Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
kafin daga bisani ya rikiɗe mata zuwa wannan tsohon. A razane ta fara ja da baya. Ya ja da baya ya buɗe bakinsa, zai fara feso mata wuta, Ƙaisar ya bayyana yana wani irin huci.
Tsohon ya buɗe bakinsa yana dariya mai razanarwa, hayaƙi na fitowa daga bakinsa, ya ce "Na sani, na san za a rina, ta wannan hanyar ce kaɗai zan hukunta ka Ƙaisar"
Cikin tsawa Ƙaisar ya ce "Kuskure mafi girma da zaka aikata, shi ne cutar da yarinyar nan, cutar da uwar gijiyata tamkar cutar da ni ne, dan haka ni da kai muke wannan rigimar babu ruwanta, domin babu ta yadda za a yi ta biya bashin da ba ita ta ci shi ba"
"Ƙarya ne, sai ta biya shi, ita ce za ta biya ka sanya wannan a ranka. Ka fi kowa sanin ba ma yafiya, ba ma yafe bashin gaba, sai ta biya wannan bashin" ya ɗaga sandarsa ya nuna Nana da ita, amma cikin zafin nama, ta ji an yi sama da ita an watsar a guri ɗaya.
A hankali ta ja jikinta tana tari, ƙaisar ya bayyana a gabanta, cikin ɓacin rai ya ce "Ki sanya a ranki ba a yi komai ba, ƙalubale da tarkuna marasa adadi mun din ga faɗa musu kenan, idan mun tsallake wani, wani sai mun faɗa masa"
Nana ta ɗago kanta a galabaice ta kalli Ƙaisar ta ce "Wai dan Allah waye wannan tsohon? Me na yi masa, Ko shi ne na aura a suffar mutum ne?"
"Sanin waye shi, ba shi da wani amfani a gare ki. Ki yi ta kanki da rayuwar ki kawai. Ko dai ki bar wannan auren mu tsira baki ɗaya, ko kuma yanzu mu ka fara wahala".
Nana ta girgiza kai ta ce "Sanin waye shi yana da amfani a gare ni, waye shi? Meye alaƙa ta da shi da yake tsorata ni, laifin me na aikata masa yake iƙirarin sai na biya? Da wace hujjar zan kashe auren nan? Ko har ka manta irin ƙalubalen da na keto?"
Shiru Ƙaisar ya yi mata yana karkaɗe rigarsa, har ta buɗa baki za ta yi magana, ta jiyo sautin wata ƙara a bayan wata ƙofa, kuma ta ji tamkar ta san muryar da ta yi ƙarar.
"Ihun me nake ji haka?"
"Je ki duba mana" ya bata amsa yana yin gaba, ya nufi kofar da sautin ƙarar yake. Yana shiga Nana ta rufa masa baya, sai dai ta yi turus da ta ga Jamila a ɗaure a jikin wani itace, jikinta babu kaya, fatarta tamkar ta ƙone, ga wasu zarurruka da aka saka, aka ɗaɗɗaure ta da su.
Hankali tashe Nana ta ce "Kai Jamila, me ta yi maka? Meya same ta haka?"
Ƙaisar ya ce "Me ta yi mini ki ke tambaya? Me ya faru bayan kin ci abincin da ta kawo miki? Idan Alhaji Zailani zai kassara yaran da ya haifa a cikin sa, saboda duniya ke me yasa ki ke tunanin dan kun haɗa uba ɗaya da ita ba za ta cuce ki ba? Dole ta karɓi hukuncin abin da ta aikata, ko da kuwa ya kama na kashe ta ne.
Nana za ta yi magana ta ji ana taɓa fulon da take kai.
Ta buɗe idonta ta ga wani irin matsanancin duhu, babu alamar haske ta ko ina. Ta yinƙura ta tashi zaune, tana faɗin hasbunallahu wani'imal wakil.
Ta miƙe tsaye tana laluben hanya, ganin duhun na ƙara tsananta. Walƙiya aka yi mai tsananin haske, da ya gauraye ɗakin, ya bayyana tsaye da sandarsa yana kallon Nana. Rikicewa ta yi ta saka ihu. ta zabura za ta kasa da gudu. Tun da ta tashi tsaye a kan katifarta yake kallonta. Sai da ta yi ihun nan, ta nufi hanyar waje, ya miƙe da azama ya riƙe ta.
Fizge-fizge ta hau yi cikin matsanancin tsoro da razani.
"Me ya faru ne?" Ya yi magana cikin nutsuwa da kamala.
Fashewa ta yi da kuka, cikin rawar murya ta ce "Tsoro nake ji, dan Allah ka daina tsorata ni"
"Me na yi miki?" Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da damuwa.
Ta ɗaga kai ta kalli kamilalliyar fuskar sa, ya lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. Ta sunkuyar da kanta tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, zuciyarta take bugawa, jikinta sai tsuma yake yi.
"Zo ki kwanta" ya yi maganar yana janyo hannunta, zuwa kan katifa. Kallonsa take yi, tana tunanin waye shi? Me yake faruwa da ita, ko dai ta tabatta Ƙaisar ya fara burkita mata hankali ne, ta fara haukan da gaske?.
Ya zaunar da ita a kan katifar ya ce "Yi bacci" ya yi maganar yana nuna mata shimfiɗar.
Duk da tana cikin tsoro da damuwa, bai hana ta mamakin yadda yau yake magana ba.
Ya sake cewa "Ki yi bacci mana"
Ta girgiza masa kai ta ce "A'a"
Ya ce "Me yasa?"
Cikin damuwa da razani ta ce "Idan na yi bacci tsorata ni za ka yi, tsoro nake ji" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye.
"Ni ba na tsorata ki, ba abin da na yi miki"
Ya saka hannunsa, ya goge hawayen da yake zubo mata, a hankali ya fara hura iskar bakinsa a kan fuskarta. A hankali jikinta ya fara sanyi, gaɓoɓinta duk suka saki, wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
****
Cike da mamaki, Hajiya Amina take kallon Alhaji Zailani ta ce "Amma yarinyar nan a gidan nan ta yi mana aiki, har murna ka ke yi yadda ta kula da Haidar, mene ne a ciki dan na je na ga inda take na yi mata Allah ya sanya alkhairi?"
Alhaji Zailani ya fututtuke fuska ya tsuke fuska ya ce "Na ce ba za ki je ba, ba dai raino ne ba, ta yi ta gama, dole ne sai kin yi hulɗa da ita? Shegen jajibe-jajibenki na tsiya, ki kwaso wa kanki wata masifar?"
"Amma Alhaji kai ka ke faɗar haka da kanka? Duk yadda ka ke da taimakon al'umma, da son mutane kai ne kuma mai cewa ina jajibo mutane, haba...
"Ya isa Amina, na ce babu inda za ki je"
Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce "Shikenan, an wuce gurin"
Ya fice fuuu ya bar mata ɗakin, nasa ɗakin ya wuce, ya zauna a kan gadonsa ya yi shiru. Ya rasa ta ina yakamata ya ɓullowa lamarin nan, ammma ko ta halin ƙaƙa yana buƙatar Nana. Saboda yadda ɗari bisa ɗari ya yi amanna da samun biyan buƙatar sa ta hanyar ta.
A wannan karon ma sai da ya tsinewa Baban Nana, dan shi ne silar wargaza komai.
*****
Jamila ce zaune a ɗakin Mama tana ta uban kuka, saboda yadda ta wayi gari da wasu irin ƙuraje, masu ƙaiƙayin tsiya da ta sosa sai su kwailaye kamar ta ƙone, ga wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon kai da take yi.
Gaba ɗaya mama ta rikice, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ta rasa yadda za ta yi da Jamila, a saka mata kaya su tafi asibiti abu ya gagara. Ga Baba shi ma yana ta fama da ciwon ƙafa, sai sayen man zafi da diclofenac yake yi, amma abu ya gagara kullum kamar turi, ji yake yi tamkar an ɗora masa dutse a kan ƙafafuwan nasa.
"Ni na rasa yadda zan yi da wannan jarabar, Jamila anya ba Nana ce ta yi miki wani abin ba, wannan wane irin abu ne?"
Nasiru ya ce "Kai wallahi Nana ba ta yi mata komai ba, hira fa kawai aka yi da cin abinci"
Baba ma ya ce "Yarinyar nan dai ba ta ma gidan nan, balle a ce ko ita ce, dan Allah a daina wannan maganar ma"
Haka Jamila ta wuni, ko ruwa ta sha sai ta yi amai, ga jikinta ya daina yi mata ƙaiƙayi sai ma wani irin zafi"
Hajiya Sa'a ce a zaune da jajayen kaya, gaban malaminta. Ransa a ɓace ya ce "Hajiya Sa'a na gaya miki a din ga bin komai a hankali, ki daina gaggawa. Yarinyar nan ba za ta taɓu ta sauƙi ba. Aljaninta ya kama ɗaya daga cikin manyan 'yan aikenmu, da ki ka yi amfani shi, ya saƙale shi a jikin kurwar yarinyar ki, yana azabtar da shi ta gangar jikinta, wannan ba dai-dai ba ne ba. Da kin sani a cikin ƙanan jakadunmu ki ka haɗa ta da wani. Amma kin haɗa ta da babban hadiminmu, ya yi masa illa"
Cikin damuwa ta ce "Tuba nake, a yi mini afuwa, amma yanzu mene ne abin yi?"
"Abin yi, dole a je a ba shi haƙuri, a saurari sharuɗɗan da zai gindaya kafin ya saki kurwar yarinyar, dama aljanin a cikin kurwarta yake ai"
"Yanzu shikenan buƙatarmu ba za ta biya a kanta ba kenan?"
"Za ta biya, amma akwai lokaci. Shi ma yana kare ta ne saboda ta sa buƙatar, amma akwai wani abu da zai ɗauke masa hankali a 'yan kwanakin nan, zamu iya amfani da wannan damar, mu yi abin da muke so" Hajiya Sa'a ta jinjina kai cike da gamsuwa.
*****
Da safe babu kowa a ɗaki sai Nana, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta gama ta buɗe ƙofar ta fito, ta ganshi yana gyara mata shimfiɗarta, ya karkaɗe mata. Ya ɗauki tsintsiya ya fara share ɗakin.
Ya ɗago suka haɗa ido, ya kawar da kansa ya ci gaba da shararsa. Saboda daga ita sai zanin wankanta ta fito, dan ba ta san yana ɗakin ba.
Nana ta ƙaraso ta ce "Ka bari, zan share ɗakin, bari na shirya"
"Ba komai, ki huta ba kya jin daɗi" ta ɗan ware ido, jin ya yi magana.
Ta numfasa ta ce "Ina kwana"
"Wane kwanan?"
"Gaishe ka na yi fa" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da kansa ya cigaba da shararsa, ya gama ya kwashe ya je ya zubar.
Ta shirya yana gefe yana aikin shan shayi, yana haɗawa da dabino yana ci.
Ta bubbuɗe kazar da Habu ya kawo, ta ɗumama, ta ɗibi miya ta haɗa su ta ƙara dafawa, ta zuba ta ajiye a gabansa.
Ya girgiza kai ya ce "Naki ne, ki ci"
Ta ce "Ai na ci, kai ba ka ci ba"
Ya girgiza kai ya ce "Na ƙoshi"
Nana ta sake tura masa kwanon ta ce "A'a ba ka ƙoshi ba, dan Allah ka ci" ta yi maganar tana saka masa cokali a kan kwanon.
Ya kama cokalin, ya ɗan yagi kaɗan zai kai bakinsa ya ce "Bismillah" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi da mamaki.
Jiki a sanyaye ta ce "Na san wataƙila ina yin wasu abubuwa, da za ka kasa gane kaina, kamar ba ni da hankali wasu lokutan. Na san babu lallai an yi maka bayani, ina fama da rashin lafiya ne" ta yi maganar tana wasa da yatsun hannunta.
Ya ce "Aa yau ba ki yi rashin lafiya ba, kin warke ai tun jiya" sai ta ga kamar bai fuskanci abin da take nufi ba.
Ta tsura masa ido, tabbas ma sha Allah, kyakyawan ne, fari ne mai dogon hanci sosai da ɗan siririn sajen sa, kuma a nutse yake. Babu babban abin da yake ɗaukar hankalinta game da shi, bayan nutsuwar sa, sai wannan kyakyawan dogon gashin da yake da shi, tamkar mace. Duk da ta kasa tantance abubuwa da dama a kansa, amma zuciyarta na ɗauke da tarin tambayoyin da take fatan bakinta ya furta.
Ya ɗago shi ma ya tsare ta da nasa idanun, yana tauna a hankali. Ta sauke nata idanun ta ce "Amm ban san sunanka ba haryanzu ba fa"
Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Zan sha ruwa" tana mamakin dalilin da ya sanya yake kaucewa wannan tambayar har sau biyu, sai ta ƙyale shi, ta ɗaukko ruwan ta ba shi.
"To ka bani wayata, na yi kallo"
"A'a" ya furta yana tashi tsaye. ya tafi gaban mudubi, ya fara shiri. Yana tsaka taje gashin nasa, ya hango Nana ta cikin mudubin, tana kallonsa. Ya ɗaukko comb ɗin ya nufo Nana, da sauri ta sunkuyar da kai.
Ya zo gabanta ya miƙa mata comb ɗin, ta tsaya tana kallon sa, ya ƙara miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa, ya gyara zamansa ya juya mata baya, ya ɗan yo baya da kansa. Ta yi shiru tana kallon kan nasa.
"Ki taɓa, na ga ki na so" wata irin kunya ta kama Nana, haushin kanta ya kama ta, yadda ta bari har ya iya gane gashin kansa yana burge ta.
Ta dafa kafaɗarsa, da nufin ta tashi, kawai ta gansu a wani ƙasaitaccen ɗaki na alfarma, maimakon ɗakin su.
Ta kalli jikinta, ta ganta sanye da wasu kayan na daban. Hannunta dai riƙe da comb ɗin. Duk yadda ta yi ƙoƙarin yin magana ta kasa.
Ta saka hannu, ta fara taje lallausan gashin nasa, ta gama ta tufke masa kamar yadda yake yi. Ya miƙe tsaye ya juyo ya kalle ta, ya kama hannunta ya sumbata ya ce "Allah ya yi miki albarka"
Kamar wadda aka jonawa shocking ta zabura, ta ga ɗakin ba kowa, ga dai kwanukan da ya ci abinci, ya wanke ya ajiye mata. Ta tashi tsam ta je ta leƙa ta taga, ta hango shi a zaune a kan kujera, a gefen gate ya kara radio a kunnensa, gefe ga butar shayin sa.
Ta dafa bango ta jingina a hankali, hawaye ya fara ziraro mata, a hankali ta ce "Ka yi nasara ƙaisar, ka burkita mini ƙwaƙwalwata fiye da baya. Na fara hauka, ba na iya tantance zahiri, tunani da mafarki. Ka cutar da ni" ta ƙarasa maganar tana sheshsheƙar kuka.
Muryar Ƙaisar ta ji tana amsa kuwwa a ɗakin. "Ba ni ba ne, ko zan saka ki hauka ba yanzu ba, da sauran lokaci, ina ƙara baki lokaci ne. Abin da na yi ta yi miki gargaɗi a kai ne"
"Allah yana tare da ni, ba zan bayar da magani ba Ƙaisar, ba na buƙata ka ƙyale ni na yi rayuwata dan Allah" ta ƙarasa maganar wani kukan yana kufce mata.
"Nana" ta ji muryarsa a bazata. Da sauri ya sauke rawaninsa a kiɗime ya ce "Meya faru?" Kasa magana ta yi, ta ci gaba da kuka.
Cikin damuwa yake kallonta, ya rasa abin da zai ce mata, ga shi da gaske kukan take mai tsuma zuciya.
"Na yi wani abu ne?" Ya furta yana kallonta. Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya sake cewa "Ba lafiya ne?"
Ta sake girgiza masa kai. Ya saka hannu ya dafa kafaɗarta, a take wani irin sanyi ya shige ta, har ƙafafuwanta.
Babu tsammani ya haɗa ta da ƙirjinsa, duk da tana jin yadda zuciyarta take harabawa da sauri, amma ta yi shiru ba ta motsa ba, ba ta tunanin a rayuwarta, akwai wanda ya taɓa ba ta wannan damar. Maimakon ta daina kukan, sai ta sake fashewa da sabon kuka, sababbi da tsofaffin damuwoyinta duk suka taso mata. A hankali ta ji ya zura hannunsa a cikin nata ya riƙe.
Duk da a ƙasan zuciyarta, tana jin mafarki ne, amma ta ji daɗin samun damar zubar da hawayen nan da ta samu.
*****
Tamkar zai tashi sama, haka yake bala'i yana kumfar baki.
"Ai dama na sani, wallahi haryanzu tana son tsohon mijinta, kuma tana magana da shi ta waya, ina da cikakkiyar shaida a kan hakan"
Wata babbar mace da fuskarta ke ɗauke da damuwa ta ce "A'a Iliyasu, ba na tunanin Mai jidda za ta yi haka"
"Au goya mata baya za ayi ma kenan? Ina da cikakkiyar shaida, ba na son mutuncinta ya zube ne kawai saboda 'ya'yana"
"A'a ba goya mata baya zan yi ba, amma ka yi haƙuri dan Allah"
"A'a a yi magana a buɗe, idan tsohon mijinta take so, to ta koma gurinsa ba dole"
Maijidda na gefe tana ta sharɓar kuka, tamkar ranta zai fita, ya gama bambamin masifarsa ya fice daga gidan.
Matar ta dawo da hankalinta kan Maijidda ta ce "Wai maijidda abin da Iliyasu ya faɗa gaskiya ne? Ana idar da sallar asuba fa ya kira ni a waya ya ce lallai na zo na ji abin da ki ka aikata"
Cikin kuka ta ce "Wallahi Adda ba a yi haka ba, roƙonsa kawai na yi ya bani dama na je na ga halin da yarinyata take ciki, an ce mini an yi aurenta, amma ban sani ba, ko ba komai Nana da Imaran su ma yarana ne, na rasa irin wannan abu ƙiri-ƙiri an raba ni da yarana"
Adda ta ce "To ke mai jidda ban da abinki, ba a gurin babansu suke ba? Ko a kan yara biyu sai ki salwantar da aurenki, da yaran nan shida saboda guda biyu ne?"
Ta ɗago jajayen idanunta ta ce "Adda su ma biyun ni na haife su, ba su da kama ta, su na buƙata ta, shekara goma sha ina tattalin wannan auren, duk da ƙiyayyar da yake nuna wa 'ya'yana amma wallahi zuciyata na Kano tare da Nana da ɗan uwanta"
"Aikuwa sai ki yi haƙuri, Allah ya ƙaddara abin da zai riga ya faru. Yanzu ki bari zan shirya da kaina, ki kawo abin da ki ke da shi da ki ka ajiye saboda aurenta, mu haɗa a kai mata ke dai ki yi haƙuri da zuwa, zuwa lokacin da zai saukko. Bari na kira shi a waya"
Adda ta kira Iliyasu, sai da ta ta tsinke ta sake kira, sannan ya ɗaga.
"Dan Allah malam Iliya ka yi haƙuri, ita ma ta ce a baka haƙuri, ba za ta sake ba"
"A'a ai na daɗe ina fuskantar take-takenta ne, kuma wallahi ba za ta sake riƙe waya ba, kuma wallahi ta sake ta taka zuwa ƙafarta zuwa garin Kano, ta fake da yaranta ta haɗu da tsohon mijinta, a bakin aurenta tun da ni na ɗan iska ba ne"
"Ai ba ma za ta sake ba, ta tuba ta daina ka yi haƙuri ka yafe mata" ya gama bala'insa, Maijidda na jin sa ba abin da take yi sai kuka.
"Maijidda ki yi haƙuri, idan ki ka kashe auren nan saboda yara biyu ya za ki yi da na gaban ki? Duk abu gidan nan akwai ci akwai sha. Idan ki ka koma gidan Gwaggo ma, ita ba cikakkiyar lafiya ba, ga babu guri gara ki yi haƙuri. Ita yanzu tun da ta yi aure ta samu ta zo inda ki ke" Adda ta gama maganganunta, Maijidda ba ta sake tofawa ba.
****
Habu ne a tsaye a ƙofar ɗakin, yana kwaɗa sallama, ya amsa masa.
Ya ɗaga labulen ya shiga, kawai ya tarar da su a zaune a gefen katifa, Buzu yana fifita mata shayi a kofi, gabanta kuma ga ledar ƙosai ga kankana. Tana tauna ƙosan a