Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
ya karɓi flask ɗin, ya yi magana.
Kawai ta shiga ɗaki, a ƙofar banɗakin, ta jefar da bokitin jin wani irin matsanancin ɗaci yana taso mata.
Ta cire hijjabinta kawai ta tsaya ta riƙe ƙugunta, ta tsaya tana jiran ya shigo, amma bai shigo ba, zuciyarta ta din ga raya mata, yana can su na hira da Siyama.
Kawai ta buɗe ƙofa ta shiga banɗaki, sai dai ta rasa uban abin da ya kai ta banɗakin ma. Ta gama tsayuwarta ta fito daga banɗakin.
Tana fitowa ta gan shi a tsaye, da flask ɗin a hannunsa, ya nufo ta zai yi magana, ta riga ta ɓarar da flask ɗin. Farfesun kifi da dankalin ya tarwatse a ƙasa.
Ya kalli gurin ya kalli yadda take huci, zuciya ta yinƙuro shi, sai dai ya ga Ƙaisar a bayan Nana, ya zubo masa ido.
Ya haɗiye wani abu, mai ɗaci. Ya kalli Nana ya ga yadda idonta ya rufe, ta fara ƙoƙarin wuce shi ta fita. Ya riƙe ta yana ci gaba da kallon Ƙaisar.
Ya kwantar da Nana a kan katifa, idanunta a rufe sai hawaye da yake fita, ta gefen idonta.
Ya durƙusa ya gyara gurin ta ɓarar da abincin.
Ya sake kallon yadda Ƙaisar ya jingina da bango, ya tsaya a kan Nana.
"Tun da ka yi abin da ka yi, ya kamata ka bani guri" Ya yi maganar yana kallon inda Ƙaisar yake.
"Gurin ka na zo ne? Idan ba gurin ka na zo ba, sai ka ƙyale ni"
"Ka zubar mini da ciki, kuma saboda rashin kunya, ka zo haɗa fitina a tsakaninmu"
Ƙaisar ya yi murmushi ya ce "Ina mamakin yadda Aljani yake shiga al'amuran bil adama har haka. Kai ka fara lalata cikin, ni kuma na zubar da shi."
Sayyid ya shafi fuskarsa ya ce "Waye Aljanin a tsakanin ni da kai?"
Ƙaisar ya ce "Ba da kai nake ba. Ka san da wanda nake"
Buzu ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me ya kawo ni ƙasar nan?"
"Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi"
"Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata"
"Ba zan tafi ba"
Buzu ya durƙusa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya ɗago Nana da take cikin yanayin gushewar hankali.
Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa Ƙaisar saƙon mutuwa ya murtuke fuska.
Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta.
Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin da yake faruwa, amma tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsa ko da ƙaramin yatsanta.
Da ƙyar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce "Sayyid" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo ta.
Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne, amma ta ji ɗakin yana ƙarnin kifi, ga kuma flask ɗin da ya shigo da shi.
Da ƙyar ta ce "Ina wanda ku ke magana da shi?"
Ya kalli ɗakin ya ce "A ina?"
Ta kalli daidai gurin da Ƙaisar ya tsaya, ta ce "Wanda ya tsaya a nan, wani dogo"
"Ban yi magana da kowa ba" ya yi maganar yana girgiza mata kai.
Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo.
****
"Suwaiba" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta.
Ta kalle shi ta ce "Ya dai?"
"Ba na jin daɗin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna"
"Me ke nan?"
"Ƙara ta za a kai kotu"
Ta waro ido ta ce "Kotu kuma? Me ka yi?"
"Kayan nan da suka yi ɓatan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni. Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani"
Ta kwaɓe baki ta kaɗa kai ta ce "Ai Alhaji Fatuhu duk ɗan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba. Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ƙarama saboda ka ƙuntata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka" Ya yi zuru da ido yana kallonta.
Ta gama maganganunta ta bar masa ɗakin.
Tana zuwa bedroom ɗin ta, ta rufe ƙofa, hawayen da ta maƙale ta ba su damar gangarowa.
Ta hau nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un"
Ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta.
Yana ɗagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce "Lafiya kuwa?"
"Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuɗi, dan Allah ka yi wani abu a kai dan Allah"
"To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuɗin ba?"
Suwaiba ta ce "Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci kuɗin kowa ba"
"Ki bari zan kira ki da Safe" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa.
Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ƙi gaya mata, ya lallaɓa ta ta yi bacci.
*****
Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daɗe tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta.
Kasancewar jini ya ɗauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ƙasa-ƙasa a wayarta.
Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ƙasa, gurin da yake kwanciya da. Gaba ɗaya sai ta ji ta damu. Ta daɗe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba.
Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ƙarasa kusa da shi, ta kwanta.
Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata.
Bayan wani ɗan lokaci ya numfasa ya ce "Kin daina fushin?"
"Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi haƙuri"
"Me na yi miki?"
"Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi ɗaki?"
"Ki na gurin kin san meyafaru?"
Ta tashi daga jikinsa, ta ce "Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta. Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri".
"Ki daina faɗar abin da ba za ki iya aikatawa ba"
"To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin."
Amma ya riƙe ta gam, yana yi mata numfashi a wuya. A gurin suka kwana tare. Sai Asuba bayan ta yi wanka ta yi salla, ta koma kan katifa.
Tana tsaka da bacci, ta ji yana tattaɓa ta, ta buɗe idonta ta kalle shi tana yanutsa fuska, saboda bacci ne a kan ta sosai.
Wayarta ya ajiye mata a daidai kunnenta.
Waƙar Ali jita ce take tashi, ta Aminiya. Shiru ta yi tana sauraren baitukan tana kallon kyakyawar fuskarsa da ya tsare ta da manyan idanunsa yana kallonta yana murmushi.
Ita ma murmushin ta sakar masa, ta yinƙura ta tashi zaune, ita sam ba ta san da waƙar ma a wayar ba, kasancewar ba gwanar jin waƙa ba ce, amma har cikin zuciyarta take jin baitukan, tamkar shi ne yake rairai
mata.
Gaba ɗaya suka manta, da batun saɓanin da ya shiga tsakaninsu.
(BAYAN MAKONNI BIYU)
Gaba ɗaya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daɗi, hankalinta ya ƙi kwanciya, tun da aka fara zaman kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daɗi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta.
Dan tashin farko Alƙali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi.
Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu maƙudan kuɗin, da ake zarginsa da sama da faɗi da su, a lokacin da yake shugabanci.
Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa.
Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuɗinsu.
*****
Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ƙwarangwal ɗin sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi.
Ɗakin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya ɗaukko ƙwarangwal ɗin jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka ɗauki ƙwarangwal ɗin jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaɗe su a jikin ƙwarangwal ɗin aka saka a cikin wutar nan.
Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu.
Sai da ƙwarangwal ɗin nan ya yi baƙi ƙirin, zaren da aka naɗe ƙwarangwal ɗin, ya kama jikin sosai. Ya kuma naɗe shi da wani zaren, sannan ya naɗe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki.
Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin ɗaki, ya din ga ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace.
Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuɗi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar"
Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karɓi ƙaddara.
Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karɓi ƙaddarata. Na kuma gode wa Allah. Abu ɗaya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni"
Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi haƙuri"
Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah"
Ji ya yi tamkar ana ƙoƙarin fizgo ƙwaƙwalwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya riƙe kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?"
Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faɗi a gurin.
Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da Ƙaisar yake nuna mata.
Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin.
"Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bamban da wannan ta wasu fannukan"
Nana ta zabura ta kalle shi ta miƙe tsaye ta ce "Ƙaisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?"
Ya ɗago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaɗin ne?"
Ta yinƙura za ta yi magana, ta yi ido huɗu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido.
Ta yi ajiyar zuciya.
"Waye Ƙaisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani.
Ayshercool
08081012143
45
Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji.
Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai.
Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau.
Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci.
Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo.
Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa.
Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce "Sayyid na kasa fahimtar abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba."
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana.
"Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki
Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba tare da na yi tsammanin hakan ba".
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?"
Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba za ki gane ba" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin.
Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso.
Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba.
Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara.
Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai, ba tare da ya kalli inda take ba.
"Amm dan Allah magana nake son mu yi"
Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki.
Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce "Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri"
Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar.
"Ka yi magana mana" ta yi maganar cikin iyayi.
Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe.
Ta sake cewa "To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana"
"Ya wuce"
Ta saki murmushi ta ce "Na gode sosai" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta.
Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta.
Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana.
Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce "Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba"
Nana ta kalle ta ta ce "Kina lafiya?"
"Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?"
Nana ta kalli Yusra ta ce "Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?"
"Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani."
Nana ta ce "Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni"
Yusra ta yi murmushi ta ce "Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk a kan ki?"
Nana ta ce "Waye dattijo?"
"Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa. Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?"
Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta rasa.
Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso kayan wardrobe tana gyarawa.
A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da ya kan saka a wuyansa wasu lokutan.
Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa.
Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na Nijar.
Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta.
Ta kalli kuɗin ta kalle shi.
"Wannan kuɗin fa?"
"Nawa ne?"
Ta kalle shi ta ce "A ina ka samu?"
Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa.
"Me ki ka ce?"
Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa.
"A ina ka samu?
"A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?"
"Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?"
Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce "A'a"
Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta kwaɗe shi ko ta samu ta huce.
*****
Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya.
Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce "Zailani, babu komai dan Allah ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?"
Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?"
"Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan