Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
takardar cikin littafin tamkar jemammiyar fatar dabbobi, ba kamar sauran takarda ba.
"Duniya sararin subhana. Ƙudura da buwaya ta Ubangiji ta sanya ya halicci jinsi daban-daban a cikin duniya, ya sanya su rayuwa a gurare daban daban. Tarayyar wasu halittun da wasu, ta haifar da gagarumin cigaba, ya yin da wata tarayyar ɗaya ne yake morar ɗaya, ko dai ta hanyar kashe rayuwar ɗayan domin su rayu, ko kuma ta hanyar bautar da ɗaya.
Zan iya cewa tun bayan wanzuwar ɗan Adam a doron duniya, al'amura suka fara canza mana kamar yadda muka samu labari, kuma muka karanta a litattafan da kakaninmu su ka rubuta dubannan shekaru da suka gabata.
Sun fasalta mana bil adama, da halitta mai tsananin son kai, da hatsabibanci fiye da duk wata halitta da take yawo a doron ƙasa. Mu jinsinmu mun kasance tamkar ruhi ne, mu na iya zuwa gurin da ba sa iya zuwa, mu na ganin abin da ba sa iya gani, mu na aikata abin da ba za su iya ba, kuma mu na doguwar rayuwar da ta zarce ta su, amma duk da haka sun fi mu hatsabibanci. Dan haka mun samu gargaɗi daga gurin kakaninmu da ba mu riski zamani ɗaya da su ba, duk da doguwar rayuwar da suke yi. Sun yi mana gargaɗi da mu guji sharri da kuma kaidin ɗan Adam.
Sai dai mun kalli jan kunnen na su, tamkar tatsuniya da hikayoyi, ta yaya halittar da muka keɓanta da wasu abubuwa na musamman sama da su za su iya cutar da mu?. Sai dai kash! Ashe rashin sani ya fi dare duhu, kuma yaro bai san wuta ba sai ya taka.
Ku biyoni ku ji yadda bil adama, ya zama sanadin rusa rayuwarmu, da haifar da matsananciyar gaba tare da kassara zuriyarmu muka watsu a duniya, cike da gaba da ƙiyayyar junanmu, bayan kasancewar mu ahali guda."
Cikin rawar jiki ta buɗe ɗaya shafin, ba tare da ko neman guri ta zauna ba, domin kuwa zuciyarta cike take da ɗoki, da son jin tayaya aka haihu a ragaya, ta yaya bil adama ya fi Aljani hatsabibanci, har ya yi silar kassara rayuwar Aljani.
Allah ya bawa kakanmu tsawon rai, ya yi dubbanin shekaru a raye, har ya fara rikiɗewa ya koma fatalwa saboda tsufa. Fatalwa ba wai mamaci ne zai dawo ya din ga tsorata mutane ba, kamar kamar yadda bil adama suka zata ba, a'a riƙaƙƙen aljani da ya tsufa shi ne yake zama dodo fatalwa ko fatalwa.
Kakanmu, mai suna Dirsham da ake yi wa laƙabi da Jaddul jinn, wato kakan aljanu, ya yi shekara da shekaru a bigiren da yake, ya tara tarin 'ya'ya masu yawan gaske. Ko a cikin sauran jinsin aljanu da ba namu ba, su na tsoron sa, kuma su na girmama shi. Na san da mamaki da na ce jinsin aljanu, za a yi tunanin ko gaba ɗayanmu jinsi ɗaya ne. A'a mu ma mu na da jinsi-jinsi kamar yadda bil adama, suke da ƙabilu daban daban, akwai jinnil Ashiƙ, sihir, amar, marid, uƙum, da dai sauransu, kuma yana rubuce a cikin wani littafi da nake kan rubutawa, wanda ci gaba ne da wani tsohon aljani ya rubuta, wanda haryanzu ina kan bincike, ban gama rubutunsa ba.
Wannan fatalwa yana rayuwa, da iyalinsa baki ɗaya, a wani ƙasurgumin daji, a wani yanki na gabashin duniya.
Tun farkon tarihin duniya, ɗan Adam bai taɓa wanzuwa a gurin ba. Yana gudanar da rayuwar sa yadda yake so da, da iyalinsa, ba tare da wani shamaki ba, adadin yawan iyalan da ya tara sai da suka fara bauta masa, wannan aljani Jaddul jinn, ya zama abin bautar su, kuma sarkin su abin roƙon su.
A hankali al'ummar duniya, su ka ci gaba da yawa, da kuma faɗaɗa a cikin duniya, su na mamayar dazuzzuka suna mayar da su alƙarya.
Kwatsam wataran hanya ta fara biyo da bil adama ta wannan daji, suna wucewa a kan dabbobin su, su ratse su tafi buƙatunsu da fatauci, hakan ya fara takura aljanun da suke rayuwa a gurin, domin kuwa su kan bi ta kan ƙanan yaransu, da sauran kayan amfanin su, su yi musu ɓarna. Aljanu suka kai wa Jaddul jinn ƙara, a kan abin da bil adama ke yi musu, amma sai ya ce ayi musu uzuri, ba sa ganinmu ne, dan haka kar a cutar da su, duk lokacin da suka zo wucewa kowa ya kwashe abin sa mai amfani kawai a ba su hanya.
A irin son zuciya irin na ɗan Adam, kwanci tashi sai suka fara yada zango a wannan daji, da aljanu suka shafe dubbanin shekaru suna rayuwa a ciki. Daga ya da zango, kawai sai suka nemi guri suka yi zamansu, kasancewar dajin akwai dabbobi masu tarin yawa, akwai tsirrai da kayan marmari sosai a ciki. Mu kan rikiɗa mu shiga jikin dabbobi mu yi rayuwa, ko mu shiga jikin bishiyoyi ko tsuntsaye, amma ba tare da tunanin makomar sauran halittun gurin ba, saboda tsabar son kai suka din ga kashe dabbobin nan su na cinyewa, suka din ga sare bishiyoyi masu ɗauke da gidajenmu, su na ƙona bishiyoyin su na gidaje. Sannan suka din ga gayyato 'yan uwansu su na taruwa a dajin nan da muke rayuwa.
A wannan lokacin, tsufan wannan aljanin da ake bautawa Jaddul jinn ya ƙazanta, bai mutu ba, kuma ba a canza sarki ba, ga rashin lafiya yana fama.
Bil adama suka din ga cutar da mu, hakan ya sanya muka fara ƙoƙarin ramawa, ta hanyar kashe musu dabbobi, yaranmu su kan shiga jikin tsutsotsi su cinye musu amfanin gona. Sai dai duk da hakan, ba su fasa cutar da mu ba yadda su ka ga dama ba, hakan ya sanya sarkin nan ƙoƙarin ɗaukar mataki da kansa.
Ya sanya yawunsa a ruwan shansu, dabbobinsu suka din ga sha su na mutuwa, yaransu suka din ga rashin lafiya, suka fara ganinmu muraran mu na tsoratar da su, mu na haukata wasu, mu ka hana su sukuni da kwanciyar hankali. Sai dai suka nuna mana gaba da gabanta, domin sun shayar da iyayenmu mamaki na wannan lokacin, suka samo wani hatsabibin boka, ya zo ya yi wani hatsabibancin ya kama Jaddul jinn , duk da tsufan da ya yi, babu tausayi ba tare da duba tsufan da aljanin nan ya yi ba, bokan ya gayyato 'yan uwansa bokaye, suka yi masa girkar wannan fatalwar aljani, ya zama mallakinsa, ya bautar da shi. Ya mallake da yawa daga cikin waɗanan jinsin na aljanu yake sarrafa su yadda yake so.
Wannan zalunci ba zamu taɓa mantawa da shi ba, sai dai ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne, domin kuwa ba mu ƙara waiwayar su ba, sai bayan wasu shekaru, dan su na ji suna gani wannan boka, ya sanya babansu a cikin wata kwalba ya ajiye a rijiya, bayan da ya daina yi masa amfani.
Sun zuriyar Jaddul sun shiryo gagarumar fansa, ta ko a mutu ko ayi rai, cike da alwashin kawo ƙarshen duk wani iri-irin zuriyar wanda suka yi mana wannan cin zarafi.
Jin ta gaji da tsayuwa, ya sanya cikin rawar jiki ta nemi guri ta zauna, domin ci gaba da karanta littafin, sai dai zamanta ke da wuya ta nemi littafin ta rasa. Ta ɗaga kai ta ganshi a can sama cikin litattafan da yanar gizo gizo ta rufe.
"Da izinin wa ki ka ɗaukar mini littafi ki ka karanta?" Ya yi maganar yana kallon ta.
Nana ta girgiza kai ta ce "Ba iznin kowa?"
"Ki ci gaba, sai kin karanto ranar mutuwar ki wataran"
"To mutuwa ai dole ce, Allah ya sa mu cika da imani" shiru ya yi mata ya ci gaba da gyara litattafnsa.
"Amma dan Allah kai a wani jinsi ka ke na aljanun?" Shiru ya yi bai bata amsa ba.
Ta ci gaba da cewa "Ina son na ƙarasa karanta littafin nan, dan jikina yana bani yana da alaƙa da abin da ka ke iƙararin kakanina sun yi. Ko su ne wanda suka gayyato bokan? Ko kuma bokan ne kakana? Dama sarkin baka ya ce na tambaye ka me kakanina suka yi maka"
"Idan ki ka ci gaba da matsawa, gwargwadon sanin labarin, gwargwadon yadda za ki saka na canza na fito miki a ainihin kalata, ki bar komai a yadda yake kawai" ta buɗe baki za ta yi magana ta ji an ce "Anty Nana" muryar ɗan ƙaramin yaron nan Muhsin, ɗalibinta ta ji.
Da sauri ta kalli ƙaisar ta ce "Muryar ɗalibina muhsin na ji"
Cikin ko in kula ya ce "Eh shi ne, tsafi ake da sunansa, za a ba wa aljana jininsa" waro ido Nana ta yi, ta nufi gurin da take jiyo muryar yaron.
Ƙaton rami ne, matar take ƙoƙarin hankaɗa shi, Nana ta ga kamar ta san matar, amma ta kasa gane wace ce, yaron ya din ga miƙo wa Nana hannu yana kuka.
Gadan-gadan Nana ta nufi matar, tana ƙoƙarin ƙwace yaron.
"Nana" ta ji an kira sunanta.
"Na'am" ta amsa da ƙyar tare da buɗe ido.
Wata Nanny da suke aiki tare a makaranta ta gani.
Nana ta ce "Laaa Inna, ke ce ya aka yi ki ka san gidanmu?"
Wadda ta kira da Inna ta ce "Ina fa, wucewa na zo yi ta unguwar nan, na yi ta tambaya aka nuno mini gidan nan. Na shigo aka ce mini kina nan kina bacci. Sai kuma ki ka tafi babu ko sallama"
"To wace sallama zan yi, ya riga ya kore ni, bari na kawo miki ruwa"
Inna ta ce "A'a yi zaman ki, dama wucewa na zo yi, na ce bari na nemi gidan su yarinyar nan na je, tun da muke tare kin sha yin rashin lafiya ban taɓa zuwa ba, ga wannan abu ya faru na ce bari na zo na yi miki jaje, harkar irin makarantun nan sai a hankali, masu karatun ma ya suka ƙare balle mu. Kin ga har gida aka je aka same ni, aka gaya mini gidan wani hamshaƙin mai kuɗi, wai 'yar sa ce za a din ga yi wa rainon yaro. Mijinta ba ma zauni bane ba, ta koma gidansu to tana da ciki, ga kuma yaro wai za a din ga kular mata da yaron, tun safe ta je makaranta ta dawo, ga albashinka kuma ga abinci. Amma da na je matar nan ta ƙare mini kallo, wai ban yi mata na yi tsufa da yawa, saboda iya shege irin na masu kuɗi"
Nana ta ce "Amma rashin sani ya fi dare duhu, da sun san irin kirkin ki, da amanar ki da ba ta ce haka ba"
Sosai Nana ta ji daɗin zuwan Inna, dan rabon da ayi sallama ace gurinta aka zo, ƙawa ko makamancin haka har ta manta, ga dai Inna dattijuwa ce amma ta na son Nana.
Hirar da suka yi, sai ta ɗebe wa Nana kewa, ta kai a ƙalla awa uku a gidan, suka yi sallar la'asar, sannan Nana ta fito raka Inna.
A hanya Inna ta ce "Ni kuwa Nana, me zai hana ke na kai ki, ko za ki yi wa matar nan, ki din ga yi mata rainon, tun da kin bar aikin koyarwar nan zaman haka babu daɗi, yana daga dalilin da ya sanya na ce lallai bari na nemo gidan ku na zo, na san baki da girman kai "
Nana ta ɗan yi shiru ta ce "Inna zan yi, amma sai na yi magana da Baba idan ya amince"
Cikin farin ciki Inna ta ce "Yauwwa Nana, ai na san ba zaki bani kunya ba, gobe in Allah ya kaimu zan zo da wuri, idan ya amince sai mu tafi kar a rigamu"
"To shikenan, na gode sosai da sosai Inna Allah ya saka da alkhairi, ga wannan kya ci goro" ta yi maganar tana miƙa mata dubu ɗaya a cikin kuɗin da baban Muhsin ya bata.
Inna ta kalla ta girgiza kai ta ce "A'a ke da yakamata a tausaya miki, kin rasa aikin ki, ni ba zan karɓa ba" Ba yadda Nana ba ta yi da ita ba, amma fafur ta ƙi, suka yi sallama.
Haka kurum Nana ta ji tana ɗoki da fatan Allah ya sa matar ta yadda, ko ba komai ta din ga samun abinci cikin kwanciyar hankali ko sau ɗaya ne a wuni.
Tun da Inna ta tafi, Nana ta duƙufa da addu'a, a kan Ubangiji Allah ya taimake ta, idan alkhairi ya tabbatar ma ya kuma kare ta daga dukkanin abin ƙi, ya sanya kuma larurar da ke tattare da ita, ta kunyata.
Ba ta samu yi wa Baba maganar ba, sai washegari da safe.
Ta zo gabansa ta durƙusa, ta gaishe shi ya amsa, ya ce "Wallahi ko sisi ban wayi gari da ita ba, balle na baki na koko ko naira ɗari ce, ita kuma waccan azzalumar ina ji ina gani, 'ya'yana ne suke kawowa amma sai ta ga dama za ta bani balle ta sammiki, bari Gaddafi ya shigo na karɓi kuɗi a gurinsa, sai na baki ki sai koko ki sha"
Nana ta zauna sosai ta ce "Baba ba kuɗi na zo karɓa ba, magana na zo mu yi. Dama wata wadda muka yi aiki tare da ita a makaranta ce, ta zo mini da wata magana. Wani gida ne suke so za ayi musu rainon yaro, za su din ga biya ta ce ko zamu je na gani, idan za su ɗauke ni na ce bari na tambaye ka"
Ya ɗan yi shiru ya ce "To ke Nana, ke da za ki yi aure? Ina ke ina wani aiki kuma?"
"Baba ko yaya ne, ko na wata ɗayan ne na rage, kuma za a din ga bani abinci, kafin na taho gida"
Sai Baba ya washe baki tare da gyara zama ya ce "Allahu Akbar, to ai babu laifi Nana, tun da za su ɗan din ga baki abin kaiwa bakin salati, to Ubangiji Allah ya taimaka ya sanya su ɗauke ki. In an samo abincin dai kar a manta da gyatumi, a kawo na neman albarka" Jinjina kai kawai ta yi ta tashi ta koma ɗaki.
Ƙarfe tara da rabi, sai ga Inna ta zo, Nana ta sanya hijjabinta suka fito, Allah ya taimaki Nana Baba ya fita, balle ya tsayar da Inna ya yi ta yi mata surut wanda aka tambaye shi da ma wanda ba a tambaye shi ba.
A hanya Inna ta ce "Nana, director fa babu lafiya, ni gaba ɗaya ma na manta wallahi, abinka da jarababben mutum kwana biyu har mun sarara a makarantun"
Nana ta ce "Subhnallah me ya same shi?"
"Oho masa, ranar dai da ya sallame ki, an tashi daga makaranta da yamma, ya yanke jiki ya faɗi, ɓarinsa na dama ya daina aiki. An kai shi asibiti an yi gwaje-gwaje an rasa me yake damunsa"
A take jikin Nana ya yi sanyi, ta shiga fargabar kar dai ƙaisar ne ya yi masa wani abu.
Inna ta ci gaba da yi wa Nana hira, kasancewarta mai surutu, hankalin Nana kuwa sam ba ya kanta.
Tun da su ka doshi gate ɗin layin, Nana take kallon dogwayen gine-ginen layin. Duk a ƙasan unguwar su rukunin gidajen yake, amma ba ta taɓa zuwa ba.
Su na daf da shiga gate ɗin layin, ta ga dandazon raƙuma sun fara fitowa daga layin.
Rikicewa Nana ta kusa yi, amma ta fara tunanin wace Addu'a za ta yi, kawai sai ayar waraddallahu lazina kafaru, ta faɗo bakinta, aikuwa ta riƙe ta din ga maimaitawa.
Sai raƙuman suka din ga darewa, su na ba su hanya, Inna kuwa ba ta san bidirin da ake yi ba, sai yarfa hannuwa take tana zuba kamar an jefe ta a ka.
Nana na sanya ƙafarta a cikin gidan, ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, ta ji gangar jikinta, tamkar ba za ta ɗauke ta ba.
Ta daure ta ci gaba da addu'a. Inna ta ce "Nana kalli gida na alfarma, kalli motoci arziki ya yi. Mu tamu ta ƙare ina fatan Ubangiji Allah ya tsunduma ki a tandun arziki Nana, idan kin tuna da ni ko 'yar wanke-wanke ki ɗauke ni zan yi miki." Halin da Nana ke ciki bai hanata murmusawa ba, amma ba ta yi magana ba.
Har cikin falon gidan suka isa, su ka gaisa da matar gidan. Ta ce "Bari na saka a kirawo muku ita"
Ta umarci wata 'yar aiki, da ta kira Shukura, sannan ta kawo musu ruwa da lemo.
Ba a jima ba, aka kawo musu uban ruwa da lemo kaya guda, har da su cincin aka ajiye musu.
Wata matashiyar mace ce, da a ƙalla za ta shekara ashirin da bakwai, ta fito da tsohon ciki tana ɗan yamutsa fuska ta zo ta zauna.
Suka gaisa sama-sama, sannan Inna ta ce "Dama wata 'yar uwata na kawo miki, ki duba ko ita za ta yi, ta din ga rainon yaron?"
Matar da suka tarar ta farko ta ce "Ahhh ni dai ta yi mini"
Shukura ta ce "Mummy"
"Ba wani Mummy, ba na son iyayi, wannan yaron naki mai shegen kukan tsiya ma, wannan dai ai ta yi kalar haƙuri kuwa. Idan kuma ba haka ba ki tattara ki koma gidan ki, ki ƙyale ni a gidana"
Murmushi Shukura ta yi ta ce "Kai Mummy, to ai shikenan, Mummy ta ce kin yi, sai ki fara zuwa gobe in Allah ya kaimu. Sai dai gaskiya ba na son ƙazanta, kuma ba na son cin zali dan ba zan ɗauka ba. Kuma goben ba da kin zo za ki fara ba, family doctor zai zo ya ɗauki jininki, a tabattar ba ki da wani ciwo. Albashinki dubu ashirin ne, za kuma ki din ga break fast, da lunch a gidan nan. Daga safe zuwa ƙarfe biyar za ki din ga kula da shi, idan ma za ki tsaya ki ci abincin dare duk babu matsala"
"In sha Allah ba zai gagara ba, kuma duk zan kiyaye"
"Shikenan, za ku iya tafiya"
"Su tafi ai kya ba su kuɗin mota, a kawo leda a ƙulle musu kayan nan, tun an cinye abincin safe, kuma ba a gama na rana ba"
Nana na noƙewa, Inna kuwa ta karɓar musu, tana ta zuba godiya kamar wanda aka gafartawa zunuban su.
Sun tashi za su tafi, har sun je tsakiyar falon, matar ta ce "Ba ki gaya mana sunan ki ba, da kuma unguwar ku"
Nana ta waiwayo ta ce "Sunana Asma'u, amma Nana ake ce mini. Gidanmu a wajen makarantar