Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
zan yi?"
Ya juyo gaba ɗayansa ya zuba mata ido.
Nana ba ta taɓa ƙare masa kallo ba, sai yanzu. A hankali ta fara jin sanyi yana ratsata, bugun zuciyar ta ya fara ƙaruwa.
Cikin sauri ta ce "To juya" ya juya mata. Ta ɗaga robar man ta na kallo, duk rubutun jiki da french ne, ba ta iya gane komai ba.
Ta tsiyayo man, sai ƙamshi yake yi, hannun ta har rawa yake yi, ta kai hannunta bayansa. Sai dai tana ɗora hannunta ta ji tsigar jikinta ta tashi, sanyi na ƙara ratsa ta.
Ta ture gashinsa gefe, ta fara shafa man a bayansa, sai dai tana shafa masa, yanayinta yana canzawa zuwa wani abu, da ta kasa tantance mene ne.
Tsayar da hannunta ta yi a guri ɗaya, ta ƙi gaba ta ƙi baya, jin zuciyarta na rayo mata wani abu a game da shi. Haushin kanta ne ya kama ta, kawai ta ja da baya ta haɗe rai. Ya sake waiwayo wa ya kalle ta. Kamar wanda aka yi wa dole ya ce "Sanyi nake ji"
Murguɗa baki ta yi, ta ja jikinta lungun katifa, ta yi masa shiru. Ganin ba ta da niyyar sake taɓa shi, ya sanya ya tashi ya nemi guri ya kwanta a ƙasa.
Shiru ta yi tana zancen zuci, iya tsawon rayuwarta, ita ba ta taɓa kai hannunta jikin wani namiji tana sane ba. Kuma ba ta taɓa jin abu makamancin irin haka ba, a tattare da wani ba.
'ki shiga hankalinki Nana, kar wannan farar fatar ta ruɗe ki" wata zuciyar ta gargaɗe ta.
Guntun tsaki ta yi, ba tare da ta shirya ba.
"Ya dai?" Muryar Ƙaisar ta dawo da ita tunaninta.
Ta kalle shi, yana ta haɗa wasu abubuwa a cikin kwalabe.
"Kai ne ko?" Ta yi maganar a ɗan ƙule.
"Na yi me?" Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba.
"Ka fi ni sani ai"
Ƙaisar ya girgiza kai ya ce "Sanin gaibu sai Allah ai, ban san me na yi miki ba"
Nana ta ce "Ka sani"
Ya ɗan kalle ta, kawai ya bushe da dariya ya tashi tsaye yana faɗin "Kar ki damu, yanayi ne da bil adama su kan kasance a ciki, ai ba ki yi wani abu ba, ba abin damuwa ba ne ba. Kuma ni bani da hannu a wannan lamarin. Sai dai ina tunatar da ke, kafin ki yi aika-aika ki tabattar da wane ne shi"
Banza ta yi masa, ta nufi wata ƙofa da take buɗe.
A hankali ta buɗe idonta, tana kwance a kan katifarta, ta kalli gurin da yake kwance, yana nan kamar yadda ya kwanta. Ya dunƙule jikinsa guri guda, jikinsa ko riga babu. Ta shafa jikinta ta ji gumi take yi, amma shi alamu suka nuna sanyi yake ji.
Ta yinƙura da ƙyar ta tashi, ta ɗaukko bargonta a saman wardrobe, ta nufe shi.
"Ka tashi ga bargo ka rufa"
A hankali ya buɗe idonsa, ya kalle ta, kawai ya mayar ya lumshe. Ba ta haƙura ba ta sake cewa ga shi ka rufa tun da sanyi ka ke ji. Ta yi maganar tana ajiye masa bargon. Hankaɗe bargon ya yi gefe a zuciye, yana ƙoƙarin gyara kwanciyarsa.
"Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka ɗazu ma ka jefa mini bedsheet a kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ƙarfi ta suma a gurin.
*****
Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana gefen gado tana shan abu a cikin kofi.
Da sallama ya shigo ɗakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce "Ya yi baccin?"
Ya ce "Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?"
Ta kwaɓe baki ta ce "Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu"
Ya ce "Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?"
Shukura ta ce "Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan"
"Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun shaƙu, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?" Ya yi magana yana karɓar kofin.
Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce "Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?"
Shukura ta ɓata fuska ta ce "Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi"
"Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya ɓaci" ya tashi ya fice ya bar mata ɗakin.
Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta.
Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya.
Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, miƙa masa hannu take yi, tana faɗin "Dan Allah ka taimake ni"
Lokaci ɗaya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dunƙulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da durƙusawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi.
Mutumin da yake bin ta ya ƙaraso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi.
Cikin tashin hankali ta ce "Daddy"
"Ki yi haƙuri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki"
Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar naƙuda take faɗin "A'a Daddy, dan Allah ka bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah"
Ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake buƙata"
Mutumin nan mai farar riga, ya buɗe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa "Dan Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi haƙuri".
Bai saurare ta ba, ya durƙusa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faɗo.
Ya ɗauke shi har mabiyiyar, ya miƙa wa Alhaji Zailani.
Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wuƙa, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwan sa a sama.
Ihu take iya ƙarfin ta, tana yi masa magiya, amma ya ɗaga wuƙar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana ɗaga kai ta ga Nana.
Nana ta jefa mata wata sharɓeɓiyar wuƙa, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa wuƙar da Nana ta jefo mata.
"Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?" Ta buɗe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta da ke ɗauke da matsananciyar damuwa.
"Meya faru?" Ya sake tambayarta.
Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali.
Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba.
*****
Da safe Nana na ta karkaɗe ɗaki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki ɗaya. Sai dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin Ƙaisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi.
"Zan yi wanka" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara ɗakin.
Ta kalle shi ta ce "To banɗakin zan biyo ka ko ya za a yi?" Ta yi maganar cikin tsiwa.
Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba, kawai ya wuce banɗakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata.
"Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba"
Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet ɗin da ta gama shimfiɗawa ya rufa yana rawar sanyi.
A hanzarce ta ɗago a ƙule ta ce "Lafiya, meye haka wai?" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda a lokacin ta gama sanya zanin gadon.
Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya ɗauki bedsheet ya sanya ya miƙe, ya watsar mata da shi a gurin.
Ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata ɗakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna ya takure jikinsa, ɗumin ranar yana taɓa shi.
Nana ta ci gaba da mita tana ƙara gyarawa.
Muryar Habu ta jiyo, ta leƙa ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ƙasa-ƙasa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji.
Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ƙofar ɗakin. Ta amsa masa. Ya ce "Na shigo?"
"Eh bismillah" sai ta ga ya shigo shikaɗai.
Nana ta ce "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Ya rayuwar?"
Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce "Lafiya ƙalau"
"Ga wannan" ya yi maganar yana ba ta leda.
Jiki a sanyaye ta ce "Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ƙaddara, wannan ɗawainiyar ta isa haka, kullum sai kun kawo mana Abinci, ga ɗawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah"
Ya yi murmushi ya ce "Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni" Nana ta jinjina masa kai.
Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce "Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ƙarar ki, ya ce ki na yi masa rashin kunya, ki na ɗaga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi haƙuri da shi dan Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki yi haƙuri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare"
Nana ta haɗiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce "Hmm ƙara ta ma ya kawo ko? To shikenan na daina"
"Ki yi haƙuri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa"
Nana ta ce "Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma dawowa"
Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya miƙe. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai.
Ya zo ya wuce ya buɗe wardrobe, ya ɗebo kayansa masu datti, da ya nannaɗe ya bawa Habu.
Habu ya karɓa, ya yi musu sallama, ya tafi.
Nana ta din ga kallonsa, bakinta fal magana, amma ya ƙi kallonta.
"Shi ne ka ce ina yi maka rashin kunya ko? To me na yi maka na rashin kunya? Dama ashe ka na magana ni ce ba ka kulawa ko?" Ya lumshe idanunsa yana kaɗa ƙafar sa.
"Idan ba ka yi mini magana, ba zan san na yi maka laifi ba, ko na san abin da ka ke so ba, da wanda ba ka so" ta gama surutunta, ganin ba shi da niyyar tanka mata ya sanya ta kama wani abin.
Kayan miyar da Habu ya kawo, ta zauna ta gyara tsaf, ta yi greating ɗin su. Ta ɗora a kan gas. Tana jin yadda yake tari, saboda zafin attaruhu. Ta dafa taliya da miya.
Ya din ga bin ta da ido, har ta gama.
Ta zuba masa ta ajiye masa komai, ta tashi ta je ta yi alwala, ta dawo ta tayar da sallar azahar.
Ta idar ta yi azkar, ta ninke dadduma, ta gan shi ya haɗa gumi, yana cakalar abincin, fuskarsa ta yi jawur, sai gumi ne yake tsatstsafo masa.
"Lafiya ya na ga ka na gumi, abincin babu daɗi ne?" Ya ja numfashi ya kalle ta, hannunsa riƙe da cokali mai yatsu.
Babu irin tambayar da ba ta yi masa ba, amma bai ba ta amsa ba, har ta gaji ta rabu da shi. A haka ya cinye abincin.
Nana ta rasa abin da ya sanya shi haɗa wannan uban gumin. Idonta ne ya sauka a kan wayarta. A take tunanin mahaifiyarta ya ƙara faɗo mata. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin.
Jiki a sanyaye ta buɗe wayar, ta shiga gurin kira, ta shigar da lambobin kamar yadda ta haddace su, cike da fatan Allah ya sa wayar ta shiga.
Babu zato babu tsammani, ta ji wayar ta shiga. Gyara zamanta ta yi tana fatan Allah ya sa ta ji abin da take tsammanni. Sai dai akasin haka ta ji muryar namiji, muryar mutumin da ta tsana a rayuwarta.
Cikin dakiya ta ce "Baba ina wuni?"
"Lafiya kalau wace ce?"
Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah me wayar nake nema"
Ya ce "To wace ce ke ɗin?"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baba Nana ce, mamana nake nema" ta yi maganar cikin rawar murya, idanunta na cika da hawaye.
"Ai dama na sani, wallahi na sani, na san ba ta fasa bibiyar tsohon mijinta ba, wallahi zan gauraya da ita"
A ruɗe Nana ta ce "Dan Allah Baba ka tsaya ka ji, wallahi ba sa waya da Babanmu, lamba ta ce, dan Allah ka haɗa ni da ita ko muryarta na ji, dan Allah.. ƙit ya kashe wayar ba tare da ta gama faɗar abin da za ta faɗa ba.
Wata irin tafasa zuciyarta ta din ga yi, cike da ɓacin rai da tashin hankali. Wasu irin hawaye masu raɗaɗi suka fara biyo fuskar ta.
Ta ɗauki wayar ta yi jifa da ita, caraf ya cafke wayar.
Ya kalli yadda hawaye yake fita daga idanunta.
Kawai ya ga ta taso za ta fita daga ɗakin, jikinta yana rawa.
Har za ta gota shi, ya danƙo hannunta ya yo baya da ita, yana ƙarewa Ƙaisar kallo da ya bayyana a gefenta yana huci!.
Ayshercool
08081012143
31
Bai kula Ƙaisar ba, ya ja Nana zuwa kan katifa, ya zaunar da ita, idanunta a lumshe, har a lokacin kuma fitar da hawaye suke yi, babu ƙaƙƙautawa. Ya taɓa tafukan hannayenta, ya ji sanyi ƙalau kamar an ciro ta daga ƙanƙara.
Ya ƙura mata ido yana nazarin ta, a take ya tuno ranar da ta shiga ɗakinsu, tana kiran Haidar, su na haɗa ido ta ja da baya ta ƙwala ihu ta faɗi.
Haka jikinta ya ƙandare, ta din ga karkarwa, ya ga wani narkeken baƙin muzuru ya bayyana a ɗakin, yana ta zagaye ta.
Ya sauke numfashi, ya sanya yatsunsa biyu, ya danna bayan kunnenta. Ya miƙe ya bar kusa da ita. A hankali jikinta ya daina rawar, ta buɗe idonta, sai dai tun da ta buɗe idon, ba ta tashi daga gurin ba balle ta ci abinci.
Ya din ga satar kallonta, amma ba ta tashi daga in da take ba, balle ta ci abinci. Yana son ya yi magana amma ya rasa me zai ce mata.
Ta tashi zaune da ƙyar, ta haɗa kai da gwiwa, ta yi kuka mai isar ta. Sai da aka kira la'asar sannan ta tashi ta yi alwala, ta tayar da salla.
Bayan ta idar tana zaune ta yi shiru, ya dawo ɗakin, ya duba gurin da ta gama girkin, babu alamar ta ci abinci.
"Ba za a ci abinci ba?" Ta ji maganar sa babu tsammani.
Ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar mai jiran ƙiris, kawai ta sake fashewa da kuka. Ya yi zuru da ido yana bin ta da kallo, bai ce ta yi shiru ba, har ta yi mai isar ta yi shiru.
Duk ya damu ganin ba ta ci abinci ba, ya rasa me zai ce mata, ga shi yanayinta ya fahimci rigimammiya ce.
Jin motsi a waje ana taɓa gate, ya sanya ya tashi ya rufe fuskar sa, ya fita ya duba waye.
Tsayawa ya yi yana kallon su, mata ne su uku, da ƙanan yara sai wani ɗan matashin saurayi.
"Sannu malam, ko kai ne mijin Nanan?" Ya tsaya tsuru yana kallon su.
"Gurin Nana mu ka zo tana nan?" ya nuna musu ɗakin su.
Suka wuce, Ummi tana cewa "Na yi ƙoƙari fa da na iya kawo mu gidan nan"
Bayan Jamila ya bi da kallo, jikinsa na ba shi wani abu a game da ita.
Wata irin zabura Nana ta yi ta rungume Ummi, ba ta taɓa tsammanin ganin su ba. Ta rungume Jamila cikin farin ciki ta ce "Dama za ku zo ba ku gaya mini ba?"
Ummi ta ce "Mu ki bamu guri mu zauna"
Nasiru ya ce "Hajiya Anty Nana amarya" daƙuwa ta yi masa ta ce "Gidanku"
Ya yi dariya ya ce "Na yi missing ɗin ki sosai"
Take ta manta da damuwar da take ciki, ta ware suka hau hira. Ta juye musu sauran abincin da ba ta ci ba, ta ce za ta ɗora musu wani.
Ummi ta ce "Ke a ƙoshe muke, ga shi wannan miya ce na ɗan yi miki, tun bayan kawo ki da kwana biyu, na so yi miki, bana jin daɗi ne. Ga ɗan cin-cin da dubulan na yi miki. Ga kuma turarukan wuta da wata maƙwanciyar ku, ta bayar a kawo miki ga humra ma. Sai kuma kaya da na ɗan ƙara sayo miki"
Nana ta ce "Allah sarki, na gode sosai da sosai Anty Ummi, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Jamcy ya garin ne?"
Jamila ta ce "Uhumm mamaki nake yi, kamar ba ke ce ki ka gama uban kuka ba, an aura miki buzu, amma kalli yadda ki ka ware yanzu"
Nana ta yi murmushi ta ce "To ba dole na ware ba, lafiyayyen ɗaki, ga wardrobe, ga katifata ga banɗakina nikaɗai ba takura ga wuta 2hrs ba yankewa"
Suwaiba ta ce "Katifa ko abin da ake yi a kan katifar?"
Nana ta ce "Duka ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Jamila, tun da dan haka ake auren"
Ummi ta ce "Dan uban ku da yara a gurin ku ke