Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
/>
Nuratu ta ƙare maganar a ɗan tsawace haɗe da sakin kuka daga ƙarshen maganar, domin wani irin zafi take ji a zuciyarta idan Sadiya na furta a zubar da cikin dake jikinta.
Lumfashi mai zafi Sadiya ta saki tana jin haushin Nuratu sosai akan maganar gani take kamar neman suna take da kuma neman ta jazama masu gaba ɗaya a ɗaure su har igiya tayi tsawo.
"Kinga Nuratu kije koma miye kiyi amma ni na baki shawari ne kawai bana son a nan gaba kiyi nadamar da bata da amfani"....
*NASAN ZAKU GANE WAJAN NAN AI, WADDA FARKON BOOK ƊIN NA ƊAN YANKO MANA TSOKACI*.......
Chapter 40
A lokacin da Nuratu ta yanke shawarar barin gidan babu Yadda Sadiya ta iya dole ta amince da ƙudurinta, saboda kwata-kwata taƙi yarda da'a zubar da cikin data samu, hakan yasa Sadiya take jin zafinta da haushinta kaɗan gani take kamar akwai abunda ta take ne yasa taƙi a zubar da cikin.
Dan haka ta ce mata wane abu zasu gaya ma Haj Mansura cewar tabar aikin nan?, kai tsaye kuma Nuratu ta ce kawai zata gaya mata ne zata koma gida ta aje aikin saboda aure da zata yi.
Sosai hakan yabawa Sadiya mamaki amma itama bata da wani abun cewar bayan hakan, saboda da haka washe gari suka kira Haj Mansura suka shiga sanar da ita abunda Nuratun ta yanke.
Sai da Haj Mansura ta ɗan shiga mamaki haɗe da damuwa kaɗan saboda tasan irin sabon da Hammad yayi da ita, duk dama yanzu yayi girman da shi ke iya yima kansa komai, dan har yana shirin shiga University dake ƙasar India tafiyar tashi bata wuce nanda wata biyu masu zuwa ba, domin an kusa gama komai na tafiyar tashi.
Dan haka bata ji komai tunowa da Yaronta yanzu ba Yaro bane, dama kuma zuwa lokacin ya kamata ace a canza ma Nuratu aiki, sai gashi kuma faɗuwa tazo dai-dai da zama zatai aure tabar aikin gidan ma gaba ɗaya.
Su Laure sunji labari barin aikin Nuratu sunyi murna da kuma ɗan mamaki, kodai ta tsorata ne da yadda Alhaji ya nuna mata?, idan ko hakane to tabbas sauran aikin nasu zai ci gaba ne akan Sadiya, dan Lare ta rantse sai su duka sun bar gidan.
Tunda Nuratu ta koma Rimaye Inna ta fara ganin wasu sauye-sauye daga wajan Nuratun, data tabbayeta mi yasa ta aje aikin nata?, kai tsaye ta ce mata sune suka ƙoro ta cewar ai yanzu Hammad yayi girman da zai iya kula da kanshi, dan haka aikinta ya ƙare a cikin gidan yanzu.
Inna ba dan ta aminta ba tabarta sai dai kullum Nuratu tana ƙara shiga tashin hankali domin yau da gobe cikin na sake ƙara girma yana bi mata jiki, Inna kallonta kawai take domin ta fara ɗarsa wani abu a ranta.
Tunda ta dawo shaƙuwa mai yawa ta ƙara kasancewa a tsakaninsu da Intee, sai ta lura tafi shaƙuwa da Hammad da yake kan zuwa duk ranar Juma'a duk sati yana Rimaye, da yake kasuwar garin duk ran Juma'a take ci, saboda haka duk ranar da zai zo ɗin Inna ke tarbarsa da abubuwan dake ƙara sa masa sun zuwa garin, da yanayin al'adar garin ta duk Juma'a sai kaga kamar ranar sallah ce ake a garin, shi yasa komai na garin na sake birge Hammad. Intee dake ƙara zama ƴan mata dan har ta fara zuwa school an ajeta SS1, sosai jikin yarinyar ke ƙara buɗewa kamar wata babba ga farin jinin jama'a, danma wani lokacin wasu mutanen na tsokanarta saboda halayen Mahaifinta, tunda ta taso bata san waye shi ba, sai da jama'a suka fara yada mata magana babu babba babu yaro shine musabbabin gano waye ainafin wadda ya yafeta, ranar data gane shine tasha kuka kamar zata mutu, dan har sai da Hammad yazo suka tafi asibiti can cikin birnin Katsina tayi jinyar data kai ta wata ɗaya, dai-dai da rana ɗaya Hammad ne tare da ita, duk da irin shirye-shiryen tafiyarsa ƙaro karatu da yake yi ƙasar waje, da kyar aka samu Intee ta warke ta dawo dai-dai, sai dai rashin son maganarta ya sake ƙara ƙaruwa sosai saita zama miskilar ƙarfi da yaji, ta sake kame kanta bata fita ko nan da can ne, sai idan zata je school, Islamiyya da Hammad ya lura ita ce idan taje take dawowa ranta ba daɗi domin anfi gaya mata magana acan, sunfi haɗuwa da yaran unguwa su tsokane ta, dan haka ne ma yasa aka ɗakko wani Malamin addini yake zuwa safe da yamma yana koyar da ita, Hammad na biyan shi duk watan duniya, saboda tun kan yakai haka Alhaji yake ɗorasa akan hanyar kasuwancinsa, saboda haka a tsaye yake da ƙafafunsa, duk wata hidimar karatunsa da kansa yake yinsu, saboda babu abunda Abbin ɗin nasa bai ɗorasa akai ba.
A wajan Nuratu sosai itama damuwar da Intee ɗin ke shiga ke sake tasiri da damuwar cikin dake jikinta ke sake ramar da ita, sai buɗewa da take sake yi, cikinta na sake fitowa, amma Inna ta zuba mata ido ne kawai tsoro na sake rufeta, tsoronta ɗaya karfa jama'a su gane cewar ƴaƴanta dama Karuwanci suka tafi bawai aiki ba, domin tasha wucewa waje tana jin irin maganganun nan, shi yasa duk itama ta shiga tashin hankali da yanayin Nuratun, duk da dai bata zargin Nuratu zata aikata irin haka, sai dai yanzu baka shaidar Ɗan yau, tayi mata shiru ne kawai taga iya gudun ruwanta.
Inna fa ta kasa haƙura ta shiga kiran Sadiya a waya ta fara mata tabbayoyi hakan ƴar uwarta Nuratu da sauye-sauyen da take gani tattare da ita. Sosai Sadiya ta cika da mamakin wai dama duk tsawon barowarta gidan bata sanar da Inna abunda ke faruwa ba dama?.
Sadiya bata da zaɓin daya wuce ta sanar da ita komai, ba ƙaramin mugun tashin hankali da labarin da Sadiya taba Inna yasaka ta, dan har sai da ta dafe bango da take tsaye tana jin jiri na shirin kayar da ita, ba dai abunda take gudu na haifar ɗan shege a gidanta shine zai faru a yanzu ba?.
Jin yadda Inna ta tayar da hankalinta yasa Sadiya ta fara kwantar mata da hankali wajan cewa.
"Inna kifa kwantar da hankalinki, akwai wani albishir da zan kira yau da na gaya ma ita Nuratun sai kuma gashi ke kin kira ni, dan haka bari na sanar dake kawai yanzu, saboda jiya Alhaji yayi kira na, yana tabbayar ina ƴar uwata?, yaga kwana biyu bata gidan, shine abun ya dame sa, ya ɗauka ko korarta akai ne, ko kuma yana zargin abunda ya wakana ne a tsakaninsu yasa ta tafi, sai dai ni kai tsaye na fito fili na sanar dashi duk wani abu dake faruwa ban ɓoye masa ba, Inna shima hankalinsa ya tashi yana tsoron a haifar masa Ƴaƴa ba tare da aure ba, mutumcinsa da jama'a suke gani zai zube ne, duk da ba'a son ransa hakan ta faru ba, amma ya ce min gobe shida Ɗan uwansa Khabeer zasu taho garin RIMAYE domin a ɗaura auransa da Aunty Nuratu, shima Khabeer ya ce bai amince ba sai dai a ɗaura nashi dani, ni kuma Inna dama gaskiya na gaji da zaman gidan nan na ce masa idan sunzo ɗin a ɗaura kawai, idan yaso nima zanyi gaya ma Matar gidan cewar aure za'a min a gida shi yasa zan bar aikin".
"Aure kuma da Nuratu da Alhaji Ahmed Mai Gwal?, anya Sadiya kin san mi kike faɗa kanki tsaye kuwa?".
Inna ta faɗa cikin ruɗewa da zallar mamakin jin zancan da Sadiya keyi, danji take kamar bata ji ba sosai, kamar kunnanta ne basu ji ba da kyau, dan har jinta take kamar ma mafarki take yi ne, zata tashi ta farka taga ba haka bane abunda Sadiyar ke sanar da ita yanzu a wayar.
"Inna miye a ciki to?, ba cikinsa bane a jikin ita Nuratun ba shin?, kuma idanma Matarshi kike ji to ba yanzu za'a sanar da ita auran ba, kawai shima zaiyi domin rufin asirinsa damu kanmu, saboda maganar mutane, kuma ni bai nuna min cewar yana son a zubar masa da cikin ba, yana son abunsa shima kamar yadda ita Aunty Nuratu ke son cikin, saboda dama yana son ƴaƴa sosai amma Matarshi ta ƙeƙashe ƙasa ta hanashi ƙara aure ta hanashi koda kallon wata Mace bare aje ga maganar auren ma, amma yanzu fa dole ce tasa za'ayi, ƙaddara da tsiya tasa za'a ƙaro mata abokiyar zaman da yanzu bazata san da ita ba, ai ga irinta nan duk ba haka ake gudar mata ba, ace Mace kinje ƙasar waje kinyi zamanki kin kyale mijinki a nan Nigeria ai haukan Haj Mansura ma yayi yawa naga wautarta ni".
Inna ta shiga sauke ajiyar zuciya tana faɗin.
"To amma fa kin riga kin san babu kyau yin aure Mace na ɗauki da ciki ko?".
"Hakane Inna amma ai kin san cikin nan bazai wuce wata ɗaya ba ko?, shi kuma auran za'ayi sa ne domin rufin asirinmu gabai ɗaya, kawai Allah ya yafe mana shine kawai".
Basu wani jima ba suka gama wayar bayan Inna ta yanke shawarar zuwa yanzu ta sanar da Nuratu abunda ke faruwa.
Inna suna gama wayar da Sadiya ta iske Nuratu a ɗakinsu, tayi tagumi sai Intee dake can harabar waje Malaminta yazo tana ɗaukar karatu dan haka yasa ta gyara zama dama bata so Intee na wajan ta ce zata yi maganar, taji daɗin ganin bata ma ɗakin.
Dan haka tayi gyaran murya Inna na sake maida hankalinta ga Nuratu, itama ganin haka yasa ta ture komai dake mata kai kawo a zuci tana maida hankalinta ga Innar dan tasan akwai magana a bakin Innar ganin yadda ta tasata gaba tana bata hankalinta.
Inna bata tsaya wani sanya ba ta shiga sanar da Nuratu duk abunda suka tattauna ita da Sadiya a waya.
A mamakin Inna ta ɗauka ko Nuratun zata ce a'a ne zata bijire da buƙatar auren Alhajin, sai taji ta sauke wata irin ajiyar zuciya mai zurfi, tana hamdala ga Ubangiji daya kawo mata mafita a ɗan ƙanƙanin lokaci, sai gashi tana tsoron sanarma da Inna sai gashi ta sani ba tare data shiga tashin hankali ba, sai gashi kuma mafita tazo mata ba tare da cikin ya fito fili jama'a sun gane ba tare da aure aka same shi ba, dama Nuratu ƙarin tsoranta kar ace cikin nan ya fito Intee ta gani, mima zata ce mata ne?, a ina ta samo shi?, gara da akai hakan.
Ai ko washe gari abun kamar ba gaske ba hakan ta kasance ma Nuratu saboda wajan ƙarfe biyu ana sallamo masallacin juma'a aka ɗaura aurenta harda na Sadiya, wadda jama'a da dama suka shaida, suka kuma cika da mamakin irin mutanen da su Nuratun suka samo suka aura, sai mutane suka fara maganar ai dama yawon duniya suka tafi, can ne suka samo masu kuɗi irin haka.
Hatta Hammad yasan da wannan aure kuma baiga laifin Abbi ba daya auri Nuratu hasalima tun jiya Abbi ya kira shi ya sanar dashi saboda yasan yaron yana da fahimta sosai, kuma ya ce ya ɓoye ma Mahaifiyarsa har zuwa lokacin daya kamata ace ta sani zai zo.
Dama shi yana son Ammi sosai dan haka ranar sosai shida Intee sukai murnar auran da Abbi yayi da Amminsu.
Ita kanta Nuratu a ranar ta rasa wanne irin abu take ji ne dangane da auren Alhaji da yanzu yake a kanta ranar tasha kuka kamar ba gobe.
Inda ya roƙi Inna da Nuratu ta tare a gidanta sati mai zuwa yana da gida a Kaduna inda zai ajeta gidaje ma ba ɗaya ba, ba biyu ba, dan haka baida matsala da inda zai ajeta.
A wajan Sadiya ma kai tsaye ta kira Haj Mansura ta sanar da ita aje aikin nata haɗe da sanar da ita auren da zata yi, hatta wadda zata aura Alhaji bai ɓoye mata ba ya sanar da ita wadda zata aura, ranar anyi tashin hankalin da har saida jinin Haj Mansura ya hau, ta kama zage-zage matsiyata sunzo har sunyi ƙaurin sunan da zasu aure ƙanin mijinta?, kenanma sun kusa kawo matsayinta?, da kyar aka samu aka kashe wutar rikicin Haj Mansura, sosai Abbi ya ƙara shiga ɗan shakku da kuma tsoran ranar da Haj Mansura zata gane cewar ya ƙara aure, to a hakan ma ba shine ta sani yayi auran ba inaga shi ta sani yayi auran shima a yau ɗin?.
Kenan dai ba ƙaramin tashin hankali za'ai da ita ba?, ba ƙaramin kai ruwa rana za'ai da ita ba.
Duk irin zagin cin mutuncin da Haj Mansura tayi ma Sadiya bata damu ba, ta gaji dan kanta ta katse kiran, tana katse kiran Sadiya ta tsaki wani dogon tsaki tana ayyana yadda Haj Mansura baƙin ciki zai kusa kasheta muddun ta gane Nuratu ce a matsayin kishiyarta a yanzu.
Su Lare fa kamar a zuba ruwa ƙasa asha tsabar jin daɗin yadda su Nuratu suka bar gidan a salin alin, sai dai sun cika da mamakin wai ƙanin Alhaji Sadiya zata aura?, nanfa baƙin ciki kamar ya kashe su, ace su duk hakan bata faru akansu ba sai wa'innan da suka zo daga baya?.
Babu wani shiri da zasuyi domin rushe auran saboda sunji wai harma an ɗaura shi.
Sosai hakan ya basu mamaki kuma Lare ta ɗora ayar tabbaya akan wannan auran, haka kawai ta fara binciken san sanin garinsu Nuratu haɗe da gidansu a garin nasu, tasan dai sunan garin nasu Rimaye amma bata san inda yake ba, dan haka taci alwashin bincike mai zafi akansu.
Sati na zagayowa Inna naji na gani aka ɗauki Sadiya aka miƙata gidan Alhaji Khabeer, dake can Niger, sosai Inna ta fidda wasu kuɗin dake gareta ta gyara ƴaƴan nata, Nuratu gyaran jiki kawaai akai mata saboda cikinta ba'a bata wasu kayan Mata ba na sha, sai Sadiya da aka rinƙa ɗirka mata magani, Alhaji Khabeer baya buƙatar akai mashi Matarshi da komai ita kawai yake buƙatar, dan haka da kansa yazo ya ɗauki Matarshi suka hau jirgi sai Niger.
Nuratu lokacin da za'a tafi da Sadiya kukan rabuwar da suka yi ma kaɗai ya isa yasa zuciyar mutum ƙaryewa.
Nuratu ma tasha kuka har biyu na rabuwa da Inna da kuma Intee domin Inna ta ce Intee na tare da ita sai aure ko mutuwa.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kowanne ɓangare suna zaune lafiya cike da takatsantsan. Hammad ya tafi ƙasar waje yabar Intee da wata irin matsananciyar kewarsa.
Bayan tafiyarsa da shekara biyu Nuratu ta haihu ta samu ƴan biyu duka Maza, sai kuma Sadiya data haifi Ɗa namiji shi kuma suka sa masa sunan Mahaifinsu Nuratu na kiransa da Mai sunan Baba, tazarar su shekara ɗaya ce.
Intee ta kammala secondary school ɗinta dan har ta fara karatunta a Kano a University dake Kano tana karantar abunda ya danganci kasuwanci.
Karatun yayi nisa ta ƙara zama budurwa, sosai tsakaninta da Hammad yanzu waya kawai suke yi, ganin yadda ta ƙara kyau da buɗewa da zama budurwa yasa Hammad fara ɗan haɗe mata fuska saboda shi wai karta raina sa ko tace zata tsaya da wani ɗan miji, ya horeta da hakan dan haka sosai yanzu take shakkarsa haɗe da tsoron Maza ma gaba ɗaya bata tsayawa da kowa, dan gani take kamar duk motsinta Hammad ɗin zai sani.
A wannan shekarun Lare haɗe da taimakon wani babban Malaminsu dake masu aiki ta gano ashe Alhaji auran Nuratu yayi, tare da yin bincike mai zurfi ta sake gasgata zarginta da kuma maganar Malamin dana sanar da ita ta sake gasgata zancansa da gaske hakan ta faru ashe?.
Ba ƙaramin tashin hankali Lare ta shiga ba haɗe da mamakin yadda akai auren Nuratu da Alhaji wai harda haihuwar ƴaƴa biyu harda ma wani shigar cikin daga yaye ƴan biyun da Malaminta ke tabbatar mata da bada aure aka sami cikinsu ba, tabbas ta samo makamar sanar da Haj Mansura, ta samo yadda zata ruguza auran Alhaji Ahmed Mai Gwal tare da Nuratu, bazata taɓa barinsu su zauna lafiya ba.
Dan haka ta shiga sake yin wani binciken ta haɗa hujjoji masu ƙarfin da zata tunkari Haj Mansura dasu, harda photon Alhaji idan zai nufi gidan Nuratu da photon ƴan biyun da akai haifa masa ba tare da anyi aurensu ba suka rufe kamar an haifesu da aure.
A lokacin Haj Mansura na ƙasar Nigeria, domin bata wuce wata ɗaya bata fita ƙasar waje ba, yanzu anyi sa'a tana ƙasar, dan haka gaba ɗaya da duk wata hujjar da Lare ta tanada ta nufi Part ɗin Haj Mansura, dan su take yau kwai ya fashe tasan waye Mijinta da irin cin amanar dayayi mata bata sani ba haɗe da ƴar aikinta data ɗauke su a baya masu amana, sai gashi yanzu sunyi mata babban taɓon da zata kasa warkewa har gaban abada......
Chapter 41
Da wani irin mahaukacin sauri ta tashi tana zabura jikinta gaba ɗaya ya ɗauki kyarma ido waje take kallon abubuwan da Lare ta miƙa mata tana mata wasu jawaban da ƙwaƙwalwar kanta ta kasa ɗauka.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Lare abunda nake gani a nan gaskiya ne ko kuwa mafarki kawai nake zan tashi naga ba haka bane?, shin abunda naji kina faɗa a kunne na gaskiya ne ko kuwa kawai gizo ne kike min kema?".
Haj Mansura ta ƙare maganar idonta jawur jikinta har lokacin yana wata irin rawar masifa.
Kamar saukar aradu haka taji maganar Lare na ƙara jaddada mata gaskiya ne abunda take gani, idan kuma har bata yarda ba tazo zata kaita har gidan da aka je Nuratu a cikin garin Kadunar, domin babu abunda bata binciko ba.
A mugun mamakin Lare wasu hawaye ne taga Haj Mansura na fitarwa na tsabar tashin hankali da zarani.
Gani tayi, tayi baya-baya ta faɗa akan kujerar dake bayanta wacce ta tashi daga kanta, duk ɗaukarta ko faɗuwa kawai tayi ƙafafunta sun ƙasa ɗaukarta, sai dai taga ashe suma ne