BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   56 / 64

165K to 168K   out of 190K words

abun da yake yi mata daɗi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta.
Dan tashin farko Alƙali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi.
Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu maƙudan kuɗin, da ake zarginsa da sama da faɗi da su, a lokacin da yake shugabanci.
Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa.
Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuɗinsu.

*****
Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ƙwarangwal ɗin sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi.
Ɗakin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya ɗaukko ƙwarangwal ɗin jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka ɗauki ƙwarangwal ɗin jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaɗe su a jikin ƙwarangwal ɗin aka saka a cikin wutar nan.
Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu.
Sai da ƙwarangwal ɗin nan ya yi baƙi ƙirin, zaren da aka naɗe ƙwarangwal ɗin, ya kama jikin sosai. Ya kuma naɗe shi da wani zaren, sannan ya naɗe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki.

Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin ɗaki, ya din ga ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace.

Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuɗi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar"

Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karɓi ƙaddara.

Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karɓi ƙaddarata. Na kuma gode wa Allah. Abu ɗaya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni"

Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi haƙuri"

Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah"

Ji ya yi tamkar ana ƙoƙarin fizgo ƙwaƙwalwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya riƙe kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?"

Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faɗi a gurin.

Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da Ƙaisar yake nuna mata.

Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin.

"Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bamban da wannan ta wasu fannukan"

Nana ta zabura ta kalle shi ta miƙe tsaye ta ce "Ƙaisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?"

Ya ɗago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaɗin ne?"

Ta yinƙura za ta yi magana, ta yi ido huɗu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido.

Ta yi ajiyar zuciya.

"Waye Ƙaisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani.

Ayshercool
08081012143


CHAPTER 46.

Hantar cikinta ce ta kaɗa, ta kalli cikin ƙwayar idonsa, jin yadda ya jefo mata tambayar, babu tsammani ba tare da ta shirya hakan ba.
Wani irin gumin tsoro da fargaba, ya fara tsatstsafo mata, saboda ba ta san ta ina yakamata ta fara yi masa bayani ba, ba ta san ma me za ta ce masa, da zai gamsar da shi, amsar da za ta ba shi ba. Sai dai a ina ya san Ƙaisar, har yake tambayarta waye shi? Ta tambayi kanta.
Ga mamakinta, sai ta ga ya tashi ya yi miƙa, ya fice daga ɗakin ba tare da jiran amsar da za ta ba shi ba, ko kuma bayanin da za ta yi masa ba.
Ta tashi ta kimtsa jikinta, babu jimawa sai ga Habu ya zo, Sayyid ne ya fara ɗaga labule, ya ganta a kintse a cikin hijjabi, sannan ya ba wa Habu damar shiga.
Sama-sama suka gaisa da Habu, ita ƙasan zuciyarta tana tsoron kishin Sayyid, shi ma Habun haka.

Ya ajiye wani galan a gaban Sayyid, ya ce "Saƙonka nan, an kawo shi ɗazu fresh ne"
Sayyid ya ce "Na Husnah ne" Nana ta saci kallonsa, ko za ta ga ya canza mata, saboda tambayar da ya yi mata, kuma bai jira ta amsa masa ba, amma ta ganshi normal.
Ta ɗan yi murmushi ta ce "Me na samu?"
Habu ya ce "Nonon Raƙumi ne da ake kawo miki, ga kuma dabino da zuma, fresh masu kyau da aka kawo daga Nijar"
Nana ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai da sosai. Habu wai kai ka ke ba shi kuɗi? Na ga kuɗi masu yawa a kayansa, ya ce kai ne ka ba shi"
Habu ya yi murmushi ya ce "Ba ki yadda da abin da ya faɗa ba ne? Ai mutum mai iyali dole sai da kuɗi, kuma na gaya miki mu na harkar kawo dabino, zuma, cukui kayan shayi, asuwaki mazarƙwaila daga can Sahara.
Nana ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta ce "To ya batun binciken da ka ke yi, a kan danginsa, ya ce mini ka na bincike a kai."
Ya ɗaga kai, suka yi ido huɗu da Sayyid sannan ya ce "Ina nan ina yi, kuma in sha Allah duk bayanin da na samo zan sanar da ke"
Nana ta ce "Ma sha Allah, kuma Habu duk 'yan garinku Buzaye, su na jin Hausa? Idan ba sa ji da yaya za mu yi magana idan an gano su?"
Habu ya yi murmushi ya ce "Mu ba ga shi mu na ji ba? Hausa na cikin manyan yaruka a Nijar, da kusan kowa yana jin yaren. Dan haka kar ki damu, tun da yana jin Hausa, danginsa ma na san su na ji"
"To Allah ya sa su karɓe ni, idan an gano su. Ina Sule kwana biyu?"
"Ya je gida, ai shi ya taho da wannan kayan ma"
A wannan karon Sayyid bai kula su ba, kuma bai sanya musu baki a hirar ta su ba, har suka yi suka gama. Ta tashi ta tattaro masa kayan wankin Sayyid ta ba shi, ya yi musu sallama. Bayan ya tafi, Sayyid ya ɗauki kayan shayinsa ya koma bakin gate. Nana ma ganin babu abin da za ta yi, kawai sai ta bi shi.
Ta samu guri ta zauna a gefensa, ta ɗan zuba masa ido, amma bai kula ta ba, ya mayar da hankali a kan shan shayinsa.
"Sayyid" ya ɗago ya kalle ta.
"In tambaye ka?"
Ya jinjina kai alamar eh.
A ɗan sanyaye ta ce "Yau na yi magana da Habu, na ga ba ka yi fushi ba"
Kawai ya yi murmushi ya ce "Kina so na yi ne?"
Ta ce "A'a, dama bai kamata ka din ga yi ba, tun da sukaɗai mu ke gani a matsayin danginka. Su Habu 'yan Aljanna ne, ina yabawa ɗawainiyar da suke yi da mu, mussaman shi, alhalin ba ku da alaƙa"
"Ke ma 'yar aljanna ce, in sha Allah "
"Kai ma haka" ta faɗa tana murmushi.
Sai kuma fuskarta ta bayyanar da damuwa, ta ce "Sayyid, ciwon nan naka yana bani mamaki, ka san komai na rayuwa na yau da kullum amma sanin waye kai kawai ka manta. Dan Allah idan ban takura maka ba, ka gaya mini abin da za ka iya tunawa, bayan da ka buɗe ido ka ganka a wannan yanayin "
Ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya kalle ta ya ce  "Kawai na ji abu ya sarƙe mini numfashi,  tari ya kama ni, ƙura tana shigar mini hancina da bakina. Na yi ƙoƙarin buɗe idona, amma abu ya gagara, saboda wata irin ƙura da na gani ta turnuƙe gurin,, da wani irin sauti da tashin ƙurar yake bayarwa. Ba na iya gane komai. Na takure jikina na lokacin da ban san adadinsa ba, daga bisani na ji shiru. Na sake buɗe idona a hankali, sai na ga ƙurar ta lafa, na ganni a cikin sahara, da wani tsoho mai matuƙar tsufa, hannunsa riƙe da sanda, gemunsa fari tas har cikinsa, ga wasu irin kaya da suka yi mugun tsufa a jikinsa.
Nan na fara tunanin waye ni, ya kuma aka yi na ganni a wannan gurin, amma na kasa tuna komai.
Na yi ƙoƙarin tuna sunana, da inda na fito, amma ban ji ko kusa da tunawa na yi ba.
Na kalli tsohon nan, da niyyar na tambaye shi, amma na kasa magana, na yi, nayi amma na kasa ce masa komai, shi kuma bai daina kallona ba.
Wata irin ƙishirwa ta kama ni, ga yunwa ina ji, amma na kasa magana. Can na hango wani mutum ya nufo ni a kan raƙumi, ya saukko daga kan raƙumin ya nufo ni da sauri. Yana ta yi mini magana, amma ba na gane abin da yake faɗa. Ya ɗago ni ya bani ruwa na sha.
Sai na fuskanci kamar ba ya ganin tsohon nan, nikaɗai nake ganinsa. Ban san meyafaru ba. Na buɗe ido na ganni a wani guri, ya ce mini Nigeria ce, tun  daga nan yake ta ɗawainiya da ni" Duk wannan bayanin da yake yi wa Nana, daki-daki yake yin sa, yana yi yana hutawa, kuma a nutse babu gaggawa.
Ta jinjina kai ta ce "Kenan mai ka na ganin, wannan tsohon kenan?"
"Ki na ganinsa ne ke ma?"

Ta jinjina masa kai, sannan ta ce "Me yasa ka tambaye ni waye Ƙaisar?"

Ya yi murmushi tare da sunkuyar da kansa, ya kalle ta ya ce "Tambayoyinki sun yi yawa Rayuwata"

"Dan Allah ka bani amsa Sayyid, wasu lokutan ina shiga ruɗu a kan abubuwan da suke gudana, ba na ganewa sosai, sai na ga kamar taɓin hankali ne da ni"

"A'a lafiyarki ƙalau, ni ne mai matsala, ni nake da taɓin hankali na sani"

"A'a lafiyarka ƙalau"

Ya ɗan kurɓi shayin hannunsa ya  ce "Ai na san gaskiya, ana kuma faɗa ina ji, ba ni lafiyar ƙwaƙwalwa ina da taɓin hankali"

Ta gyara zamanta, ta ce "To wai gurin masu magani da ku ka je, babu inda aka yi nasara, ko alamun nasara?"

"Eh" ya amsa a taƙaice.

"Amm Sayyid"

"Kaiii na gaji, dan Allah ki daina tambayar nan, ba kya gajjya ne?"

Ta yi murmushi ta ce "Idan zan kwana ina magana, in dai da kai ne, ba zan taɓa gajiya ba. Sannan ka yi haƙuri abin da na yi maka dan Allah, na zubar da abin da ka shiga da shi ɗakinmu, raina ya ɓaci ne, kuma na ga ban kyauta ba"

"Kuma ke ta ce na kaiwa, shi yasa na karɓa"

Ta ce "Makirci ne kawai na mace, amma  na ga alamar ta girgiza da ganinka, kamar ta fara son ka ne ma"
Ya yi shiru bai ce komai ba. "Ba zaka kula ni ba?"
"Me zan ce?"
"To kar ka kulanin, kuma wallahi naga abin da raina zai sosu, sai ka neme ni ka rasa"
Kawai ya sunkuyar da kai yana murmushi.
"Dariya ma na baka ko? Amma idan ni ce sai ka wani haɗe rai, ka yi ta yi mini faɗa"
"Ki yi shiru, ki huta"
"Na ƙi yin shirun, wallahi idan sonka take yi, sai kun ga abin da ba ku zata ba"
Ya ce "Ai na ma gani"

Siyama ce ta nufo su, Sayyid ya yi hanzarin mahar da takunkumin fuskar ya rufe fuskar sa.
Ba ta kula Sayyid ba ta ce "Nana, yau girki nake son yi, ki zo mu je mu yi"
Nana ta yi murmushi ta ce "Ma sha Allah, bari na zo" ta yinƙura ta tashi, Sayyid ya bi ta da kallo. Suka shige cikin gidan tare da Siyama.

Siyama na matuƙar jin daɗin hira da Nana, gani take kamar ta samu sauƙi, tun da Nana tana jin irin abin da take ji. Kuma tattaunawar da suke yi.

"Kamar haka da nake yi wa Sagir girki, na zo ba na iya yi, saboda zuciyata raya mini take, na cakawa kaina wuƙa, ko na ƙona kaina da ruwan zafi"

Nana ta ce "Subhnallah. Yaushe wai ki ka fara ciwon nan ne?"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Lokacin da su Mami, suka tare a gidan nan, na zo ganin gida, lokacin na dawo daga umara. Kawai daga tafiyata gida, na din ga jin tsoro cikin dare. Dama da ciwon kai na tafi gida. Ina bacci sai na ji ana shafa ni da daddare. Sosai fa nake jin ana taɓa ni, idan na faɗa ba a yadda. Lokacin mijina yana neman aure. Aka ce kishi ne ya sa  dan Allah ba zan yi kishin mijina ba ina son sa Nana?"

Nana ta ce "A'a dole ki yi kishi mana, tunda ki na son sa"

"To daga ƙarshe, mamansa ta ce sai ya rabu da ni, wannan kishin idan ban kashe kaina ba, zan kashe shi ko matarsa. Aikuwa ya sake ni"

Nana ta numfasa ta ce "Ki yi haƙuri ki ci gaba da addu'a, idan ki  na da rabo sai ki ga kin koma"

"Anya kuwa Nana? Mami ta ce babu ni babu shi, ba shi da mutunci da shi da iyayensa da 'yan uwansa"

"Kar ki damu fa, idan da rabo sai ki koma, amma a yanzu dai, ki fauwwala wa Allah komai" Ta jinjina kai ta ce "Haka nex

Muryar Hajiya Halima suka ji, tana ƙwala wa Yusra kira. Yusra ta amsa da "Na'am, gani nan"

"Me ki ke yi a kitchen ne?" Ta yi maganar tana shigowa kitchen ɗin.

"Girki mu ke yi, ni da Nana"

Nana ta ce "Hajiya ina wuni?"

"Lafiya ƙalau Nana, lallai taku ta zo ɗaya da Yusra, na ga tana ɗan sakin jiki ta yi walwala da ke, dan Allah ki kula saboda kar ta yi wani abin da zai cutar da ita, ba ta da cikakkiyar lafiya. Ni fita zan yi"

Nana ta ce "Tom, a dawo lafiya"

Ta amsa da Allah ya sa, ta bar kitchen ɗin.

Suka girka faten dankali da kifi, yanayin yadda Yusra ke girki, ya tabattarwa Nana, yana daga cikin abubuwan da take son yi. Su ka yi lemon mangwaro, suka saka a fridge ya yi sanyi.
Bayan sun kammala, ta kalli Nana ta ce "Ki zuba kai kai wa mijinki, kar ya huce"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a mu ci kawai, zai iya gwale ni ya ƙi ci"

Yusra ta ce "A'a, zai ci. Duk abin da ki ka ci, ki din ga ba shi, za ki ga ya ƙara son ki sosai da sosai. Da haka muke yi ni da Sagir" cikin tausayawa Nana take kallonta, alamu, sun nuna har da zafin rabuwa da mijinta ya sanya larurata yin gaba. Saboda aljani ya fi samun damar shafar mutum, a lokutan fushi, damuwa, ko kuma najasa.

Haka ta takura wa Nana, ta zuba abincin a flask, ta fita. Yana zaune yana facing hanyar shiga gidan, ta tsaya cak tana kallonsa, hakan ya sanya shi tasowa ya nufo ta.

Ya ƙaraso, ta nuna masa guri ta ce ya zauna, ya zauna ya dube ta ya ce "Kin bar ni, nikaɗai"

Ta buɗe faten dankalin, ta ce "Abinci zan baka"

Ya kalli harabar gidan ya ce "A nan?"

"Eh mana, ba kowa ai. Bai kamata a ce kullum daga ɗaki sai bakin gate ba, canza abubuwa yana sanya nishaɗi a zukata"

Ta sauke masa rawaninsa, ta ɗebo dankalin a cokali, ta kai bakinsa. Ya buɗe ta saka masa.

Bayan ya haɗiye ya ce "Ba ke ki ka yi ba"

"Ni na yi "

"Ba ke ba ce. Babu yaji, babu tafarnuwa, bai ji maggi sosai da sosai ba"

Ta kwashe da dariya, ta ce "Sayyid ko numfashi na yi, sai ka gane, ka haddace komai nawa. To na ji amma tare muka yi ai" ya ci gaba da buɗe bakinsa, yana karɓar Abincin. Tana yi tana cire masa ƙayar kifin da ba ta fita ba.
Ya gama ta ba shi lemon ya shanye, ya ce "Na gode sosai"

Ta kalle shi ta ɓata fuska, ta ce "Ba ka ce ba"

Fuskarsa ɗauke da murmushi, ya kamo fuskarta, ya sumbaci goshinta ya ce "Allah ya yi wa rayuwata albarka"

"Wannan ai wayo ne, amma shikenan na gode" gani ta yi ya tsaya cak, yana kallon guri ɗaya. Ta waiwaya sai ta ga Siyama ce a bayanta, hannunta riƙe da wayarta ta kara ta a kunnenta. Wani abu ya soki zuciyar Nana,ganin kallon da take yi masa. Bai yi magana ba, ya nufi gurin da yake zaune da farko.
Nana ma ba ta kalli Siyama ba, ta wuce ta, ta shige. Hira ta je suka ci gaba da yi da Yusra. Sai dai duk wata hirar ta Yusra shirme ce, amma ta fitowa da Nana abubuwa da dama, da suke damunta.
Sai dai galibin hirar ta ta,na zamanta da mijinta ne, da irin son da take yi masa. Sai da ta ji tamkar ta ce wa Hajiya Halima, su haɗa wa Yusra maganin da na gargajiya bisa doron addini. Amma yanayin yadda take ganin gidan, sun ginu a kan doron aƙidar boko, babu lallai su amince da hakan.

Sai da ana daf da fara kiraye-kirayen sallar magariba, sannan Nana ta fito.

Har ta wuce lungun da shuke-shuke suke, ta koma da baya ta leƙa, ta ganshi a gaban famfo, yana alwala. Ta cire takalmanta, cikin sanɗa ta nufe shi, tana zuwa daf da shi ta faɗa bayansa, ta maƙale wuyansa.

"Ya aka yi ne?"

"Wai ba ka ji tsoro ba?"

Ya yi dariya, ya ce "Tun lokacin da ki ka fito daga cikin gidan, nake jin kina kusanto ni a jikina"

"Ka daina tsorata ni, da wannan maganganun na ka"

"Ɗaga ni, alwalata za ta karye"

Ta noƙe kafaɗa ta ce "A'a"

"Dan Allah"
Ta sake cewa "A'a" ya saka hannunsa ya jawo ta daga bayansa, ya tara hannunsa a famfon, ya taro ruwa ya watsa mata a fuska. Ba shiri ta miƙe tana ajiyar zuciya. Ba ta farga ba ya ɗauki tiyon da yake bawa flours ruwa, ya fesa mata a jikinta.
Tamkar ta fashe da kuka ta ce "Kuma idan na rama ka hau karkarwa ba ka son sanyi ko?" Wani irin nishaɗi ne yake ratsa zuciyarsa, a wannan

56 / 64