Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   34 / 40

99K to 102K   out of 118.4K words

Haj Mansurar tayi shi yasa ta koma ta zube akan kujerar.

Zabura Lare tayi ido waje take salati tana kallon Haj Mansura jikinta na rawar tsoro tana kallonta zuciyarta ta fara gaya mata cewar.

"Idan kika sake kika kira jama'a suka ga halin da take ciki, Alhaji zaiyi binciken abunda yasa ta suma, idan ko ya gano kece kika binciko wannan binnan nan sirrin nasa da ya shafe fin shekara biyu yana ɓoye mata, ke yau kika fallasa shi, to hukuncin da zai miki Allah kawai ne ya sani".

Wata zufa ce ta shiga keto ma Lare dan haka jikinta na rawa ta fara waige-waige ta rasa dami zata sa Haj Mansura ta farka daga suman da tayi, ƙwaƙwalwar kanta taji a cikin kanta ance ki samo ruwa ki watsa mata tunda ba mutuwa tayi ba suma ne.

Ai a zabure ta ruga har tana shirin faɗuwa ƙasa ta fice daga bedroom ɗin a ƙasan parlon Haj Mansura ta samo ruwa a firiza, tana zuwa hannunta tsabar rawar da yake tama kasa buɗe robar ruwan sai da kyar da suɓin goshi ta samu robar ta kwance ta, jiki na rawa ta shiga tsiyaya mata ruwan a jiki, tsabar bata cikin hayyacinta bata san duka ruwan ta sharara mata shi jiki ba, ga ruwan mai sanyi.

Haj Mansura jin saukar ruwa mai sanyi bata san lokacin data dawo hayyacinta ba, tana jan wani irin dogon lumfashi mai ƙarƙafaffan sauti, a zubure ta miƙe tana bin inda take da kallo, cike da mamaki ƙwaƙwalwarta ta ƙara tariyo mata duk abunda Lare ta shigo tana sanar da ita.

Jikinta na masifar rawa kamar mazari ta sake raramar photon da Lare ta kawo mata na Alhaji da Nuratu da ƴaƴan shegun da aka haifa harda wani cikin.

Girgiza kanta Haj Mansura ta fara yi kamar ƙadangaruwa ta fara faɗin.

"Kai da ace wani ne ya baki labarin nan bake kika binciko ba to da tabbas kawai sai na ƙaryata ki ne, da kuma ace babu hujjar tabbatar min da hakan, sana na saka an ɗaure min ke har igiya tayi tsawo, domin ban taɓa kawowa a raina cewar wai wata rana Alhaji zai min haka ba, mi yasa bai sanar dani ba ne?".

Wani irin zafi take ji ƙirjinta na mata haɗe da wata irin bugawar zuciya data wuce masali.

Koma tayi baya ta zauna akan kujerar data tashi tana jin wani jiri na son sake kayar da ita, idonta take ji har wani yaji-yaji a cikinsu, dafe saitin zuciyarta tayi yadda take jin tana mata wani irin soya ji take kamar tana ci da wuta, so take ta yarda da abunda take gani ashe Alhaji zai iya auranta wata ba tare da ya sanar da ita ba?, ashe zai iya ƙara aure yayi zamanshi da Matar shi hankalinsa kwance?, ita ya barta sakarai marar hankali ko?.

"Miƙo min ruwa, mi ƙo na sha Lare zuciyata nake jin kamar zata fashe".

Ta faɗa da kyar da jikinta gaba ɗaya kyarma yake idonta sun ƙara rinewa sunyi jawur.

Ganin fa yanayin da Haj Mansura ke sake shiga yasa Lare gabanta faɗuwa duk da dama tasan tabbas zata iya shiga fin haka ma, amma yanzu sai take ganin zata fa iya haɗiyar zuciya ta mutu fa, mi zai faru to?.

Da gudunta taje ƙasa ta ƙara samo mata ruwa mai sanyi ta kawo mata.

Haj Mansura kasa ɓille murfin robar tayi tsabar yadda jikinta ke rawa haɗe da yadda jikin nata yayi mata wani mugun sanyi.

Lare ta miƙamawa kawai ta san mi take nufi dan haka ta ɓalle mata itama da kyar ta miƙa mata, tunda ta kafa kai saida ta shanye ruwan gaba ki ɗaya tana jan wani irin lumfashi mai zafi tana fesarwa.

Jikinta na rawa bakinta ma haka maganarta na shaƙewa ta shiga faɗin.

"Lare miƙo min waya ta maza-maza".

"To amma Ranki ya daɗe mi yasa bazaki fara zuwa gidan ita Nuratun ba idan yaso kayi mata dukan da zata ji tsoro ta gudu tabar miki mijinki kiyi mata cin mutuncin da ko kare bazai ci ba".

"Kije ki miƙo min waya kawai, wannan aikin bani kaɗai ya kamata nayi sa ba, zan kira ƴar uwata dake aure a Funtua ina son yau ta iso garin nan, tare zamuje da ita".

Lare ta juyo ta ɗakko wayar ta kawo mata, number ma sai da Lare ta kamo mata ta danna kiran saboda yanzu fa kwata-kwata jikin nata ba ƙarfi mamaki da zallar firgici da razani sun shanye ɗan ƙarfin da take ji.

Kira ɗaya bugu biyu ta ɗauka jiki ba ƙarfi har a cikin muryarta zaka gane ta miƙe da kyar ta ce.

"Sha'awa kawai fa matsala a gidan nan nawa".

Sha'awa dake cikin wayar ta cike da tashin hankali ta ce.

"Aunty Mansura matsala kuma?, ta micece ne?".

Wata wawar ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana koro mata duk abunda ke faruwa da wadda aka sanar da ita.

Zan iya cewa daga cikin wayar Lare na iya jiyo yadda Sha'awa ta lailayo wata ashar ɗin da tunda take a duniya bata taɓa jin irin zagin ba sai yanzu.

"Kai Aunty Mansura ki ce irin yadda Alhaji yayi min za'a miki kenan?, kuma kike zaune babu wani mataki da kika ɗauka akanta har zuwa yanzu".

"Hmmm Sha'awa kenan, ai gara ke sadda za'a kawo miki kishiyar ma ke an sanar dake, da saninki akai auran, kuma ma tsohuwar Mata ce aka auro miki wacce ta gama haihuwa a waje, nifa yarinyar ce fa shataf, duka fa haihuwarta ɗaya kuma daga gani rabuwa ce tazo masu da mijin nata da alama zamansu basu wani daɗe tare ba, saboda lokacin da suka zo da goyan Ƴarta duka bazata wuce wata shidda ba ko bakwai fa, abun mamakin ma ni wai Alhaji sai da ya nemi yarinyar nan da iskanci kamin ya aureta, wai sai da ya ɗirka mata ciki shine aka binne abun ya aureta duk dan kar mutane su gane bada aure aka samu cikin ba, ai ko zata gane ta aure min Miji danna rantse da Ubangijin daya yoni saina ɗora mata ciwon zuciyar da sai yayi ajalinta, ni yanzu kawai so nake yau-yau kizo garin Kaduna ki tayani cin uban shegiyar. Ni da tafiya zanyi gidanmu ma naje can sai ya zaɓa ko ni ko ƙasƙantacciyar can, wacce take min aiki wai a cikin gida na ya rasa wacce zai auro min sai wacce ta zauna a ƙarƙashina tana min aiki, wallahi Allah Alhaji ya cuce ni Allah ya isa tsakanina dashi wallahi".

"Kinga Aunty Mansura ban baki shawarar ki koma gida ba wai kice kinyi yaji, domin kin san halin Abbu bazai taɓa bari kima kwanar masa a gida ba, maido ki zaiyi ɗakinki kuma yaji abunda yasa kika dawo, idan yaji abunda bai kai ya kawo bane bai kuma saɓa Shari'ar Muslunci ba kin san mi zai faru ai, kin riga kin san Abbu baya ɗaukar shirme ko shashanci, dan haka kiyi zamanki a gidanki ni zan taho yau ɗin, kawai bala'in da zamu kunno mata dole ta gudu da ƙafafunta tabar miki gidanki keda mijinki, idan ko bata bari ba Aunty ki ce masa dole ne ya haɗe ku gida ɗaya ta yadda zaki rinƙa ƙunsa mata baƙin cikin da zaiyi ajalinta, zata san ta auri mijin Mansura ne tun yanzu ai".

"Tabbas wannan shawarar taki tayi Sha'awa, ina jiranki sai kin iso, kina fa gani har ƴar uwar nan tata ta auri ƙanin mijina, bafa a daɗe ba na kira ai ina baki labari, amma ashe wai rana ɗaya ma ake sanar dani sunje anyi auran, da yake muggan munafukai ne babu yadda akai na sani, anya wa'innan mutanen ba asiri sukai masu ba kuwa?".

"Hmm Aunty kenan babu wani asiri fa, raba kanki dana Ɗa miji idan cutarsa ta tashi, raba kanki da idan idonsa ya kyalla ido yaga Macen da zuciyarsa ke so, hmm ke dai kawai saina zo. Mu ai Aunty bama asiri aiki muke a aikace kawai".

Sallama sukai badan sun gama maganar ba tana kashe wayar Lare ta fara sosa kanta tana cewa.

"Ni ko Ranki ya daɗe mi zaisa bazan kaiki wajan Malamin dake min aiki ba, tunda shinema ya gano min wannan binnan sirrin da suka ɓoye fa, amma Haj ya kike gani?".

Wani tsaki Haj Mansura taja dan ita fa kwata-kwata bata yarda da asiri ba, abunda ma suka fi tsana ne a gidansu, basu taso suka ga anayi ba, dan haka ma Abbu ɗinsu Mahaifinsu ya horesu da ƙin shirka da aikin sihiri, dan haka ne ma suka tsani Malaman tsubbu da Bokaye, basu taɓa ma'amala dasu ba, su dai ka barsu da wani abun amma kwata-kwata basa shirka.

"Ke kinga Lare aikin ki yayi kyau tabbas kuma zan linka miki albashinski, dan haka zaki iya tafiya, ai kin san bana aikin asiri kinfi kowa sanin na tsani masu yinsa, kema dan dai kawai kina kawo min Information na gidana, amma da badan haka ba da yanzu na kore ki a gidan nan nawa, zan kuma sake jan kunnanki Lare daga yanzu karna sake jin kina bin Malaman tsubbu idan na sake ji zakiyi ta bakin aikin ki".

Da wani irin sauri Lare ta ɗago tana kallon Haj Mansura dake maganar babu wasa, dan haka tayi saurin girgiza kanta tana faɗin.

"Tuba nake Ranki ya daɗe insha Allah daga yau an daina".

"Yayi zaki iya tafiya".

Lare ta fice tana farin cikin ita dai tunda an ƙara mata albashi tasan ba ƙana nan kuɗi yanzu zata rinƙa ɗiba ba, dan haka gargaɗin Haj Mansura na tabar bin Malaman tsubbu bai dameta ba, ita dai tasan idan ta tashi taga abunda yafi ƙarfin kanta zata je ne Hajiyar ma bata sani ba.

Sai kusan yamma tukunna Sha'awa ta ƙaraso cikin garin Kadunar kai tsaye gidan ƴar uwarta tayi ma tsinke bata je ko gidansu dake a garin ba, dama kuma asalin ƴan nan ne Kaduna ita aure ne ya kaita Funtuar.

Sosai Haj Mansura taji daɗin isowar tata lokacin saboda tasan duk inda Alhaji yake baya gida a yanzu, dan haka da Lare aka tafi domin ita ce zatayi masu jagora zuwan gidan.

Sosai Haj Mansura ta cika da bala'in mamakin irin uban gidan da Alhaji ya aje Nuratu kamar ma yaso yafi nata kyan gani, wani irin baƙin ciki ne ya rufe mata zuciya har idan Sha'awa na mata magana take kasa amsawa.

"Jar uban nan kaiiii, kinga gidan nan ashe a cikinsa aka aje wannan ƙasƙantacciyar?, bala'i lallai Maza".

Sha'awa ta ƙare maganar tana riƙe bakinta.

Mai gadi bai tsaya tabbayar su waye ba ganinsu da Mota mai kyau ya ɗauka ko ƴan uwan Alhaji ne yasa kawai ya buɗe masu get suka shiga, da yake Sha'awa ke tukin Motar da Motar data taho suka taho kawai.

Tunda suka sauka daga Motar suka nufi cikin gidan Haj Mansura ta kasa magana sai haɗiyar zuciya da take tana bin uban gidan da kallo, tabbas ya zarce nata nesa ba kusa ba, kuma abunda yasa yafi nata shine yafi nata yawan Part, dan kusan Part na gidan kusan guda huɗu ne a gidan.

Baƙin cikin da take ji a zuciyarta faɗarsa ma ɓata baki ne kawai, wata wutar kishi haɗe da hassada ce kawai kece a zuciyarta.

Kafarta har gurɗewa take wajan idasa shiga makeken parlon da take ganin kamar yaso ma yafi nata, sai dai kishi ne kawai daya rufe mata ido amma baza'a iya haɗa nata da wannan ba.

Ido waje Haj Mansura ke kallon ƴan yaran dake mugun kama da junansu, a zaune a parlon suna wasa yaran da bazasu haura shekara biyu da rabi ba, kamarsu ɗaya da Alhaji kama ma wacce daka gani zaka shaida tabbas jininsa ne.

Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya sake ciyo Haj Mansura idonta sun kaɗa sunyi jawur, sai Sha'awa dake danna zagi duk wadda yazo bakinta furzar dashi take.

Nuratu dake kitchen sai da gabanta ya yanke ya faɗi jin kamar hayaniya a parlon nata, sai dai tasan su Hassan basa wannan hayaniyar, dan haka jikinta na ɗan bata ba lafiya ba ta fito daga kitchen ɗin.

"Kai kamar wani cikin nake gani tattare da ita fa?".

Sha'awa ta faɗa a watsa ce tana nuna Nuratu data fitowa tayi wata irin mutuwar tsaye daga inda take tana jin wani irin tashin hankalin da tunda take bata taɓa jin makamancinsa ba.

Wani kalar bushashshan miyau ta haɗe tana jin yadda maƙoshinta ya bushe lokaci ɗaya tsabar tashin hankalin data riski kanta.

Ba abunda Nuratu ke faɗa sai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un tana sanar da Ubangiji.

Haj Mansura bata san lokacin data matsa har inda Nuratu take ba, ganin haka ya sake sawa ma Nuratu jin gabanta ya ƙara yankewa ya faɗi.

Tsabar yadda zuciyarta ke bugawa a ƙirjinta sai data dafe saitin zuciyarta tana salati da salallami.



"Dole kiyi salati mana tunda kinga shaiɗanu a gabanki ba?".

Sha'awa ta faɗa tana ƙara matsowa itama a gabanta.

Wani malalacin murmurshi wadda yafi kuka ciwo Haj Mansura ta saki tana cewa.

"Ba shakka Nuratu har kin ƙara sakin jiki kin ƙara ɗaukar wani cikin da Mijina ko?, naga fa Yara gasu nan ƴan gaba da fatiha sun fara wayo".

Gaban Nuratu ya sake faɗuwa sosai har bata san lokacin data ware idonta a zare tana bin Haj Mansura da wani irin kallon tsoro ba.

"Mamaki kike ne na sanin da nayi cewar kamin Mijina ya aureki sai da kuka gama watsarku a waje?".

Nuratu ta kasa hakuri ta ce.

"Ba'a san ranmu hakan ta faru ba, dan Allah kiyi hakuri ba'a san raina na auri mijinki ba da.....

Kyakkyawan mari mai zafi da ƙarar sauti Sha'awa ta ɗauke Nuratu dashi.

Wadda yasa Nuratu sakin ƙara haɗe da dafe kumatunta tana kallon Sha'awa da mamaki.

"Kallon ubanmi kike min algunguma makira kawai, ke har kina da bakin magana ne wai ma?, marar kunyar wofi, har kina da kunyar kallon tsabar idon Aunty Mansura kina bata hakuri wai?, sannunki fa na ce kinji?, sarkin rashin kunyar duk duniya, to yau zaki gane Mijin waye kika je kika aura, domin wallahi yau sai munci uwarki".

Runtse idonta Nuratu tayi da ƙarfi tana jin zafin zagin da Sha'awa ɗin tayi mata.

Kamin ma ta ce wani abu Sha'awa ta rufeta da wani masifaffen dukan data kaita ƙasa, su Hassan dake can suka fara kuka domin basu san rigima ganin abun yasa su fashewa da kuka.

Nuratu na kiran Innalillahi saboda wani duka da Sha'awa ta kaima ruwan cikinta, yasa ta sakin wata ƙarar azaba tana sakin salati mai ƙarƙafaffan sauti.

Sai taga ta kasa koda muƙa hannunta ne yasa Haj Mansura janye Sha'awa daga kanta tana matsawa sosai inda Nuratu take kwance tana riƙe da cikinta tana juye-juyen azaba ta kalleta da kyau ta ce.

"Baki ga komai ba ai Nuratu, na tanadar miki kwando-kwandon rashin mutumci da bala'i idan har kika ce zaki ci gaba da zama a cikin gidana da sunan kina auran mijina, Nuratu saina saka miki ciwon da sai yayi ajalinki wallahi, babu Boka babu Malam amma zaman gidana sai ya gagare ki zama".

Ta ƙare maganar ta juya ta ce "muje shi Alhajin zai zo ya same ni har gida ai zaiga saƙon dana barsa gata nan data sha jiki".

Ficewa sukai Sha'awa na sake zugata tana faɗin sai tayi sati ɗaya a garin idan yaso har sai Nuratu ta gudu da ƙafafunta.

Koda Alhaji yaje gidan Nuratu yaga irin halin da take ciki sosai hankalinsa yayi mummunan tashi har sai da suka je asibiti aka duba lafiyarta, inda Doctors sukai ta faɗa ya akai aka bari wani abu ya bugar mata ciki?, bayan ansan tana da Yaron ciki kuma?, hakuri ya rinƙa bawa Doctors ɗin da kyar suka shiga dubata aka kwantar da ita asibitin saboda sai ta ƙara samun kulawa.

Kai tsaye idonsa ya rufe ya nufi gidan Haj Mansura ransa a mugun-mugun ɓace, Nuratu ta roƙesa yabi komai a hankali tunda dai sune sukai mata laifi bai kamata ya ɗauki wani mataki akanta ba, amma ji yake saifa yayi mata rashin darajar da itama taje ta aikata, ai ko darajar cikin dake jikin Nuratun ta duba tayi haƙurin ta sauka lafiya kamin koma miye tayi.

Koda yaje yadda ya rufeta da faɗa yasa Haj Mansura bata san lokacin data ci kwalar rigarsa ba tana fashe masa na wani irin kukan baƙin cikin da tun ɗazu take so tayi sa amma ta rasa wadda zatai mawa, sai gashi yazo yana sake ƙara mata wani zafin akan wadda yasa ta ciki.

Kukan nata ne ya dawo dashi hayyacinsa, tausayi ta bashi dan haka yayi shuru bai iya ce mata komai ba, saima ficewa da yayi ya bata waje.

Haj Mansura baƙin cikin hakan yasa sai da ƙara jan Sha'awa suka je gidan Mai gadi ya ce ai Matar gidan na asibiti, har asibitin da Nuratu ke jinya sai da tasa aka nemo mata shi, har can suka ƙara zuwa sukai mata cin mutuncin da sai da taji garama ace dukan nata suka sake yi, ranar tayi kuka kamar zata shiɗe, koda Alhaji yaji so Nuratu tayi ya sake ta kawai bazata iya zama da Haj Mansura zaman kishi ba, tafi ƙarfin duk wani tunaninta, ya bata hakuri da kyar ta sakko kai tsaye shi kuma Alhaji yaje ga Abbu Mahaifinsu sai da yaje kofar gidan nasu kuma miya tuna ya fasa shiga haka kawai yaji kamar rashin adalci ne zaiyi ma Haj Mansurar kai ƙararta ga Mahaifinta, kuma bayan yasan tabbas shi yayi mata laifi.

Yaje ga Haj Mansurar ya lallasheta haɗe dayi mata alƙawarin babu Macen da zata kaita a wajansa, inda Haj Mansura ta kafa sharaɗin dole Nuratu ta dawo gida daya da ita, idan ba haka ba kuma akwai sauran kallo.

Bai ji wani abuba suka fara shirin komawa wani gidansa dake Aurora Wrestling Estate, dan yafi duk sauran gidajen kyau da yawan Part, dama kuma gidan ba'a daɗe da gamasa ba zaman gidan ko Mata huɗu ne zasu iya zama ba tare da kowacce ta haɗu da ƴar uwarta ba.

A

34 / 40