BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   22 / 64

63K to 66K   out of 190K words

dai bai kamata ya biye mata ba".

Matar ta sake yatsuna fuska ta ce "Sai ka ce shi ne kaɗai ɗansa, da zai bi ya ɗaga hankalinsa haka?.

Likita ne ya yi sallama suka amsa baki ɗaya, ya ƙaraso tare da nurse, suka gaisa ya yi musu ya mai jiki, sannan ya shiga dudduba jikin Muhsin.

Cikin damuwa Alhaji Fatuhu ya ce "Likita wai haryanzu babu takamaiman abin da yake damunsa?"

Likitan ya kalle shi ya ce "Mu na ta ƙoƙarin ganowa Alhaji, ka yi haƙuri mu na kan bincike ne. Yanzu dai zan rubuta NG-tube, aje a sayo a saka masa, saboda a din ga ba shi abinci"

"Meye shi ɗin?"

"Roba za mu saka masa a hanci, a din ga ba shi abinci ta ciki"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, na shiga uku shikenan ba zai tashi ba?" Mahaifiyarsa tayi maganar cikin kuka.

Likitan cikin tausayawa ya ce "A'a zai tashi in Sha Allah, ki yi haƙuri kar ya zauna babu abinci ne, amma zai warke in sha Allah" Shi kansa Alhaji Fatuhu dauriya kawai yake yi, ji yake yi tamkar ya fashe da kuka. Yana da yara biyar, Muhsin ne na shida ƙarami, 'yar sa ta biyar kusan shekarar ta goma sha biyar daga baya ya auri maman Muhsin, dan haka yaron ya shiga ransa nesa ba kusa ba.

Likita ya ɗan yi amfani da kalaman kwantar da hankali, Alhaji Fatuhu ya mayar da hankali kan maman Muhsin, yana ta rarrashinta, saboda sosai take kuka, ba tare da jin nauyin mahaifiyarta da take zaune ba ma.

Ɗaya matar ce ta tashi, cike da kishi ta yi waje, ba tare da ta yi musu ko sallama ba.

Kakar Muhsin, ta yi gyaran murya ta ce "Ni kuwa Alhaji, na ce mai zai hana a jarraba na gargajiya. Ayo rubutu a ba shi ko Allah zai sanya a dace" A take ya haɗe rai, fiye da yadda fuskarsa take ya ce "A'a Umma, ba za a ba shi wannan ƙazantar ba, yanzu ma ana fama an rasa gane kan sa ina ga an ba shi abin da ban san ya aka yi aka wanke ba, da wani ruwa ma aka wanke ba a ba shi infection."

"To ai ana rubutawa a bawa mutum, sai ya wanke da kansa, kuma ayoyin Allah za a rubuta a wanke a ba shi, ko ayi masa tofi a ruwa, a ba shi"

"A'a Umma ba musu nake yi miki ba, amma ni dai a bar wannan maganar ga likitoci nan su na iya ƙoƙarin su a kansa"

Umma ta jinjina kai ta ce "To shikenan" ya jima a gurin, sannan ya tashi ya tafi domin yana da abubuwan yi sosai da sosai.

Yana fita Umma ta ce "Yau na ga tsiya, ko ba za a sha rubutu ba, amma ai a sha tofi, su turawan da suke yin maganin ya san tsiyar da ake haɗawa? Ke rungumi ɗanki, ki yi ta tofa masa abin da ya sauwwaƙa na Alqur'ani."

Cikin kuka ta ce "Wallahi Umma ina tofa masa, shi ma yana yi masa, rubutu ne dai ko a tofa ruwa a bashi yaƙi yarda"

"Tun da ya tafi tofa ki bashi, ba gara shan rubutun ba, ka san Alqur'ani ne ba, shi na yahudawan ya san da me aka haɗo ne?" Haka Umma ta ci gaba da sababi.

*****

Cikin ikon Allah, tun shaƙar da Nana ta yi wa Suwaiba, ba ta sake ihun Nana tana sha mata jini ba.

'yan kuɗin hannun Nana, na gurin baban Muhsin su take ta lallaɓawa tana kashewa a hankali.
Da magariba ta yi wanki ta gama duk ta shanya, su Jamila duk su na tare da Mama, suna hira.

Baba ya yi gyaran murya haɗi da yin sallama, suka amsa masa, ya ƙaraso ya ce "Nana, jeki ga yaron can ya zo yau. Dama Ummi na kira na tambaya ba'asin ƙin zuwa da ba ya yi, balle a ci gaba da shirye-shirye, ta yi magana da shi ya ce "wulaƙanci ki ke yi masa, ki yi ta haɗe rai, kuma imarana na yi masa rashin kunya. Na rarrashe shi na ba shi haƙuri yanzu, kuma na gaya masa Imranan baya nan, wallahi ki ka sake ki ka je ki ka yi masa rashin mutunci, sai na saɓa miki"

Ba ta ce komai ba, sai dai a duk lokacin da aka yi zancen Saleh, ranta ɓaci yake yi. Ta yi iya ƙoƙarinta a kan ta taushi zuciyarta ta fara son shi, amma abu ya gagara.

A ƙofar gida ta tarar da shi, sai dai yau an yi sa'a dogon wando ne a jikinsa. Askin banzan nan dai shi ne a kansa, wanda yake haɗuwa ya ƙara masa muni.

"Amaryar da ba kya nema na"

Nana ta kai zuciyarta nesa ta ce masa "Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau. Baba yana ta mitar ba na zuwa, balle a ci gaba da shirye-shirye. Ni kuma ke ɗin ce in dai zan gani hankalina ba ya iya kwanciya. Sai sha'awarki ta addaba mini, amma ke ko kaɗan ragewa juna zafin nan na ga alamar ba za ki yadda ayi ba. Zamanin nan in dai da soyayya fa babu abin da ba ayi, kuma ai Allah gafurun rahimu ne"

Zuba masa ido ta yi, kunnuwanta na karɓa maganganun rashin ɗa'ar da yake yi, cike da jahilci da wauta. Ya ƙara matsawa kusa da ita ya ce "Yi magana mana Nanasko, wallahi in dai ina ganinki, ba zan taɓa samun nutsuwa ba, ko ɗan taɓa ki na yi, na samu sukuni"

"Wallahi ka taɓa ni, sai ka yi dana sanin zuwanka duniya. Kai abin da ka ɗauka aure kenan?"

Saleh ya ce "Eh mana, idan ba shi ba ne mene ne? Ni fa idan aka ɗaura aure kafin mu tafi Ikkon zan fara more angoncina, dan haryanzu ban samu ɗaki ba. Duk ɗakunan tsada suke yi. Ba na son kuma gidan haɗaka mai maza da mata ne"

Nana ta ce "Ka jahilci ma'anar aure idan haka ne, maganganu ka ba sa nuna komai sai zunzurutun wauta da rashin sanin ciwon kai"

Ya ce "Ba komai na ji na yadda" yayi maganar ba tare da jin zafin maganganun Nana ba.

Tsaki ta yi, ta juya za ta koma cikin gida, kafin baƙin ciki ya saka ta wanka masa mari, ko ta ci masa mutunci. Kawai ya riƙo hijjabinta yana "Haba Nanasko, haka za ki tafi babu sallama irin ta masoya, ko na lalata ki fa ni ne zan aure ki, ba kuma zan guje ki ba, rungume ki kawai nake so na yi, na ji ƙirjinki a jikina"

"To sannu tsinanne, sakar mini hijjabi, kafin na ci zarafin ka"

Ƙara matsawa ya yi yana ƙoƙarin haɗeta da bango, ta tattaro ƙarfinta, ta hankaɗa shi ƙasa, ta juya da saurin gaske ta shiga gida, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.

"Ke Nana har kin dawo? Ya tafi ne?"

"Eh" ta faɗa a taƙaice ta shiga ɗaki.

Ta cire hijjabinta ta riƙe a hannunta, zuciyarta na wani irin tafasa yanzu shikenan wannan shi zai zama mijinta, uban 'ya'yanta? Ta san duk bayanin da za ta yi wa Baba, ba zai yadda ba, ba ma zai fahimce ta ba, saboda idonsa ya rufe burinsa kawai ta yi aure ta yi gaba, mussaman yanzu da Mama ke ta yi masa barazanar zube masa yaransa ta tafi.

Muryar Baba ta ji a ƙofar ɗakin cikin faɗa ya ce "Ina magana kin yo gaba, bai ce miki komai ba game da shirye shiryen?"

"Baba bai ce mini ba, ni wallahi Baba ba na son sa, ko ƙaunar ganinsa ba na yi, bai cancanci a ba shi aure ko ya zama uban da zaka zaɓawa 'ya'yanka ba, dan Allah Baba a fasa auren nan" ta yi magana cikin magiya, hawaye na zirarowa daga idanunta. Tsaki kawai ya ja ba tare da ya ce mata uffan ba, ya yi gaba abin sa.

*****

Yanayin damuwar da Nana take ciki, bai hana ta yin murmushi da ta ga Haidar ba.

Shi ma murmushin ya yi, ya saukko daga kan kujera ya nufo ta.

"Ba ka ce ba"

Ya durƙusa a ƙasa, cikin gwarancin yara ya ce "Anty ina kwana" kamar yadda Nana ta koyar da shi.

Ta ce "Lafiya ƙalau, sai ɗayan"

"Good morning"

"Mornin my boy, how are you?"

"I am fine, thank you" ya faɗa yana tashi tsaye, haɗe da yin tsalle.

Ita dai tana son yara sosai da sosai, ko ma tana da rabon yin auren oho. Ta tambayi kanta ta bawa kanta amsa.

Ƙamshin turaren Hajiya ne ya karaɗe falon.

"Nana har kin zo?"

Cikin girmamawa Nana ta ce "Eh, ina kwana Hajiya"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya ɗan naki?"

Nana ta kalli Haidat ta ce "Haidar, ka manta?"

Ya kalli Mummy, ya durƙusa ya ce "Mummy ina kwana, good morning"

Baki buɗe Hajiya take kallon Nana da Haidar. "Ikon Allah, Haidar ne da gaisuwa yau? Nana ke ki ka koya masa?" Ita dai murmushi kawai ta yi, idan ba a fara koya masa abubuwa yanzu ba sai yaushe?.

Bakinta ya kasa rufuwa, cikin matsanancin farin ciki, saboda duk son da suke yi wa yaron, azabar kukansa ya sanya suke ƙyale shi.

Shukura ta fito tsaf za ta tafi makaranta, Haidar yana kallonta, amma bai je gurinta ba.

Mummy ta ce "Shukura, Haidar fa iya gaisuwa, ka gaishe da mamin ka" Noƙe kafaɗa ya yi yaƙi ko kallonta.

Nana ta ce "To ɗaga ni, mun ɓata kuma yau ba zan karanta maka littafin ba"

Daga kwance ya ce "Mami ina kwana"

Ɗan kwaɓe baki ta yi, ta amsa ta fice.

Da yamma da Nana ta tafi, ganin da sauran lokaci, ya sanya ta hau abin hawa ta tafi gidan Ummi.

Ummi na ganinta ta ce "Alhamdilillah, da gidan zan tafi ai, na kira Baba na gaya masa, ya ce ba kya nan ki na gurin aiki"

Nana ta ce "Me ya faru?"

"Dama game da maganar shirye-shirye ne, kuma kwatsam jiya Saleh kwana ya yi da ciwon ciki a asibiti ya kwana, ɗazun nan na dawo na ce dama yakamata ki zo mu je mu duba shi"

A hankali Nana ta furta "Ƙaisar"

Ummi ta ce "Me ki ka ce?"

"A'a ba komai"

"A'a bari na kaɗa miya, mu je ki duba shi, yana jin jiki sosai wallahi, jiya wai har da dafara ya din ga fitarwa"

"Allah ya ba shi lafiya, amma ba zan je ba"

"Nana, ba za ki je ba kuma? Wanda za ki aura ɗin?"

"Wallahi Ummi ba na ƙaunar sa, na danne zuciyata ne na amince na aure shi, domin farantawa Baba, amma na ga alamar garin faranta masa, zan shigar da rayuwata da yarana cikin madauwamiyar nadama ne. Ummi ke kan ki kin san Saleh ba mutumin kirki ba ne na, kawai dan ku na son na yi auren nan ne"

Da fari Ummi ta hasala, amma sai ya danne ta ce "Nana, ana duba miki yanayin rayuwa ne. Ko ba mutumin kirki ba ne ba, idan ya shiryu sanadin ki, sai ki samu lada. Ba da ke muka karanta littafin ƙarfe a wuta ba a gidan nan, da Jauhar ta yi juriya ba ki ga yadda ta canza mijinta ba..

"A'a fa Ummi, littafi ba gaskiya ba ne, kuma shi Vipern ai ba ɗan iska bane ba, koma ba haka ba, kin san ina da juriyar da zan iya kamanta abin da Jauhar ta yi, amma wannan misalin da wancan da ki ke bayarwa gaba ɗaya ba iri ɗaya bane ba. Ina mamakin ace a aurawa namiji mace ta gari zai shiryu, lalatacciya kuma kowa gudunta yake yi. Ke ba ki san abin da ya yi mini ba, gaskiya ba zan iya auren sa ba wallahi"

"Nana, ki tsaya ki saurare ni.."

Banza Nana ta yi mata, ta ɗauki ledarta, ta fice daga gidan.

Washegari Nana ta koma gidan rainon yaronta. Ta riga ta saba, ko ba ta tarar da kowa a falon ba, ɗakinsa take tafiya, ko ta tafi kitchen gurin Jummai, ta taya ta aikin girki.
Sai dai ta tarar Haidar baya ɗakinsa, ta dawo Falo sai ga Mummy.

Suka gaisa, ta ce "Nana ba ki ga ɗan naki ba ko? Yana gurin kakansa, yau sai da Haidar ya gaida kowa, har fatiha ya fara iyawa. Kin yi ƙoƙari sosai mun gode"

Nana ta ce "Bakomai"

"Babansa ma da aka yi waya da shi, yana ta murna, yanzu ma kakansa ya ce ki je, yana son ganinki. Amma kafin nan akwai 'yan kayana da na Shukura da muka yi kwalema, ki duba idan da wanda za su yi miki, wannan da ki ke sakawa duk sun mutu" Nana ta ce "To"

Mummy ta yi wa Nana jagora, har ɗakinta, ta ɗebo mata kayan fal, ga uban dogwayen riguna, kaya masu tsada, ba su yi komai ba wai ba a so.

"Idan ki na so, kafin ki tafi, duk ki ɗiba ki tafi da su, ki canza wannan na jikin ki, ki je ɗakin Haidar sai ki saka"

Nana ta karɓi doguwar rigar da Hajiya ta bata, ta tafi ɗakin Haidar.

Ita kanta ta yaba kyawun da ta yi a cikin kayan, ta daɗe tana burin sanya ire-iren waɗannan rigunan, amma Allah bai bata dama ba.

Ko da ta koma gurin Mummy, ta yi ta koɗa mata irin kyan da ta yi a cikin kayan.

"Ma sha Allah, Nana haka ki ke tubarkallah mai kyau, kin ga diri ma sha Allah. Mu je Alhaji yana ta murna yadda ki ke kula masa da jikansa".

Nana ji ta yi tamkar ta ce ba zata je ba, amma ba ta da wani zaɓi da ya wuce rufa wa Hajiya Amina baya, suka tafi sashin Alhaji Zailani.

Haidar na ta tsalle-tsallensa a falon, yana kaiwa yana komowa. A hankali ya ɗaga kai ya kalli hanyar da suke shigowa.

"Alhaji ga ta"

Sai dai ya ƙare wa Nana kallo sannan ya ce "Ma sha Allah, zuwan ki gidan nan kin zo da kyakyawan alkhairi fa, na ji daɗi sosai da sosai, yadda ki ke kula da jikana, na yi mamakin yadda yake yadda da mutane yanzu har ya iya gaishe ni" Nana ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsunta ko kallon Alhaji Zailani ba ta son yi. Ita dai ba ta taɓa ganinsa ba, amma ta rasa ya aka yi take yi masa kallon sani, ta tsane shi har haka.

Ya kalli Mummy ya ce "Amina, ina ga a ɗakin ki fa na bar glass ɗi na, ina ta son tura kuɗi, amma ba na gani sosai"

"Ok bari na ɗaukko maka" ta yi maganar tana tashi. Tana fita ya dawo da idanunsa kan Nana, yana ƙare mata kallo yadda zai samu riba biyu a tattare da ita. Ga kyakyawar ƙirar jikin da Allah ya yi mata ga kuma taurarin ta.

"Matso daga nan mana mu yi magana" yayi maganar yana nuna mata gefen ƙafarsa.

Ta ce "A'a nan ma ya isa"

Ya numfasa ya ce "Na ji daɗin irin kulawar da ki ke bawa Haidar. Amma nima ina da wata buƙata da nake neman agajin ki"

Cikin mamaki Nana ta ce "Ni kuma? Ƙwarai kuwa" ya yi maganar muryarsa na rawa.

Ayshercool
08081012143
Page 20

Dawowar Mummy ce, ta sanya shi yin shiru.

"Ba a ɗakina fa ka bar shi ba, na duba baya nan" cewar Hajiya Amina tare da ƙoƙarin zama a kusa da shi.

Ya ce "Too, ikon Allah ko ina na yar da shi Allah masani. Nana ko?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Nana.

Ta jinjina masa kai. "Ɗauki yaron ki, ku tafi zan bayar da saƙo a kawo miki, mu na godiya sosai da sosai"

Nana ta miƙe, ta kamo hannun Haidar suka fita. Duk da rigar ta ɗan yi mata yawa, saboda ta Hajiya Amina ce, amma hakan bai hana bayyanar da yadda ƙugunta yake juyawa ba.

Bayan ta gama duk abin da za ta yi wa Haidar, ta tafi kitchen tana taya Jummai aiki, su na ɗan taɓa hira.

Sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin, me mutum kamar Alhaji Zailani yake nema a gurinta? Duk da zuciyarta tana ƙoƙarin kawo mata ko wata muguwar ɗabi'ar zai nuna mata, amma sai ta kawar da wannan tunanin.

Jummai ta ce "Nana dan Allah miƙa wa buzayen nan abinci, Shukura zan dafawa nata abincin, kafin ta dawo ta yi ta bala'i"

Nana ta ce "To"

Ta ɗauki ƙatuwar cooler abincin, tana tafe Haidar na biye da ita.

Habu ta tarar ta ba shi, ya karɓa tare da yin godiya. Maimakon su koma cikin gidan, sai ta ƙyale Haidar ya yi ta wasa yana tsalle-tsallensa, tana gefe tana kallonsa, tana jin daɗin ganin yadda yake wasa cikin nishaɗi. Muhsin ne ya faɗo mata, take ta nemi annurin fuskarta ya ɗauke. Jikinta ya yi sanyi, tana matuƙar son ta san halin da yake ciki.
Tashi ta yi daga inda take, ta kama hannun Haidar, da nufin su koma cikin gida, amma ya ce shi ba zai koma ba, haɗe rai ta yi ta kalle shi, ba tare da ta ce masa komai ba, a take ya nutsu ya bita suka koma.

Bayan la'asar ta gama abin da take yi, ta ɗaukko kayan da Hajiya Amina ta bata, ta yi musu sallama ta fito.

Da fari shayi yake sha, yana zaune a kan benci, yana facing ɗin ƙofar falon, tana fitowa ya ja rawaninsa ya mayar, ya rufe fuskarsa.

A hankali take tafiya, tana ɗan rarraba ido, ko ƙifta idanunsa ba ya yi, har ta farga kallonta yake yi, suka yi ido huɗu da shi. Sai dai wannan karon ba ta ji faɗuwar gaba ba.

Ta yi saurin ɗauke nata idon, ta sake ɗaga ido, ta ga still ita yake kallo, ga shi shi, ba a ganin fuskarsa sai idanunsa kawai. Murguɗa masa baki ta yi, ta harare shi, amma tamkar maye ya ci gaba da kallonta. Sai kuma tsoro ya kama ta, ta haɗa da sauri, ta ƙarasa gate ɗin, ta fara ƙoƙarin buɗewa, amma ta gan shi a rufe. Tayi-tayi amma ta ga ashe key aka saka ta ciki aka rufe gate ɗin.

"Dan Allah buɗe mini ƙofa, zan tafi gida" ta yi maganar da sigar magiya. Sai dai kamar an gina shi, ko motsi bai yi ba, balle ta sanya ran zai amsa mata.

"Bawan Allah dan Allah ka buɗe mini, zan tafi gida ne na tashi" ko kallonta bai yi ba, ya ci gaba da kaɗa ƙafarsa a hankali.

Ajiye kayan hannunta ta yi, ta ɗan ƙara matsawa daf da shi, ta ce "Malam magana nake yi, ko baka jin hausa?" Takaici ya kama Nana, ko kurma ne ai yakamata ace ya na jin sauti, kuma tun da ya ganta a gurin ai ya san tafiya za ta yi.

Sule ne ya nufo ta, hannunsa riƙe da kwanon abincin kare, ya ce "Malama kin

22 / 64