Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
ba ta dawo ba fa" matashin yaron da bai wuce shekara goma sha biyu ba ya bashi amsa.
"Ba ta dawo daga ina ba?"
"Makarantar islamiyya"
"A yanzun da magaribar nan, ke Jamila, Sa'adatu wai kuna ina ne ina ta magana kun mayar da ni mahaukaci?"
Jamila ce ta fito tana yamutsa fuska ta ce "Baba ba ta dawo ba fa"
"To tana ina? Ina ta tafi? Ko an aiketa ne?"
Rabi ce ta fito ta ce "Wai Nanan yarinyar goye ce ne da ka ke ta wannan haƙilon saboda ita? Idan ta gama yawon nata za ta dawo ai"
Guntun tsaki ya yi ya ce "Kai sani da aka tashe ku daga islamiyyar ba ka ganta ba?"
Sani ya ce "Ban ganta ba, kuma mu ne ƙarshen tafiya, yau na makara aka sakamu kwashe butocin alwala muka gama aka kulle makarantar"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba bankaɗawa ta yi, tayi wani wurin ba"
"Ko kuma yawon watsewa ta tafi ba"
"Allah ba zai nuna mini watsewa a kan 'ya'yana ba" yayi maganar yana ficewa daga gidan.
Nana kuwa tun da ta fita daga islamiyyar, babu wanda ya ganta, dan haka ta ci gaba da tafiya ba tare da ta san in da take sanya ƙafafuwanta ba, ba ta iya tantance rana ce ko dare ma, sai dai tana jin yadda zafin rana yake ratsa ƙafafuwanta da kuma tafin ƙafarta, da take takawa babu ko takalmi. Ita dai burinta ta yi nesa da in da take, ko ta fita daga halin da take ciki, ko kuma tserewa abin da take jin tamkar ajalinta ne yake tunkarota.
Wani matsakaicin gida ta tunkara, babu sallama babu neman izinin masu gidan, kawai ta afka ciki. Ɗaya daga cikin jerin ɗakunan ta shiga, ta cire hijjabin jikinta na islamiyya, ta cukuikuye shi, ta yi fulo da shi, ta kwanta.
Kusan mintuna goma sha biyar, da shigarta babu motsin kowa a gidan. Wani matashi ne yayi sallama, ya ji shiru, ya sake sallama ya ji shiru.
Saka kai yayi ya shiga ciki yayi tozali da Nana a kwance tana bacci. Turus yayi yana kallonta, yana tunanin ita kuma wannan daga ina.
Shaiɗan ne ya shiga ƙawata masa kyakkyawar baƙar fatarta mai sheƙi, da kuma ilahirin jikinta.
A hankali cikin sanɗa ya shiga ɗakin, yana cigaba da ƙare wa ƙirjinta kallo.
Ɗan dukan gefen carfet yayi, dan ya tabattar da idonta biyu ko bacci take yi.
A hankali yake ƙoƙarin kai hannu jikinta, kwatsam! Ya jiyo muryar matar gidan a ƙofar gida tana gaisawa da maƙwabta.
Cikin hanzari yayi baya ya dawo tsakar gida ya tsaya.
Sallama tayi tare da yara ƙanana, ya amsa yana mazewa.
"Saleh, zuwa babu sanarwa haka?"
Ya ɗan sosa kansa ya ce "Wallahi kuwa, ina ta sallama amma gidan shiru babu kowa"
Ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, kuma yarinyar maƙwabta na bari a gidan, ta jire mini na je ɗaukko su hafsa daga makaranta shi ne ta bar mini gidan a buɗe haka?"
Saleh ya ce "Aikuwa ta yi ganganci da ta bar miki gidan babu kowa haka"
"Aikam yaushe ka shigo garin ne?"
"Shekaranjiya da daddare na ce yau bari na ɓullo mu gaisa"
"Aikuwa ka kyauta" ta yi maganar tana ɗaga labulen ɗakin.
Turus tayi, tana maimaita"Innalillahi wa innalillahi raji'un" ganin mutum a kwance.
Ya kalleta ya ce "Lafiya kuwa?"
Ba ta amsa masa ba, ta ƙarasa tana ƙare mata kallo, ta kai hannu ta taɓa ta ta ce "Nana" sai dai shiru ba ta amsa ba.
Ta kalli ƙafafuwan Nanan, futu-futu, har da jini alamar ta taka abubuwa a hanya.
"Subhnallah, kar dai da ƙafa ta taho Nana, Nana tashi mana" sai dai ba ta motsa ba.
Cikin basarwa Saleh ya ce "Anty lafiya kuwa? Wace wannan ɗin dama da mutum a gidan nake ta sallama ba a amsa ba?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, dan shi gaba ɗaya ma bai lura da raunin da yake ƙafarta ba.
Anty ta ce "Ƙanwata ce wallahi, ba ta da cikakkiyar lafiya ne, ga wayata ta lalace balle in kira gida in ce tana nan, kuma ni Wallahi ban haddace lambar kowa ba, balle na kira na gaya musu"
Suka ci gaba da jimantawa, Nana kuwa ta ci gaba da baccinta, mai kama da suma.
Baba yayi sintiri zuwa islamiyyar su Nana babu adadi, tun yana yawon neman ta har ya gaji.
Suwaiba ta ce "Wataƙila mutanenta ne su ka yi wani wurin da ita"
"Ba wasu mutanenta, ayi ta fakewa da sheɗanu tana rashin mutunci, ta taɓa yin irin haka ne? Allah ne kaɗai ya san gidan uban wanda ta tafi"
Baba ya ce "A'a ba na tunanin za ta je wani wurin ba mu sani ba, tun da ba ta taɓa yin hakan ba, amma ina Jamila ma?"
"Ta na gidan uwa ɗakkinta ɗin nan, maman khairat, tun azahar tana can"
Baba ya ce "Kuma haryanzu goma saura na dare, ba ta gida uban me take yi a gidan mutane?"
Mama ta ce "A'a yau na ga abin tsiya, to malam ba abincin safe babu na rana, ba dole yarinya ta tafi in da za ta samu ta ci ba? Ai gara ita an san in da take, 'yar ka fa? Shi ya yi nasa wuri, ita ma gashi ta kama gabanta" Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba.
Shirun sa ke da wuya, Jamila ta yi sallama, suka amsa baki ɗaya, Baba ya ɗaga kai zai yi magana, sai yayi shiru ganinta da babbar leda.
"Mama na dawo"
"Sannu jamila, ya ki ka barota?"
"Lafiya kalau Alhamdilillah, baba sannu da gida"
Baba ya ce 'Yauwwa Jamila, amma ina ki ka tafi haka ba kya gida?"
Jamila ta taɓe baki ta ce "Baba Allah ya gani na gaji da raragefen shiga banɗaki ne, ga yunwa ina ji shi yasa na tafi gidan maman khairat na wuni a can"
Baba ya ce "Ku yi ta haƙuri ku na addu'a, in sha Allah za a gyara katangar nan, kuma a gyara masan, mutanen unguwar nan ne ma, babu haɗin kai da zuciyar taimako, amma yadda iftila'in nan ya afko mini, ai kamata yayi ayi gidauniyar da za a tallafa mini"
Mama ta ce "Kai wa ka ke tallafawa idan matsalarsa ta tashi?"
"Rabi wai babu damar na yi magana, sai ki nemi tozarta ni a gaban yara"
Ta girgiza kai ta ce "Ba wani tozarci gaskiya ce"
Bai bi ta kanta ba, ya kalli Jamila ya ce "Jamila, Nana fa ba ta dawo gidan nan ba, tun ɗazu ake neman ta ba a ganta ba" Jamila ta tsaya da juye abincin da take yi ta ce "To ina ta tafi?"
"Wallahi ban sani ba, an rasa in da ta shiga "
Jamila ta ce "Kuma ita ba waya ba, balle a kira ta kuma dai na ga ba ta taɓa yin irin haka ba"
"Wallahi kuwa. Kai Sani ɗaukko kwano a zuba mini abincin nan nima na saka a cikina, dan rabona da abinci tun safe, ashe akwai sauran masu zuciyar taimako a unguwar nan, irin wannan abinci haka Jamila"
Haka Baba ya karkace aka lamushe abinci da shi, har ya nemi ya manta batun ɓatan 'yar sa Nana.
*****
Misalin ƙarfe tara na safe, Nana ce a zaune, tana kurɓar kunun tsamiya, duk da babu sukari a cikinsa, amma ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, ga dankali da aka take mata kwano da shi, wanda rabonta da ta ci ta ƙoshi haka har ta manta.
Ummi ta dube ta ta ce "Nana, wai garin yaya aka yi ki ka taho gidan nan a ƙafa haka? Tun jiya kin ƙi magana"
Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban san ya aka yi ba, ni dai kawai ina islamiyya na ji duniya ta yi mini zafi, kamar zan mutu shikenan ban san meyafaru ba, na dai ji ina bacci, kawai na farka na ganni a nan"
Ummi ta ce "Ohh wannan larura taki Allah ya yaye miki Nana, an gode Allah ma da ki ka yo nan ba wani wurin ki ka yi ba, in ƙara miki dankalin ne?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a na ƙoshi Alhamdilillah"
"Nana ina kyautata zaton mutanen nan ne, suka hana miki samun mijin aure har yanzu, ga Habibu, rumi-rumi an fara magana aka fasa, ni a yanzu ma akwai wani a ƙasa kuwa?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.
"Wallahi Nana ina yi miki fatan ki yi aure, ki bar wannan gidan namu, da ba a iya amfana maka komai, idan ba uwarka ce ta yi maka ba, kin ganni nan duk da yau da daɗi gobe babu, yau mu ci gobe mu yi haƙuri, ga azabar dangin miji, amma ya fiye mini wannan gidan namu, da kamar a cikin sa aka yi wahayin babu, ke kanki a yunwace ki ke, ga Baba ya damu ki yi aure, dan Allah kalli wata breziya a jikinki, dan masifa duk kin ƙuƙƙuleta, wallahi da na shiga banɗaki na tarar da phant ɗinki, na za ta tsumma ne da yarwa zan yi, wannan wace irin rayuwar azaba ce?"
Nana ta sunkuyar da kai ta yi shiru, dan duk abin da ummi take faɗa gaskiya ne, amma waye zai aureta da wannan larurar a haka? Malam Auwal na islamiyyar su, na ta nuna mata alamar soyayya amma ta yi burus, dan ta san yau da gobe sai Allah, babban fatanta ta rabu da wannan larurar, duk da tana burin yin auren, dan ita kaɗai ta san masifar da take ciki.
"Kin san wani abu Nana, akwai wani mai magani da na ji maƙwabciyata su na magana rannan, zan yi mata magana ta kwatanta mini wurin, anjima mu kama hanya mu je ko Allah ya sanya a dace, daga nan na je na duba idan an gyara mini wayata sai na raka ki gida"
To kawai Nana ta iya cewa, ta cigaba da shan kununta a hankali.
*****
"Alhajin Allah"
"Na'am malam" ya amsa yana tattara nutsuwarsa a kan mutumin da yake zaune, a kan tabarma, gefensa ga carbi mai dubu, ga wani ɗan farantin katako da ƙasa a kai. Yayi shiru ya na nazartar ƙasar da ya yi wa zane-zane a gabansa.
"Malam me ka gani ne?"
"Eh to, buƙata zata biya Alhaji Zailani, amma gaskiya za a sha gwagwarmaya, ga magauta ko ta ina a tattare da kai, arziki zai ninku fiye da yadda ka ke zato, amma gaskiya zaka sha wahala, ƙila ma ka iya rasa ranka, kuma a gidan huɗu ga wata kujerar siyasa nan ko ta mulki da zaka iya samu, sai dai gidan uku ya nuna shi ma akwai bala'i, da tarin ƙalubale"
Alhaji zailani ya yakice gumin da yake tsatsafo masa daga goshinsa ya ce "Yanzu malam menene abin yi, dan ko a yanzu kasuwancina harkokin sun fara ja da baya"
Ya sake zazzana ƙasa, ya ɗago ya ce "Eh ga wani ƙulli nan a binne a kusurwa huɗu na mararraba, a kanka, amma warware wannan ba zai yi wahala ba, yanzu mafita ɗaya ce da za a samu mai burujin aƙrabu, ko hutu ko surdanu da zai dace da burujin ka, kuma za su taimaka maka ka kai ga ci, ba tare da ka fuskanci ƙalubale ba"
Alhaji Zailani ya tattara hankalinsa, ya gyara zamansa ya ce "Malam Gambo to tayaya zan gane su, kuma a ina za a same su, ko nawa ne zan bayar a samo"
"Ba samo su za ayi ba, ka samu mace mai ɗaya daga cikin waɗannan burujan, ka kwanta da ita, zaka samu buɗi ta in da ka zata da in da baka zata ba, taurarinta za su haskaka naka da suke ƙoƙarin disashewa, sannan za ta ɗauke wannan wahalar da zaka sha, kafin ka cimma muradinka"
Ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "In dai mata ne gasu nan kamar jamfa a jos, tayaya zan gane wadda ka ke nufi?"
Malam Gambo ya numfasa ya ce "Wadda namiji bai taɓa kusanta ba ake so, kuma idan aka samo ta sai na duba ranar sa'ar burujanku. Kuma ba a fuska za a gane mai irin tauraron da nake faɗa ba. A samo mai suna Nadiya, ko ɗausiyya, ko badariyya"
Alhaji zailani ya ce "Ni yanzu malam ina zan samo waɗannan sunayen?"
"Bincikawa za ka saka ayi, ko Asma'u ma zai yi, amma shi ma da sharaɗi, idan aka samo ɗin sai na lissafa adadin sunanta da na mahaifiyarta na tabattar da haɗuwar aikin"
"Shikenan malam, in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina, zan samo in sha Allah, ga wannan ba yawa" yayi maganar yana ajiye masa kuɗi a kan shimfiɗarsa.
*****
Ummi ce ta kalli Nana a ɗan fusace ta ce "Wai nuƙu-nuƙun me ki ke yi ne haka Nana?"
"Wallahi Anty ummi ba na son zuwa wurin maganin nan ne, idan ki na da niƙab ki bani na saka, kar na je wanda suka sanni su ganni"
Sheƙeƙe ummi ta kalli Nana ta ce "Au to sai me, ba neman lafiya ki ka je ba, duk wanda ya ce ya sanki shi uban me ya kai shi? Ki wuce mu tafi dan Allah"
Jiki a sanyaye Nana ta bi Ummi, sai dai gaba ɗaya ranta babu daɗi, sai dai ta wani ɓangaren tana ƙarfafar zuciyarta a kan wataƙila ta dace da maganin.
Maƙil suka je suka tarar da gidan mai maganin, tamkar ana rabon gafara, mata ne suke ta shiga suna fita.
Suka samu wuri suka zauna, wasu a shigo da su a rirriƙe, wasu kuma da ƙafafuwansu. Ga manyan mata masu shigar alfarma da kuma yaku bayi.
Wasu na ta tumamin iskokai, wasu na kwancez Nana dai ta raɓe ta yi shiru a gefen ummi, kasancewar Ummi ba halinsu ɗaya da Nana ba, tuni ta saki jiki suna hira da matan wurin, wannan ta ce matsalar yara ce ta kawota, wannan ta ce matsalar miji, wasu kishiya wasu larura, wasu su ce mayu ne suka kama su, wasu kuma matsalar rashin mijin aure ne ya kaisu.
Nana ta din ga nazarin matsalolin daki-daki, ita a tunaninta matsalar rashin lafiya ce kawai za ta kai mutum wurin mai magani, wadda suke samun saɓani da miji maganin me za a bata, ban da ta kai wa Allah kukanta?
Ummi da wayo da dabara, da iya daɗin baki da hira, ta yi wa matan nan wayo, ta ce Nana zata shigar a gani ba ta da lafiya, kwananta uku ba ta magana, kasancewar tun da suka zo ba ta ce uffan ba.
A tsanake yake ƙare masa kallo, yadda ya zauna ya tanƙwashe ƙafafuwansa, yake ta wasa da yatsun hannunsa, yaƙi ɗagowa su haɗa ido.
Ya mayar da idanunsa kan Habu, da yayi shiru yana jiran bayani daga bakin mutumin.
"Wannan ciwon nasa gaskiya ba zan ɓoye maka ba, idan na matsa ni zan shiga matsala, sai dai ku bincika wani wurin"
Cikin damuwa Habu ya ce "Yanzu babu yadda za ayi ace ko sunansa ya tuna? Ya san duk wani abu da ya shafi rayuwar yau da kullum, amma ya manta duk wani abu da ya shafe shi"
Mutumin da yake zaune a kan sallaya, "Ka san wa ka kawo mini kuwa? Anya ka san waye?"
"Na sani" Habu ya amsa cike da ƙwarin gwiwa, cikin gurɓatacciyar hausar sa"
Mutumin yayi murmushi ya ce "Ka san dai abin da ka sani, ka bar shi a haka kawai kar ka matsa sanin abin da yake a ɓoye" jiki a sanyaye habu ya kalle na zaunen ya ce "Tashi mu tafi" ya yinƙura ya tashi, ya tsaya ya kalli malamin ya saki murmushi ta cikin rawaninsa suka fice.
Babu tsammani Nana su na tsaye a ƙofar shiga wurin mai magani, wasu mutane suka fito, ƙafafuwansa kawai ta kalla ta ji jikinta ya saki, zuciyarta ta tsinke ta sulale za ta faɗi a wurin, Ummi ta riƙe ta da sauri tana salallami.
A hankali Nana ta bi bayansa da kallo kasancewar ya riga ya wuce, zuciyarta ce ta raya mata ta bishi da gudu ta ga waye, daina ganin kowa ta yi sai itakaɗai a cikin sahara, sai kuma shi wannan mutumin da ba ta ga kowaye ba, yana tafe yana jan akalar raƙumi ya yi nesa da ita, tana hango shi a can nesa sai kuma manyan sawayen raƙumin da nasa.
"Nana" ta ji muryar ummi a kunnenta, ta buɗe ido ta kalle ta a hankali ta kalleta.
"Sannu Nana kin tashi" ba ta amsa ba ta ɗaga kai ta gansu a gidan Ummi.
"Anty yaushe muka dawo?"
Ummi ta ce "Hmm tun ɗazu, ai tun kafin mu shiga wurin mai maganin, ki ka sume, ya ce manyan dakarun aljanu ne a kewaye da ke, mu na shiga ya gansu"
Cikin mamaki Nana ta ce "Ya ga su wa?"
"Aljanun mana" ta bata amsa cike da ƙwarin gwiwa.
"Dama mutum yana iya ganin aljani a suffarsa?"
"Ban sani ba, tambaya dawanau, yanzu ga magunguna nan da hayaƙi kowane zan nuna miki yadda za ki yi amfani da shi, ki ci abinci muje na raka ki gida" Nana ta jinjina mata kai kawai, amma bakinta akwai tarin tambayoyi.
Da yamma Ummi, ta taso Nana a gaba domin ta rako ta gida. Ko da suka je gidan, mamaki ne ya cika Nana, ganin an zube kayan aikin gini a ƙofar gidansu, a iya tunaninta Baba ba shi da wata hanyar da zai samu kuɗaɗen da za ayi musu wannan gyaran.
"Nana, haka gidan ya koma? Ummi ta yi maganar cikin mamaki.
"Eh, sai ma kin shiga, rijiya ta haɗe da masai, amma na ga an kawo kayan aiki ban san a ina aka samo su ba"
Da haka suka shiga gidan da salallama, Suwaiba da take wanke-wanke ta ɗago ta kalle su, ta ce "Too yau kuma Allah ya yi miki dawowa daga yawon kenan?"
Ummi ce ta ce "Wane irin yawo kuma?"
But Mama ta fito daga ɗaki ta ce "To ina ta tafi idan ba yawon ba? Wa ta gaya wa za ta je wani wurin? Kwana biyu babanku ya hana mu sakat, saboda ba a ganta ba, ana ta cigiya a unguwa, dama na gaya masa wani wurin ta yi"
Har Ummi ta ɗauki numfashi za ta yi magana, Baba ya yi sallama.
Suka amsa masa baki ɗaya, baki sake ya bi Nana da kallo, ya ce "Nana daga ina ki ke? Ina ki ka tafi baki gaya mini ba? Ko wurin uwartaki da ba ta san muhimmancin ki ba ki ka wanke ƙafa ki ka tafi?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "Haba Baba, dan Allah ka tsaya ka ji mana, ka san halin da take ciki na rashin lafiya, shekaranjiya na je ɗaukko yara daga makaranta, ina komawa gida na tarar da ita, a baje a ɗaki ƙafafuwanta duk jini ko takalmi babu,