Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
Ya aka yi ka hau kanta, tun da na ga ba da kai a ka fara yi mata girka ba, kuma ya aka yi ka canza sunanka? Ya aka ƙarke da sarkin aska kuma a garin? Ta yaya duk nake da alaƙa da wannan abubuwan?"
Wani irin takaici ya turnuƙe Ƙaisar, ya tashi a fusace da niyyar ya yi jifa da ita, ko ya samu ya huce, sai kuma ya fasa kawai ya fice ya bar ta a gurin.
Ta ce "Wallahi sai na kai ƙarshen littafin nan, ko da kuwa za ka kashe ni ne, sai na ga ƙwal uwar daka, sai na karanta har ƙarshe ko me za ka yi sai dai ka yi"
Sannu a hankali yake shafa fuskarta, yana kallonta, kamar wata jaririya haka ta yi miƙa sannu a hankali, sai da ta banƙare gaba ɗaya. Ita gaba ɗaya ta manta da shi a kan katifar, a zatonta ita kaɗai ce a kan katifar, sai da ta ji ta a jikin mutum. Ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai kuma ta ɗan tsorata, ta yinƙura da sauri. Amma ya riƙe ta yana kallon ta.
"Amm lokacin salla ya yi ko?" Ya ɗaga mata kai alamar eh.
"To bari na je na yi alwala"
Ya cika ta tashi, ta je ta yi alwala, sai da ta fito sannan ya ce "Zan yi wanka"
Ta ce "Wanka kuma? Yanzu?"
Ya ɗaga mata gira daga kwance.
"Ka yi da safe mana, gari da sanyi yanzu"
Ya lumshe idanunsa ya buɗe, ya ce "Tare mu ka kwana a shimfiɗa, kuma ya dai kamata na yi wanka"
Ba ta ce komai ba, ta yi shiru, Allah ya taimake ta, tana da ruwan zafi a tea flask ta haɗa masa. Ya yi wanka ya yi alwala ya fita Masallaci.
Nana kuwa bayan ta idar da sallar asuba, ta zauna a inda take ta fara karatun Alqur'ani.
Ya dawo ya tarar da ita, ya tsallake ta, ya nemi guri ya kwanta.
Wajen ƙarfe takwas ya farka, tuni Nana ta gyara ɗakin yana ta ƙamshi, tana zaune a kusa da socket, tana caji tana danna waya.
Ya ɗora hannunsa a kan cinyarta, ya rufe fuskar wayar, ta waiwayo ta kalle shi ya ce "Ina kwana?"
Murguɗa masa baki ta yi ta ture hannunsa. Ya tashi zaune, ya matsa kusa da ita ya ce "Na yi laifi ne?"
"Ai ka san me ka yi mini"
Ya ce "A'a abun tun shekaranjiya ba ya wuce ba?"
"Ni ba wannan ba, jiya na yi ta baka haƙuri amma ka haɗe rai ka ƙi kula ni, ka ƙi cin abinci ma" ta ƙarasa maganar tana hararsa
Ya ɗan yi murmushi ya sake matsawa, tamkar zai shige cikinta ya ce "Na ce idan ina fushi ki daina kula ni"
Ta noƙe kafaɗa ta ce "Ni ba zan iya ba"
Murmushin fuskarsa ne ya faɗaɗa cikin matsanancin farin ciki ya kama hannunta ya ce "Ki yi haƙuri, idan raina ya ɓaci, ko bani da lafiya, bana iya magana. Wasu lokutan ina kasa magana haka kawai, amma ya fi idan raina ya ɓaci."
"To ni da ba ni na yi laifin ba, sai ka daina yi mini magana? Na fi ka jin haushin abin da aka yi maka fa"
"Na sani, ban san ya aka yi nake iya magana sosai ba idan ina tare da ke, ina iya yin sati ban iya yin magana ba, kuma ina son na yi amma ba ta fitowa. Amma ke yanzu ina yin magana da ke sosai, ina jin daɗi"
Nana ta kwashe da dariya ta ce "Bagware idan ka yi magana dole sai mutum ya gane kai ba bahaushe ba ne ba"
Yayi dariya ya ce "Na fiki iya Hausa sosai, buzuwata saka kaya muje sayo abun karyawa1"
Cikin murna Nana ta ce "Yauwwa, dama ina son na fita na ga waje, tun da aka kawo ni ban taɓa fita ba".
Dama ta yi wanka, ta saka hijjabi a kan kayanta, shi ma ya saka kaya, suka rufe ɗakin su ka fita.
Sosai unguwar ta yi wa Nana kyau, duk da ruwan da ake yi, babu alama a unguwar saboda akwai wadatattun magudanan ruwa, ba kamar unguwarsu ba, da ruwa ɗaya sai unguwar ta shafe kwana uku maƙil da ruwa da azababben sauro.
Ya saka hannunsa ya riƙo na Nana, ta ɗaga kai ta kalle shi, ya kashe mata ido. Sosai abin ya ƙayatar da ita.
"Sayyid"
Ya kalle ta, yana jiran jin abin da za ta ce.
"Dan Allah ina son ka bani dama, na je gida na duba Baba, yana ciwon ƙafa tun bayan biki ƙanwata ma da suka zo, ba ta da lafiya. Kuma ka ga a al'adarmu yakamata mu je mu yi wa mutane bangajiya"
"Mene hakan?"
Ta yi murmushi ta ce "Mu yi musu sannu, saboda hidimar biki da suka yi, ka ga Shukura ma babu lafiya tana asibiti, maman yaron da nake raino"
"Tom"
Nana ta ce "To yaushe za mu je?"
"Zan gaya miki"
"To na gode sosai mai rawani"
Gurin da yake zuwa sayen ƙosai suka je, Nana ta yi mamaki ganin har a manyan motoci ake zuwa gurin sayen ƙosai, da kunu gurin matar.
Nana ce ta yi wa mai ƙosan magana ta gaishe ta.
Matar ta ce "Laa kece matarsa ko 'yar uwassa?"
Nana ta yi murmushi ba ta ce komai ba.
"Allah sarki, yana zuwa sayen ƙosai ai, na nawa za a baku? Ki ce masa na ce kwana biyu bai zo sayen ƙosai ba, ban iya maganar su ba"
Nana ta ce "Ai yana jin ki"
Matar ta ce "Haba dai? Ba kurma ba ne?"
Nana ta kwashe da dariya ta ce "Yana magana"
"To ai kullum ya zo kuɗi yake bayarwa kawai, ko ya rubuta"
Ya yi mirsisi kamar ba a kan shi ake magana ba, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya bawa Nana.
Kamar Nana ta san matar, suka din ga hira, ta sallame su, suka nufi gida.
"Sayyid dan Allah ka din ga yi wa mutane magana, ko dan saboda yanayin rayuwa. Ka ga da yawa ana ɗauka ko kai kurma ne" shiru ya yi mata, haryanzu ba ta gama fahimtar sa ba.
Ba ta damu da rashin bata amsar waccan maganar ba ta sake cewa "Yauwwa, dan Allah akwai gidaje a bayan gidan nan ne? Ina son sanin gidan Anty Haula, ina son na kai mata ziyara nima"
"Babu gidaje a baya"
"Amma ta ce mini gidanta a bayan inda muke yake"
Ya ce "Mu duba tare" ya biyo da ita ta bayan layin, wasu irin manyan gidaje ake yi, sai dai duk kangwaye ne, babu ma alamar wani gida da yake da mutane a gurin.
"Ina ga ban gane kwatancen ba, idan ta sake zuwa na tambaye ta. Amma sai na din ga jin hayaniya a bayan ɗakin, kamar akwai mutane a gidan" kawai ya kalli Nana ba tare da ya ce mata uffan ba.
Ko da suka gama karyawa, roƙonsa ta yi tana son shiga cikin gidan, ta gaida Hajiyar. Ya ce "A dawo lafiya, idan kuma da maza ki dawo" ta jinjina masa kai tana murmushi.
Yau ma a falon saman benen, ta iske Hajiyar gidan, tana waya a matuƙar fusace.
"Ni wallahi na gaji, idan ka dawo ka san yadda za ka yi da ita. Ni me ake yi wa Yusra a gidan nan, balle a ce depression ya kama ta? Ga anti depressants ɗin nan, mun je mun ga Likita an bata, amma ta ƙi sha. Sai kuka, ba damar na yi mata magana ko nasiha ce sai ta hau kuka ta ƙule ta wuni a ɗaki"
Nana ba ta iya jin abin da ake faɗa a cikin wayar, ta gama bambaminta, ta kashe wayar.
Nana ta gaisheta ta amsa, ta ɗora da cewa "Yi haƙuri kin same ni ina waya ne"
Nana ta ce "Babu wani abu, bari na gyara falon"
Matar ta ce "Yauwwa dan Allah da kitchen ma"
Nana ta ce "To" ta fara gyara ɗakin, tana cikin mopping ta fara jiyo wani sauti, da ta rasa sautin mene ne, kamar ana buga wani abu. Ta basar ta ci gaba da aikinta amma sautin ya ci gaba da fitowa daga wata siriryar hanya.
"Ƙaisar" ta furta a hankali. Kwana biyu hankalinta ya ɗan fara kwanciya, amma ta fuskanci matsalolinta na ƙoƙarin sake dawowa.
Ta gama mopping ɗin falon, ta tafi kitchen ɗin, nan ma ta fara tattarewa kamar ba kitchen ɗin mata ba. Kaca-kaca ga tarkacen kwanuka wasu abinci duk ya bushe.
Ta haɗa kwanukan a sink, ta fara wankewa.
A hankali ta ji sautin nan ya biyo ta har kitchen ɗin, ya ci gaba da nufo inda take, ba ta waiwaya ba, ta fara karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakin ta.
Aka jefo mata kofi a cikin sink ɗin, mai jefowar ta nufi hanyar barin kitchen ɗin. Tamkar an dasa Nana ta kasa motsi, sai da ƙyar ta kalli ƙasan rigar matar har ta fice.
A hankali Nana ta fara jin sanyi, gabanta ya fara faɗuwa, hakan ya tabattar mata da akwai matsala. Kawai ta ɗauraye hannunta ta bi bayan matar.
Tamkar ana hankaɗata ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ɗakin. Wata farar mace ta gani a ɗakin, a zaune fuskarta ta yi ja alamar ta yi kuka. Ta zubo wa Nana ido.
Nana ta taka a hankali ta nufi gadon da matar take, ta zauna a kusa da ita.
"Sannu"
"Yauwa" ta amsawa Nana.
"Shigowata ta uku kenan, ban taɓa ganin ki ba" matar ta yi ƙurii da ido tana kallon Nana.
Nana ta miƙa mata hannu, da nufin su gaisa.
Tamkar doluwa, matar ta bawa Nana hannu da nufin su yi musabaha.
Su na gaisawa jikin Nana ya hau rawa, ita kuma launin fatar matar, ya ƙara yin jawur, idanunta ya fara zubar da hawaye.
Nana ta ce "Wace ce ke?"
Bakinta yana rawa ta ce "Ha...ha..Haulat"
"Me yasa ki ka yi mini ƙarya? Ki ka zo mini a matsayin mutum? Kuma me ki ke yi a jikin bil'adama?"
"Fansa na ɗauka, nan gidan a nan mune rayuwa da 'yan uwana, kawai su ka gina gida, hankalinsu kwance su ka yi zaman su, ba su yi tunanin akwai wata halittar a gurin ba. Da sun gabatar da karatun Alkur'ani ne ma, da mun haƙura mun tashi, amma kawai suka yi gini suka zauna"
Nana ta numfasa ta ce "Kuma sai ki shiga jikin wanda bai ji ba bai gani ba ki zauna? Kun san ba ma ganin ku, me yasa za ku din ga zaluntar mu, ba za ku yi mana uzuri ba? Yanzu kin kyauta an ce matar nan ba ta ci ba ta sha, sai kuka kin yi adalci kenan?"
"Nima ba a yi mana adalci ba, ramawa muke yi"
Buzu yana zaune a kan benci, ya saka hanyar fitowa daga gidan, yana jiran ya ga ta ina Nana za ta fito, dan tana fita ya ji zaman ɗakin ya dame shi.
Kawai ya hango ta, ta fito idanunta a rufe, ta nufo shi. Sai da ta kusa ƙarasowa, sannan ya nufe ta yana son tambayarta ko lafiya. Kawai ta tafi za ta faɗi ƙasa.
Riƙe ta ya yi yana mamakin me ya same ta haka?
Ɗakinsu ya shigar da ita, ya kwantar da ita, yana mamakin yadda jikinta ya yi sanyi ƙalau.
Mamaki ne ya cika Nana bayan da ta ganta a tsakiyar daji, da ita da Haula.
"Wace ce ke? Kuma me yasa ki ka yaudare ni ki ka zo mini a matsayin mutum?"
Haula ta yi dariya ta ce "Kamar dai yadda na gaya miki, laifi aka yi mini nake ramawa. Kwatsam kuma ke ma sai na haɗu da ke. Yanzu a duniya babu abin da nake ƙauna sama da hadimin ki, shi ya sanya ma har na yi yinƙurin taimakon ki, dan na samu shiga a gurin ki"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Waye Hadimin nawa?"
"Ƙaisar, tun da na buɗi ido a duniya ban taɓa ganin kyakyawan matashin Aljani mai kyau da cikar zati kamar sa ba"
Galala Nana ta kalle ta, ta ce "Ƙaisar ɗin? Wannan zanƙalelen abin?"
"Ƙwarai shi, saboda na burge shi na zo na cinye gubar da aka kawo miki a wainar fulawa, sai dai kash! Haƙa ta ba ta cimma ruwa ba. Ina roƙon ki, ki taimaka mini na samu Ƙaisar, ni kuma na yi miki alƙawarin barin jikin matar can, da taimaka miki da duk abin da ki ke so"
"Tirrr Allah ya yi mini tsari da sake ja wa kaina wata jarabar, ta hanyar haɗa kaina da ku, shi ma maraba nake nema da shi, ido rufe, balle na sake rakito ki, ki je can Allah ya daidaita ku. A'uzu bi kalimattilahi tammat" Nana ta furta a zahiri tana hamma. Ta tashi zaune ta ga an rurrufe ko ina na ɗakin, an kuna garwashi a ɗan kaskon dafa shayinsa.
"Sayyid" ta kira sunansa da ɗan ƙarfi, amma ta ji shiru.
Ta yi mamakin dalilin da yasa ya rufe ko ina haka. Ta shiga banɗaki ta yi alwala, saboda an idar da sallar azahar ma.
Da ya shigo ɗakin ya tarar da ita ta idar da salla, bai ce mata komai ba, ta ɗora girki tana yi masa hira, saboda ba ta iya tuna komai ba. Jin ya yi shiru ba ya tanka mata, ya sanya ta yin shiru.
*****
Yaya Atine ce ta zo gida duba Baba, ta ga yadda yake tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa.
Ta jinjina kai ta ce "Wai Isa wannan ƙafar taka, ka je asibiti kuwa?"
"Atine da wani kuɗin? Kin san auren 'ya na yi kwanan nan ai, mai nasara nake saya da aboniki sai a ji garau da nake haɗiya, shi ne nake samun afuwa na yi bacci"
Ta kwaɓe baki ta ce "Yanzu kana nufin duk kuɗaɗen da ka samu, da auren Nanan babu wanda za ka je Asibiti, ni fa zuwa na yi idan zan samu wani abu ma ka ɗan bani, gidana ko ƙwayar shinkafa babu"
"Haba Yaya Atine, ina su Nazifin da za ki zauna babu abinci?"
"Kai ina Gaddafi, ka ke zaune a haka?"
Baba ya ce "Gaddafi tun auren Nana ya tafi Ikko"
"Ka ga kawai ka fito da kuɗi, idan kuma matarka ta saka ka a gaba, ta tatse ka shikenan dama ka saba abin kunya"
Caraf Mama ta ce "Ina zunubin yake balle romonsa? Ina abin yake ni kar a yi mini sharri, ban ci komai ba"
"Idan ma kin cin ai ba za ki ce kin ci ba, ni Wallahi kamata ya yi ka mayar da hankali su ma su Jamila ka aurar da su, ko ka samu ka huta. Ni ina suke nema tun da na shigo ban gan su ba"
"Su na nan sun je gidanmu" Mama ta ba ta amsa tana tsuke fuska, saboda kar ma ta ja zancen.
Ta gama surutanta, ta tashi ta tafi"
****
Nana kuwa haka su ka ƙarasa wunin su, ba tare da wani yana kula wani ba, ya koma mata buzunsa. Sai dai hakan bai damu Nana sosai ba, saboda ya yi mata bayani. Duk da shirun bai yi mata daɗi ba, ɗan kulatan da yake yi, ba ƙaramin daɗi take ji ba.
Sai dai tana zaune, tana addu'ar kwanciya bacci, ya shigo ya gama abin da zai yi ya ɗane kan katifa. Ya zauna ta ƙarasa addu'a ta shafa shi ma ya shafa.
Yana shirin ya ga ta kwanta, amma ta ƙi kwanciya.
Ya ce "Mu kwanta"
Ta murguɗa baki ta ce "Ni ba bacci zan yi ba"
"To mu zauna"
"Ni kawai sai ka wani din ga yi mini shiru, ni ka daina irin haka ba na so" Zuciyarsa na azalzalarsa ya tambaye ta abin da yake cikin zuciyarta, saboda har wani irin zafi yake ji a ƙirjinsa, amma ya kasa furta komai. Ya rasa me ma zai yi gaba ɗaya.
"Ba zaka kula ni ba ko?"
"Husnahhh" ya furta a kunenta. Zirrr tsigar jikin Nana ta tashi.
"Ki amsa ni"
"Na'am" ta furta a tsorace. "Ni mahaukaci ne, nima ba na gane rayuwar da nake yi, rayuwata ta banbanta da yadda sauran mutane suke ta su. Ni baƙo ne a duniyar nan taku. Ke kaɗai ce Ahalina, da ke kaɗai nake gane kan wannan rayuwar. Ba zan iya zama yadda ku ke ba gaba ɗaya, duk da ke ma wasu lokutan kin bambanta da rayuwar sauran mutane. Amma ki yi haƙuri da yadda ki ka same ni"
"Sayyid"
Ya amsa mata da "Ma vie"
"Dan Allah ka gaya mini gaskiya, zan karɓe ta a duk yadda take, dan Allah kai wane jinsi ne? Ka na tsorata ni wasu lokutan"
Hannunsa bai daina yawo a jikinta ba ya ce "Na fi yadda ni halitta ne kamar ke, mutum ne ni, amma ban san ya ake yi... Sai kuma ya yi shiru, kuma ya hana Nana sake cewa uffan, ta hanyar jan su zuwa duniyar ma'aurata, mai cike da al'amura masu tsayawa a zukata da wahalar mantawa.
Duk da, da faransanci yake gaya mata wasu kalamai, da ba ta san ma'anarsu ba, amma kai tsaye maganganun nasa suke shiga zuciyarta, tare da haifar mata da wata irin nutsuwa, duk da wahalar da ya bata.
Ta ƙara narkewa a jikinsa, ga bacci na son ɗaukar ta, amma zuciyarta da ƙwaƙwalwarta, na kan kalaman da ko fassarar su ba ta sani ba, sai dai tsananin daɗin da suke yi mata, ya sanya ta ci gaba da sauran su.
Sun shafe lokaci a haka, sannan da ƙyar ta tashi ta fara yin wanka, sannan shi ma ya tashi, sai dai kan ya dawo tuni bacci ya yi awon gaba da ita.
*****
Tamkar Nana ta taka rawa yau, saboda murnar za su fita yau, ya ce mata tare za su je dubiyar.
"Amma babu matsala ba za su buƙace ka ba mutanen gidan? Kar mu yi laifi"
"Na gaya musu"
Da wuri ta gama komai, suka shirya suka fita tare.
Ta ɗaukko dubu goma a kuɗin hannunta, ta tsaya ta yi sayayya a hanya, sannan suka tafi.
Asibitin da aka kwantar da Shukura suka fara zuwa.
Haidar ne ya fara gano ta, ya zabura daga jikin mahafinsa ya nufo Nana da wani irin gudu, cikin matsanancin farin ciki.
Caraf Nana ta ɗaga shi, ta rungume tana juyi da shi a gurin. Kawai ya ƙara ƙanƙame ta ya saka kuka.
Ita kanta Nana hawaye ne ya cika mata ido, cikin sanyin murya ta ce "Is ok sweetheart, ya isa haka" ta yi maganar tana shafa kansa cike da ƙaunar sa.
Yanayin kamaninsu da ta gani da Sagir, ya sanya ta gane shi ne mahaifin sa.
Ta ƙarasa suka gaisa, ta ce masa "Dan Allah a wane ɗakin suke?"
"Su na ciki room 2 VIP, sai dai ba sa bari a shiga"
Ta ce "Subhnallah jikin har ya yi tsanani haka, Ubangiji Allah ya ba ta lafiya, Hajiyan na ciki ne?" A fusace