Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
karɓa suka cinye"
Nana ta ce "Gashi ya bani" ta miƙa wa Baba kuɗin da ba ta san ma nawa ne ba.
Ya saka hannu ya karɓa, ya duba naira dubu biyu ce. "To shi wannan saurayin naki kuma da haka ya zo, ka zo wurin budurwa ka ɓuge da bata dubu biyu kamar abin tsiya. Wancan saurayin naki Sule ya fi abin arziki. Ungo ga wata naira ɗari nan a aljihuna kya sai awara, wannan kuma ayi 'yan dabaru a ci abincin dare"
Nana ta karɓi naira ɗarin ta ce "To Baba na gode sosai"
Shigarta ɗaki ke da wuya, Suwaiba ta ja uban tsaki ta ce "Wallahi Nana ba zaki taɓa kan gado a rayuwar ki ba, yanzu kuɗin duk ki ka ɗauka ki ka ba wa Baba, alhalin kin wuni daga ke sai ruwan koko a cikinki, kuma dai duk wannan abin da ki ke yi, dan ya ce kin fimu ƙaunarsa, amma ba tausayinki yake yi ba, haryanzu kallon ki yake yi da laifin babar ku"
Tabbas maganganun Suwaiba haka ne, amma har ga Allah tana tausayin mahaifin nasu da gaske, ba ta ƙaunar gori da wulaƙancin da mama take yi masa a kan riƙe gida, amma ita ta lura ko a jikin sa, hakan baya wani damun sa.
"Nana, wai da gaske Auwwalun gidan mai koko ne yake zuwa wurinki? Wannan na ajin saukar, lokacin mu na zuwa islamiyya?"
Cike da ƙwarin gwiwa Nana ta ce "Eh shi ne, meyafaru?"
"Lallai Nana, me na sama ya ci balle ya jefowa na ƙasa? Ban da koyarwar nan fa, ban ce yana da wata sana'ar ba"
"Suby arziki ai na Allah ne, kuma ni 'yar waye da zan ɗaga kai na ce sai wani?"
Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Lallai kam"
Nana kuwa a zuciyarta, tana addu'a Allah ya tabattar mata da alkhairi, ko a daji malam Auwal yake rayuwa, muddin zai rabata da rayuwar wannan gidan na su, ta samu farin ciki haka take fata.
Ta cire hijjabin jikinta, ta saka wani ta fita tsakar gida ta tarar da mama su na ta dambarwa da Baba a kan dubu biyun da ta bayar.
Kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ta ce "Baba dan Allah zan je bakin layi, idan maimuna tayi waina na sayo"
Baba ya ce "To hanzarta, ba na son fitar daren nan, mussaman da ba lafiya ce da ke ba, ki hanzarta" ta nufi hanyar fita cikin takunta mai kama da na ƙasaita.
Dai-dai lokacin da yayi sallama yake shigowa, ita kuma ta saka kai za ta fita, suka yi kiciɓis, gabanta ya yanke ya faɗi, ta ja da baya cikin tashin hankali da bugun zuciya mai tsanani.
Ayshercool
08081012143
What's app only please.
BUZU
Aisha Adam (Ayshercool)
YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/002)
BRIGHT PENS 3rd batch
arewabooks ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724
08081012143
P5
Daga tsakar gida Baba ya ce "Muryar wa nake ji haka, kamar Gaddafi?"
Kallon kallo Gaddafi suka yi da Nana daga bisani ya ce "Za ki matsa, ko sai na bi ta kan ki?" Jikinta na tsuma, ta ja da baya ta bashi hanya.
Sai da ya ja tsaki, sannan ya shiga cikin gidan.
"Kai kuwa Gaddafi ya da zuwan dare haka, kamar mara gaskiya?"
Ya numfasa ya ce "Na tsaya wani uzuri ne a hanya, fatan na same ku lafiya?"
Baba ya ce "Lafiya ƙalau, ya ikkon?"
"Lafiya kalau, amma ya na ga gidan duk ya canza?"
Baba ya kalli gidan ya e "Damunar nan, ruwan ƙarshe da aka yi ne, ya yi mana gyara, ya zubar mana da katanga, masai ta haɗe da rijiya... Cikin alfahari mama ta karɓe zancen, da bashi labarin cewa mijin uwar ɗakin Jamila ne, ya sanya aka gyara katangar gidan.
Ko da Nana ta dawo, duk su na tsakar gida, sun kewaye Gaddafi, ana hira ya ajiye musu ledojin da ya zo da su.
Ɗakinsu ta shiga ta zauna, ta cinye wainar fulawan, da bai fi loma huɗu ta yi ba, kuma babu in da ta je mata sam.
Ƙasan zuciyarta, tana ta addu'a, Ubangiji Allah kar ya kawo abin da zai haɗata da Gaddafi, saboda karon su ba ya yi mata daɗi.
Tana zaune Nasiru ya shigo ya kawo mata abin da aka raba aka bata, ta karɓa tayi godiya, ta ajiye a gefenta ta kwanta, ba tare da ta buɗe, ta ga ko mene ne ba.
Sannu a hankali Malam Auwal yake nufo in da da take yana murmushi, ita ma murmushin take yi, tana jiran ƙarasowarsa, sai dai kafin ya ƙaraso in da take, ya bayyana cikin ainihin suffarsa mai tsayin gaske, ya shiga tsakiyarsu. A hankali ya din ga rage tsawonsa ya dawo daidai da tsawonsu.
Danƙo malam Auwal yayi, ya zura hannunsa a cikinsa, yana zaro kayan cikinsa, yana watsarwa a ƙasa, ya ƙarasa har maƙogwaronsa, ya zura faratansa zai zaro maƙogwaronsa.
A fusace Gaddafi ya fito tsakar gida yana bala'i ya ce "Wai wannan 'yar abu kazan uban, ba ta daina wannan iskancin ba dama?"
Mama da suka fito tare da Baba daga ɗaki a burkice, suka yi burki a tsakar gida, su Suwaiba tuni sun yo waje daga ɗakin, cikin rige-rige. Nana kuwa na cikin ɗakin, tana ta uban kuka da gurnani, tana ihu iya ƙarfinta.
"Gaskiya na fara gajiya da wannan bala'in, kullum sai bawa ya sanya haƙarƙarinsa a ƙasa ya kwanta, ya fara bacci, sannan ta fara ihu, gaskiya na fara gajiya." Mama ta yi maganar a ƙufule.
Ɗakin Gaddafi ya nufa a fusace, Baba cewa yake "Gaddafi ka bi ta a hankali dan Allah, ka tofa mata abin da ya sauwwaƙa".
Yana shiga ya tarar da ita, tamkar ana girgizata, yatsun ƙafafuwanta duk sun ƙandare, kamar kuturwa.
Ƙafa ya saka yayi ball da ita, tamkar abar banza, yana zabga mata ashariya.
Sai dai ba ta san yana yi ba, iya ƙarfinta take ƙoƙarin karanta addu'a a cikin baccin, amma ta kasa.
Gaddafi ya danƙo ta, ya fito da ita tsakar gida, ya watsar da ita a wurin, ya ce "Ku wuce ku kwanta, idan ta gama iskancin ta tashi, ba wani aljanu iya shege ne kawai, kowa ya koma ɗaki ya yi kwanciyar sa".
Jikin Baba ya yi sanyi ganin halin da Nana ke ciki, ya ce "Ba iya shege bane, na kira ma an yi mata karatu fa, kalli yadda jikinta yake yi" yayi maganar yana tsugunawa a kanta, duk da wannan abun na Nana shi kansa ya ishe shi.
Wasu lokutan, sai yayi tunanin ko ƙarya take yi, amma idan ya yi la'akari da wasu abubuwan, sai ya ga normally mutum ba zai iya haka ba.
Sanyin Asuba, da zafin cizon cinnaku ne, ya sanya Nana farkawa, daga nannauyan baccin da take yi, da babu komai a cikinsa ban da azaba da wahala.
Ba ta damu da yadda ta ganta a tsakar gida ba, a tunaninta ita ta fito da kanta ta kwanta a gurin, dan yanzu ba ta mamakin yadda wasu abubuwan suke faruwa da ita.
Alwala tayi ta shiga ɗakinsu, ta yi salla, sannan ta tashi su Suwaiba.
Cike da farin ciki ta tashi, dan yau ɗin ta kama litinin ce, za a koma hutun makarantar boko.
Domin tana koyarwa a wata private school, da Nanny ta nema a makarantar, sai malamar da take koyar da 'yan kindergarten ta koma garinsu, aka bata riƙon ajin, kasancewar tana da kwalin sakandare, sai dai ƙoƙarinta da sabon da tayi da yaran, ya sanya suka ƙyale ta, suke ba ta dubu bakwai a wata. Tana matuƙar jin daɗin, yadda take shiga cikin ƙananan yaran, su yi ta tsalle-tsalle da wasa tana koyar da su. Sai dai ta tsananta addu'a, Allah ya rufa mata asiri, kar ciwonta ya tashi a makarantar, ta cutar da 'yan yaran.
Tana ta hanzari, ta gama abin da zata yi, ta shirya ta fita, Gaddafi ya shigo da buta a hannunsa, da alama sai a lokacin zai yi sallar asuba.
Yana ganin Nana ya tsaya ya ce "Yauwwa ke Nana, dan abu ta kaza kazanki, idan ki ka kuma tashi cikin dare, ki ka hana mutane bacci kina yi mana ihu, sai na yi miki shegen duka, dan wallahi sai na karya ki na gaya miki. Mahaukaciyar banza maƙaryaciya" Duk da ba wannan ne karon farko, da ake kallon ƙaryar ciwon take yi ba, amma tana mamakin yadda za ace, tana wulaƙanta kanta a gaban mutane, ta hanyar yin wasu abubuwa tamkar mahaukaciya.
Ba ta fatan ko maƙiyinta, Allah ya jarrabe shi da irin larurarta, ba dan haka ba da ta roƙi Allah ya jarrabi Gaddafi da jarrabawar da ya daɗe yana ƙaryata ta, a kai.
Ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da gudanar da aikinta, ba ta damu da rashin samun abin da za ta karya ba, duk ta ga an yi abin karin kumallon, ta kammala shirinta ta fice.
Nana akwai ƙoƙarin sammako, dan haka kusan hatta malaman, duk a makarantar suka tarar da ita, ta ji daɗin ganin yaran sosai, kamar yadda su ma suka ji daɗin ganinta, suke ta murna tamkar sun ga mahaifiyarsu.
*****
Ƙurii ta yi masa da idanu, yadda yake ta jujjuya kofin kokon hannunsa, ya kalli yarinyar da take kwance a kan katifa ya ce "Ita wannan ba ta tashi rashin lafiya ba, sai da aka koma makaranta?"
Babbar macen da take gefe tana karyawa ta ce "Dama rashin lafiya ana saka masa lokaci ne? Larura ce Allah ya kawo mata" ya jinjina kai ya ci gaba da cakalar abincin.
"Wai Auwwalu me yake damunka ne?"
Auwal ya numfasa ya ce "A ina?"
"Ka ƙi cin abinci, sai jujjuya kofin kawai ka ke yi" ya jinjina kai ya ce "Mama magana na ke son yi, amma ban san yaya za ki kalli abin ba"
Ta ajiye kofin hannunta, ta ce "Ko ma a yaya zan kalle shi, gaya mini ina sauraron ka"
Ya tattara hankalinsa, cikin nutsuwarsa da kamala ya ce "Mama dama akwai wata yarinya ne, da nake zuwa wurinta, to shi ne mahaifinta ya ce in tura magabatana ayi magana"
Tayi masa ƙuri da ido, sai da ya kammala, sannan ta ce "Me ka taka haka ne Auwwal, da zaka ɗaukko maganar aure? Fili ne fa kawai da kai a ƙasa, babu muhalli ba wata uwar da ka ke yi tun da ka kammala makaranta, bayan koyarwar nan sai 'yan kame-kame, abin da ka ke samu mu kanmu bai ishe mu ba, balle ka yayimo mana wata a bar maganar nan, kar ka sake tayar da ita yanzu maganar aure, ba nan ba ce"
Auwwal yayi shiru, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ba ya son mutuncinsa ya zube a idon Nana, da mahaifinta. Har cikin ransa yake son ya taimaketa, mussaman da ya fuskanci ita sam ba ta da buri, kamar na sauran 'yan matan zamani.
****
A wannan karon ma, Alhaji zailani ne a zaune a gaban Malam, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Wanda aka samu ka ce duk ba su yi ba, abin ba zai yiwu da su ba, na rasa abin yi gaba ɗaya"
"Alhajin Allah, ai ci gaba da duddubawa za ayi, za a samu dai ba za a sare ba, sai kuma ɗaya aikin da na baka, yaya ake ciki yau kwana ashirin da huɗu da fara shi ko?"
Alhaji zailani ya ce "Eh, na kusa kammala shi wannan, kuma na fara ganin alamun nasara"
Mutumin yayi dariya ya ce "In dai zaka yi biyayya, to za ka samu duniya yadda ka ke so, shi wanda ka ke maganar a kansa, shi ma ba a zaune yake bane ba, wani shu'umin aljani nake so ya yi mana aikin nan, zai iya dan yana da juriya da baƙin naci, amma fafur yaƙi"
Alhaji zailani ya tattare babbar rigarsa ya ce "Dan Allah ka tambaye shi, ko me yake so zan yi masa, ba ni da burin da ya wuce, na ga bayan fatuhu, gaba ɗaya shi ya hana arzikina haɓaka, ba a faɗar sunan kowa sai nasa"
"Ai duk wani tayi, da mu kan yi wa aljani, domin mu saka shi aiki yayi, na yi masa ya ce ba zai yi ba, akwai aikin da yake yi. Makirin aljani ne, idan na matsa masa zai iya ɓata mini wasu ayyukan, amma ka ci gaba da waɗanda na baka, sallar asuba da la'asar sai kwanakin da na ɗibar maka sun cika, sannan za ka ci gaba. Zan so ace kafin lokacin a samo yarinyar nan, aikin zai fi tafiya dai-dai "
"In sha Allah, zan ci gaba da ƙoƙarin hakan, za a samo yarinyar duk in da take"
"To shikkenan, kai nake sauraro" yayi maganar yana ci gaba da zazzana ƙasar gabansa.
*****
Shigar Nana gida babu daɗewa, Baba ya ce mata, taje gidan da Jamila take zuwa, ta kira masa ita. Nana ta ji daɗin hakan, domin a zatonta Baba zai tsawatar wa Jamila ne, saboda yadda take zuwa ta shantake a gidan, ta wuni kamar a gidan ubanta.
A ƙalla Nana tayi sallama ya kai sau huɗu, sannan aka amsa aka ce ta shiga.
Jamila ta tarar a zaune a falo, tare da matar gidan maman khairat, sai kuma wata hamshaƙiyar mata a gefe, su na ta hira.
Rashin dacewar hakan Nana ta gani, bai kamata ace Jamila tana tsakiyar su, su na ta uwar hira har tana sallama ba sa jin ta ba.
Nana ta kalli maman khairat ta ce "Ina wuni?"
Cikin sakin fuska ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ke ba kya zuwa gidana, Jamila ce kawai 'yar ɗakina" Nana tayi murmushi, ta kalli matar da tun da ta shigo, ta ƙure ta da ido. Haka kurum gaban Nana ya faɗi, amma ta dake ta gaishe ta.
Cikin ƙasaita ta amsa mata "Lafiya ƙalau 'yan mata ya ki ke?" Nana ba ta iya amsawa ba, jikinta ya hau rawa har bakinta ya nuna ta ce "Ja.jam..jamila Baba yana kiranki" tana faɗar haka kawai ta juya ta fice.
Maman khairat ta ce "Jamsy, meya samu yayarki ne?"
Cikin ko in kula ta ce "Wallahi ban sani ba, kin san tana da aljanu ba wuya ta burkice, kamar sun taɓa mata ƙwaƙwalwa ma"
Maman khairat ta ce "Subhnallah, ƙwaƙwalwa kuma?"
Jamila da ta tashi tana ɗaukar mayafinta ta ce "Wallahi Anty, to sai ta tashi cikin dare tana kurma ihu, ranan fa kwananta biyu ba ta gida, babu ma wanda ya san in da take ba, kullum cikin ciwo take"
Matar da take gefe ta ce "Allah sarki, har ta bani tausayi, amma ta burge ni a nutse take masha Allah. Masu irin larurarta na buƙatar tausayawa da ja a jiki, kar ku ƙyamace ta, abin zai yi mata yawa"
Jamila ta ce "Ai ko ba ka ƙyamace ta, ka yi gudun ceton ranka, duk da ba ta duka, amma idan ta fara ihu cikin dare da gurnani, layin nan ba wanda zai rintsa.
Yanzu hatta ƙawayenta sun daina zuwa wurinta, saboda tsoron kar su kwasa" Jamila ta daɗe tana ba su labarin Nana, sannan ta tafi gida.
Nana kuwa tun da ta baro gidan, jikinta yake wata irin tsuma, zuciyarta take bugawa, haka kurum jikinta ya din ga bata akwai wani abu na ba daidai ba, a tattare da gidan, ko kuma matar da ta tarar a gidan.
"Hasbunallah wa ni'imal wakil. Wa hifzan min kulli shaɗanin marid " ta din ga maimaitawa cike da fatan Allah ya daidaita mata nutsuwarta.
Gaza cigaba da addu'a ta yi, bayan da ta jiyo Baba yana tambayar Jamila, wai gidan uwar ɗakin nata, ba su gama abinci ba, yunwa yake ji, Gaddafi ya bayar da kuɗin cefane, amma an yi girki an hana shi.
Wani malulun takaici, ya turnuƙe Nana, duk wani salo na zubar da kai, Baba ya iya shi, kuma hakan shi sam baya damunsa ko kaɗan.
Tun da Gaddafi ya dawo, Nana take iya ƙoƙarinta, wurin ta kaucewa yin duk wani abu da zai haɗa su, amma hakan ba ya sanya wa, ta tsira daga zagi da cin mutuncinsa.
Wannan bai dame ta ba, kamar yadda malam Auwal ya rage shiga harkar ta, zuwan ma ya daina yi gaba ɗaya, sosai abin yake damunta, zuciyarta na ta son gazgata cewar Aljanin da yake bibiyarta ne, ya shiga tsakaninsu amma wata zuciyar ta hana ta yadda da hakan, domin malam Auwal mutum ne mai addini, kuma ta yadda duk abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, Aljani bai isa ya hana Ubangiji ikonsa ba.
Duk da ya hanata yin kwalliya a lokacin zuwa makaranta, ko da kuwa man leɓe ne, dan haka yau ta saka jam baki, ko zata samu ya kula ta.
Ta riga kowa zuwa a ajinsu, ta ɗauki tsintsiya, ta fara share ajin, ta shimfiɗa musu tabarma, ta fito harabar makarantar ta share iya in da za ta iya.
Tana shirin komawa ajinsu, Auwal ya shigo makarantar, jinkirta tafiya aji tayi, ta tsaya ya zo zai gifta ta, ta ce "Yaya Auwal ina wuni" wani zirr ya ji a jikinsa, yanayin yadda ta gaishe shin, ya ce "Lafiya ƙalau" ya wuce ta zuciyarsa cike da damuwa, kamar ya waiwayo ya kalleta, sai jikinsa ya ba shi: shi take kallo, dan haka ya fasa waiwayowa.
Tana ɗan jima a wurin a tsaye, daga bisani ta nufi ajinsu, gwiwa a sanyaye tana tunanin meyafaru Auwwal ya canza lokaci guda.
Tana ta kallon Alqur'aninta, tana son ta yi tilawa, amma zuciyarta na ta gargaɗinta, da tunatar da ita, halin da za ta iya shiga, muddin ta ce za ta karanta.
Tana nan zaune, 'yan ajinsu, suka taru suka fara tilawa.
Malam Auwal ne ya shigo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai dai da ta ɗaga kai, sai su yi ido huɗu da shi yana kallonta.
Sai dai kafin ya kammala ƙarin, ƙafafuwanta sun riƙe gam, su na yi mata wani irin zugi kamar ana karyata.
Gwargwadon ɗaga muryarsu a karatun, gwargwadon raɗaɗi da zugin da ƙafafun nata suke yi mata.
Ba a tashi ba, ta ɗauki jakarta ta bar makarantar, da ƙyar ta nufi gida, tana taka ƙafafuwan nata da kyar.
Ummi ta tarar a gidan, tare da Baba a tsakar gida.
Amsa sallamar Nana suka yi, suka tattara hankalinsu a kanta.
Ummi ta ce "Ummi ya dai na ga kina bin bango, kina tafiya a hankali?"
Ummi ta kalli ƙafafuwanta ta ce "Ƙafafuwana ne suke yi mini ciwo, ba a tashi ba ma na taho gida"
Baba yayi caraf ya ce "Haka dai, kullum cikin ciwo ki ke Nana, yau ƙafa in anjima ciwon kai, gobe kuma ciwon ciki, idan ki ka ƙoshi kuma sai ihu da kururuwa, ni wannan lamarin ciwon naki ya ishe ni wallahi. Can a dangin babarki ki ka kwaso wannan jarabar, ni dangina babu irin wannan"
Ummi ta ce "Baba