BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   59 / 64

174K to 177K   out of 190K words

kujera, ya ce masa "Sannu"

Sayyid ya jinjina kai, Nana ta dawo hannunta riƙe da kati, idanunta sun yi ja, alamu suka nuna, da ta tafi karɓo katin, kuka ta yi a hanya.

Mai Adaidaita sahun ya ce "Tsaya da shi a nan, bari na duba idan da alfarmar da za a iya yi mana, a shiga da shi ya ga likita.

Ta ce "To na gode" ya karɓi katin ya yi gaba.

Sayyid ya riƙo hannun Nana a nasa, ya kwantar da kansa a jikinta, yana murza hannunta a hankali.
"Sannu Sayyid" ya ɗaga mata kai kawai.

Mintuna biyar, sai ga mai adaidaita sahun ya ce "Yauuwa bari na shigar miki da shi"

Ya sake kama Sayyid, ya kai mata shi har gaban likita. Ya zaunar da shi sannan ya kalle su ya ce "To ni na tafi Allah ya ƙara afuwa."

Nana ta ce "Na gode bawan Allah, Ubangiji Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi, ya jiƙan magabatanka, Allah ya buɗa maka na gode sosai da sosai"

"Amin bakomai, ai yi wa kai ne, Abokina Ubangiji Allah ya baka lafiya"

Sayyid ya ɗaga masa hannu, ya jinjina kai.

Ta ce "Ya ce ya gode"

"Ba wani abu" ya fice ya bar ɗakin likitan.

Nana ta yi wa likitan bayanin abin da ya faru, ya kalli Buzu ya yi masa tambayoyi. Ta ce "Ai ba zai iya magana ba"

Ya ce "Ok, to ya sauke rawanin, zan duba shi" Nana ta sauke masa.

Likitan ya sanya stethoscope ɗin sa a ƙirjin Sayyid, ya saurara. Sannan ya ɗaura masa BP.

Ya din ga kallon fuskar Sayyid, ya kama hannunsa ya duba pulse ɗin sa. Nana kuma ta zuba masa ido, kamar ta shiga cikin kan likitan, ta ji mai ya gano.

"Hajiya tun yaushe yake da hawan jini ne?"

Cikin mamaki Nana ta ce "Hawan jini kuma?"

"Eh mana, jininsa ya hau fiye da kima, ko ba ki san yana da shi ba?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ban sani ba. Sayyid ko dama ka na da hawan jini?"

Yanayin kallon da ya yi wa Nana, yasa ta kalli likitan ta ce "Shi ma bai sani ba"

Likita ya ce "Gaskiya dai jininsa ya hau sosai, kuma zuciyarsa babu lafiya. Bradichadia nake ji a pulse ɗin sa. So yanzu za mu yi managing jininsa da ya hau. Zan rubuta allurai da magunguna, ki sayo a yi masa.
Zan rubuta muku gwaje-gwaje, idan an yi za ku dawo ranar Monday mu gani"

Jikin Nana ya yi sanyi a raunane ta ce "Likita ba za a ba shi gado ba? A haka zamu koma gida har Monday, ka ji fa zuciyarsa ba ta bugawa sosai"

"Ki yi haƙuri. Abin da zan iya yi masa kenan, ko na ce a ajiye ku babu gado a nan. Kuma dole sai an yi gwaje-gwajen nan tukuna, sannan zamu san abin yi. Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Maybe ma hawan jinin ne ya kawo rashin bugawar zuciyar sosai, amma da ya sauka za a iya samun ci gaba"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan, na gode sosai Likita"

"Babu wani abu kar ki damu, zai samu lafiya in sha Allah"

Ta ce "Allah yasa, kuma Likita zai iya warkewa? Na ji an ce har abada ba a warkewa daga matsalar hawan jini da matsalar zuciya."

Cikin ƙwarin gwiwa likitan ya ce "A kimiyyance, sun ce ba su da magani, sai dai a yi managing symptoms kuma a canza life style. A addinance kuma mun san babu abin da ya fi ƙarfin Allah. Babu wata cuta da ta gagari Allah ya yaye wa bawansa"

Wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, bayan samun ƙwarin gwiwa daga bakin likitan. Ya rubuta allurai da magungunan da za a yi masa. Ta karɓa ta yi masa godiya.

Da ƙyar Sayyid ya taka ya bar ofishin, Nana ta zaunar da shi a kan benci, ta fita ta sayo alluran da za a yi masa. Amma duk Nurses ɗin sun yi busy, aiki ya yi musu yawa.
Nana ta koma gurin likitan, ta gaya masa, ya taso da kansa ya zo ya zauna ya yi wa Sayyid alluran.

Yana yi yana yi wa Nana nasiha. Bayan ya gama yi masa allurar, ya saka ta bashi maganin, ya ce bayan awa ɗaya zai sake duba bp ɗin sa.
Likita ya koma office, Nana ta fita ta sayo masa abin da zai ci, dan bai karya ba ga shi an fara kiran Azahar. Da ƙyar ya ɗan ci kaɗan, ya ce mata salla zai yi. Ta kai shi waje, ya yi alwala ta shimfida masa ɗan kwalinta, ya hau ya yi sallar. Bayan ya idar ita ma ta raɓa ta yi. Baya ta idar, ta miƙe masa ƙafafuwanta, ya kwanta a kai. Tana son taɓa ƙirjinsa, amma tana tsoron ta taɓa ta ji zuciyarsa ba ta bugawa sosai.
Sai da suka yi kusan awa biyu, sannan Likita ya sake duba jininsa. Ya ce "Alhamdillah jininsa ya sauka, ba kamar yadda ku ka zo ba, zuciyar ma ta fi da bugawa. Yanzu ku je idan an yi wannan gwaje-gwajen, zuwa Monday sai ku kawo, ko ba ku same ni ba, za a duba shi in sha Allah"

Nana ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "Mun gode sosai da sosai Likita, Allah ya sa ka ajiye aiki lafiya"

"Amin Allah ya sauwwaƙe" ya miƙe ya tafi.

Nana ta kalli Sayyid cikin tausayawa ta ce "Rayuwata, ya ka ke ji yanzu?"

"Alhamdillah" murmushi ta yi, jin ya yi magana.

"Ma sha Allah, sauƙi ya samu, zaka iya tashi mu je gida?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Ta tashi shima ya yinƙura, cikin ikon Allah, babu wanda ya riƙe shi har suka fita titi, duk da a hankali dai yake tafiyar.

Su na zuwa gida, ta dafa ruwa ta yi masa wanka tsaf, ta canza masa kaya. Ta lallaɓa shi da ƙyar ya ɗan ƙara Abinci.

Cikin damuwa ta ce "Sayyid, wai ya aka yi ka samu hawan jini dan Allah, ko wani abun nake yi maka da baka jin daɗinsa?" Ya girgiza kai alamar a'a.

"Amma na yi mamaki. Saka mini lambar Habu, ai ya kamata na sanar masa" ya karɓi wayar, ya dannan mata lambobin, ya miƙa mata. Ta karɓa tana jiran wayar ta shiga, amma waya ta ƙi shiga. Wai layin a rufe yake.

Cikin damuwa ta girgiza kai ta ce "Layin a rufe yake, bari zuwa anjima sai na sake gwadawa.

Horn ɗin motar Hajiya Halima ne ya cika layin, Nana ta ɗauki hijabi ta fice. Yana ƙoƙarin yin magana amma ba ta tsaya ba.
Ta leƙa ta tabattar Hajiya Haliman ce, sannan ta buɗe gate ɗin.

Hajiya ta shigo da motar, Nana ta rufe ƙofar, ta dawo ta nufi motar Hajiyan, ganin ta tsaya ba ta wuce ciki ba.

Nana ta ce "Hajiya sannu da zuwa"

"Meye haka? Ina mai gadin da ba zai fito ya buɗe gate ɗin ba? Ina ma ku ka tafi ne, babu wanda ku ka sanarwa, ku ka bar mana gida a haka, wane irin wulaƙanci ne haka?"

Cikin girmamawa Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri. Wallahi ba shi da lafiya ne, hankali a tashe muka tafi Asibiti. Mun yi kuskure ki yi haƙuri dan Allah"

"To dole ne? Idan ba zai iya ba ai sai ya ajiye aikin ko? Amma ba zai yiwu na ɗauke shi aiki, ya din ga bar mini gida haka ba. Kwanaki ma haka ku ka yi mini, ya ce ke ce ba ki da lafiya, shikenan ku kullum cikin ciwo ku ke, idan ba zai iya ba ku ajiye mini aikina, na nemi wani" gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, jikinta ya yi sanyi sosai. Ta ce "Ki yi haƙuri dan Allah" Hajiya Halima, ta fizgi motar, ta yi cikin gidan.

Tun da Nana ta koma ɗakin, ya ƙura mata ido, amma ta basar ta ce "Sannu Sayyid" kawai ya kawar da kansa ya lumshe idanunsa.

****
Cikin damuwa Fadila take yi wa Hajiya Suwaiba magana, duk da yanayin fuskarta cikin ko in kula take amsa mata.

"Ni gani nake kamar za mu ɗora wa Alhaji Zailani ɗawainiya a ce mu koma Asibitin da yake da file, ya ɗauki nauyin Daddy. Kin ga haryanzu kashe kuɗi ake yi, ba ma a gano me yake damunsa ba. Amma shi Alhaji Zailani ya dage, kina ganin babu matsala?"

"To da da matsala zai ce, a kai shi ne? Tun da mun kasa affording nan Asibitin, kuɗinmu ya ƙare, idan muka koma na gwamnati, ai dariya za a yi masa. Gara mu koma can ɗin".

Raudah da a baya, take biyewa mahaifiyarta ita da ƙannenta, suke zabga wa Fadila rashin kunya son ransu, yanzu gaba ɗaya ta saduda. Musamman ganin yadda Fadila ba ta da nutsuwa duk ta rame, saboda damuwa saɓanin da da suke tunanin, kuɗin mahaifinsu ne kawai ya sanya ta aure shi, kamar yadda mamansu ke nanata musu.

Ta ce "Mummu Anty fa gaskiya ta faɗa, nima gani nake yi, tamkar ɗora wa Daddyn su Shukura nauyi ne, ba fa mu san ranar barin Asibiti ba"

"Na saka baki da ke ne?" Rauda ta girgiza kai tare da yin shiru.

Fadila ta sake cewa "Ni kuwa ya maganar kuɗaɗen kuwa? An gama biya ko haryanzu da saura?"

"Da an gama biyan ai za ki ji"

Fadila ba ta haƙura ta sake cewa "Dama gidan da Umma take ciki ne, shi ne ya bata, mun yi magana da ita, a sayar da shi za ta koma gidan Yaya da zama. Sai kuma gwala-gwalaina na aure, duk su na nan. A sake rage bashin, a kuma biya kuɗin makarantar su Hibba. Jiya da ya ɗan farfaɗo sai da ya yi maganar su. Ƙuri Hajiya Suwaiba ta yi mata da ido, domin ta tabattar da gaske take yi, ko kuma makirci ne kawai da iya Duniya.
"Fadila" ya kira sunanta da ƙarfi.

Gaba ɗaya suka nufe shi, saboda tun jiya bacci kawai yake yi, kamar sumamme.

"Kar ki sayar da gidan Umma, ba ta na yi. Ni Allah zai kawo mini ɗauki" Ya yi maganar tamkar yana magana da kurame, saboda yadda yake ɗaga murya.

Fadila ta ce "To, ba sayarwa za a yi ba"

"Kin haihu ne?"

Ta ce "A'a"

"To Allah ya raba lafiya. Dan Allah ku cewa likitan nan, ya zo ya cire mini robar fitsarin nan, ta dame ni wallahi"

Rauda da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Daddy ka yi haƙuri, ka ga ba iya tashi ka ke yi ba, zuwanka banɗaki zai baka wahala. Ka yi haƙuri ka bar robar fitsarin nan "

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan Raudana, na gode"

"Sannu Daddy" ta yi maganar idanunta na zubar da hawaye.

A ranar Alhaji Zailani ya aiko da mota, aka mayar da Alhaji Fatuhu Asibitin su Doctor Sharif.

A gaban iyalan Alhji Fatuhu, ya din ga jaddadawa Doctor Sharif, a kula da amininsa, duk abin da ya kama a yi masa, shi zai din ga biya. Suka yi ta godiya.
Daga bisani ya bi bayan Doctor Sharif, suka fita.

"Ka na ji na Sharif?"

"Eh Alhaji"

"Wannan mutumin ko me za a yi masa, ba zai taɓa warkewa ba. Kawai dai ku din ga yi masa abin da ya sauwwaƙa da duk wani abu da zai ƙara rikita masa jiki. Ka sanya ido sosai a kansa, zan din ga kiran ka, ina jin halin da yake ciki. Zan tafi umara ne."

"Ba ka da matsala Alhaji"

"Shikenan, za ka ga saƙo in sha Allah"


****

Nana kuwa tun tana kiran lambar Habu, tana sanya ran za ta same shi, zai ɗauka har ta sare.

Ga jikin Sayyid sai godiyar Allah, babu wani ƙarfi a tattare da shi. Sai dai akwai ƙarfin hali, a haka wasu lokutan yake fita buɗe gate.

Jiki a sanyaye take kallon shi, ta ce "Sayyid, gobe in Allah ya kaimu, Litinin za mu je gwaje-gwajen da aka bamu, ga shi haryanzu ban samu Habu a waya ba. Ko gidan zan je na duba ko lafiya?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a" ta yi shiru tana kallonsa, dabara ta faɗo mata, ta ɗauki wayarta ta fara duba lambar Hajiya Amina. Amma ko sama ko ƙasa ta nemi lambar a wayar ta rasa. Ta duba iya in da za ta iya dubawa amma ba ta samu lambar ba.
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa, jikinta ya ba ta shi ne ya goge lambar ba wani ba.

Ta koma gefe ta yi shiru, ta rasa abin da yake yi mata daɗi a ranta, gaba ɗaya a tsorace take da ciwon nan nasa. Cikin dare ba ta iya bacci, da ta fara bacci, sai ta tashi, ta duba ta ga ni ko yana numfashi, ta ɗora hannunta a kan ƙirjinsa, ta ji ko zuciyarsa na bugawa, gaba ɗaya ba a nutse take ba.

Daren ranar Lahadi, Nana ta tafi cikin gidan, domin sanar da Hajiya Halima, batun komawa Asibiti da za su yi da safe.

Siyama ta tarar a falo, tana kallo tana ciye-ciye.

Nana ta ce "Dan Allah gurin Hajiya na zo" ko inda Nana take ba ta kalla ba, ta ci gaba da kallon Tv. Ganin Siyama ba ta da niyyar kula ta, ya sanya ta nemi guri ta zauna, ta fara zaman jira.
Aƙalla Nana ta shafe awa ɗaya da rabi, ƙarshe ma Siyama ta tashi ta bar mata falon. Har Nana ta yanke tsammanni, sai ga Hajiya Halima ta saukko daga kan bene.

Nana ta yinƙura ta ce "Hajiya ina wuni"

"Lafiya ƙalau" ta nemi guri ta zauna.

Ya kalli Nana ta ce "Ya aka yi?"

"Dama Hajiya zuwa na yi na gaya miki dan Allah gobe in Allah ya kaimu, za mu yi sammako, mu je Asibiti ne an bamu gwaje-gwaje, shi ne na ce bari na zo na gaya miki kar mu yi laifi".

Kamar Hajiya Halima ba za ta yi magana ba, sai kuma ta kalli Nana ta ce "Shi kuma gadin, da buɗe gate ɗin ni zan  je na zauna na yi?"

Nana ba ta yi tsammanin jin haka daga bakin Hajiya Halima ba, amma ta dake ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri Hajiya, in sha Allah ba zamu jima ba, ki yi haƙuri"

"Ni fa kin ga Nana, idan abin nan ba zai yiwu ba, a haƙura kawai. Na nemi wani, ku je ku nemi lafiya babu yadda za a yi ga aiki, sai dai ku bar mini ƙofa ku na can yawon Asibiti, ba fa zai yiwu ba"

Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na sani amma in sha Allah zai samu lafiya ya ci gaba da aikin, ki yi haƙuri"

Hajiya Halima dai, ba ta cewa Nana su je ko kar su je ba, Nana ta tashi ta koma ɗakinsu, duk jikinta a sanyaye.

Wayewar garin Litinin, Nana ta kammala komai da wuri, ta tafi cikin gidan, domin sake gaya wa Hajiya Halima, amma ta tarar ba su ma tashi daga bacci ba.

Ta ga idan ta tsaya jira, za su iya makara, dan haka ta fice, ta samu abin hawa suka tafi.

Nana ta ɗauka abin mai sauƙi ne, amma wuni suka yi yawo, daga nan zuwa nan, wasu gwaje-gwajen, aka ce ma ba za su fito a ranar ba, sai bayan kwanaki biyu. Ga shi duk kuɗin hannunta suka ƙare. Ƙarshe ba su samu ganin likita ba, da tasa tasan da suke hannunsu ba, saboda sai bayan la'asar liƙis sannan suka samu teses ɗin.

Su na komawa Nana, ta ɗora girki, zuciyarta ta yi ta raya mata, ta je ta gurin Hajiya Halima dai, ta ƙara ba ta haƙuri, amma ta fasa saboda ba ta san me za ta tarar ba, kar ta yi mata wulaƙanci.

Nana ta ci gaba da bashi magungunansa, tana kula shi, zuwa kwanaki biyun da aka ɗibar musu, komawa karɓar sakamako. Idan ana buƙatar buɗe gate, ita take zuwa ta buɗe, idan kuma ya ji jikin nasa da sauƙi, sai ya je ya buɗe da kansa.

Nana ta sake zuwa ta sanar da Hajiya Halima za su koma Asibiti, nan ma ta din ga ƙanan maganganu, Nana dai ta yi ta ba ta haƙuri. Ta fito suka fita da Sayyid.

Suka fara zuwa, suka karɓo gwaje-gwajen, suka koma Asibiti. Sai dai wani likitan suka gani daban.
Likitan ya ce ba za su iya kula da case ɗin sa a nan ba, saboda akwai matsala a zuciyarsa, dan haka aka tura su Asibitin gaba.
Can ma da suka je, aka yi masa hoton ƙirji, aka yi masa ECG, shi ma da ƙyar suka samu, dan sai da Nana ta bayar da cin hanci, sannan aka yi cuku-cuku, aka ba su result ɗin a ranar, sai dai shi ma da suka koma likitan da zai duba su, ya tafi. Nana tamkar ta ɗora hannu a ka ta fasa ihu, gaba ɗaya ma ta rasa abin yi, ga shi dakiya kawai take yi, ba ta son ta yi kuka ya gani, ta san yana yin kuka, za ta ɗaga masa hankali. Kawai ta zauna ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daɗi.

"Mu tafi gida"

"Sayyid ba mu ga likitan ba zamu koma?"

"Eh mu tafi" jiki a sanyaye Nana ta tashi, suka nemi abin hawa suka koma gida.

Sai dai su na zuwa gidan, suka din ga bugu, amma gate ɗin a rufe. Tun Nana tana sanya ran za a buɗe har ta sare. Ta zauna a kan ɗan dakalin da Sayyid ya zauna, ta rasa abin da yake yi mata daɗi.

Ta sake jarraba kiran wayar Habu, amma still ba ta shiga, ta damu sosai da rashin jin ɗuriyar su Habu. Ta samo ruwa suka yi salla a ƙofar gida, tana ta tunanin mene ne abun yi? Har magariba ta yi, sauro ya fara bin su, Nana tana bugun gate ɗin, amma shiru.

"Sayyid yanzu mene ne abin yi?" Bai yi magana ba, sai ga motar Hajiya ta dawo, tare da Siyama.
Nana ta yi ajiyar zuciya, ta tashi ta nufe su fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Hajiya ashe fita ku ka yi, kawo mukullin a buɗe" ta miƙa wa Nana mukullin, ta buɗe musu gate ɗin. Wani abu mai ɗaci ya ɗar su a zuciyar Sayyid, ganin yadda Nana ke kokawa da ƙaton gate ɗin da ya fi ƙarfinta.
Ba su damu da tambayar Nana ya mai jiki ba, amma Siyama  ta ƙura masa ido, tamkar idonta zai faɗo.

Suka wuce da mota, Nana kuma su ka tafi ɗakinsu.
Wasu lokutan jikin nasa, sai ya ɗan samu afuwa, lokaci ɗaya kuma sai jiki ya burkice ya kasa komai.

Sai ranar Juma'a, sannan suka samu su ka ga Likita. Likitan ya duba gwaje-gwajen da aka yi

59 / 64