Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
yi a kanz sai ta kai Gaddafi gurin 'yan sanda. Ana bata haƙuri shi kuma ya ce "Idan ba ta kai shi gurin 'yan sanda ba, ba Hudu mai ice ne ya haife ta ba" wato mahaifinta.
Duk da Baba yana cikin wannan tashin hankali, amma ya lura da sauƙin da ya samu, game da ciwon da ƙafarsa take yi masa tun jiya. Sai dai damuwa da tashin hankali ya sanya, bai mayar da hankali a hakan ba, ya karkata ga son kashe wutar da ta taso a gidansa.
****
Hajiya Amina na tsaye cikin matuƙar damuwa, Doctor Sharif ya ce "Hajiya ki yi haƙuri, amma a daren nan, za mu yi mata tiyata domin a ceto ta, da abin da yake cikinta.
"Kuma Doctor babu wata matsala, babanta ba ya kusa, haka ma mijinta"
"To Hajiya ai ba zamu bar ta haka a cikin ciwo ba, ki na kallo ba ta hayyacinta dole mu ceto ta da abin da za ta haifa".
Jiki a sanyaye Hajiya Amina ta karɓi consent form, ta saka hannu, tana mamakin yadda suka kwanta lafiya ƙalau da Shukura, har likitan da ya ganta da yamma, yana faɗin za a sallame ta washegari, a ce lokaci ɗaya ta rikice, duk da ba a tara sani da Allah, kuma babu kusa babu nesa a gare shi.
Haka tana tsaye aka turo Shukura a kan gado, aka shiga da ita tiyata. Ta koma gefe jikinta a sanyaye tana ta adduo'i daban-daban, tana fatan Allah ya sa ba abin da Shukuran take faɗa ne, zai faru ba, da take cewa tana ji a jikinta kamar mutuwa za ta yi, ba za ta rayu ba.
Shukura a hankali ta buɗe idonta, tana kallon likitoci a kanta, ba ta san me suke yi mata ba, ita dai tana jin ana girgiza ta.
Anesthetic ɗin ya ce "Kin farka?" Ta lumshe idanunta ta buɗe alamar eh.
"Ɗaga ƙafarki sama mu gani"
"Ba zan iya ba" ta faɗa a hankali.
Ya ce "To yauwwa, suma ki ka yi ne, shi yasa saboda kar a rasa ki, a rasa babyn, ake yi miki tiyata ba zai yiwu mu ci gaba da barin ki da shi ba, sai mu rasa ku, kuma ba mu sani ba sarkinmu ne na gobe ko shugaban ƙasa" ya yi maganar da sigar wasa.
Ta kasa dauke idanunta daga kan Doctor Sharif, da ya haɗa gumi suke ta ƙoƙarin ciro jaririn.
****
Ƙarfe bakwai da rabi, Nana ta dafa ruwa, ta kai masa banɗaki.
Ta zo kansa ta ce "Sayyid taso ka watsa ruwa, za ka ji daɗin jikinka sosai da sosai"
Ya tashi ya zauna, ya ɗan jima a zaune, sannan ya yinƙura, ta bi bayansa ta raka shi ƙofar banɗakin, ta miƙa masa zanin hannunta ta ce "Idan ka gama ka lulluɓa sai ka fito" bai karɓi zanin ba, ya kalle ta, sannan ya kalli banɗakin.
A take ta gane Abin da yake nufi, amma wani irin nauyin sa take ji, saboda ba su yi sabon da za a ce ta sake ta saba da shi haka ba. Amma ganin ya ja ya tsaya, ya ƙi gaba ya ƙi baya, ya sanya ta wuce shi, ta shiga banɗakin.
Bayan ta ya biyo, yana bin bango, saboda jirin da yake ji, Nana ta din ga sinne kai, tamkar ta gudu saboda tsananin kunyar da ta lulluɓe ta.
Kafin a gama wankan, ita ma sai da ya jiƙa ta jalaf da ruwan, tamkar ɗan ƙaramin yaron goye. Tana zuba masa ruwa a jiki yake zabura, kamar zai shiɗe, sai ya rirriƙe ta. Da dabara a hankali ta ci gaba da zuba ruwan a jikinsa. Ta gama ta goge masa jikinsa su ka fito.
Da ta kalle shi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, amma ta din ga dakewa, tana mazewa.
Ta soya dankalin Hausa da suke da shi, ta dafa shayi, ta zuba masa ta ajiye masa a gabansa.
"Ko na baka a baki?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
Ta yi murmushi, ta saka hannu tana ba shi.
Ya ƙura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi, ya ɗage girarsa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa.
Nana ta ce "Ai na san maganar ta ɗauke, ba sai ka yi mini magana ba, na fahimta" ya sake kallon ta da mamaki.
Ta ce "Ka manta ka ce mini ruhinka yana rayuwa a cikin nawa? Shi yasa nake fuskantar yinƙurinka ko ba ka furta ba"
Murmushi ya yi yana jinjina kai, ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya ɗago su daidai ƙirjinsa, 🙏 ya risunar da kansa alamar ya gode sosai.
Nana ta sauke hannun ta ce "Babu godiya tsakanina da kai, duk da ban san wace irin rayuwa ka baro a baya ba, amma kula da kai dolena ne Sayyid"
Idanunsa suka cika da hawaye, ya kamo hannayenta, ya din ga sumbata, ciki da waje. Tausayinsa ya ƙara mamaye ilahirin jikinta, cikin dakiya ita ma ta sumbaci hannunsa, ta ci gaba da bashi abinci. Sai da ya ƙoshi, sannan ta saka hau kan katifar ya jingina, ta rife masa ƙafafuwan sa da bargo.
Ta tashi tana gyara ɗakin, horn ɗin mota ta ji, ya ɗago ya kalli Nana. Ta ce "Ka zauna kar ka tashi" ta saka Hijjabinta ta fita waje.
Matashin saurayin nan da take gani a gidan, mai tara samari su na kallon Ball ta gani a cikin mota. Ta ƙarasa inda motar take ya sauke gilashin motar ta ce "Sannu da fitowa"
Ya ce "Yauwwa sannu"
"Ka ga ba ya jin daɗi ne, ba shi da lafiya, bari na buɗe maka"
Ya dubi Nana ya ce "Subhnallah me ya same shi?"
"Zazzaɓi ne yake damun sa"
"Allah sarki, wataƙila malaria ce, unguwar akwai sauro sosai. Kin ga wani magani da likita ya bani ɗaya na sha, na ji daɗin sa sosai da sosai, nake yawo da shi a mota. Ki ba shi ga paracetamol ma, zai ji daɗin sa. Je ki kawai zan buɗe ƙofar Allah ya sauwwaƙe"
Nana ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai"
"Ahh ba damuwa" Nana ta ji dadin mutuntawar da ya yi mata, duk da za su yi sa'anni da shi, amma ya yi mata karamci saɓanin 'yar uwassa da ta wulaƙanta mata miji"
Ya sauka ya buɗe gate ɗin ya fita, ya dawo ya rufe.
Nana na shiga ɗakin, ta tarar da shi a tsakiyar ɗakin a tsaye, yana muzurai.
"Ya na ganka a tsaye kuma? Ka kwnata ka huta, ga magani ma ya bayar ya ce a baka, sai ka samu ka sha"
Ya koma kan katifar, ya kwanta, ba tare da ya tanka mata ba.
AREWABOOKS
*****
Shukura ba ta san adadin lokacin da ta shafe ba ta hayyacinta ba.
A hankali ta buɗe idonta, amma sai dai dishi-dishi take gani, tana jin maganganu, amma sama-sama, ba ta gane me ake cewa. Sai sannu a hankali idanunta suka washe ta gane komai.
Mummy ta taso tana faɗin "Sannu Shukura ya jikin"
A wahale ta ce "Mummy"
"Na'am Shukura"
"Ina abin da na haifa?"
"Ki kwantar da hankalinki, an kai shi nursery ne, an saka shi kwalba"
Kawai Shukura ta fashe da kuka tana faɗin "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba mafarkina ne zai tabatta ba, dan Allah Mummy ni a karɓo mini ɗa na, a ciro shi daga kwalbar ba na so a dawo mini da jaririna ba na son wata kwalba"
Cikin damuwa Mummy ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Shukura yanka ki aka yi fa, ko awa uku ba a yi ba, sai kin yi wa kan ki illa? Mene ne dan an kai shi nursery?"
"Ni dai ba na so, ki ce su dawo mini da ɗa na, wallahi zan tashi na je na karɓo ɗa na, idan ba za ki karɓo mini ɗa na ba"
"Shukura ina za ki tashi ki je, jikinki da ciwo meye haka ne?"
Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi da gaske, sai ta tashi sai dai ƙafafuwanta suka ƙi motsawa. Hargowar Shukura da kukanta, ya janyo hankalin ma'aikatan gurin. Suka haɗu a kanta ana ba ta haƙuri, amma fafur ta ƙi yin shiru. A dole aka yi mata allurai ta koma bacci.
Sosai yake tsala gudu a kan titin, yana fatan ya isa gari ya waye.
Yana yi yana kallon inda ya kwantar da jaririn a gefensa, jikinsa kaca-kaca da ƙazantar haihuwa da sauran jini, ga mahaifarsa a gefe ita ma kaca-kaca da jini a jiki.
Yaron baya iya kuka, sai kaɗan-kaɗan, bakinsa sai rawa yake yi, saboda azabar sanyin da yake ji.
Alhaji Zailani yana yi yana kallon yaron, sai dai ƙirjinsa ya yi masa nauyi, ya rasa dalilin hakan. Yana matuƙar ƙaunar Shukura, haka kurum ya din ga jin kamar bai kyauta mata ba. Amma da ya tuna girman buƙatar sa, na mamaye duniyar sa da samun duk abin da ya sanya a gaba, sai ya ƙara azama da ƙara gudun giyar motar.
Daji ne sosai da sosai, ya yi parking ya ɗaukko jaririn, ya fita ya nausa cikin duhun duƙununun dajin.
Yana tafe ya hango wuta tana ci, ya ƙarasa gurin da wutar take ci. Malam Gambo ne sanye da jajayen kaya, ya nufo shi yana faɗin "Ka kusa makara fa"
"A yi mini afuwa, amma ina fatan wannan aikin zai zama daidai da sadaukarwata ta shekara".
"Ƙwarai kuwa, ba za a sake neman jini daga gare ka ba a wannan shekarar"
Ya miƙa wa Malam Gambo jaririn, ya saka hannu ya karɓi yaron, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwansa a sama, ya danna tafin ƙafar jaririn, a take ya tsanyara ihu, ihun jaririn ya cika dajin.
Malam Gambo ya haska fitila, ya ɗaukko wani abu a cikin wata jaka, ya saka shi a wuta, ya yi ja ya juya bayan yaron, ya zana wani hatimi a jiki, ya sanya sunan Fatuhu Magaji a cikin hatimin. Yaron ya din ga tsala ihu tamkar ana zare masa rai.
Suka haɗu da shi da Malam Gambo, suka tona rami, suka binne jaririn da ransa.
Duk da ba yau Alhaji Zailani ya saba irin wannan abubuwan ba, amma na wannan karon shi kansa ya girgiza zuciyarsa.
Malam Gambo ya ɗauki mahaifar, ya ce "Wannan na 'yan aike ne, su za su cinye ta, kai za ka iya tafiya, bayan kwana talatin za mu zo a cire ƙwarangwal ɗin, za a yi wani aikin da shi. Ka huta ka yi yadda ka ke so Alhajin Allah, in dai Duniya ce ka same ta yadda ka ke so".
Suka yi sallama Alhaji Zailani, ya hau motarsa ya nufi gida.
A wani irin mugun razane Nana ta tashi daga nannauyan baccin da take yi, ta tashi zaune. Tsaf abin da ta gani ya dawo mata kai fes ba ta manta komai ba.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ka duba lamarin nan, Allah ya sa shirmen mafarki ne"
Tashi ya yi zaune shi ma ya ce "Me ya faru?"
Ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce "Babu komai, maganar ta dawo?"
"Eh" ya faɗa a taƙaice.
"Sannu ya jikin?"
"Alhamdilillah"
"Ko na ɗaukko maka maganin da aka bani, ya ce yana da kyau ka jarraba sha"
Ya ce "Ba na sha" ya yi maganar yana kwanciya.
Ta dafa shi ta ce "Sayyid, duniya ba za ta yiwu mu rayu mu biyu ba kawai, dole wasu lokutan mu na buƙatar taimakon mutane, dan mu rayu cikin aminci mu ma. Na san haƙƙoƙinka na aure da suke kai na, dan baka da cikakkiyar lafiya ba ya nufin zan ci amanar auren ka.
Na san ni Ahalinka ce, kuma wani shinge da babu wanda zai ratsa shi." Ya yi mata shiru.
Ta kwanta a gefensa, tana shafa gashin sa, ta ce "Sayyid ka yi mini magana mana"
"Ba ki san me nake ji ba ne"
"Na sani mana, ka manta ruhinmu ɗaya ne?" Ya yi shiru ya lumshe idanunsa yana jin daɗin, yadda take wasa da gashin sa.
"Sayyid"
"Ma vie"
"Dan Allah da gaske Alhaji Zailani ya ce maka ka sake ni?"
Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Eh, ya ce zai ba ni kuɗi. Zuciyata kamar zan mutu a ranar"
Ta ce "Me ka ce masa?"
"Ba zan iya tunawa ba, kawai dai na ji numfashina zai ɗauke ne, na manta meyafaru"
Ta ɗan yi murmushi ta ce "Rayuwa kenan, daga ni har kai dai gamu nan kawai, Allah ya shiga al'amarinmu. Sayyid ina jin tsoron kar ka tuna waye kai, ni kuma ka manta da ni"
Ta ji shiru, bai yi magana ba. "Sayyid " ta kira sunansa, amma tuni ya yi bacci. Saurin baccinsa har mamaki yake bata.
Zuciyarta kuma ta ci gaba da hasko mata mummunan mafarkin da ta yi, da Alhaji Zailani, dan haka take ta fatan, gari ya waye, ta kira Hajiya Amina ta ji yaya ake ciki.
Sai dai ta kasa komawa bacci, ta din ga tunane-tunane daban-daban a cikin ranta.
Ba ta san adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji ya ce "Ba ki yi bacci ba haryanzu? Mafarki ba gaske ba ne ba fa"
Nana ta ce "Ba mafarki na yi ba, na kasa baccin ne"
"Ƙarya babu kyau, kin tsorata a mafarki. Kuma kin gaji ma yau sosai, kina ta kula da ni, na gode sosai bari na yi miki tausa"
"A'a ci gaba da baccinka, daga tausar nan har a yi asuba ba zan yi bacci ba, bar ni kafin a kira salla na rage na yi baccin"
Dariya ta ji yana yi ya ce "To a bari sai bayan sallar asuba"
"A'a ba ni da lafiya" ya ƙara matsawa kusa da ita, ta ji shiru har ya sake komawa bacci.
Ƙaisar ta gani yana ɗaure Sayyid a jikin wata itaciya. A razane ta nufe shi ta ce "Ƙaisar mene ne haka? Me ya yi maka?"
"Kar ki kuskura ki zo gurin nan, ai na gaya miki tun da ya kwance ƙullin nan, sai ya ɗanɗana shi ma"
Nana ta ce "Wai tayaya ya kwance ɗaurin da ka yi? Shi da ba aljani ba, kuma bai san abin da yake ɓoye ba, ka sauke shi dan Allah"
"Ke ki ke ganin shi mutum kamar kowa, na gaya miki kar ki kuskura ki zo gurin nan, zan yi miki illa"
Ba ta tsaya ba ta ci gaba da tunkarar sa.
Hankaɗe ta ya yi gefe, ya cigaba da ɗaure Sayyid a jikin itacen nan.
Ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta sake nufar sa, sai dai kafin ta ƙarasa, tsohon nan ya bayyana ya make Ƙaisar gefe.
Da sauri Nana ta ƙarasa, ta hau kwnace Sayyid da yake a galabaice, ya fita daga hayyacinsa. Faɗa ne ya kaure tsakanin Ƙaisar da tsohon.
Sayyid ya yi shiru, ya zubawa Nana ido, yana jin duk yadda take, furta abin da take gani a cikin mafarkinta a zahiri.
Ya cigaba da kallon fuskarta, ds yadda gumi ya tsatstsafo mata a goshinta, ta rirriƙe shi gama tana kuka.
Ya saka yatsunsa biyu a ƙyerta ya danna, a take ta yi shiru, jikinta ya saki.
Da Safe yana ta bacci, ta tashi ta yi aikace-aikacen ta.
Bayan tashin sa ya karya, ya yi wanka ya fita waje, sai dai tun da ya tashi bai yi magana ba.
Ta gama aikinta ta fito, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi tana yi masa hira, yana jin ta amma ba ya magana.
Kubra ce ta nufo inda suke zaune, tana tahowa ya sunkuyar da kai.
Nana ta tashi ta ƙarasa inda take, ta ce "Sannu ina zuwa haka?"
"Fita zan yi"
"Ki je ina?"
"Fita kawai zan yi" ta bawa Nana amsa.
Nana ta miƙa mata hannu da nufin su gaisa.
Ita ma ta miƙa mata suka gaisa, sai dai a wannan karon Nana ba ta ji sanyi ba. Nana ta kalle ta daga sama zuwa ƙasa, riga da wando ne na bacci a jikinta, kanta ko ɗan kwali babu.
Nana ta ja ta ɗakinsu, ta shimfiɗa mata sallaya ta ce "Zauna" babu musu ta zuna.
Nana ta zuba mata abinci ta ce "Na ji an ce ba kya cin abinci, bismillah mu ci" babu musu ta kama cokali ta na cin abincin.
Cikin tausaywa Nana take kallonta, tana matuƙar jin tausayin mai fama da irin wannan larurar, wanda duk ba shi yake ɗauke da larurar ba, ba zai gane wahalarta ba. Mussaman idan na kusa da shi, ba su fahimci kan ciwon ba.
Ta cinye tas, Nana ta ɗauke kwanon ta kalli Nana ta ce "Na daɗe ban ci Abinci da yawa ba"
Cikin kulawa Nana ta ce "Me yasa?"
"Ba na so kwata-kwata. Ba ma na iya bacci."
"To me ki ke ji a jikin ki?"
Ta ɗan yi shiru ta ce "Kawai dai ji nake mutuwa zan yi, sai na yi ta kuka"
Nana ta tashi ta ɗaukko mata pillow, ta ajiye mata ta ce "Kwanta da yardar Allah za ki yi bacci" ta kwanta ta yi shiru, Nana ta kunna mata karatun Alkur'ani. Ta nutsu tana saurara, har bacci ya ɗauke ta. Farin ciki ya kama Nana, ganin ta yi bacci. Ta ce "Ya Allah, kai ka ke jarraba bayinka da larura, wasu ka haska musu maganinta, wasu kuma ka ɓoye. Ya majiɓancin lamarinmu, Allah ka yaye mana wannan larurar".
*****
Misalin ƙarfe goma da rabi da safe, Baba yana ya bala'in an ba shi koko ɗan kaɗan babu sugar, alhalin an san ba isar sa zai yi ba.
Mama ta ce "Da ka samu wannan ɗin ma, Jamila ce ta bayar da kuɗin gasarar, yarinyar da ka ke nufi da sharri kai da ɗan ka, sai ka bari idan ka nemo, ka fara kawowa sai ka nuna isa da iko"
Sallamar da aka yi ya amsa, yana jiran ya ga suwaye, sai dai ya saroro baki buɗe yana kallon masu sallamar. Su ka shigo niƙi-niƙi da kaya a hannun su.
Mama ta fito daga kitchen, ta ga suwaye, ta ce "Too ikon Allah, yau kuma da abin da muka tashi kenan?"
"Lafiya yaya aka yi?" Ya tambaye su kamar ya ga annoba.
"Malam Isa ai kwa bamu guri mu tsuguna tumu tsuguna tukuna"
"Ba wani a baku guri ku tsuguna, ba na son fitina, meya kawo ku?"
Ɗaya daga cikin su ta ce "A'a duk ba abin zafi ba ne ba ai, labarin auren Nana mu ka ji, shi ne muka zo mu tabattar"
Baba ya ce "Eh, haka ne na aurar da Nana, tun da 'yata ce, kuma ina da hurumin aiwatar da hakan"
Saude ta ce "Haka ne, amma mahaifiyarta da mu ma, mu na da hakki a kan ta, ai yakamata a sanar da mu"
"Ba zan sanar ba, na ce ba zan sanar ba ɗin? Me sanar mukun zai amfanar?"
Mama ta ce "Rakiya auren ne fa aka yi shi babu shiri, saboda magana ta nemi ta ɗaukko mana aka yi shi, ba wani taron kirki aka yi ba"
"Amma duk da haka, ai ya