Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
gal babba a ɗakin, ga labulaye da wardrobe mai guda biyu da mudubi ƙarami, ga kuma carfet a tsakiyar ɗakin.
Yaya Atine ta ce "Yanzu a sati ɗayan ku ka yi wannan shirin?"
Sule ya ce "Eh, wani mu muka yi, wani kuma Hajiyar da muke yi wa aiki ce, ita ta sai labulaye da abin shimfiɗar nan, da kayan ɗakin ma, abubuwa kaɗan mu ka ƙarasa"
"Lallai tana da kirki sosai, bayan kayan da ta je ta kai mata gida. Amma Ummi babanku ya tafasa makaronin asara ko cokali fa bai saya wa Nanan ba"
Ummi ta tsuke fuska ta ce "Babu kitchen kenan? A ina za mu ajiye mata kayan kitchen ɗin"
Sule ya ce "Ai abu ne na maleji, sai dai a ajie mata a nan ɗin, tun da yana da girma sosai"
Anty Saude ta ce "Bawan Allah kuma cikin gidan da mutane?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh akwai, sai dai ba ma zauna bane ba"
Ya Atine ta shiga banɗaki, ta kunna famfo ta ga ruwa na zuwa, ga shi har da wearing ɗin nepa da sola na gidan a ɗakin.
"To yanzu ina angon, mu fa ko sau ɗaya ba mu gan shi ba"
Sule ya ce "Yana nan tafe, sai an jima za a rako shi, idan kuma za ku jira ne to shikenan"
Yaya Atine ta waro ido ta ce "A ina ɗin? Wannan unguwar duk kangwaye, ku wuce mu tafi ke Nana Allah ya baku zaman lafiya"
Ummi ta riƙe hannun Nana ta ce "Nana kin dai ji abin da Baba ya gaya miki, ki yi haƙuri da abin da ƙaddara ta zaɓa miki, ki yi zaman ki, ke kin san wannan gidan namu, ba gurin da idan ka bar shi zaka so koma masa bane. Ki zama mai tuna wace ce ke, kuma daga ina ki ke, sharrin da ake yi miki kawai a gidan ya ishe ki. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗayyiba. Na karɓi kuɗin sadakin ki a hannunsa, da kyar ya bayar da dubu hamsin, wai sauran da su aka yi hidimar biki. Ina son ɗan sayo miki kayan kwallita, da underwears idan kin amince, idan ba ki amince ba na baki kuɗin ki"
A hankali Nana ta ce "Duk yadda ki ka yi na amince"
"To shikenan, ga wata dubu ashirin ki riƙe a hannunki, a irin kuɗin gudunmawar bikin ki ce, ko za ki yi amfani da su, a sha amarci lafiya" Nana tana ji suka tafi suka bar ta ita kaɗai ƙwal.
Shiru garin, ko ƙwaƙƙwaran motsin wani abin ba ta ji, ta ɗaga kai tana kallon ɗakin.
A zuciyarta ta din ga addu'a, tana roƙon Allah ya shiga lamarinta. Yawan gane-gane da Nana take yi, ya sanya zuciyar Nana fara ƙeƙashewa. Ta bayan ɗakin take jin hayaniya, ana surutai da dake-dake ana hira, tamkar a irin gidan yawan nan.
Kiran sallar magariba ta ji, ta tashi tsam, ta shiga banɗakin ta ɗauro alwala, ta dawo ɗakin ta yi sallar magariba.
Bayan ta idar duhun magariba ya ƙara yi, sai dai ɗakin akwai hasken fitilar solar.
A hankali kuma tsoro ya fara shigar Nana, ta daina jin hayaniyar da take jiyowa, ko ina ya yi tsit.
Daga bisani kuma ta din ga jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa, sai kuma hasken fitilar ɗakin ya ɗauke baki ɗaya. Ta kifa kanta a kan ƙafarta, jikinta ya fara tsuma.
A hankali ta ɗago kanta, ta ganta a cikin sahara a zaune, sai sautin iska da yake kaɗa yashin saharar. A wannan karon ma yana tsaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa. Tashin sautin kaɗe-kaɗe ta din ga ji, ba tare da ta ga daga inda kiɗan yake tashi ba, ga wata zazzaƙar murya da take ta rangaɗa guɗa, muryar na amsa kuwwa a dajin. Ya taka a hankali ya je gabanta, ya miƙa mata hannu. Ta ɗago a hankali ta kalle shi, ta ɗaga hannunta za ta miƙa masa. Ta ji an yi sallama firgigit ta buɗe idonta tana kallon mai yin sallamar.
Ayshercool
08081012143
Page 28
Da Sule suka yi ido huɗu, ya shigo wasu buzayen suka biyo bayansa, hannunsu riƙe da kaya.
Ya kalli Nana ya ce "Afuwan mun tsorata ki ko? Ki yi haƙuri ba mu zo da wuri ba, mun tsaya mun yi salla isha'i ne.
Ita dai Nana ba ta ce komai ba, aka din ga jere cartons na ruwa a ɗakin.
Ita dai ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.
A hankali ta din ga jin tamkar numfashinta zai ɗauke, wani irin bugu zuciyarta take yi, sanyi yana ratsa ta.
Ta ɗago kanta domin shaƙar wadatacciyar iska, kar numfashinta ya ɗauke.
Fararen kaya ne a jikinsa, irin na buzaye, ya yi rawani da shuɗin yadi, ga wata ɗamara da ya yi da wani shuɗin yadin, gefen ƙugunsa kuma soke da takobi a cikin kubenta, wuyansa yana sanye da wani abu, na fata wanda ya ɗara laya girma, kuma bai kai girman jaka ba. Yatsunsa sanhe da zobunan azurfa, ga kuma ƙarfen tagulla a tsintsiyar hannunsa, ya dafe gefen cikinsa, shigar ta buzaye ce, kuma ta wata fuskar kamar ta larabawa.
Yana gaba Habu yana bayansa, shi ma ya sha kwalliya cikin shigar buzayen. Wani irin daddaɗan ƙamshin turare,
ya karaɗe ilahirin ɗakin, Nana ba ta taɓa jin turare mai tsananin ƙamshi kamar wannan ba.
Sai kuma sauran buzayen aƙalla su biyar, duk sun sha kwalliya.
Dadduma suka shimfiɗa masa ya zauna. Gaba ɗaya suka zauna a gefe, suka yi shiru. Habu ya ce "Mu yi addu'a" aka fara Addu'a.
Nana ba ta san a tsakaninsu waye mijin nata ba, sai dai tana ƙoƙarin satar kallonsa, duk da kamar kullum kamar yadda ta saba ganinsa, fuskarsa a rufe take da rawani.
Ba ta san me aka karanta a addu'ar ba, saboda ta lula tunani, sai muryar Habu da ta ji ya kama sunanta.
"Nana"
Ta ce "Na'am"
"Da farko dai ina mai ba ki haƙuri a kan abin da ya faru, kin san komai Allah ne yake ƙ'addarawa. Jikina ya yi matuƙar sanyi da abin da ya faru. Na gane dalilin wannan auren ne ya sanya muka baro gida. Ki yi haƙuri bawa ba ya tsallake ƙaddararsa. Ina yi muku fatan alkhairi da fatan Allah ya baku zaman lafiya. Na san abubuwan da mu ka ba ki na aure, be kai abin da ake kashe muku na aure ba, amma ki yi haƙuri a hankali za mu duba a yi miki, kin san masu ƙaramin ƙarfi ne mu. Dama ɗan kuɗin gadin tarawa muke yi, za mu tura gida wannan abu ya bijiro, kuma kuɗin hannunmu duk ya ƙare. Dan Allah ki yi haƙuri da abin da Allah ya ƙaddara miki."
Nana dai ba ta ce komai ba, ya sake nuna mata kayan da suka zo da su ya ce "Ga sayayya nan, abin wanka ne da kayan wanke baki, da ɗan abin da ba a rasa ba na kayan tsafta. Yanzu mu na sauri mu koma, ba wanda zai kula da ƙofa dole mu koma da wuri, amma zamu dawo da yardar Allah" su ka ƙara yi musu fatan alkhairi.
Shi kuwa tun da ya zauna, ƙwaƙwƙwaran motsi ma bai yi ba, balle ya tofa wani abu ba.
Sai da Nana ta ga sun miƙe baki ɗaya shi yana zaune, sannan ta fara zazzaro ido.
Gaba ɗaya sai suka juya yare, su na yi masa magana, har suka gama maganar, shi dai bai ce uffan ba.
Ɗaya bayan ɗaya suka fice, hakan ya ƙara tabattar mata da shi ne mijin nata. A take ta tuna Sule ya taɓa gaya mata ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa. 'kenan mahaukaci Baba ya aura mini?' ta tambayi kanta.
Ƙoƙarin tuna wasu abubuwan take yi a kansa, amma abu ya gagara, ta ji gaba ɗaya kanta ya toshe.
Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta yi sallar isha'i.
Sai dai bayan ta yi alwala da ƙyar ta baro banɗakin, saboda duk taku sai ta ji tamkar zuciyarta za ta fashe.
Ƙafafuwan ta su ka gaza ɗaukar ta, a dole ta zauna ta kalli gabas, ta tayar da salla. A zaunen ma jiri take yi, da haka ta yi salla.
Shi dai bai kula ta ba, bai kuma tashi daga gurin da yake a zaune ba, kamar gunkin budda.
Ta idar da sallar, ta koma jikin bango ta matse jikinta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ji take kamar ta kurma ihu, ga sanyin nan da take ji ƙaruwa yake yi, tsigar jikinta sai tashi take yi.
"Allah ka dube ni, dan Allah ƙaisar kar mu yi haka da kai, ni hauka shi hauka ta ya ya za a yi wannan zaman" ta furta hakan a hankali.
Sun shafe dogon lokaci, kamar babu halitta mai motsi da ta wanzu a gurin, Nana tana ta tufka da warwara a zuciyarta, kawai ta ga ya tashi tsaye. Zuciyarta ta ƙara tsinkewa da tsoro da razani, tare da hakaito mata miyagun abubuwa, yanzu idan ya yankata a gurin nan ya gudu fa? Mussaman wannan takobin da take gani.
A hankali yake tafiya, ya tafi gefen wardrobe ɗin ɗakin, da aka kafe abin rataye kaya. Ya cire takobin ya rataye ta. Ba tare da ya waiwayo ba, ya fara kwance rawaninsa. Kasancewar ya juya mata baya, ya sanya ta zuba masa ido ko ƙiftawa ba ta yi. Ya kwance rawanin gaba ɗaya, ya ninke Nana ta zuba wa sarautar Allah ido, ganin kansa ɗauke da gashi baƙi wuluk, ya tufke shi tamkar an yi wa kan bahauhishiya saloon.
Ya saka hannu ya zare rigar jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana kallon gefe, kamar mara gaskiya.
A hankali ta ƙara ɗagowa, ta ganshi da dogon wando, da shirt, ya ninke rigar da rawaninsa, ya buɗe wardrobe ɗin ya saka kayan a ciki.
Ba ta san ya aka yi ba, kawai sai gani ta yi sun haɗa ido. A take ta tuno ganin da ta yi masa, har ta suma a ɗakin su.
Da wata irin azama ta tashi, duk da bugun zuciyar da take ji da kuma jiri, ta ja da baya ta tsaya cikin tsoro da razani.
Ya ci gaba da kallonta, ba tare da ko ƙifta ido ba.
Kawai Nana ta fashe da kuka, ba tare da sanin dalilin da ya sanya ta kukan ba.
Gani ta yi ɗakin yana juya mata, ya kawar da kansa daga kallonta, ya fice daga ɗakin. Fitarsa ke da wuya ta silale a gurin ta faɗi.
A hankali ta fara juyi tana tari, a cikin kunnuwanta take jin bugun zuciyarta, ta ja jikinta ta tashi da ƙyar. Ta karkaɗe hannunta saboda ƙura, ƙaisar ta gano sanye baƙar riga tana jan ƙasa, yana shirya litattafan sa, yana goge su.
Da ƙyar tarin ya ɗan lafa mata ta ce "Ƙaisar"
"Ya aka yi?" Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.
"Tsoro nake ji, ji nake yi kamar zan mutu. Ba ka ji yadda zuciyata take bugawa ba"
"Ina jin yadda take bugawa mana, ai mutuwar ma za ki yi idan ba ki yi wasa ba, tun da ke dai kin ƙware a taurin kai. Wannan mutumin ƙila shi zai yi ajalin ki. Ki kan ji bugun zuciya da sanyi ne, idan ina guri to me yasa ba na gurin daga ke sai shi ki ke jin bugun zuciyar?" Ya jefo mata tambayar.
Nana ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ware ido, amma ta kasa magana. Ya ce "Eh, ai na gaya miki ba ki da tabbacin abin da ki ka aura, mutum ne ko kuma jinsinmu" yana gama maganar ya yi gaba. A rikice Nana ta bi shi tana faɗin "Dan Allah ka tsaya ka saurare ni, yanzu ya zan yi dan Allah?"
Ya waiwayo ya kalle ta ya ce "Au tambayata ma ki ke yi ya ya za ki yi? Shirka fa ki ke ƙoƙarin ko kin manta?"
Nana cikin kuka ta ce "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi tsoro nake ji idan na ci gaba da rayuwa da shi, zan iya mutuwa"
Ƙaisar ya ce "Ai da da na gaya miki ba ki yadda ba" ya juya zai tafi, ta riƙo rigarsa"
"Zan watsa ki ta waje, idan ki ka kuma bi na"
Za ta yi magana ya ce "Sai kuma ki yi" kawai ya ɓacewa ganinta.
Kawai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da kuka.
Yana zaune a gefen ɗakin nasu, ya na shan hantsi, sai ga Sule ya zo da kwandon kayan abinci.
"Ango har ka tashi? Ya mariée ɗin ?"
Ya nuna masa ɗakin, alamar tana ciki. Gaba gaɗi Sule ya nufi ɗakin da kwandon Abincin cikin hanzari Buzu ya miƙe ya tsaya a ƙofar ɗakin.
Sule ya ce "Au yi haƙuri, bari na zauna daga nan" ya nemi guri ya zauna a gefensa.
Nana kuma ta buɗe idonta, ta ganta kwance a kan katifar, jikinta babu naɗin lafayar da aka kawo ta da shi, sai riga da skirt ɗin ta na ciki, kanta ko ɗan kwali babu. A razane ta dubi jikinta tana tambayar kanta, ko ya yi mata wani abin ne?. Ta kalli gefen katifar ta ga lafayar a ninke a ajiye. Da azama ta yinƙura ta faɗa banɗaki, amma ba ta ga alamar an yi mata wani abu ba.
Ta yi tsarki, ta yi alwala tana ta istigfari ta yi sallar asuba, cike da jin kunyar Ubangiji, yadda lokaci ya ja gari ya yi haske ba ta yi salla ba.
Bayan ta idar tana jiyo Sule yana ta zuba da yaren su, shi dai ba ta ji maganar sa ba. Ta yi mamakin abin da ya sanya Sule kasa yin zuciya ya ci gaba da surutu ba tare da ana kula shi ba.
Babu tsammani ya shigo ɗakin, ba tare da ko sallama ba. Aikuwa ta zabura ta ja da baya tana kallonsa.
Kai tsaye ya nufo ta, ya ajiye mata kwandon Abincin a gabanta. Ya nemi guri ya zauna ya zuba mata ido, da kwandon kayan abincin a tsakiyar su.
Nana ta sunkuyar da kanta, sanyi na ratsa ta.
"Zan ci abinci" ta ji muryarsa kamar daga sama, ɗaga kai ta yi ta kalle shi, ji ta yi kamar ta ce masa to ya ci mana, sai kuma ta tuna ashe fa wai yanzu mijinta ne. Mamaki ne ma ya kamata, dan har a lokacin tana mamakin idan ba kurma ba ne ba.
Ta janyo kwandon ta sassuke abincin, ta fara ƙoƙarin zuba masa, kawai ta ga ya tashi ya fita. Sai ga shi ya dawo da abin da suke hura wutar dafa shayi, har da butar shayin ma, da alama abin da suke yi a wajen tun ɗazu kenan, shan shayin.
Ya buɗe cikin kayansa, ya ɗaukko turaren wuta, ya zuba a kan sauran garwashin. Take ɗakin ya karaɗe da ƙamshi mai daɗin gaske. Ya samu guri ya zauna, ya karɓi abincin, ya koma gefe ya sauke takunkumin rawaninsa ya hau ci.
Nana kuwa kasa cin abincin ta yi, ta yi tsuru sai satar kallonsa da take yi, ya gama ci ya ɗauki kwanukan da ya ci, ya fita waje ya wanke ya dawo ya ajiye mata. Ya tsiyayi sauran shayinsa na butar, ya shanye abin sa.
Ya kewaye ta, ya ɗauki pillow ya koma can gefe ya ajiye ya kwanta. An shafe tsawon lokaci, na zaune ba tare da sanin abin yi ba. Jin yunwa ta uzzura mata ya sanya ta ɗan zuba abincin ta fara ci. Tun tana cakala har ta saki jiki, ta ci gaba da zurawa kawai suka yi ido huɗu, tana ta loma. Sai kuma ta yi sak, ta ci gaba da ci ta kasa kamar wadda ta aikata rashin gaskiya, kuma ya ƙi daina kallonta. Ƙarshe sai haƙura ta yi da cin abincin, kallon da yake yi mata duk ya sanya ta damu.
*****
Gidan su Nana tun a ranar kowa ya watse, dan baba faɗa ya yi ta yi, yana cewa duk wanda ya kwana sai dai ya nemi abin da zai ci, shi ba shi da abin da zai sake bayarwa a bawa mutane.
Suwaiba ta ƙarewa ɗakin su kallo ta ce "Ohhh abin tsiya, ko tsinke ba ta bari ba, duk ta kwashe komai balle mu gada."
Mama ta ce "Au ke har wata tsiyar ki ke saka ran gada a gurinta? Me za ki gada banda gayyar masifa, ai gara da tarkata komai ta tafi, ma sake mu miƙe ƙafa mu huta mu ma"
Jamila da ta shirya tsaf za ta fita ta ce "Aikuwa dai"
"To kafin hankali ya dawo kan ku, Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari 'yan uban uban su, wanda kowa sai ya koka a tashi kan munafukan unguwa da na family"
Suwaiba har da tsalle ta ce Amin Mamanmu maganin kukanmu.
Jamila ta yi murmushi ta ce "Ni dai sai anjiman ku"
Mama ta ce "To a sauka lafiya"
*****
A tsanake take kallon yadda mai gidan nata, yake ɗan yamutsa fuska bayan ya kammala cin abinci.
A hankali ta ce "Daddy"
"Na'am baby"
"Ya dai? Jikin ne ko garin? Na ganka so silent"
Ya ɗan yi miƙa ya ce "Pressure ce ta ɗan yi mini yawa wallahi, ina shirin tafka asara ne, kwana biyun da ban je kasuwa ba, har an yi mini ɓarna wallahi. Ga kaya sun iso Nigeria na gama clearance amma coustom sun ƙi sakar mini kayan"
"Subhnallah, in sha Allah ba za ka yi asarar ko naira biyar ba. Allah zai warware komai, bari mu duƙufa da addu'a in sha Allah ba wani abu"
Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, ɗan duba mini paracetamol idan ki na da shi, kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau"
Cikin damuwa ta ce "In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na buƙar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ƙaddara"
Ya girgiza kai ya ce "A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daɗi"
Ta tashi ta ce "Bari na ɗaukko maka" ta nufi bedroom ɗin ta.
*****
Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ƙarya.
"Na rasa gane abin da ya faru gaba ɗaya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura ɗin, na ba shi kuɗi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi ɗin a zahiri, ban kira shi ba na kasa tunawa, ni dai kawai na ganshi