda aka saɓa alƙawri da yarjejeniyar mu ba. Dan haka zan kasance tare da ku a gurin girka, dan kuwa komai zai iya faruwa, za ta iya rasa rayuwar ta ma. Kar ka kuskura ka yi mata girka da baƙaƙen aljanu, dan abin ba zai haifar da ɗa mai ido ba, sai mun haɗu a gurin.
Ayshercool
08081012143
Kakan Lanti ya ci gaba da shirye-shiryen yi wa jikarsa girka.
Ya samo ƙaramin ƙoƙo, da 'ya'yan wuri, tsirkiya ya haɗa garaya.
Ya haɗa caki, ta hanyar samun butar duma ya fafe ta, ya zuba busassun 'ya'yan tafasa, da zogale a ciki, ya toshe bakin.
Ya tsayar da ranar yi wa Lanti girkar aljanu, ya sanya ranar Lahadi. A sirrance ya aika saƙon gayyata zuwa ga bokayen maƙotan garin.
Bayan almuru, yaje ya saku ƙatuwar Bishiyar kukar da ke wajen garin, ya je ya samu, ya naɗe da farin yadi.
Ya koma gida, ya tono randar nan, ya ajiyeta a tsakar gida, ta kwana tsumin cikinta ya yi sanyi.
Ya koma ya dafa wani magani, ya zuba a cikin kwatanniya. Mutane suka din ga mamaki wayewar gari, da suka ga wannan farin yadi a jikin bishiyar