Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
dama dai kin amincewa buƙata ta na taimakon soyayyata da na yi duk wata kasada da ki ke buƙata, je ki sai an jima" ta juya ta koma, Nana ta bi ta da kallo har ta ɓacewa ganinta.
Tana ta saƙe-saƙe, har ta ƙarasa gurin da yake zaune a kan benci, ta zauna a kusa da shi.
Ya ce "Kin dawo?"
"Eh, me ka ke yi mini da waya ne?"
"Kallo" ya bata amsa a taƙaice.
"Yauwwa Sayyid, dan Allah gidan Anty Ummi nake son zuwa, na gaishe ta, kuma a yi mini kitso, tun da na tsefe kaina, na ban yi kitso ba" ya yi mata shiru.
Jin ya yi shiru ya sanya ba ta sake maganar ba.
Bayan ya yi sallar azahar, ya ci abincin rana, ta ɗaukko reza ta zauna, tana yanke masa farce. Kamar wadda aka takara ta ce "Sayyid su Habu kwana biyu ba su zo ba, Allah ya sa lafiya"
AREWABOOKS
Yadda ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya sanya Nana nutsuwa, da tuna katoɓarar da ta aikata. Ba shiri ta ja bakinta ta tsuke. Har ta gama yankan farcen bai sake kula ta ba.
Nana a ranta ta ce "Na shiga uku, wannan baƙin kishin ya yi yawa. Daga tambaya?'.
Duk wasu 'yan kame da kame, da Nana za ta yi, ya kula ta ya yi mata shiru, ya ƙi kula ta.
"Allah ya haɗa ni da gamona"
Ya fita sallar isha'i, ta kira Ummi, suka gaisa, take bawa Ummi labarin zuwan su Adda Saude.
Ummi ta ce "Gaskiya Nana idan an kwana biyu, ki ɗauki mijinki ku je ku gaishe ta, duk tijarar da mijinta zai yi, ki rufe ido ki je ku gana, mutuwa ake ji"
Nana ta sauke numfashi ta ce "Haka ne, shi ma haka ya ce min, kuma ina da wannan tunanin. Ina cikin damuwar rashin sanin halin da Imarana yake ciki ma."
"Kin ga ki rabu da wannan, namiji ne ranar da Allah ya nufa, zai waiwayo gida, tun da an ce an riga an kama wanda su ka yi kisan kan"
"To shikenan. Ina nan tafe zan zo ki yi mini kitso ma, kaina tun da na zo da kitson biki da na tsefe, babu kitso a kaina ne, ina lallaɓa shi ne ya ƙi bari na"
Ummi ta kwashe da dariya ta ce "Au ya ƙi barin ki, har hana fita unguwa yake yi? Yana gane abubuwa dama?"
Nana ta ce "Kai. Ba fa ko yaushe yake cikin halin rashin lafiya ba. Yana gane komai sai dai idan abin ya waiwayo ni faɗa ma mu ka yi wallahi ya ƙi kula ni, kuma so nake ya bari na zo wallahi"
Ummi ta ce "Ikon Allah, wallahi har mamaki nake yi, mutumin da ba ya kallon mutane, balle ya yi magana, ashe yana yi. To ai shikenan idan ya bar ki a satin nan, har da gyaran jiki zan yi wa wata amarya, na haɗa da ke"
"Hajiya Ummi sabga, sana'a ta kankama, to sai kin ji ni"
Ta ajiye wayar, ta kunna turaren wuta a ɗakin, ta yi shirin kwanciya, tana ta lissafin yadda ta rarrashe shi, sai dai nauyin hakan take ji, da wata irin kunya tana tunanin ta ina za ta fara.
Ya shigo da sallama, muryarsa ƙasa-ƙasa Nana ta amsa tana kallonsa.
Ya rage kayan jikinsa, tana tsaye a gaban mudubi.
"Sannu da zuwa"
Bai ko kalle ta ba, ya kashe fitla ya haye kan katifa ya mimmiƙe.
Yadda Nana ta faɗa kan katifar, ta danne masa hannu , ta zata zai yi magana, amma ya shiru bai ce uffan ba.
Nana ta rasa me za ta ce masa, ƙarshe ma ya juya mata baya gaba ɗaya.
Nana a ranta ta ce "Allah ya yaye maka Sayyid"
Ta zura hannu ta warware gashinsa, "Sayyid ka din ga yi mini uzuri nima, ba na son irin wannan fushin na ƙyaliya, yana takura zuciyata sosai. Amma shikenan" ta yi maganar muryarta na rawa, kamar za ta fashe da kuka. Ta yinƙura za ta juya, amma ya riga ta juyowa.
"A'a kar ki yi kuka"
"To ni ka daina yi mini irin haka"
"To na daina" ya faɗa yana kai hannunsa fuskarta.
"Kar ki yi kuka fa" jin yadda ya shiga damuwa nan da nan, ya sanya ta ci gaba da kunna shi, ta hanyar yin taɓara iri-iri.
A ranta ta ce "Ohh, wai yau ni ce ba a son na yi kuka, da uban wa ya damu idan ma rijiya zan cika da hawaye?"
Ta ƙarfin tsiya ta saka ya din ga rarrashinta, da Hausa da French.
Da Asuba kuwa sam bai tashi da alamar ma ya yi fushi ba, saboda kar ta yi kuka.
Bayan ya dawo daga salla, tana kwance a jikinsa ta ce "Dan Allah Sayyida ka bar ni na je a yi mini kitson nan, na je gurin 'yar uwata dan Allah"
"A'a"
"Dan Allah Sayyid."
"Idan kin tafi wa zai kula da ni?"
Ta yi murmushi ta ce "Zan ajiye maka duk abin da ka ke buƙata, dan Allah ka bari na je Please. Ba dan kar na zaunar da kai ba, sai mu tafi tare ma, to ka ga bai kamata na bari ka na jira na ba"
"A dawo lafiya" ta zabura ta ce "Ka yadda na je?"
Ya jinjina kai. "Allah ya saka mini kai a aljanna na gode sosai Shugabana"
Ya yi murmushi ya ce "Sayyid yanzu kuma Shugaba"
"To ai duk abu ɗaya ne" kyakyawar sumbata ya samu a bakinsa, daga matarsa saboda tsananin farin ciki da ta shiga.
Da safe ta ya ƙoƙarin gama girki da wuri, ta ɗora masa na rana, ta dafa ruwan zafi ta zuba masa a flask da duk abin da take sanya ran zai nema.
Ta yi wanka ta fara shiri, su ka yi waya da Hajiya Amina, take gaya mata kwana huɗu kenan, an yi wa Shukura aiki yaron ya rasu. Nana ta ji ta damu sosai da sosai, ta yi mata jaje ta ce za ta je ta duba ta.
Ko da ta ajiye wayar, ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka ji Shukura ta haihu yaron ya mutu, dan Allah zan biya na duba ta, sai na tafi gidan Ummi."
"A'a"
Ta marairaice ta ce "Dan Allah, kar su ga kamar wulaƙanci ne, an gaya mini abu ban je ba"
Ya kalle ta ransa a haɗe, ya ce "Kar ki je gidan nan" ta tsuke bakinta, kar ta je gidan Ummin ma, ya hana ta zuwa.
Har bakin hanya ya raka ta, sannan ya koma.
Ta yi tunani ta ga yadda ya tsuke fuskar nan, babu lallai ya bari ta je, kuma Hajiya Amina ba ta cancanci haka daga gare ta ba. Duk da ba shiri suke yi da Shukura ba a baya, amma tana matuƙar tausayinta.
Kawai ta yanke shawarar ta je a gurguje, ta duba ta ta wuce gidan Ummi.
Habu ne ya buɗe mata gate, yana ganin ta, ya yi murmushi suka gaisa ya ce "Ina mutumin?"
Ta ce "Yana gida, bai san zan zo ba, wata unguwar na tambaye shi, dan Allah kar ka gaya masa na zo"
"A'a kar ki damu, ba zan gaya masa ba, ina fatan duk ku na lafiya?"
Nana ta ce "Lafiya ƙalau, ba ka zuwar mana kwana biyu"
"Ai na ga babu wata matsala ne, ku na lafiya shi yasa"
"Ko kuma shi ne ya hana ka zuwa, Sayyid kishinsa ya yi yawa"
Ya yi murmushi ya ce "Sayyid kuma?"
Nana ta jinjina kai ta ce "To na rasa da sunan da zan kira shi, amma dan Allah da wani sunan aka ɗaura mana aure da shi ne?"
"Kamar dai yadda na gaya miki ban san komai a kansa ba, kawai cewa na yi a saka Muhammad, amma ban san sunansa ba nima"
Ta jinjina kai ta ce "To da gaske kai ne ka ke ba shi kuɗin da yake kashe mana? Na ga kuɗin aikin gadin ba wani yawa ne da su ba"
Ya ɗan yi dariya ya ce "Ai ainihi ba gadi ne sana'ata ba. Ina safarar dabino ne, da mazarƙwaila da cukui da sassan raƙumi, daga Nijar zuwa Nigeria na rarrabawa 'yan kasuwa. A garin haka ma na tsince shi. Na fara gadi ne saboda na samu na zauna guri ɗaya, a nema masa magani, amma haryanzu ba a dace ba, masu maganin sai su ce abin ya fi karfinsu"
"Amma Malam Habu, me aka ce muku yana damunsa?" Horn ɗin mota su ka ji, ya ce "Bari na buɗe ƙofa"
Ta ce "Shikenan, nima bari na hanzarta"
Ta shiga cikin gidan, Jummai ta din ga murna da ta ga Nana, ta yi mata jagora har ɗakin Hajiya Amina, inda Shukura take jinya.
Sosai Nana ta jajantawa Shukura, tare da ba ta haƙuri, da ƙarfafa mata gwiwa a kan girma da muhimmancin tawakalli ga Musulmi.
Hajiya Amina har so take Nana ta zo, ko tana cikin damuwa, ire-iren wa'azinta, a kan tawakalli da dogaro ga Allah na ƙara mata ƙwarin gwiwa.
Nana ta tambayi ina Haidar, aka ce mata yana gidan kakarsa.
Muryar Alhaji Zailani ta ji ya shigo ɗakin, yana kiran sunan Hajiya Amina.
Gabanta ya faɗi, ƙwaƙwalwarta ta shiga fafutukar tuno mata, da abin da ta gani a mafarki amma ta kasa, duk da zuciyarta na raya mata mummunan abu ne, kuma kamar a zahiri ya faru. Saboda kaucewa zargi, Nana ta yi ta maza ta gaishe shi.
Shi kansa ya yi mamakin ganin Nana, ya daidaita nutsuwar sa, ya amsa mata ya ce "Ashe amarya ce ya mai gidan?"
"Yana nan lafiya ƙalau. Hajiya bari na tafi ina sauri ne, sai na sake dawowa."
Cikin sauri ta ɗauki jakarta ta yi waje, Shukura na ta yi mata godiya.
Ba ta tarar da Habu ba, kawai ta buɗe gate ɗin ta fice. Ganin da ta yi wa Alhaji Zailani, ta din ga jin tamkar ta aikata wani mummunan saɓo ne.
Tana ta sauri, unguwar shiru babu kowa, ta ga an sha gabanta da mota. Ta ja ta tsaya ƙirjinta na dukan uku-uku.
Duk wannan saurin, na ki tsere mini ne? Idan na so kamo mini ke zan saka a yi, na yi duk abin da nake so, kuma babu wanda ya isa ya ce dan me, ko ya tuhume ni. Biyo ki na yi na ƙara tabattar miki da ina nan a kan baka ta, wallahi ba zan rabu da ke ba, sai buƙata ta ta biya."
Cikin dakiya ta ce "Allah ko? A baya ban taɓu ba, sai a yanzu ka ke tunanin zan taɓu? To kar ka fasa, ka ci gaba da bibiyata da mugun nufinka, kar ka fasa" ta zagaye motar ƙasan zuciyarta tana tsananta addu'a ta bar gurin.
Gidan Ummi ta tafi, Ummi ta yi farin cikin ganinta sosai da sosai, su na hira ana gyara Nana. Nana ta bata wasu daga cikin kayan da su Adda Saude suka kawo mata.
Aka wanke mata kai, aka yarfa mata kitso ƙanana, ta yi mata dilka ta zana mata lalle ja da baki, ta turara ta da turarukan wuta.
Nana ta ce "Inyee ko ranar aurena ban samu wannan gatan ba"
"Ai biya za ki yi, ki je gida ki ce ya biya kuɗin gyaran da na yi miki"
"Ba zamu biya ba ɗin" ta yi maganar tana dariya.
Ummi ta bata labarin yadda Saleh, duk ya shiga damuwa da tashin hankali, saboda auren da ta yi, ya tattara ya koma Lagos ma. Daga haka kuma suka koma tattaunawa a kan matsalolin gidan su, yadda Baba ya bar ragamar gida a hannun Mama, gantalin da Jamila take yi, har ta bata labarin dukan da Gaddafi ya yi mata, ga Imarana babu ma wanda yake cigiyarsa. Suka ci gaba da jajanta matsalolin na su, da a yanzu ba su san ma hanyar saita wannan gida na su ba. Gefe ɗan gidan Yaya Atine ya ce yana son Suwaiba, Mama ta ce ba za ta bawa Faƙiri 'yar ta ba.
Sun daɗe su na hira, Nana ta bawa Ummi kayanta da take so a ɗiɗɗinka mata.
Ummi ta duddubo mata wasu kayan kwalliya, da sauran 'yan kayan buƙatu ta rako ta titi, ta samu abin hawa ta tafi gida.
Ana ta kiraye-kirayen sallar magariba Nana ta isa gida, sai dai ba ta tarar da shi ba.
Ta yi salla, kasancewar ta zo da abinci daga gidan Ummi, ya sanya ba ta ɗora girki ba, ta dai kunna gas ta ɗora masa shayi.
Har aka yi sallar isha'i shiru bai shigo ba, sai kuma abin ya fara damunta. Ga shi shi ba waya ba, wayarta ma tana hannunsa, ba waya ta fita.
Tana nan tana kallon hanya, ta ji yana rufe gate. Ajiyar zuciya ta yi, ta jira ya shigo ɗakin.
"Sayyid, duk na damu na ji ka shiru, ina ka tafi ne?"
Ko kallon gurin da take bai yi ba, ya wuce ta ya shiga banɗaki. Sororo ta tsaya tana mamaki.
Ta koma gefe ta jira, ya fito. Ya sake nufar wardrobe. Ta bi bayansa ta na magana. "Sayyid wai meyafaru ne? Ina ta magana ka yi mini shiru"
Ya duba jallabiyar da zai saka ya kwanta. "Sayyid ka yi magana mana"
Ya ajiye jallabiyar, ya kalli Nana a tsanake ya ce "Me yasa na ce kar ki yi abu ki ka yi?"
Gabanta ya faɗi, ce rauni ta ce "Me na yi?"
"Tambayata ki ke yi? Ban ce kar ki je gidan mutumin nan ba? Ban gaya miki ba?" Ya yi maganar cikin ɗaga murya.
Cikin sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ban...
"Kar ki yi mini ƙarya kin je, me yasa ki ka je?"
Ta girgiza kai tana tsuma, saboda yadda ya burkice mata.
Ya Kano hannunta ɗaya ya ɗora a ƙirjinta, ya kama ɗaya ya sanya a ƙirjinsa, ta ji yadda zukatansu ke bugawa a tare.
""Haryanzu ki na tunanin ƙarya nake yi, da nace miki akwai ruhina a jikinki?"
Ya saki hannayenta, ya kuma tsare ta da ido, ya ce "Me yasa ki ka je bayan na ce kar ki je?"
Nana ta yi shiru ta ƙi magana.
"Magana nake yi miki" ya ƙara maganar yana ɗaga mata murya.
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga gaba ɗaya ya canza, fuskar sa kamar bai taɓa dariya ba, jikinsa yana tsuma.
Tsorata ta yi, ta ƙara ja da baya, kawai ta ji ya riƙe wuyanta.
Ayshercool
08081012143
Idanun Nana suka yo waje, ta ji numfashinta ya yi sama, ta saka hannu ta rirriƙe nasa tana kakari.
Da ƙyar ta kalli fuskarsa, gaba ɗaya ta canza naman fuskarsa sai rawa yake yi. Tsohon nan ta ga ya bayyana a gefensa, riƙe da sandarsa yana kallon ta yana dariya.
Jikinta ne ya saki a hankali, ta sauke hannunta. Ya yi jifa da ita kan katifa ya yi baya, yana jin tamkar ana jan kansa.
Tana durƙushe tana wani irin tari, haɗi da kakari, tana ta yinƙurin amai, amma babu abin da yake fita daga bakinta sai wani irin yawu mai yauƙi. Ta ja jikinta da ƙyar ta jingina, ta lumshe idanunta ta buɗe a hankali. Ta ga Ƙaisar ya zura mata ido.
Ya gyara zamansa ya ce "Yanzu da ki ka fara ɗanɗana kuɗarki, wataƙila za ki yarda da abin da nake gaya miki. Laifi na biyu kenan da ya aikata mini, zan kuma taɓa shi a inda ba ya zato".
A wahale Nana ta ce "A'a Ƙaisar, koma dai mene ne, ni ya yi wa dan Allah ka rabu da shi, wannan tsohon na gani a tare da shi, kuma idan ka ce za ka yi masa wani abu, kai ma wannan tsohon wahalar da kai yake yi."
"Ba ke za ki gaya mini abin da zan yi, ki rufe mini baki. Kuma kuskure mafi girma da ki ka aikata, bayan ƙin amincewa da buƙata ta, shi ne ɗaukar cikin da ki ka yi, ba zan taɓa lamunta a samu zuriya ta tsatsonki ba, na ci gaba da ƙuntata rayuwata ina wahalar banza a kan mutane marasa alaƙawri kamar ku ba"
Nana ta kalli cikinta ta kalle shi ta ce "Ciki kuma?"
"Ƙwarai, ga ɗan tayi nan a cikin ki, tun a ranar farko da ku ka kasance tare. Kin ɗauki abin da ke kan ki ba ki da tabbacin wane jinsi ne"
"Mutum ne, Sayyid bil'adama ne, da aljani ne ba zai iya tarayya da ni a zahiri ba, sai dai a cikin bacci, ko ta hanyar amfani da gangar jikin ɗan Adam "
"Ko?"
"Eh" ta ba shi amsa.
"Yaro yaro ne. Kin tabattar bil adama ne, daga ina? Daga wace nahiyar? Wane shiri ki ke da shi, a kan sanin waye shi da inda ya fito? Har ki ka sakankance ki ka amince da ɗaukar ciki?"
Ƙoƙarin juyawa Nana ta yi a kan katifar, amma ta ji jikinta a ɗaɗɗaure kamar an yi mata duka. Ga wani irin azabar sanyi da yake ratsata ko ta ina, tamkar an ajiye ta a cikin ƙanƙara. A cikin kunnuwanta kuma take jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da kuma sauri. Ga wani irin nauyi da kanta ya yi mata tamkar an ɗora mata. Ga azababben ciwo da yake yi mata, tamkar zai rabe.
Ta juya da ƙyar tana numfarfashi, tana son lalubar abin da za ta rufa, wani irin huci ne ya daki fatarta, ta buɗe idanunta da ƙyar, ta kalli gefenta.
Yana kwance jiginsa na ta jijjiga, yana numfarfashi.
Ta din ga jan jikinta a hankali, ta matsa ta hau kan ƙirjinsa ta kwanta, ba tare da fargabar zai sake yinƙurin cutar da ita ba.
A hankali ta ji zafin jikinsa, ya fara ratsa ta, ta fara rage jin sanyin da take ji, wani wahalallen baccin ya sake yin awon gaba da ita.
"Asmy" ta ji ya kira ta da wani sunan kuma. Ta buɗe idonta da ƙyar ta kalle shi.
Garau da shi kamar babu abin da ya faru.
"Salla" ya faɗa a taƙaice, jikinsa duk danshin ruwan alwala, ya fice ya tafi masallaci.
Da ƙyar ta tashi, tana daddaga bango, ta shiga ta yi alwala, ta dawo ta yi salla a zaune, ta kwanta.
Ganin ba ta tashi da wuri ba, ya sanya shi fara rage aikace-aikacen ɗakin, amma ya ga babu alamar za ta tashi balle ta ɗora girki. Ya matsa kusa da ita ya tashe ta. Ta tashi zaune da ƙyar, kanta kamar ana buga mata guduma.
Ya ƙura mata ido ya ga duk ta canza, sai dai ta yi masa kyau a ido sosai, ƙanan kitson kanta, sun dace ba ƙin gashinta, ga hannunta lalle ja da baƙi ya yi mata kyau sosai da sosai.
Ta saukko daga kan katifar, ta ɗauki wata roba, ta ɗaukko lemon tsami ta yanka, ta fara matsawa a bakinta. A hankali tashin zuciyar da take ji, ya fara raguwa. Shi dai ya zuba mata ido.
Ta gama