Author : Aysha Cool Category : Hausa Read
sama-sama.
"Waye ni?" Ya yi maganar cike da mamaki, yana kallonta.
Ta ce "Eh shi nake son sani, ba na gane abubuwan da suke faruwa, ka yi mini bayanin waye kai? Daga ina ka ke? A ina danginka suke? Saboda na samu nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali ka gaya mini"
"je ne sais pas (ban sani ba) ni ma haryanzu ban san waye ni ba"
Ta buɗe baki za ta yi magana ya riga ta ta hanyar cewa "Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya"
"Ni ba ni da nufin ɗaga maka murya, amma ka yi mini bayani, ba na gane kan yadda al'amura suke faruwa, ta yaya za ka din ga bi na cikin mafarki kuma... Sai kuma ta yi shiru, ganin yana sauraren ta da mamaki a fuskar sa.
"Kuma me?"
"Ka din ga tsorata ni" ta ƙarasa a sanyaye.
"Ni kuma? Ta yaya zan bi ki mafarki? Mafarki ba gaske bane ai, kuma wani ba ya shiga baccin wani. Kuma me na yi na.." sai kuma ya yi shiru, ya kasa ci gaba maganganun da yake son yi, suka tsaya a iya ƙirjinsa da maƙogwaronsa.
A ƙoƙarin sa na ya yi maganar, kawai sai ya fara tari, ba tare da maganar ta fito ba. Sai kuma Nana ta rikice ta fara dana sanin abubuwan da ta gaya masa. A take Ƙaisar ya faɗo mata. Ta san babu abin da ba zai iya aikatawa ba, duk domin ta amince da abin da yake so.
"Sannu, ko na baka ruwa?" Ya girgiza mata kai ya fita.
Kawai ta zauna ta tattara hannunta, ta zabga uban tagumi ta ma rasa mene ne abin yi, a tsakanin shi da Ƙaisar waye yake raina mata hankali.
Tun da take ta taso, ta fara ganin Ƙaisar a siffofi daban-daban, bai taɓa yinƙurin yin makamanciyar wannan alaƙar da ita ba, ko a farke ko kuma a bacci. Ita hasalima idan ana irin wannan zantukan har mamaki take yi, ba ta taɓa jin wani abu mai kama da feelings ba, sai da aka yi mata wannan auren, ta fara rayuwa inuwa ɗaya da wannan Buzun.
Sai dai yadda mafarkin nata ya kasance, tamkar zahiri ba mafarki ba, tun da har ta farka ta tarar sakamakon abin da ya kwana a zahiri.
Guntun tsaki ta ja, ta tashi da ƙyar ta fara gyaran ɗakin.
Da ta gama ta shirya cikin hijjabi ta fito harabar gidan ba ta gan shi ba, kawai ta yi shigewar ta cikin gidan.
A falon gidan ta tarar da matar, tana mopping, Nana ta gaisheta. Ta ɗan saki fuska ta amsa ta ce "Kwana biyu ba ki shigo ba"
Nana ta ce "Ba ni da lafiya ne, kawo na yi miki"
"A'a ba komai, kar ki damu zan goge" Nana ta ƙarasa ta karɓa ta ce "Bani zan goge. Masu aikin naki ba su dawo bane?"
"Wallahi tsoron su nake ji ne, tun da suka yi mini sata ne, su ka gudu sarƙoƙinmu na gold kaf suka sace. Shi yasa yanzu nake ƙoƙarin mu yi komai da kanmu falon ma sai a yi sati ba shara, tun da ba yara"
Nana ta karɓi mopping, ta goge ɗakin tsaf, sai dai ta din ga jin jikinta wani iri babu daɗi.
Har su Tv duk Nana ta karkaɗe ta goge mata, bayan ta gama sai ga wani saurayi mai kama da matar ya shigo, da gayyar abokansa.
Bayan Nana ta gama da falon ƙasan, matar ta ce "Dan Allah taimaka ki karkaɗe mini falon saman ma"
Nana ta ce "Babu damuwa" ta hau saman benen, sai dai hawanta ke da wuya, ta ƙara jin jikinta babu daɗi, kamar za ta fita hayyacinta. Sai ta fara sauri ta yi ta kammala, ta kammala kafin wani abin ya faru.
Ga mamakinta ta ga wata matashiyar budurwa, za ta ɗan girme mata, ta fito daga wani sashi na ɗakunan saman benen, tsiga-tsigal da siraran ƙafafuwanta ta saka mini skirt sai vest a jikinta.
Nana ta kalle ta ta ce "Sannu ina kwana" Sai a lokacin ta kula da Nana ta ce "Yauwwa" ta nufi wata ƙofa.
"Siyama" matar ta kira sunanta. Cak ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am"
"Wai Yusra ba za ta fito ta karya ba ne?"
Siyama ta ɗan ɗage kafaɗa ta ce "I don't know"
Matar ta ɗauki wayar ta, ta danna sannan ta kara a kunnenta.
"Ki fito falo, ina son ganin ki" ta ajiye wayar, tana mita ƙasa-ƙasa. Nana a ranta ta din ga mamakin, da mata kamar wannan a gida, amma a ce saboda babu mai aiki an yi sati ba a yi shara ba.
Nana ta nemi guri ta yi zamanta a kan carfet, tana kallon t.v. sai dai har ta shafe lokaci a zaune, ba ta ga wadda aka kira ɗin ta fito ba.
Aƙalla Nana ta kai awa biyu, tana kallon film a MBC2 na divergent. Sai da aka gama ta yinƙura ta tashi ta ce "Na tafi"
Matar ta ce "Har za ki tafi? Duba dining akwai ragowar bredi, ina ga har da sauran dankali ma ko za ku yi amfani da shi"
Nana ta yi murmushi ta ce "A'a Hajiya na gode sosai, idan na tafi da shi sai dai na ajiye, a ƙoshe muke sai anjima" ba ta ma jira mai Hajiyar za ta ce ba, ta yi waje abin ta, tana jinjina rainin hankalin matar, dan wulaƙanci ma ita za a bawa ragowar buredi.
A harabar gidan ta hango shi yana ta kaiwa yana komowa, ita tun da ta samu kallo ma har ta manta da shi. Wani irin kallo ya yi mata da sai da ta ɗan tsorata. A hankali take takawa tana satar kallonsa, har ta wuce bai kula ta ba, bai kuma bi ta ɗakin ba.
*****
Alhaji Fatuhu ne yake zaune yana kallo, ya ɗan kalli matarsa Fadila ya ce "Kin an yi wa malamr su Muhsin aure kuwa?"
Ta ce "Haba dai?"
"Ƙarya na yi kenan?" Ta dafe bakinta da sauri ta ce "Afuwan"
Ya ce "Haka na ji a bakin Yaya Sa'a, ashe wai ta santa"
Fadila ta ce "Haka na ji ranar da ta zo gaisuwa, amma ba ta kyauta ba, abin babu gayyata"
"Ni tun kwanaki ta ce mini za ta yi auren ai, na ma zata tuni an yi fa, ashe sai kwanan nan aka yi, amma duk da haka zan bayar da wani abun a bata"
"Gaskiya yakamata, ni ma zan bayar, ina fatan Allah ya kawo rabo, ta yi yaronta takwara"
Ya ɗan yi murmushi yana tuna yaron nasa.
Ta ce "Yauwwa Daddy, ya ciwon kan kuwa?"
Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ke dai a yi sha'ani kawai, daurewa nake yi amma duk da haka Alhamdilillah"
"To sannu Allah ya ƙara afuwa"
"Amin babyna" ta yi murmushi tana ɗan yi masa fari da ido.
*****
Yunwa ce ta ishi Nana, ita ba azumin ba, amma ba ta ci komai ba, ta ɗora girki, sai dai fafur ya ƙi shigowa ɗakin.
Muryar Habu ta ji yana ta kwaɗa sallama, ta saka hijjabi ta leƙa, ta ga Buzu ba ya gurin. Ta amsa sallamar ta ce ya shiga.
Ya shiga yana sake sallama, ta amsa masa ta ce "Ina ga ya ɗan fita ne"
Cikin damuwa ya ce "Ya fita kuma, ina yaje?"
Nana ta ce "Nima ban sani ba, amma ai dama yana fita"
"Duk da haka, kar ya din ga nisa, ki din ga hana shi fitar, kin san ba shi da cikakkiyar lafiya"
Nana ta ce "Ta yaya zan hana shi fita, ni ka zo gaɓar da nake son a zo. Ni fa mutumin nan tun da aka yi auren nan, ko sunansa ban sani ba, kullum na tambaye shi sai ya ce mini sunan shi Buzu. Yakamata na san waye shi, a ina ku ke a ƙasar ku? Kuma yaushe za mu je na ga danginku. Tun da a haka tawa ƙaddarar ta zo."
Habu ya numfasa ya ce "Kin yi gaskiya Amarya, shi yasa na yi ta ce miki ki yi haƙuri, ki karɓi ƙaddara, sai a yanzu na ƙara tabattar da wannan ƙaddarar ce ta haɗo mu baki ɗaya.
Magana ta gaskiya, ban san waye Buzu ba, a sahara na tsince shi cikin mawuyacin hali, mai kama da gushewar hankali da ɗimuwa. Yanayin kamaninsa ya sanya na san ɗan uwa ne buzu, kuma buzyen ma kala-kala ne, na ji yana iya hausa ya kuma iya French, shi yasa na tabattar da Buzun Nijar ne. Na yi yinƙurin tafiya da shi Nijar, saboda idan na bar shi a saharar nan, zai iya rasa ransa, ban kuma san da wa zai haɗu ba, dan haka na yi nufin tafiya da shi Nijar, domin neman ahalinsa. Sai dai da na yi yinƙurin nufin komawa Nijar da shi, sai guguwar sahara ta taso, ta rufe hanyar baki ɗaya. Dole na canza hanya na nufo Nigeria, jikina ya bani akwai wani abu, domin duk wata hanya da zan bi mu koma Nijar na kasa samun ta.
Ina da wasu abokai a Nigeria, su na kira suka karɓe ni, da niyyar a taimaka mini, a samo masa magani. Saboda duk abin da na tambaye shi game da shi bai sani ba, sunansa, waye shi, daga ina yake, ina za shi duk bai sani ba. Wasu lokutan zai yi miki abu lafiya kalau na cikakken mai hankali, sai dai ba zai taɓa iya ce miki waye shi ba. Wasu sai ya burkice, ba magana yana ma iya daina gane mutane gaba ɗaya. Ba ya son magana ko da yana normal, sannan wasu lokutan ya kan burkice ya din ga jijjiga. Duk gurin mai maganin da muka je a Nigeria sai a ce ba za a iya ba shi magani ba. Shi yasa tun da aka yi auren nan, za ki ga kusan kullum ina zuwa, ina kawo muku abin amfani, wallahi ina matuƙar tausayinsa ne. Ba shikaɗai ba har da ke ma"
Jikin Nana ya mutu murus, ta ce "Yanzu shikenan ba ku san kowa na shi ba? Me na aura kenan?"
Cikin kwantar da hankali Habu ya ce "Akwai dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ku, da babu wanda ya sani sai shi. Ni kaina na fuskanci ƙalubale baro ahalina na taho Nigeria nema wa wanda ban sani ba magani. Idan ki ka saka hannu ki ka dafa mini a kan wannan jihadin, Allah ne kawai zai biya mu. Idan ba ki amince ba kuma shikenan babu dole, sai na wuce gaba a raba auren, dama mahaifinki ne ya matsa ya sanya aka yi auren dole".
Ba su ankara ba kawai su ka gan shi a cikin ɗakin, ya ajiye abin dafa shayinsa, da kayan dafa shayin, ya juya zai bar ɗakin.
Habu ya tashi da sauri yana faɗin "Tun ɗazu na zo ai, ba ka nan ga kayan dahuwar shayin nan na kawo maka"
Banza ya yi masa ya nufi hanyar fita, Habu ya bi shi da sauri, ya riƙo hannunsa amma ya fizge yana yi masa wani irin mugun kallo.
Ayshercool
08081012143
Habu bai yi zuciya ba, ya sake bin bayan Buzu, ya juya yare, ya tsaya yana yi masa magana, ya din ga zuba babu ƙaƙƙautawa.
Nana kuma mamaki ne ya ishe ta, ganin Yadda Habu ha rikice gaba ɗaya, kuma ita ba ta ga abin da ya yi na ba daidai ba, da zai yi wannan rikicewar kamar mara gaskiya ba.
Ita wasu lokutan har mamaki yake bata, kamar tsoron buzun yake ji, shi da yake taimakonsa amma ba ya ƙaunar ya ga ɓacin ransa ko kaɗan.
Nana ko a jikinta, ba ta ma san yadda suka ƙarke ba.
Sai dai ta yi ta jujjuya maganganun da Habu ya gaya mata. Yanzu shikenan haka za ta ci gaba da rayuwa da mutumin da ba a ma san suwaye danginsa ba? Ko a daɗe ko a jima dole tana buƙatar sanin waye shi, kuma suwaye ahalinsa.
Ba ta taɓa jin lallai tana son ganin Ƙaisar ba sai a wannan lokacin. Ba shiri ta kwanta ta hau bacci, ko za ta gan shi, amma ba ta ga komai ba, har ta gama baccin ta tashi.
Bayan farkawarta ta ga wayarta a gefenta, a lokacin yamma ta yi sosai da sosai. Da sauri ta ɗauki wayar, ta kira lambar Ummi, dan tun da suka zo, ba ta ji ya suka je gida ba.
Sai da ta kusa katsewa, sannan Ummi ta ɗaga.
Nana ta yi sallama, Ummi ta amsa ta ce "Kai, Nana a ina ki ka samu waya?"
Nana ta ce "Dama ina da ita, kin san lambar ki na haddceta, saboda ke ce line 911 ɗi na"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Eh lallai kam, ya ki ke ya mai gidan?"
"Alhamdilillah, ya ku ka je gida, ban samu na kira ku ba, bayan tafiyar ku na ɗan yi rashin lafiya ne"
Ummi ta ce "Alhamdilillah, mun je gida ƙalau. Kai Nana daga zuwa sai rashin lafiya, a dai ciki ba ne ko?"
Nana ta kwashe da dariya ta ce "Dan azaba auren kwanaki sai ciki?"
"Eh mana, tun da ina jin fitsarar da ki ke yi, ranar da mu ka zo"
Nana ta ce "Wallahi kawai cika baki ne, ji na yi za su raina mini hankali ne. Kuma ba na fatan ko alama, a ga ɓaraka a tattare da aurena"
Ummi ta ce "Allah sarki Nana, in sha Allah auren nan, sai ya baki kwanciyar hankalin da ba ki taɓa tsammani ba. Ke Jamila fa babu lafiya fa"
Nana ta dafe ƙirjinta ta ce "Babu lafiya kuma? Me ya same ta?"
"Oho, ni mun yi waya da maman, ban gama gane kan zancen ba. Wai tun da mu ka baro gurin ki, washegari ta tashi ba ta iya tsayuwa, wani abu duk ya feso mata a jikinta".
Nana ta girgiza kai ta ce "Hmm na san cewa aka yi ni ce ko?"
"A'a wai sun je gurin wani mai magani, aljani ne yake hawa kansa ya bayar da magani, ya ce musu wai wani aljani suka yi wa laifi" Kan Nana ya sara, ta yi shiru tana son tuna wani abu, amma ta gagara tuna komai.
Ummi ta ci gaba da cewa "Shi ne ya basu magani, wai ya sha sannan a yi sadakar ƙosai mai zafi da la'asar"
Nana ta ce "Ita sadakar ƙosan ta mece ce, sharaɗin mene ne? Kin ga Mama ba za ta din ga kiyaye irin wannan yawace-yawacen ba ko? Wane irin sadakar ƙosai mai zafi da la'asar?"
"A'a ni ina zan sani, tun da ba ni na ba su maganin ba, ina gefe labari aka bani"
Nana ta numfasa ta ce "Sadaka mahaɗin Addu'a ce, amma wannan sharuɗɗan da ake sakawa ne, ni ba na gane kansu"
"To ni ya za ni tsitsiye ni, labari kawai na ji, ban ma je na duba ta ba"
Jikin Nana a sanyaye ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya sauwwaƙe ya jikin Baban?"
"To da sauƙi, ni rabona da gidan tun biki, amma sun ce yana jin jiki, ƙafar nan tana yi masa ciwo sosai"
Nana ta ce "To shikkenan, zan samu na je na duba su baki ɗaya, in sha Allah, amma jikina ya yi sanyi, na san ciwon Jamila cewa za a yi nice"
"Ke rabu da su dan Allah, ni wallahi na jiye miki daɗin auren nan, Allah ya sanya shi ne mafi alkhairi, amma da zaman wannan gidan namu, ba gara auren ba, kullum cikin bala'i. Ko banza ɗakin ki a cike yake da kayan abinci"
Nana ta ɗan yi shiru, kamar ta gaya wa Ummi halin da ake ciki, na rashin sanin dangin mijinta, amma ta basar. Ta ce "To Allah ya sa mu dace"
na gode sosai ki gaida yaran"
Suka yi sallama, Nana ta tashi ta ɗan yi gyare-gyaren ta, ta ɗauki magic coal ɗin sa da yake haɗawa da gawayi, ya kunna wutar dafa shayi, ta kunna turaren wuta. Ta ɗauki wayarta ta kunna karatun Alqur'ani.
Fafur ya ƙi shigowa ɗakin, sai bayan isha'i.
Ya shigo da 'yar ledarsa, ya ɗauki kwano ya zazzage fruit, ya je ya wanko abin sa, ya dawo ya zauna a gurin zamansa, ya fara ci a hankali.
Nana ta na kallon sa, zuciyarta ɗauke da tunani daban-daban.
Ta dake zuciyarta, ta tashi ta tafi kusa da shi ta zauna.
Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya nuna ya san tana zaune a gurin.
"Ba za ka ci abincina ba ne, ka je ka sayo fruit ka ke ci?" Sannu a hankali yake tauna apple ɗin bakinsa, bai kula ta ba.
"Ni mamaki ma nake yi, idan ka je da yaya ka ke sayayyar, magana ka ke yi musu, ko kuma ni ce kawai ba ka kulawa?"
Ya ɓare ayaba zai kai bakinsa, ta riƙe hannun, ta sauke shi ƙasa a hankali. Ya ɗago idanunsa yana kallon ta. Ta yi saurin sauke nata ta yi murmushi ta ce "Na san na yi maka laifi, bai kamata abubuwan da na gaya maka ba, ka yi haƙuri ina cikin damuwa ne, amma ka yi mini afuwa ba zan sake ba" ya sunkuyar da kansa ya yi shiru.
"Ka yi magana mana" ta yi maganar a raunane.
Ture ta ya yi daga kusa da shi, ya tashi ya bar mata ɗakin. Abin ya yi wa Nana ciwo, sai dai ta tuna bayanin Habu daki-daki, tabbas wasu abubuwan da yake za ka san ba normal yake ba.
Ta tashi zuciyar ta cike da damuwa, sai dai a zuciyarta ta ƙuduri aniyar jure kowane irin ƙalubale, tun da ba duka yake ba, ba kuma zagi yake yi ba, gara zamanta a nan da shi sau dubu, a kan ta koma gidan su.
Ta kunna gas ta ɗora ruwa, domin ta yi wanka kafin ta kwanta, garin akwai yanayin hadari, dan haka akwai sanyi.
Tana ɗan dube-dube, da goge kan mududinta, ta ga ɗan littafin da yake yawo da shi, ko ta ga yana karantawa, da biro a cikin drower mudubi.
Ta ɗauka ta buɗe, ta ga kyakyawan rubutunsa, wani da French, wani da hausa.
"A ba ni kankana, da ayaba na dubu biyu. A bani buredi mai kyau babba guda ɗaya. Ina son wannan jan abin, na kuɗin da na bayar" sai da Nana ta yi dariya, wato duk a rubuce yake sayen abin da yake zuwa da shi. Tana shirin buɗe wani shafin, ta ji wutar gas ɗin na fita da yawan gaske, tukunyar kai na wata irin tafasa kamar ta diro daga kan gas ɗin.
A gigice ta nufi gas ɗin ta sauke, abin ya ba ta mamaki, dan ko mintuna biyar a yi da ɗora ruwan ba, yake wannan tafasar.
Ta juye ruwan a flask, ta sake ɗora wani.
Yana tafasowa ta