BUZU BOOK1 COMPLETE Hausa Read Novels By Aysha Cool.txt

Author :  Aysha Cool Category :  Hausa Read

Chapter   44 / 64

129K to 132K   out of 190K words

Sayyid ya ja hannunta, zuwa cikin asibitin. Sagir ya miƙe da sauri ya bi bayan su, saboda ga Haidar a gurin Nana, shi kuma ya ja Nana sun yi ciki ba sallama ba komai.

A ƙofar ɗakin suka tsaya, Sagir ya ƙaraso ya ce "Bari na yi wa Mummyn magana" ya shiga cikin ɗakin, Nana ta dubi Sayyid ta ce "Daga tsayawa tambaya, sai ka ja hannuna mu tafi ai ba zai ji daɗi ba"

Wani mugun kallo ya yi mata, da ya tilasta mata yin shiru da bakin ta.

Hajiya Amina ce ta fito fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin "Ga 'ya ta, ga 'ya ta" ta rungume Nana. Nana ta durƙusa har ƙasa tana gaida Hajiya Amina.

"Lafiya ƙalau Nana, kin ga yadda ki ka yi kyau tubarkallah? Haidar yau ga Nana"
Ya yi murmushi yana sake riƙe hannun Nana.

Hajiya Amina ta ce "Allah sarki, tare da mai gidan ku ke ashe, mu na ta ƙin abin nan da ganin an zalunce ki, Allah dai ya ƙulla lamarin. Sannu ka ji ya gidan?" Hannu ya ɗaga wa Hajjya Amina tare da risunar da kansa ƙasa cikin girmamawa, ba tare da ya yi magana ba.

Nana za ta yi magana, mijin Shukura ya leƙo ya kalli Nana ya ce "Ta ce ki shigo" mamaki ya kama Nana, amma ta ɓoye hakan. Ya karɓi Haidar saboda kar ta shiga da shi, ya damu Shukura. Nana ta shiga ɗakin da sallama, babu haske sosai a ɗakin, amma ana iya ganin komai da yake ɗakin. Nana ta ƙarasa gaban gadon da Shukura take. Sai dai ta ɗan tsorata ganin Shukura duk a kumbure.

"Sannu Maman Haidar, ya ƙarfin jiki?"

Ta yinƙura da kyar, Nana ta taimaka mata ta jingina da jikin gadon ta ce "Jiki da sauƙi Nana, dama za ki zo duba ni?"

"Haba Maman Haidar, me zai hana? Ni ban za ci za ki kawo yanzu ba ki haihu ba ma. Sannu" Ta jinjina kai ta dudduba ɗakin ta ga daga ita sai Nana a ɗakin. Ta kama hannun Nana ta ce "Na san a zamana da ke, wataƙila na yi miki abubuwa marasa daɗi, duk da ina yaba ɗawainiyar da ki ke yi da Yarona. Sai dai kowane mutum akwai irin baiwar da Allah ya yi masa, komai kallon ƙasƙancin da ka ke yi masa.
Wannan maganganun nawa, ba sa rasa nasaba, da yawan miyagun mafarkin da nake yi da ke"

Gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta kalli Shukura ta ce "Da ni kuma?"

Sai kuma Shukura ta rikice, ba ta san ta ina za ta fara yi wa Nana wannan bayanin ba, amma ta dake ta ce "Mafarkai nake yi marasa daɗi, kuma ina yawan ganinki kin zo za ki taimaka mini. Ni dai kawai ki saka ni a addu'a a tsorace nake, ji nake yi tamkar zan bar duniya, ba zan rayu ba".

"A'a maman Haidar, kamar ba wayayyi ba, mafarki fa ba gaske ba ne ba, duk da wasu lokutan ishara ne, amma mafarkin annabawa ne yake ɗari bisa ɗari gaskiya. Sai kuma wasu bayin Allah da a kan yi wa ishara a mafarki. Wasu lokutan shaiɗan ne kawai yake wasa da hankulanmu, amma ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki babu wani mai yi sai Allah, kuma babu wanda ya isa ya yi miki abin da Allah bai yi miki ba. Sannan in sha Allah zan saka ki a cikin addu'a ba dan ki yarda cewa ganina da ki ke a mafarki a zahiri nice zan taimake ki ba, Ubangiji za mu nufa da buƙatunmu baki ɗaya, shi zai magance koma mene ne, ki kwantar da hankalinki dan Allah"

Shukura ta jinjina kai ta ce "Haka ne, na gode sosai da sosai Nana, na gode"

"Ba komai Allah ya ƙara afuwa, bari na je, na ji an ce ba a bari a shigo a gan ki"

"To shikenan na gode" ta ji daɗin kalaman Nana, mussaman da ta yi ta nanata mata, mafarki ba gaskiya ba ne, wasu lokutan sharrin shaiɗan ne kawai.

Nana ta fito daga ɗakin, jikinta duk a sanyaye.

Hajiya Amina ta taso tana faɗin "Nana kin fito?"

"Eh Hajiya, Ubangiji Allah ya bata ingantacciyar lafiya, Ubangiji Allah ya raba ta da cikin nan lafiya"

"Amin ya Allah Nana"

"A'a Hajiya ina Haidar ɗin?"

"Babansa ne ya tafi da shi yanzun nan"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kash, ban gama ganinsa ba Hajiya"

"Ki yi haƙuri, jiransa ake yi, yana tafiya da Haidar ne gurin kakarsa ake kai shi, ni kin ga ga jinya, abin zai yi mini yawa ne. Amma in sha Allah zan saka a kawo miki shi har gida."

"To shikenan, ga wannan a bawa yarona, wannan kuma a saya wa Maman Haidar wani abin, ban san me take so ba"

Hajiya Amina ta ce "Nana har da ɗawainiya har haka, dan Allah ki bari kar ki takura kan ki, zuwan ma da ki ka yi na ji daɗi sosai da sosai "

Nana ta ce "A'a Hajiya, idan ba ki karɓa ba ba zan ji daɗi ba, dan Allah ki karɓa"

Hajiya Amina fuskarta ɗauke da murmushi ta karɓa ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, ki yi wa mijinki godiya ma ya ba wa Haidar kuɗi, Allah ya saka da alkhairi. Na ga haryanzu ba ya magana"

Nana ta ɗan saci kallonsa, ta yi murmushi ta ce "Ba komai Hajiya"

Ganin hirar t su ba zata ƙare ba, ya sanya shi yin gaba, Nana na ganin ya yi gaba, ta yi wa Hajiya Amina sallama a gurguje, ta nufi hanyar da ya bi.

"Shi ne za ka yi gaba ka bar ni?" Ya waiwayo ya kalle ta ya ci gaba da tafiya.

Ta tsaya tana yi wa Nurses ɗin gurin sallama, ya ja ya tsaya tare da waiwayowa yana hararar Nana. Ta yo gaba tana murmushi, tare da mamakin yadda yake so ta ƙarfin tsiya sai ya mayar da ita irin sa, na rashin kula mutane.

Yana zuwa bakin ƙofar fita, ya ja ya tsaya, Nana ta ƙaraso tana ƙoƙarin duba, abin da ya hana shi fita amma ya tare ta, shi bai shiga ba, kuma ba dawo ba.  Ta leƙa ta gefensa, ta ga mene ne ya hana shi wucewa, kawai ta ga Alhaji Zailani, tare da Doctor Sharif, a take gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ja ta tsaya cike da razani da fargaba.

Ayshercool
08081012143
38

Alhaji Zailani ma gabansa ne ya faɗin, cikin fargaba yake bin ƙwayar idon Buzun da kallo, tare da mamakin ganinsa a gurin a dai-dai wannan lokacin.

A hankali Sayyid ya ja da baya, taku biyu, ya sanya hannunsa ya riƙo Nana ta bayansa, ya ba su hanya.

Alhaji Zailani ji yayi tamkar an zare masa lakar jikinsa, jikin nasa ya yi wani irin sanyi, wani abu mai kama da tsoro ya shige shi. A hankali ya taka ya shigo, yana ƙoƙarin kallon Nana da ke tsaye a bayan Sayyid, amma Sayyid ɗin ya hana hakan, saboda yadda ya ƙare babbakewa ya kare ta.
Ita kanta Nana ji ta yi yanayin ta na ƙoƙarin canzawa, ta saka hannu ta riƙe na Sayyid, tana addu'a a cikin zuciyarta.
Wani irin baƙin ciki ya mamaye zuciyar Alhaji Zailani, ganin yanzu wannan Buzun ne mijinta, da ya aure ta ya san da yanzu buƙatar sa ta biya, wani abin yake hari ba wannan ba, amma Mahaifinta ya yi masa sagegeduwa.
Doctor Sharif ya ce "Alhaji lafiya kuwa?"

"Eh lafiya ƙalau" Har Alhaji Zailani ya yi gaba, ya tsaya ya sake waiwayowa, amma ya sake ido huɗu da Sayyid, ya kange Nana, ya kare ta babu yadda za a yi ya iya hango Nana yadda yakamata. Sai da Sayyid ya tabattar Alhaji Zailani ya bar gurin, sannan ya waiwayo ya kalli Nana, yadda duk jikinta ya yi sanyi, ya kamo hannunta suka fita waje.

Bai dai ce mata komai ba, ta tare musu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai su.

Gaba ɗaya Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ta rasa dalilin da ya sanya, gaba ɗaya ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Duk da tana zaton hakan baya rasa nasaba da mugun nufin da Alhaji Zailani ya taɓa nuna mata, amma ta rasa dalilin da ya sanya gaba ɗaya take nema ta rikice, ta fita daga hayyacinta.

A hankali ta kwanta a jikin Sayyid. Cikin damuwa ya dube ta, ya dafa ta ya ce "Ba lafiya ne?"

Ta ce "A'a"

"To Meyafaru?"

"Ba komai" ta furta a hankali kamar mara lafiya.

"Ko mu koma gida ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Sannu" ta jinjina masa kai.

Sai da suka je daf da titin unguwar su, sannan ta tashi daga jikinsa, tana kallon titin nasu.

Suka je gurin da za su sauka, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa wa mai Napep ɗin su ka tafi.

"Sayyid"

Ya waiwayo ya kalle ta.

Sai kuma ta yi shiru, dan rasa me za ta ce masa ta yi.

Tsayawa ya yi yana ƙare wa ƙofar gidan su Nana kallo. Ko ina faci ga uwar kwata a layin.

"Bari na shiga na yi musu magana, sai ka shigo"

Ya jinjina mata kai ya ce "Zan je masallaci "
Ta ce "To shikenan, a yi mini addu'a"
Ya ɗaga mata hannu, tare da jinjina mata kai, ita kuma ta shiga cikin gidan.

Sallama ta yi, Nasiru yana tsakar gida yana goge takalminsa, yana ganin Nana ya tashi da gudu ya nufe ta.

Nana ta rungume shi tana murmushi, "Nasiru ya garin?"

"Lafiya ƙalau"

"Ina mutanen gidan ne?"

"Mama ta ɗan fita, Baba kuma ya je masallaci"

Nana ta ce "Samo mini tabarma na zauna a nan, ina su Jamila?"

"Jamila daga warkewarta ta tafi yawo, Suwaiba ma ba ta nan"

"Ohh ya jikinta kuwa, mu ka yi waya da Ummi, ta ce mini tun da ku ka dawo ba ta da lafiya "

Nasiru ya ce "Eh, amma ta warke, Mama ta ce wai me magani ya ce Aljani suka yi wa laifi. Aka yi sadakar ƙosai, aka dafa zakara aka bin...

"Ammm ya jikin Baba kuma" Nana ta katse maganar Nasiru.

"To ga shi nan dai, yanzu zai shigo ai ki gan shi"

Nana ta ɗaukko wayarta ta ce "Nasiru ga wayata, ga kuɗi ka yo mini turin fina-finai dan Allah" ya karɓa ya miƙe tsaye tare da faɗin an gama yanzu kuwa.

Nana ta tashi ta fara tattare tsakar gidan, saboda yadda aka bar shi kaca-kaca. Ta gama sharewa Baba ya yi sallama, ta ɗago ta kalle shi. Da ƙyar yake taka ƙafarsa yana bin bango. Ya tsaya sororo ya ce "Ke me ki ke yi a gida kuma?" Duk da Nana ba ta ji dadin tambayar da ya yi ba, saboda ta san yana tunanin ko auren ya samu matsala ne, amma ta yi murmushi ta ce "Baba duba ku na zo yi" Ta yi maganar tana gyara masa tabarma a tsakar gida.

Ya ƙarasa ya zauna da ƙyar, Nana ta koma gefensa ita ma ta zauna ta ce "Sannu ya jikin naka?"

"Jiki ga shi nan mu na lallaɓawa abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa"

Ta kalli ƙafafuwan nasa ta ce "Wacce ce take ciwon a ciki?"

Ya ce "Duka, sai dai wannan ta fi ciwon" ya yi maganar yana nuna mata ƙafarsa ta hagu.

"To Baba ka je Asibiti?"

"Da wane kuɗin zan je Asibitin? Na gargajiya zan koma, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ta dawo da ke gidan nan?"

Nana ta yi murmushi mai ciwo tana buɗe jakarta, ta fito da leda tana faɗin "Baba idan matsala ta dawo da ni, ba zaka karɓe ni ba ko? Ai ka yi mini addu'a ka ce Allah ya bani zaman lafiya, in sha Allah matsala ba za ta kawo ni ba sai alkhairi" ta yi maganar tana ɓare dafaffen ƙwan da ta fito da shi daga leda.

Ta gama ɓare ƙwan, ta miƙa wa Baba, ya saka hannu ya amshe, yawun bakinsa na tsinkewa.

"Baba na san ni mai laifi ce a gurinka, na ɓata maka rai a kan abubuwa da dama, mussaman na bijirewa auren waɗanda ka so na aura, amma ina son mu saka a ranmu cewa, dukkanin su Allah bai ƙaddara akwai mijina a cikin su ba. Ni yanzu babban fatana ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, na san dole na fuskanci tuhuma na abin da ya kai ni ɗakin su magadi, amma ba abin da ka ke tunani ba ne Baba, da zan lalace da ban kawo wannan lokacin ban lalace tun a baya ba." Tuni hawaye ya wanke mata fuska, zuciyarta na wani irin tafasa da raɗaɗi. Baba bai ce mata komai ba, sai karɓe ƙwan da yake yi yana lamushewa.
Ta goge hawayen ta, sai da ta ɓare masa dafaffen ƙwan nan guda biyar, ta ɗebo ruwan randa ta kawo masa ya karɓa yana sha.

Ta ɗaura alwala ta yi sallar azahar, bayan ta idar, Nasiru ya shigo gidan yana faɗin "Nana ga wayar ki, an ciko miki ita da fina-finai fal"

Ta yi murmushi ta ce "Na gode yaron kirki"

Mama ta yi sallama ita da Suwaiba, sai da suka ɗan yi turus ganin Nana a gidan babu tsammani.

"Lafiya dai na ganki a gida? Ba dai auren ne ya samu matsala ba"

Nana ta waiwaya ta kalle ta, ta yi murmushi ta ce "A'a ganin ku na zo yi, na gaishe ku, aurena bai samu matsala ba" Mama ta kwaɓe baki tana rataye mayafinta a kan igiya.

Nana har kallon Mama take yi, tana mamakin wai ita ba ta san ƙarara a fili take nuna ƙiyayyar da take yi mata ba.

Nana ta ce "Suwaiba ya ku ka zo gida?"

"Lafiya ƙalau wallahi, mu na dawowa Jamila ta kwanta rashin lafiya"

"Haka Ummi take gaya mini, shi yasa yau na yinƙuro na fito. Nasiru duba idan ya idar da salla, ya shigo ya duba Baban mu tafi, ban yi girki ba"

Nasiru ya ce to.

Suwaiba ta ce "Nana wai waye yake ba ku Abinci? Gidan da ku ke aikin ne suke ba ku?"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a wanda ya ajiye ni ne yake kawowa, ba kuna nan ya kawo muku fura ba"

Nasiru ya ce "Yana waje, na yi masa magana bai kula ni ba"

Nana ta yinƙura ta ce "Bari na yi masa magana"

Yana zaune a wani dakali da yake kallon gidan su Nana.

Yana ganin ta fito ya miƙe tsaye yana kallon Nana.

Ta ƙarasa ta ce "Sayyid, zo mu je ku gaisa da Baban"

"Wai in shiga?"

Ta ce "Eh, ku gaisa da Babana ka duba shi"

Nana ta yi gaba ya bi bayanta,

Gaba ɗaya suka zubo masa ido, sai dai kansa a sunkuye, har suka isa gaban Baba.

"Sannu" ya furta a hankali yana tunanin ko haka ya kamata ya ce?

"Yauwwa sannu, ya iyalin?"

Ya ce "Alhamdilillah"

Baba ya ce "To madalla"

Nana ta ce "Sayyid, ga ƙanwata wadda su ka zo ranar, ga mamana, ga kuma Nasiru da suka zo a tare"

Bai kalli inda Mama take ba, ya ce "Sannu"

Yanzun ma kwaɓe baki ta yi ta ce "Ji wata irin gaisuwa, haka ake gaida sirikai?"

Nana ta ce "Ki yi haƙuri, ba hausa sosai ne"

Buzu dai bai tanka musu ba, ya miƙa hannu ya ɗora a kan ƙafar Baba, ya ce "Allah ya sauwwaƙe"

"Amin na gode" ya ɗan jima yana kallon ƙafat, sannan ya ɗauke hannunsa, ya saka a aljihunsa, ya ciro kuɗi ya ajiye wa Baba a gefen ƙafarsa ya tashi tsaye.

Nana ta bi kuɗin da kallo, ba tare da ta san ko adadin nawa ba ne ba.

Baba ya ce "Duk wannan haka, to na gode sosai Allah ya yi albarka"

Nana ta ce "Baba bari mu tafi gida, Allah ya baka lafiya ya ƙara afuwa, dan Allah a gaida Jamila idan ta dawo"

Sayyid tu ni ya yi waje, domin shiga gidan su Nana ji ya yi tamkar ya yi tsirara, gaba ɗaya idanun mutanen gidan da bai saba da su ba ya ji ya takura masa.

Suwaiba ta ce "Ke Nana wai mijin nan naki kamar dodo, baya sauke wannan takunkumin na fuskar shi, ko ba shi da haƙora ne?"

Nana ta yi dariya ta ce "Biyo ni waje na saka ya sauke miki rawanin ki gan shi. Baba Allah ya sauwwaƙe idan Jamila ta dawo a yi mata sannu" Nana ta ja takalmanta ta yi waje.

Tana fita waje, ta yi karo da Gaddafi. Turus Nana ta tsaya cikin tsoro, sai ma ta rasa me za ta ce masa.

"Nana me ki ke yi a gida?"

"Zuwa na yi duba Baba, ina wuni?"

"Lafiya ƙalau, ya ki ke ya gidan?"

"Lafiya ƙalau, ashe ka dawo"

"Eh na dawo shekaranjiya" Nana ta yi tsuru-tsuru, tana hango Sayyid da ya tsaya yana kallon ta, ya tsuke fuska tamkar ya fashe.

"Amm ai tare ma muke da shi" ta faɗa cikin kame-kame.

Gaddafi ya waiwaya, ya kalli Buzu ya mayar da idonsa kan Nana ya ce "Amma babu wata matsala dai ko?" Nana ta jinjina masa kai.

Gaddafi ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko kuɗi ya miƙa mata ya ce "Ga wannan, kya sai wani abun"

Ta saka hannu biyu ta karɓa, tana mamakin yadda duk Gaddafi ya canza.

"Nana duk yadda za a yi, ki riƙe auren ki, ki ƙaddara wannan shi ne zaɓi mafi alkhairi da Allah ya yi miki, kin san zaman gidan nan namu ba daɗi ne da shi ba"

Nana ta jinjina kai ta ce "Na gode sosai da sosai Yaya"

Ta nufi inda Sayyid yake, idanunsa kawai suka tabattar mata da a hasale yake.

Har suka je gida bai sake tanka ta ba.

Su na zuwa a gurguje Nana ta yi sallar la'asar, ta ɗora girki, dan ba su ci komai ba.

Shi kuwa tuni ya haɗa kayan shayinsa, yana ta tafasawa yana sha.

Ta ɗaga labule ta ce "Sayyid, na gama girki, ka zo ka ci" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayinsa.

Sai da ya gama jan ajin, sannan ya shigo ɗakin, ya ɗauki nasa abincin ya fara ci.

*****

Mutumin yana zaune a kan kujera, a wani katafaren falo, ya ƙare wa Jamila kallo ya ce "Wannan ce yarinyar?"

Hajiya Sa'a ta ce "Ita ce ranka ya daɗe"

"Kuma kin tabattar za ta riƙe amana? Ba za ta tona asirin ƙungiya ba?"

"Ƙwarai kuwa, na yi mata duk abin da ya kamata"

Ya yi dariya ya ce "Babu laifi, wannan Shekarar da ita za mu yi taronmu na shekara"

Ita dai Jamila ba ta iya cewa komai ba, sai tsananin mamaki, ganin daular da ba ta taɓa tunanin akwaita ba.

Bayan Hajiya Sa'a sun gama magana da mutumin, ta ɗauki Jamila su ka fita.

"Hajiya yanzu dama haka garin Abuja yake?

44 / 64