Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
sanya ta motsa a hankali, ta yinƙura ya kama ta, ta tashi tsaye.
"Ka canza kaya ka yi sallar, bari na wanke jikina"
Ya motsa baki, amma magana ta gagara, ya dage yana ƙoƙarin yi, amma gumi ya fara tsatstsafo masa.
"Ya lafa mini, ka yi salla kar ka makara, zan wanke jikina" da ƙyar ya fita, ta rufe banɗakin ta wanke jikinta, duk da tana jin sauran ciwon kaɗan kaɗan.
Ta fito yana salla, ta ɗaura zani, kan ya idar ta goge gurin da ta ɓata, ya idar ya ƙaraso gefen katifar da ta zauna, idanunta har sun faɗa saboda wahala.
Ya zauna ya saka ta a gaba, ga magana amma abu ya gagara, ta kwanta a kan cinyarta, ga ciwon buguwar jiya, ga rashin lafiya da ba ta gama warkewa ba, ga kuma wannan matsalar da ta tashi da ita.
A hankali yake shafa jikinta, yana ɗan matsa mata, ta ji daɗin hakan sosai da sosai.
Wajen ƙarfe bakwai, ta kira Ummi, Ummi ta ɗaga ta ce "Lafiya, kira da sassafe?"
"Kira ni kuɗina ba su da yawa"
Ummi ta kira ta, ta ce "Lafiya na ji muryarki a haka?"
"Ba na jin daɗi ne Ummi, dan Allah tambayar ki zan yi, idan mutum yana da ciki yana period ne?"
"Wane irin period kuma? Dama ciki ne da ke? Haba ni fa in ce ranar da ki ka zo na ga alama wallahi. Meyafaru?"
"An ce akwai, kuma yau na tashi da ciwon mara ina zubar da jini"
"Kai, subhnallah bari na sallami yara, gani nan zuwa gidan naki"
Duk da jikinta babu ƙwari, ta tashi ta saka kaya, ta kunna turaren wuta, Saboda a hancinta ba ta daina jin ƙarnin jinin nan ba.
Wajen tara da rabi sai ga Ummi.
Ummi ta gaishe shi, ya ɗaga mata hannu tare risunar da kansa, ranar farko da Ummi ta gan shi babu rawani, ya sha kitso a kansa jelar ta sauka a kafaɗarsa.
Ta ƙarasa inda Nana take cikin kulawa ta ce "Sannu Nana ya jikin?"
"Alhamdilillah"
"Gaskiya ki zo mu je a yi scanic, mu tafi Asibiti"
Nana ta girgiza kai ta ce 'A'a ba sai mun je ba, ni ba na son mu je, a yi ta huda ni"
"To Nana lafiyarki ba ta fi komai ba, tashi mu je"
Nana ta kalle shi, yadda ya tsare su da ido, ta ce "Sayyid za ta raka ni Asibiti, ka zauna kar su zo yau ma a neme ka, baka nan ya zama abin magana."
Ta kalli fuskarsa ta ce "Na gane, ba sai ka yi magana ba"
Ya tashi ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya ɗaukko kuɗi, ya miƙa wa Nana.
"Ka bari da kuɗi a gurina, wanda Imrana ya bani"
Tsuke fuska ya yi, dole ta saka hannu ta karɓa, ya ɗauki mayafin yin rawaninsa ya yafa a kansa, ya biyo su har bakin gate, yana kallon Nana.
Ta ɗaga masa hannu tare da yin murmushi, shi ma ya ɗaga mata.
Su na fita Ummi ta dasa mita, ta ce "Jaraba, wannan kallon da yake yi miki, sai da na ji kamar na bar masa ke na yi tafiyata, Nana sai ka ce auren Soyayya bawan Allah duk a rikice yake. Kuma dan Allah yana magana, anya na taɓa jin maganarsa kuwa?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yana yi mana"
"To ai ban taɓa ji ya yi ba. Kai tubarkallah Nana Allah ya baki kyakyawan miji, sai ki yi ta kaffa-kaffa saboda 'yan mata. Kodayake yadda yake yi ɗin nan ma wace za ta ce tana so?."
Nana ta yi murmushi.
Ummi ta sake cewa "Na ji daɗin ganin yadda ya nuna damuwarsa a kan ki, Ubangiji Allah ya sanya ya ɗore. Nana idan hankalin mace a kwance yake a gidan mijinta, komai mai sauƙi ne"
Da haka suka ƙarasa Asibiti, su na zuwa aka tura su scanic, da suka yi suka koma, aka tabattar da cikin ya fita. Aka ba wa Nana magunguna suka dawo gida.
Yana ganin dawowar su, ya tashi. Nana ta yi masa murmushi suka wuce ɗaki.
Nana ta cewa Ummi"Kar ki gaya masa, zan gaya masa da kaina"
Ummi ta ce "To shikenan" ta wanke wa Nana kayan da ta ɓata, ta ƙara gyara mata ɗakin, ta yi mata girki. Duk yana waje ya kasa shigowa. Sai da Ummi ta gama ta yi wa Nana sallama, ta fito za ta tafi, sannan ya taso.
Da ƙyar ya iya cewa "Na gode" shi ma sai da ya ji tamkar numfashinsa zai ɗauke.
Ummi ta ce "Ba komai Allah ya ƙara lafiya".
Ya shiga ɗakin da sauri, ya tarar da Nana a zaune a gefen katifa, ya zauna a kusa da ita, ya kamo hannunta, tare da tsare ta da ido. Yana jiran ta yi magana.
Ta numfasa ta ce "Sayyid, ɓari na yi"
Yanayin fuskarsa ya sanya ta fahimci bai gane me take nufi ba.
"Cikin babu, ya fita, jinin da na zubar cikin ne ya zube"
Ji ta yi tamkar hannunsa da ya riƙe ta da shi, ya yi mata shocking, saboda wani irin zirr da ta ji.
A take fuskarsa ta yi jawur, ya ji tafukan hannayensa sun ɗauki zafi, jijiyoyin kansa sun mimmiƙe. Ya ci gaba da motsa bakinsa zai yi magana, amma ya kasa.
"Sayyid lafiya kuwa? Ko wani laifin na yi maka?"
Ya din ga murza tafukan hannayenta da ɗan ƙarfi, yana sauke numfashi.
"Sayyid mene ne?"
Bai yi magana ba, jin ya kasa maganar ya sanya, ya saki hannunta, ya nemi guri ya kwanta yana haki sama-sama.
Abun duk sai ya ɗaure wa Nana kai, to mene ne ma'anar hakan? Me ya sanya shi canzawa haka lokaci guda? Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa. Ta ɗan matsa kusa da shi, ta taɓa jikinsa ya ji ya fara ɗaukar wannan zafin. Kafin ta yi wani yinƙuri tuni ya fara wannan jijjigar, jikinsa yana kakkafewa. Kawai ta zuba wa sarautar Allah ido, tare da rashin sanin cikakken abin yi.
Ayshercool
08081012143
Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji.
Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai.
Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau.
Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci.
Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo.
Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa.
Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce "Sayyid na kasa fahimtar abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba."
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana.
"Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki
Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba tare da na yi tsammanin hakan ba".
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?"
Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba za ki gane ba" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin.
Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso.
Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba.
Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara.
Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai, ba tare da ya kalli inda take ba.
"Amm dan Allah magana nake son mu yi"
Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki.
Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce "Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri"
Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar.
"Ka yi magana mana" ta yi maganar cikin iyayi.
Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe.
Ta sake cewa "To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana"
"Ya wuce"
Ta saki murmushi ta ce "Na gode sosai" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta.
Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta.
Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana.
Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce "Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba"
Nana ta kalle ta ta ce "Kina lafiya?"
"Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?"
Nana ta kalli Yusra ta ce "Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?"
"Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani."
Nana ta ce "Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni"
Yusra ta yi murmushi ta ce "Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk a kan ki?"
Nana ta ce "Waye dattijo?"
"Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa. Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?"
Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta rasa.
Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso kayan wardrobe tana gyarawa.
A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da ya kan saka a wuyansa wasu lokutan.
Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa.
Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na Nijar.
Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta.
Ta kalli kuɗin ta kalle shi.
"Wannan kuɗin fa?"
"Nawa ne?"
Ta kalle shi ta ce "A ina ka samu?"
Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa.
"Me ki ka ce?"
Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa.
"A ina ka samu?
"A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?"
"Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?"
Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce "A'a"
Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta kwaɗe shi ko ta samu ta huce.
*****
Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya.
Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce "Zailani, babu komai dan Allah ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?"
Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?"
"Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za a karya masu ƙaramin jari"
"Ƙananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ƙullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan shugabancin nan, su ka ke tausayawa?"
Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Nima da ƙaramin ɗan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karɓi tayin riƙon ƙwaryar shugabancin nan da aka yi maka" Alhaji Fatuhu ya ɓata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karɓa.
*****
Gaddafi tuni ya koma gurin neman khɗinsa, saboda takaicin abubuwan suke faruwa a gidansu, ya fara damunsa.
Baba ƙiri-ƙiri haka ya zuba ido ya yi shiru, ba ya iya cewa uffan, sai dai ya zuba ido a kan lamarin gidansa. Sai ma dai idan an dafa a zuba a ba shi ya ci. Sosai al'amuran gidan su Nana, suka fara canzawa kullum sai an ɗora abinci sau uku a rana saboda hidimar da Jamila take yi da su. Ƙarewa ta saka ana ta yi musu gyare-gyare a cikin gidan.
Babban abin da yake damun Hajiya Sa'a da Jamila, shi ne yadda take ta ƙoƙarin janyo ta, cikin ɗaya mummunar ɗabi'ar da suke aikatawa ta lesbian.
Sai dai Jamila ta kafe da kai da fata, taƙi amincewa da hakan.
Sai da Hajiya Sa'a ta yi mamaki, saboda a ƙulumboton da ta yi wa Jamila, babu yadda za a yi ta iya kaucewa duk wata buƙata da ta zo mata da ita, amma ta kasa galaba a kan Jamila.
Duk wani shashashanci da suke yi tana kallo, amma sam ba ta ji abin ya kama hankalinta ba, balle ta yi sha'awar aikatawa.
Ta fito harabar gidan tana shirin tafiya, sai ga Mus'ab ɗa ɗaya tilo ga Hajiya Sa'a. Yana ganin Jamila ya tsaya. Duk da ba shiga harkarsa take yi ba, amma ta yi ƙoƙarin tare shi daga shiga cikin gidan, ya yi mummunan gani.
"Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau Jamila. Ya ki ke?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Amm Yaya Mus'ab ko za ka ajiye ni a hanya ne, ba na jin daɗi"
Ya yi murmushi ya ce "Me zai hana? Bari na kai wa Mummy saƙon nan"
Da sauri ta ce "A'a ai bacci take yi, ta ce kuma kar a tashe ta"
"Ok to mu je na ajiye ki" ta yi gaba ya bi ta a baya.
*****
Nana kuwa ita ma a wannan karon, basar da Sayyid ta yi, ta ƙi kula shi sam. Shi ma ya maze ya share ta.
Baccinta ya yi nisa sosai ta ganta a daji ita kaɗai ƙwal. Ta ɗaga kanta ta ga wani ƙaton tsuntsu yana shawagi a saman kanta.
Ba ta tsorata ba, ta ɗan ja numfashi ta ce "Ƙaisar laifin me na yi maka, ka zaɓi ka hukunta ni ta wannan hanyar? Me ya sa za ka zama dalilin zubewar cikina?"
Tsuntsunan nan saukko ƙasa, ya yi girgiza Ƙaisar ya bayyana. Ya zauna yana fuskantar ta ya ce "Komai ma kin yi mini, babu abin da ba ki yi mini ba, abin da ya dace nake yi"
"Ba ka tsoron Allah Ƙaisar, ba ka tsoron Allah ya kama ka da hakkina, abubuwan da ka ke aikata mini na cutarwa.
Kai ka yi mini, wannan tsohon ya yi mana, mijin nawa ma na fara daina gane kansa. Ya fara ƙoƙarin cutar da ni"
Ya ɗan kalli saman bishiya sannan ya ce "Babu abin da ban gaya miki ba ai. Amm kin tuna abin da na nuna miki, Alhaji Zailani yana yi wa abokinsa? Da gaske ya faru a zahiri. Kuma tsafi gaskiyar mai shi, domin kuwa al'anura sun fara juya wa Alhaji Zailani baya. Nan zuwa wani ɗan lokaci zai rasa komai nasa. Lafiyar sa da dukiyarsa."
Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Dan Allah idan ka na dama ka yi wani abu a kai mana. Ka tona abin da aka yi masan"
Ya girgiza kai ya ce "Ba ma shiga abin da babu ruwanmu, ko warware wani abu da aka yi wa wani, muddin ba yarjejeniya aka yi damu, aka bamu damar yin hakan ba. Zan iya taimakonsa ne kawai bisa amincewar ki, da kuma umarnin ki. Zan gaya miki inda abin yake ya saka a je a tone, ko kuma ki je ki tone. Idan ba haka ba nan da kwanaki uku rak za a tono ƙwarangwal ɗin yaron nan, a kuma yin wani tsafin da ita."
Har Nana ta motsa baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa, dan tana amincewa a taimaki Alhaji Fatuhu ba ta san me zai biyo bayan hakan ba, ka iya tabbatar da buƙatar Ƙaisar a kanta.
AREWABOOKS
Kasancewar ba ta salla, ya sanya har gari ya waye tana bacci.
Bayan ta yi wanka ta rasa abin yi, ta ɗebo kayan wankin ta, ta shiga banɗaki ta wanke. Nasa dama Habu ne yake zuwa ya ɗauka.
Ta gama, ta saka hijjabinta, ta ɗaukko bokitin, ta fito daga ɗakin. Yana kan kujera a daf da gate ɗin, yana aikin dafa shayi, gefensa ga radio tana yi.
Ba ta kula shi ba, ta zagaya baya, ta yi shanyar kayan nata. Ta fito ta ja ta yi turus tana kallon ikon Allah.
Siyama ce a tsaye, da ɗan ƙaramin flask a hannunta. Nana ba ta san me take ce masa ba, ta ga ya sauke rawanin fuskarsa ya saka hannu