Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
masa, da hoton zuciyarsa sannan ya kalle su ya ce "Maganar gaskiya Hajiya, zuciyar mijin ki akwai matsala. Yana fama da Av block stage 2"
"Ni dan Allah ba sai ka yi mini bayani ba, dan Allah ya za mu yi. Mun sha wahala kafin mu ganka Doctor "
Ya ce "Ki yi haƙuri, zan ɗora shi a kan magunguna, zamu din ga yi mu na monitoring zuciyarsa. Zan rubuta muku allurar da za a yi masa, saboda a kiyaye zuciyarsa daga shiga stage 3. Idan ya tafi stage 3 to 4, to sai dai a yi masa aiki, a saka na'urar da za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa."
Sayyid dai ya yi shiru, ya sunkuyar da kansa.
Cikin rawar murya Nana ta ce "Doctor,ni yanzu duk ba na gane wannan bayanin naka, meye abin yi? Me za a yi masa yanzu?"
"Zamu yi masa allura ne, amma sai under ECG machine, to kuma gaskiya a Asibitin nan, zaku iya kaiwa wata biyu ba a yi masa ba."
Cikin matsanancin tashin hankali, Nana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Dan Allah babu yadda za a yi, a taimaka mana, yana shan wahala wallahi. Wasu lokutan ba ya iya bacci, saboda numfashinsa."
Likitan ya ɗan kalli Nana sannan ya ce "Idan da kuɗi a gurinku, sai na kwatanta muku, wani Asibiti, da za ku je a yi muku"
Cikin azarɓaɓi ta ce "Likita ina ne?"
"Can wani Asibiti ne a by pass, za a yi masa allurar tsawon watanni ukku, duk wata za a din ga yi masa allurar, bayan an yi zai yi kwanaki uku a Asibitin, kafin ya tafi gida. Naira dubu ɗari biyu da hamsin ce, duk yi ɗaya".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Nana ta furta a hankali jikinta a matuƙar sanyaye.
Sayyid ya kamo hannunta, ta kalle shi murya ƙasa-ƙasa ya ce "Mu tafi gida"
"A'a Sayyid, ba shi ne mafita ba" ta mayar da hankalinta kan likitan ta ce "Dan babu wani abin yin sai wannan?"
"Gaskiya wannan ne kawai abin yi, sai dai idan ba ku da hali, ku bi layin na nan Asibitin, shi kuma dubu ɗari da Ashirin ne. Kuma idan aka bari ba a yi ba, ya ci gaba sai dai a yi masa aiki, a saka masa na'ura naira Million huɗi, kuma shi ma aikin sai a Lagos ake yin sa.
Yanzu zan rubuta muku magunguna, wanda zai din ga amfani da su, zuwa lokacin da ku ka yanke shawarar abin da za a yi.
Nana ji take kamar ta ɗora hannu a ka, ta rusa ihu, saboda kaf abubuwan da likitan ya lissafa babu ɗaya da take tunanin zai yiwu. Ya rubuta musu magunguna, suka tafi gida.
Da wuri suka koma gida, sai dai tun da suka koma, babu wanda ya iya yi wa wani magana, tamkar kurame, haka suke zaune a ɗakin.
Ta lallaɓa shi da ƙyar ya ɗan ci Abinci, ya koma gefe ya zauna ya yi shiru, babu tsammani Nana ta ga Siyama ta ɗage musu labule. Nana ta kalle ta, shi kuma ko motsi bai yi ba, balle ya buɗe idonsa.
"Mami na neman ki" ta yi maganar tana satar kallon Sayyid, da yake zaune babu rawani"
"Ina zuwa" Nana ta faɗa a hankali.
"Shugaba, bari na je kiran da ake yi mini na dawo"ya jinjina mata kai ta tashi ta fita.
Bayan mintuna kusan talatin, ta dawo ɗakin, ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da harkokinta.
Sai da aka yi sallar la'asar, sannan ta dube shi cikin tausasa murya ta ce "Dan Allah Sayyid ka bari na je na sanar da Habu halin da ake ciki. Mu na buƙatar sa da gaggawa, abubuwan sun yi mana yawa mussaman yanzu da... "Ta kore mu ko?" Ya tari numfashin Nana.
Ras! Gabanta ya faɗi. Ta buɗe baki za ta yi magana, amma ta kasa, sai ma hawayen da take ta maƙalewa, da suka samu damar zirarowa tamkar an kwance famfo.
Ayshercool
08081012143
49
Ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi da raɗaɗi.
Tun da Siyama ta zo ta kira ta, zuciyarta take dukan uku-uku, har ta shiga falon, ta samu Hajiya Halima. Ta durƙusa ta gaishe ta, ta amsa mata sama, sannan ta dube ta ta ce "Amm dama, na kira ki ne, a kan tun da mijinki babu lafiya. Kin ga ba zai yiwu yana kwance babu lafiya, ku ku na yawon Asibiti, a din ga bar mini gida haka ba. Na zata abin na ƙare ne, to ban ga alamar zai samu lafiya nan kusa ya ci gaba da aikin ba. Saboda haka nake mai baki haƙuri, ga haƙƙinsa na wannan watan, dubu saba'in na ƙara muku dubu talatin, na sallame ku. Ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya sanya kaffara ne. Na saka an nemo mini wani mai gadin ma, jibi in sha Allah zai zo ya fara aiki, sai ku kwashe kayan ku. Duk ba wani daɗewa za mu ci gaba da yi a gidan ba, mu ma zamu koma can inda mijina yake a Abuja. Mijin Hajiya Amina, da ta haɗa ni da ku ya sai gidan nan, mu ma Abuja zamu koma"
Duk yadda ƙirjin Nana ya buga da ƙarfi, amma ta yi iya ƙoƙarinta, tattara nutsuwarta da nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un a zuciyarta.
A zahiri kuma, ta sanya hannu biyu, ta karɓi kuɗin daga hannun Hajiya Halima, tare da sakin murmushi mai ɗauke da ma'anonin da zuciya ce kawai za ta iya shaida su. Ta ce "Mun gode sosai da sosai da wannan damar da aka bamu Hajiya. Ina fatan a zamanmu da ku tsawon watanni biyar zuwa shidda, ba mu yi wani abu da zai ɓata muku rai ba. Idan ma mun yi mu na neman afuwarku a yafe mana dan Allah. Idan kun je Abuja dan Allah a gaida ƙawata, a ce ina yi mata fatan alkhairi sosai da sosai."
Hajiya Halima ta ce "Ba komai, Allah ya ba shi lafiya" Nana ta miƙe jiki a sanyaye ta fita.
Nana na fita Hajiya Halima ta murza goshinta ta ce "Kai, na yi abu zai dame ni, yarinyar nan ta bani tausayi sosai da sosai. Ban so na sallame su yanzu ba, yanayin idon mijin da yadda na tarar da shi a kwance da muka dawo, ya tabattar mini da yana jin jiki. Ni ban san dalilin da ya sanya Alhaji Zailani ɗaukar wannan matakin ba, kuma ya ce kar na kuskura na gaya wa Hajiya Amina"
Siyama ta kwaɓe baki, ba ta ji ta damu da korar su ba, saboda ta tsani Nana, amma tana jin kewar daina ganinsa da za ta yi.
Sayyid ya ƙura mata ido, yadda take ta rusa kuka, ya saka hannu ya share mata hawayenta, ya ce "Ki daina kuka, ki je ki nemo Habu, da zan iya da kaina zan je. Amma da na fara tafiya nake jin haki" Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta, ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta.
Ta fito ta mayar da hijjabinta, ta ce "Bari na je, ko ka na da buƙatar wani abu, kafin na fita?"
Ya girgiza kai ya ce "Sai dai ki kula da kan ki, ki dawo mini lafiya Rayuwata" wasu hawayen ne su ka cika mata ido, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "In sha Allah shugaba" ta fice daga ɗakin cikin matsananciyar damuwa.
Haka kurum ta din ga jin gabanta yana faɗuwa, jikinta a matuƙar sanyaye, amma ta danganta hakan, da halin da suke ciki.
Sai dai duk da yamma ce, layin gidan Alhaji Zailani shiru, ba ta hango dandazon buzayen a zaune, su na shan shayi ba. Kamar yadda suka saba. Da ƙyar take jan kafarta, ta ƙarasa cikin layin. Ta je ƙofar gidan Alhaji Zailani ta fara bubbugawa.
Sai da ta buga sau uku, sannan wani matashin dattijo ya buɗe. Nana ta ɗan yi turus sannan ta ce "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau yaya aka yi?"
"Amm dama, gurin Habu na zo, ko Sule masu gadi a gidan nan"
Ya ɗan ware ido sannan ya ce "Buzaye ko? Ai yau kwanaki huɗu da suka wuce, aka zo da wata doguwar mota, duk aka kame Buzayen layin nan kaf, aka tafi da su, babu wanda ya san inda aka kai su"
Cikin matasanancin mamaki, Nana ta ce "Baba su waye suka tafi da su? Laifin me suka yi?"
Ya ce "Allah masani 'ya ta. Doguwar mota ce dai baƙa ƙirin, ke motocin uku ne ma, biyu a farkon layi, duk su ka kame su, ɗaya motar dai rubutun fransanci ne a jiki, babu wanda suka yi wa bayani, suka tafi da su".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta maimaita cikin matsanancin tashin hankali ta ce "To dan Allah Hajiya Amina tana nan?"
"A'a, sun tafi Umara, tun washegarin faruwar abin"
Nana ta sake cewa "To dan Allah bawan Allah, babu wani wanda zan samu wani bayani daga bakinsa a layin nan" Gaskiya ban sani ba, sai dai ki zagaya ki tambaya. Ya koma cikin gida ya rufe gate ɗin.
Nana ta ji ƙafafuwanta na wata irin rawa, har suna neman gaza ɗaukar ta. Da ƙyar ta din ga ɗaga su, tana tafiya ba tare da ta san inda ta dosa ba.
Ta yi shiru tana tuna maganganun Hajiya Halima, da ta ce mijin Hajiya Amina ne ya sai gidan da suke ciki. Wato yana sane ya yi abin da ya yi kenan. Ta koma tunanin suwaye suka ɗauke buzayen layin gaba ɗaya, lokaci ɗaya ko dai wata ɓarnar suke aikatawa, akwai abin da suke ɓoye mata? Tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi.
Har ta je titi, ba ta tsaya da tafiya ba, ba kuma ta daina tunani ba. Idonta ya sauka a kan mai sayar da gurji da ƙuli-ƙuli. Kawai ta ji ranta ya biya, duk da damuwar da take ciki. Ta miƙa masa ɗari biyu ya bata, ta samu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai ta. Tun a napep ɗin, ta cinye gurjin tas.
Tana zuwa gida aka fara kiraye-kirayen sallar magariba. Ta shiga gidan jikinta duk a sanyaye, sai dai da ta duba ɗakinsu, ba ta tarar da shi ba. Gabanta ya sake faɗuwa, ta fara tunanin ko an zo shi ma an tafi da shi, ba ta sani ba.
Ba ta gama yanke hukunci ba, ta ji cikinta na hautsunawa, ta faɗa banɗaki da gudu, ta din ga sheƙa amai. Sai da ta amayar da gurjin da ta ci kaf. Tun tana yinƙuri, abu na fitowa har komai ya daina fitowa.
Da ƙyar ya tsaya, ta wanke gurin, ta duba kantar abin sabulu na banɗakin, ta ɗaukko abin gwajin ciki, ta yi fitsari ta tsoma a ciki. Layi biyu ya fito raɗa-raɗa. Jikinta ya hau rawa, wani irin kuka ya kufce mata.
Wani aman ne ya sake taso mata, ta din ga yinƙuri, amma babu abin da ya yi saura a cikin nata, sai kakari da yawu mai yauƙi da yake fita daga bakinta.
Ji ta yi ya dafa ta, ya kunna famfon banɗakin, ya din ga taro ruwan a hannunsa, yana kai wa bakinta, tana kuskurewa.ya zuba ruwa ya wanke gurin. Ya kalli tsinken gwajin da ta yi, ya kama ta,ta tashi tsaye, jiri na kwasarta, fararen idanunta sun rine zuwa launin ja. Ya taimaka mata ta yi alawala.
Suka fito daga banɗakin, sai a zaune ta yi salla, saboda yadda iya aman da ta yi ta wahala. Duk sauran cikin da suka din ga zubewa ba ta amai, amma wannan ta ji abin babu sauƙi.
Bayan ta idar da sallar, ya kalle ta ya ce "Ina Habun?" Ta yi shiru tana kallonsa cikin tausayawa, ta ma rasa ta ina za ta faro masa bayanin.
"Yi magana"
Ta ɗan motsa bakinta, sai kuma ta yi shiru. Ya ƙara tsare ta da ido. Ta ɗan ja numfashi ta ce "Na je, wai kwana huɗu da suka wuce, an je da wata mota layin, duk an tafi da Buzayen layin, har da su babu wanda ya san inda aka kai su" sak ya yi yana bin ta da ido, tamkar bai gane me take nufi ba. Ta yi shiru tana tsoron kar abin da ta faɗa, ya ta'azzara ciwonsa.
"Ba sa nan kenan? Babu wanda ya san ina suka tafi?"
"Eh abin da aka ce mini kenan, kuma da alama kama su aka yi"
"Hsbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta tare da sunkuyar da kansa ya yi shiru.
"Dan Allah Sayyid ka kwantar da hankalinka, ka ga baka da lafiya, ina son ka warke. In sha Allah, Allah yana tare da mu. Dan Allah kar ka ɗaga hankalinka. Sonake na nutsu na ga yadda zan yi na haɗa kuɗin da za a yi maka allurar nan, ko guda ɗaya ce"
Ya kalle ta cikin damuwa ya ce "A'a dan Allah kar ki damu, kar ki takura wa kan ki. Iya ɗawainiyar da na saka ki ma, ta isa. Mutuwa ce dai na sani, Allah ya sa na cika da imani, kuma ki yi mini addu'a, t... Bai rufe bakinsa ba, ta dunƙule hannunta ta dake shi a ƙirjinsa da ƙarfinta cikin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.
"Ba ka tausayina, na san dole kowa zai mutu, amma me yasa kalaman ka ba za su zama na ƙarfafa gwiwa a gare ni ba, sai dai ka kashe mini zuciya da sanya mini tsoro da razani. Ga ɗanka a cikina, ga ka babu lafiya, nan a kore mu, ga shi 'yan uwanka ba a gan su ba, kuma ka saka ni a gaba, kana gaya mini wannan maganganun. Har ka manta ka ce kowannenmu ruhin ɗayanmu ne a jikinsa? Dama faɗa ka ke yi dan jin daɗin bakinka ba ka so na, ba ka tausayina" Yanayin yadda take kukan, ya sanya ya fahimci tsagwaron damuwa ce, ta rasa yadda za ta yi, shi ne ta yi amfani da wannan damar take hucewa. Ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Ta ci gaba da kuka tana surutu, ganin ya yi mata banza ya sanya ta haɗa hannunta, ta hankaɗe shi daga gabanta ta tashi ta fita daga ɗakin. Ƙofar ɗakin ta fita, ta samu guri ta zauna ta yi shiru. Sauro ya baibayeta da cizo amma sam, ba ta jin zafin cizon sauron, sai tunanin mene ne mafita a wannan halin da suke ciki.
Ya fito daga ɗakin, kawai ya danƙi hannunta, ya mayar da ita cikin ɗakin. Ta fizge hannunta, ta koma gefe ta ja ta tsaya a tsaye. Sai ya ƙyale ta, ya tayar da sallar isha'i, ya idar ya yi kwanciyar sa.
Ita ma sallar Isha'in ta yi, sai dai kuma amai ya saka ta a gaba, ta kasa sukuni. Da ta zauna sai amai, haka za ta tashi ta tafi banɗaki.
Ta duba cikin kayan da take dafa masa tea, ta samu kanumfari ta saka a bakinta. Ta yi zamanta a ƙasa ta ƙi hawa katifar ma, ta kwanta a ƙasa. Sai dai bacci ya gagari idonta, tunaninta kawai mene ne mafita? Ina za su koma? Yaya za ta yi da rashin lafiyar sa.
Ta kalli inda yake, idonsa a lumshe. Gani ta yi kamar ba ya numfashi. Ta yi wata irin zabura, ta nufe shi ta kara hannunta a hancinsa. Ta ji ba ya numfashi, wata irin rikicewa ta yi za ta yi ihu, ya janyo ta ta faɗo kan katifar, ya zagaye ta da hannayensa, yana numfashi sama-sama, yanayin fitar numfashin nasa, ya sanya ta ƙara tsorata, saboda ba a daidai yake fita ba.
"Ka daina tsorata ni, kuma ka cika ni"
"A'a ki dain fushi"
"Ya zan yi na daina, bayan ba ka tausayina"
"Ina yi, na daina ba zan sake ba" daga haka bacci ya ɗauke shi. Amma Nana ta kasa bacci, ko baccin ya fara ɗaukar ta, sai ta buɗe ido a rikice, ta duba ta ga yana numfashi. Sai daf da Asuba, nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Da safe Nana ta fita ta sayo ƙosai, ta dawo ta tarar ya yi wanka da kansa. Cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ba ka bari na dawo na yi maka ba, kar ka wahala"
"Ni jariri ne?" Ya yi maganar cikin haki.
Idonta ya cika da hawaye ta ce "Ina jinka a jikina, fiye da jaririna"
Ya yi murmushi ya ce "Rayuwata Husnah" yadda ta ga Abincin ma ya gagara ci, abin ya ƙara razana ta, ita dama kasa ci ta yi. Saboda ƙamshin ƙosan ma amai ya saka ta. Saboda ta ga yana so ne sosai ya sanya ta je ta sayo masa.
Ta ba shi magungunansa ya sha, ya kwanta a kan katifa ta din ga danne hawayenta.
Ta ɗaukko ƙatuwar bagco, ta fara kwashe kayansa na wardrobe, ta zuba a ciki, ta ɗebo nata kayan ta zuba. Ta ɗaga kai suka yi ido huɗu tana kwashe kayan,ya yi sauri ya lumshe idanunsa. Ta share hawayenta ta ce "Sayyid, bari na je na ƙaro bagco, wannan ba za ta isa mu kwashe kayanmu ba"
"Ina zamu koma?"
"Zan laluba mana, in sha Allah ba zai gagara ba".
Cikin damuwa ya ce "Haƙƙina ne, ni yakamata na yi, ki yi haƙuri"
"Shugaba, ba na son Irin wannan maganar da ka ke yi wallahi. Bari na je na dawo" ta ɗauki kuɗi ta fice.
Ba ta zame ko ina ba, sai can gidan su.Ta sha mamaki ganin yadda gidan su ya ɗauki gyara, ko ina shar kamar ba gidan ba.
Sai dai hakan ba shi ne a gaban ta ba, ta yi sallama ta shiga gidan. Cikin matsananciyar sa'a, ta tarar da Baba a gidan.
Mama ma tana nan, su na ta hira a tsakar gida.
Suka amsa mata sallama, Baba ya ce "Too Nana yau a gari? Ai na zata dangin uwa taki, ko Imrana sun tafi da ke?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Baba su kai ni ina? Ina wuni Baba."
"Lafiya ƙalau"
Ta kalli Mama ma ta gaishe ta, ta amsa cike da za zaƙuwar son jin abin da ya kawo Nana, ganin fuskarta ɗauke da alamun damuwa, duk da murmushin da take yi.
Suwaiba ta fito daga ɗakinsu, jin muryar Nana, Nana ta kalle ta, ganin yadda wata jibgegiyar kaza baƙa ƙirin, da bataliyar 'ya'yanta aƙalla, sun kai ɗari, su ma baƙaƙe ƙirin, su na ta fitowa daga cikin ɗakin, su na biyo Suwaiba.
"Suwaiba kina nan dama, ina Jamila?" Ta kalli Nana, ba ta ce mata komai ba, ta nufi banɗaki ta shiga, kajin nan suka bi ta ciki suma.
Nana ta dawo da hankalinta kan Baba, sai dai ta kasa magana.
Ya ce "Nana ya aka yi ne?"
"Amm Baba dama,