Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ma bata bari na shigo mata gidan miji ba, amma sai dai waje ya gama ƙure mata saboda lokacin da Babanku ya aure ni ana saura kwana ɗaya aure yaje ya sanar da ita, kamar zatai hauka duk yadda ta shiga ta fita waje ya riga da ya ƙure duk wani kulle-kullenta baiyi aiki ba, saboda nima ba sakara bace ba haka nan na shigo gidan nan ba, saboda dama tun kan Babanku ya zo neman aure na nasan da labarin Matarshi Asabe, cewar ita ce ke fidda duk wata Macen da zai kawo mata a matsayin kishiya, shi yasa har zuwa yanzu bata ci galabar fitar dani daga cikin gidan nan ba".
Shuru Amina tayi tana yagar Kaza tana jin Inna nata bata labari, wani labarin ma daka ji kai kasan daɗin Kazar da ake ci ne yasa ake bada shi.
*House No 19, Tudun Yola Kano state Nigeria*
"Haj Bharaka kinji abunda nake so ki nemar ma wannan Yarinyar tawa aiki a gidajen da kika saba kai ƴan mata aikatu dan Allah, domin wallahi muna buƙatar aikin ne cikin gaggawa".
Haj Bharaka ta gyara zama tana duban Sakina ta ce.
"Amma wannan ɗiyar Yayar nan taku ce Nana ko?".
"Kware kuwa da gaske Haj Bharaka ita ce".
"Ta ɗan bamu waje zamuyi magana, saboda tabbas akwai gidan da suke son yarinya kamarta sai dai aikin nasu yasha banban da sauran da nake kai Yara aiki, ita wannan aikin babu lallai uwarta ta amince dashi, amma fa Sakina nake gaya miki akwai wasu maƙudan kuɗaɗe da za'a rinƙa biyanta dasu, farkon fara aikin ko za'a bada kusan million ɗaya a fara riƙewa".
A mugun ruɗe Aunty Sakina ta waro idonta waje tana duban Haj Bharaka cike da tsananin mamaki. Kai ashe Sakinar da arziƙi tazo mata?, amma farko ta koreta da yanzu uwarta bata dawo mata da ita ba shikenan da tayiwa arziƙi ƙulli?.
Sakina dake ƙasa kanta a ƙasa tunda taji abunda Haj Bharaka ke faɗa gabanta ya shiga dukan Uku-uku, wata irin fargaba da tsoro ne suka rufe ta, ko dai saida ita Haj Bharaka zata je itayi?, idan ba hakaba yaya za'ai ace daga fara aiki a fara baka naira Million ɗaya haba dai akwai ayar tabbaya a maganar Haj Bharaka.
"Ke tashi ki bamu waje idan muka gama maganar zan kira ki".
Tashi tayi jiki a sanyaye ta wuce ɗakin Sawwama da bata ma gidan ta wuce School tun safe. Ba haka taso ba, taso ace anyi maganar komai a gabanta taji miye yasa Haj Bharaka ke faɗin ba kowanne aiki bane kamar sauran?.
"Haj Bharaka million ɗaya fa naji kina faɗa?, shin wannan maganar haka take ko kuwa?".
"Kamar yadda kika ji na ce haka zancan yake. Amma fa ba'a nan gizo ke saƙar ba, gidan da zan kaita gida ne babba gidan masu arziƙi ne sosai wadda suka ci arziƙi suka tada kai dashi, sai dai fa bawai aiki normal suka so ba, a'a wacce zata auri ɗan mai gidan wadda ya kasance nakasashshe baya iya komai, wani lokacin wani ciwo nashi na tashi wadda yake kawo ma mutum duka, sai dai idan har ciwon nan bai tashi ba ko magana ba iyayi yake yi ba, a haka yake a kwance a kullum fitsari nan kashi nan, shi yasa ake son aura masa Mace wacce zata kula dashi, amma fa sai mai hakurin gaske kawai zata iya zama dashi, saboda ansha kawo masa Mata masu kula dashi suna guduwa saboda basa iya hakurin masa hidima, basa kuma jure uban dukan da yake masu aduk lokacin da ciwon nasa ya tashi, domin idan ciwon ya tashi har shaƙe maka wuya yake da kyar ake kwatar mutum a hannunsa, to sai kawai masu gidan suka yanke cewar kawai ayi masa aure Matarshi ta rinƙa kula dashi, to shine fa kowacce daga cikin family nasu ta ce ba dai ita ba wallahi, sai dai aje can a nemo bare marar gata gaba da baya a aura masa. Amma wallahi Sakina nake gaya miki idan kinga wannan bawan Allahn irin tsananin kyan da Allah ya zuba masa zakiyi mamaki ne, kyau ne dashi harna tashin hankali yadda kika san aljani haka kyansa yake, nifa da naje gidan aka kaini na gano sa kusan zarewa na kusanyi, kawai wannan nakasar tashi ce kawai ta kawo masa cikas a cikin rayuwarsa, amma da ace mai lafiya ne hmm ba ƙaramin namiji za'ai ba tsayayye kuma ƙaƙƙarfa mai kwarjini da haiba za'ai ba a wajan nan, da Mata sai sun kusa hauka akan sonshi, sai dai kash ga yadda Allah yayi shi".
Wani irin goran lumfashi Aunty Sakina ta saki, tunda Haj Bharaka ta fara bata labarin ta natsu ita kawai take saurara.
Zuwa can ta sake sauke wata ajiyar zuciyar ta ce.
"To amma shi a haka aka haifeshi ko kuwa dai daga baya ne ciwon nashi ya same shi?".
"To wannan ne ban sani ba Sakina, ni dai kawai abunda na sani ne na gaya miki".
"Shikenan karki damu zamuyi waya da ita Aunty Nanar, zanyi duk yadda zanyi dole ma ta amince, idanma taƙi dai babu gidan uwar da za'a riƙe mata Yarinyar ai, dole zata sa ta aminta ma".
"To shikenan ni zan wuce idan kunyi magana sai ki taɓo ni kawai a waya".
Tana ƙare maganar haɗe sa miƙewa ta ɗauki wayarta. Har ƙofar waje Aunty Sakina ta rako Haj Bharaka ta wuce........
*TSANIN ƘADDARA, Na kuɗi ne akan Naira ɗari biyar kacal #500, Free pages zai tsaya ne daga na 10 insha Allah, labarin har zuwa yanzu bama a kamo zaranshi ba, dogowar tafiya ce wacce ban taɓa yin irinta ba, har yanzu akwai jaruman da basu kai da fitowa bama, dan haka kayi sauri ka biya naka domin yin wannan dogowar tafiyar da kai, kusan cewa bana taɓa labarin banza a ko yaushe*..
Idan ka shirya biya kudin saika saka kuɗin ka a wannan account ɗin dake ƙasa👇.
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank.
Saika turo shaidar biya ta wannan number ɗin dake ƙasa itama👇.
08130479973
*TSANIN ƘADDARA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
Chapter 10
*House No: 17 Aurora Wrestling Estate Estates Kaduna Nigeria*
Yau ta kama Monday tunda ta tashi take lanƙanji, sai faman ɓata rai take haɗe da turo baki gaba, kwata-kwata bata son wannan aikin da aka haɗa da Ya Hammad wadda yanzu ba zama inuwa ɗaya suke yi dashi ba, idan har sun zauna ɗin ko to tabbas sai yayi mata muguntar tashi.
Ammi ce ta buɗe ƙofar bedroom ɗin ta shigo, turus taja ta tsaya tana duban Intee, sai kuma ta idasa shigowa sosai tana faɗin.
"Wai Intee miye haka ne iyee?, kin san cewa yau Monday harsu Hassan sun wuce wajan aiki hatta Yayanki Hammad ya wuce".
Taɓe baki tayi tana cewa.
"Ammi nima yanzu zan wuce ai saura kaɗan na idasa shiryawa. Amma Ammi su Hassan basa da lectures yau ne?, Ammi gani nake haɗa aiki da karatu kamar akwai wahala a ciki".
Ammi ta zauna bakin bed ɗin Intee ta ce.
"To tunda Abbinsu ya gama yanke hukunci ai babu yadda zanyi, kawai dai munyi magana dashi jiya yake cewa duk ranar da basu da Lectures ne zasu rinƙa zuwa Company ɗin, kinga ai da sauƙi, gara su saba tun yanzu tunda karatun nasu baifi shekara uku su idasa shi ba. Inaga ma idan akai hutu su duka harda su Hanan zasu tafi Niger".
Da wani irin sauri Intee ta waigo tana kamo hannun Ammi tana langwaɓar da kai ta ce.
"Dan Allah Ammi amma harda ni za'a tafi Niger ɗin ko?, wallahi nayi miss ɗin su Mai sunan Baba Allah".
Sakin hannunta tayi Ammi ta ce.
"Kije ki shirya kinfa makara har tara saura kuma kin san halin Yayanki Hammad babu ruwansa idan ya tashi hukuntaki ko sa baki bazanyi ba".
Da sauri ta idasa shirya tasa wata Lifaya ruwan jinin Kare, wacce ba ƙaramin kyau tayi mata ba, Hips ɗinta sunyi bala'in fitowa a cikin lifayar, amma fa a haka sosai ta suturta jikinta, gashi kalar data saka sai taka ƙara haska kalar fatarta, lipstick kawai tasa mai kamar kalar jan baki ja kaɗan sai kuma ta ɗakko kwalli da kyar ta iya sakawa danma Ammi tayi magana ne saboda a gabanta ta gama shirin sai taga bata saka kwalli ba, Ammi ta ce maza ta saka kwalli, tana saka kwalli ba ƙaramin taimakawa yayi ba wajan sake fiddo da ainafin wani irin sirin kyanta, kallo ɗaya idan kayi mata bazaka iya ɗauke idonka akanta ba, tayi wani irin kyau mai fisgar mutum.
A hankali tasa hannunta ta ɗauke jakarta haɗe da ɗaukar key ɗin Motar ta da jiya Abbi ya mallaka mata ita, akan Motar nan sai da aka sake wata rigamar wacce tasa Intee ɗin kuka, har tana cewa da bazata taɓa hawan Motar ba, sai da Abbi ya nuna mata ai shi ne ya bata Motar ba wai Ummu ba dake ta bala'in cewa wai ya fifita Agola akan ƴaƴansa.
Tana fitowa harabar gidan kallo ya dawo kanta ƴan aiki sai maganarta suke suna zunɗanta.
Bata san suna yi bama dan kai tsaye inda Motarta take ta nufa tana wata irin tafiya tata mai cike da natsuwa.
"Kai kai kai Lare ki duba kiga wannan yarinyar fa, neman Maza zata rinƙa zuwa aikin nan ko kuwa? ".
"Kamar ya neman Maza Laure?".
"A'ato idonki tuwo ne a ciki da baki ga yadda taci wani uban wanka ba za'a tafi aiki, sai kace wacce zata je gasar kyau ta duniya".
Da wani irin sauri Laure ta waigo dan ita ta bada baya ne, duk ɗaukarta maganar Intee ce kawai ta kawo mata ba wai ganinta tayi a harbar gidan ba.
Ido waje baki buɗe Lare ke bin Intee da kallo a lokacin da take ƙoƙarin buɗe Motar da ta shiga.
Da kyar ta rufe bakinta ta ce.
"Ah ah dole ki ce haka Laure wannan uban gayu kamar zata je gasar kyau?".
"Ai shine abunda nake ce miki, kinga dole Maza yanzu su rinƙa sintiri a gidan nan, kinga ai da ba fita take ba, yanzu ko akuyar ɗaure ta samu sake, dole kiga ana biyo ta, wannan dai duk wadda zai ɗora idonsa akanta ƙarya yake ya ce baiji wani abuba".
"Ke Laure yo ni ai kaina ƴar uwarta Mace kallonta kawai nake bana son ɗauke ido na akanta tsabar yadda gayunta yayi min kyau, kai ya subhalallahi gaskiya dole ƴan Maza su ruɗe fa a nan wajan, Allah ina gaya miki".
Daga can ƙofar shigowa part ɗin Ummu Maryam ce tsaye riƙe da waya a hannunta, maganar su Lare mai aiki ce ta katse mata wayar data fiddo da ita tana yi.
Fahimtar da wa suke magana yasa ta bata ma san lokacin data waiga inda Intee take ba.
Sadda zata kai idonta wajan dai-dai lokacin Intee tasa ƙafa tana idasa shiga gaban Motar tayi mata key cike da kwarewa taja birki tana nufar tangamemen bakin get ɗin gidan, masu gadi da masu tsaron bakin get ɗin suka buɗe mata get suna miƙa mata gaisuwa tana amsawa harta cilla hancin Motarta tabar gidan kwata-kwata.
Ai Maryam mutuwar tsaye kawai tayi tana kallon yadda take tukin Motar kanta cike da birgewa da tsantsar iya motar da tayi, uwa uba kuma gayun data ɗauka shine abunda yafi tsayama Maryam a zuciyarta.
Yayama za'ai waccar Aljnar Yarinyar tana ɗaukar wannan uban wankan ace kuma Y Hammad yana yin tozali da ita a kullum ai tasan bazai taɓa mata kallon so ba ko birgewa ba, indai yana ganin irin su Intee a gabansa.
Wani malolan baƙin ciki da wata irin tsanar Intee haɗe da jin wani irin bala'in haushinta tsantsa a zuciya, har wasu hawayen baƙin ciki ne taji sun taru a cikin kwayar idonta.
Intee ko cike da kwarewa da taka tsantsan take tukinta da yake tasan Campanyn da Ya Hammad ɗin ke jagoranta kai tsaye babu gargada canta nufa.
Komai an bata na shaidar zamowarta ma'aikaciya a Campany nin, dan haka tana zuwa bakin ƙofar ƙaton get ɗin Campanyn masu tsaron baƙin get ɗin ganin mota suka tsaida ita, gilas ɗin Motar ta sauke tana nuna masu shaidar zamowarta ma'aikaciyar Campany nin, ai ganin wata babba ce a cikin ma'aikatan ma yasa jiki na rawa suka shiga buɗe mata get ɗin suna faman bata girmanta haɗe da kawo gaisuwa, cike da ƴar sakewa take amsawa kamin ta maida gilas ɗin Motar ta rufe taja Motar zuwa cikin harabar Campany nin.
Parking tayi ta a parking lot na Campany nin wadda yake shaƙe da Motoci iri da iri kala da kala.
Akwai ƴan tsirarun ma'aikata wa'inda ke shiga da fice a harabar Campany nin.
Bata damu ba tunda Motarta ta shigo cikin Campany nin wasu dake harabar basu san lokacin da suka tsaya ba suna kallon Motar wacce ta ɗauki hankalin jama'a da dama ko daga fitowar ta gida taga yadda jama'a ke kallon Motar, itama kanta tasan Motar tayi kyau da alama taci kuɗi masu yawa kamin a mallake ta, shi yasa Ummu ta ruɗe tana ta zafga masifa tun jiya, dan har yau bata daina yada masu magana ba duk akan anba Intee Mota, su ko su Hassan dama kowannen su da Motarshi dama.
Kallo ne ya koma kanta gaba ɗaya har masu tsoron get ɗin na ciki sai da suka saki baki da hanci suna bin Intee da wani irin mayen kallo kamar idonsu zai faɗo, iya kyau Intee ɗin ƙarshe ce ata fagen kyau da ɗaukar wanka ga uwa uba kyan dari dana surar jiki, gaba ɗaya ta gama tafiya da imaninsu.
Bata wani tsaya ba ta fara takunta tana tafiya cike da birgewa, ai tafiyar kanta gani suke cike da gayya take yinta, gani suke tajan hankali ce da tsantsar yanga ce kawai, sai dai basu san dama can haka yanayin tafiyar tata take ba.
Ƙofar shiga ainafin cikin Campany nin ta nufa sai da ta ɗan tsaya ta gama tantance ta tukunna ta buɗe ƙofa ce mai amfani da na'urar Camputer, shigarta sai da tahau lifta ta hau da ita hawan farko harta kaita wajan inda take da tabbacin a nan ne Office ɗin Y Hammad ɗin yake.
Tunda Lifta ɗin ta tsaya ta buɗe ƙofa ta fito gaba ɗaya ma'aikatan da suka duƙufa suna aiki basu san lokacin da suka fara binta da wani irin kallon mamaki haɗe da mamakin wacece wannan kuma?, wasu ko tsantsar kyanta da gayun data sha ne ya ɗauki hankalinsu, wasu ƴan Matan ko lokaci ɗaya hassada da jin haushin Intee ya rufe masu zuciya, ganin kai tsaye hanyar Office ɗin data nufa.
Wani ma'aikaci ne ya taso yana cewa.
"Ranki ya daɗe ba'a bin hanyar shiga Office ɗin Ƴallaɓai Hammad kai tsaye sai dole anga P'A nasa, ko Mai taimaka ma P'A nasan, yanzu babu P'A ɗin sai dai matakin P'A ɗin".
Murmurshi kaɗan Intee ta saki tana dubansa kai tsaye ta ce.
"Muje kayi min jagora zuwa Office ɗin mataimakin P'A ɗin".
Murmurshi kaɗan matashin saurayin ya saki mai suna Abdul haka kawai dama tunda Intee ta shigo hankalinsa da tunaninsa yayi wajanta, dama neman abunda zai fara mata magana yake, kawai sai yaga ta nufi ƙofar da zata kaita Office ɗin Ƴallaɓai Hammad, kawai ya sai samu abunda zai fara mata magana dashi cike da zumuɗi ya nufo inda take, ya ɗauka irin ƴan Matan nan ne masu zuwa wajan Ƴallaɓai Hammad ɗin kuma masu wulaƙanci duk ɗaukarsa zata yarfa shi ne sai yaga ta sakar masa murmurshi haɗe da masa magana mai daɗi sosai yaji daɗi, suna tafiya ya ɗan waiga yana duban abokan aikinsa maza yana masu murmurshi haɗe da ɗaga masu hannunsa guda biyu.
Har Office ɗin ya rakata har ciki, sai dai Mataimakin P'A ɗin yana ganinta ya tashi jiki na rawa ya ce.
"Ranki ya daɗe barkanki da zuwa".
Ai Abdul bai san lokacin daya kalli Intee ba cike da mamakinta, ashe wata ce ma a Campany nin?, bai sake tsinkewa ba sai da yaji Idiris yana faɗin ai ita ce P'A ɗin Ƴallaɓai Hammad ɗin ma gaba ɗaya.
Abdul bai san lokacin da ya ce mata ba "kiyi hakuri Ranki ya daɗe ban sani bane, ashe kece sabuwar P'A ɗin Ƴallaɓai Hammad ɗin ma?".
Murmurshinta mai saka ƴan Maza sakin layi ta sakar masa, wadda yasa Abdul ruɗewa yana kallon tsantsar kyan da Allah ya zuba ma Intee ɗin.
Shi kansa Idiris ɗin kyan nata ya ɗan ruɗashi, amma ya maze yana ce ma Abdul zai iya tafiya zai mata jagora da kansa zuwa Office ɗin Ƴallaɓai Hammad.
Abdul na fita Idiris da Intee suka fice suma zuwa Office ɗin.
Intee a mamakinta sai da taga sun sake hawa wata Lifta ɗin lokacin da suka buɗe ƙofar data so buɗewa farko Abdul ya tsaida ita, duk ɗaukarta zata ga Office ɗin kawai idan ta buɗe ƙofar, sai taga ashe wata Lifta ɗin ce zaka sake hawa, sosai taga Campany nin girmansa ya wuce duk tunaninta ko hasashenta.
Tana sauke su Intee ta sake ganin wasu ma'aikatan dake aiki nan dandai su basu da yawan azo a gani.
Nanma tunda suka shigo kallo ake binsu dashi wadda ba Idiris ɗin ake kallo ba Intee ce kawai ake bi da kallo.
Wata ƙofa suka nufa sai da suka tsaya wajan wata wacce sai an nemi izininta tukunna ta sanar da Ƴallaɓai Hammad yasan da zuwanka kamin ku shiga cikin ainafin Office ɗin nashi. Idiris yayi mata wasu ƴan bayane tukunna,
Sai da tayi wasu ƴan danne-danne a Camputer kamin ta ɗaga wani kira tana faɗin.
"Okay Sir".
Kawai ta faɗa tana dawo da dubanta kansu kamin ta ce.
"Ƴallaɓai Hammad yana ciki yana jiranku".
Ta ƙare maganar tana bin Intee da wani kallo na ƙasan ido, haka kawai ta fara jin kishin Intee ɗin saboda kusan Matan dake aiki a Campany nin duk son Ƴallaɓai Hammad suke wasu ma haka kawai zasuji kishinsa a zuciyarsu.
Wani irin miyau ta haɗe tana bin bayan Intee da kallo, lallai ba abunda Intee bata haɗa ba, kyanta da kyan jikinta yayi