Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
naki masu kama dana mayu".
Ɗauke idonta Humaira tayi akan Ma'u tana furzar da iska a bakinta tana jin wani irin haushin ƴan gidan gaba ɗaya har shi Y Harun ɗin wadda ko saninsa batai ba, tasan tabbas dole ya ɗauki hali irin nasu na rashin tarbiyya da girmama ɗan Adam.
Inna ce ta katse shuru da Humairar tayi dan taga yadda Ma'un ta wani ja ta tsaya akan Humairar tana nuna kanta kamar wacce ke shirin kai mata mari a fuska.
"Allah Sarki Ma'u ashe yau Harun zai sauka ƙasar?, Masha Allah Ubangiji ya kawo shi lafiya, karku damu kije komai da kika sani za'ai masa kamin nanda jirginsu ya iso".
Kamar Ma'u zata yi tsaki sai kuma ta fasa tana komawa ta fice daga parlon kawai cike da tsantsar takaicin Humaira ɗin, taso ta bata amsar da bata gimsheta ba ta falla mata mari komi zai faru Allah sai dai ya faru dama cike take da ita.
Tana fita Inna ta dawo da dubanta inda Humaira take ta ce.
"Wai ke Humaira sai yaushe zaki canza ne wai?".
Turo baki Humaira tayi tana yin ƙasa da kanta ta ce.
"Inna yanzu kuma miye nayi dan Allah?".
"A'a ba abunda kikai kinji, baki ji ne tana miki magana ba?, ai sai ki amsa ta koda abunda take gaya mikin bai miki daɗi ba, kinga Humaira a fa gidan Mahaifinsu kike zaune to fa dole kiyi hakurin zama dasu. Yanzu dai tashi muje kitchen ɗin tare mu fara aikin, ai shi Harun ɗin baida matsala kamar taso, domin ni yana girmama ni sosai".
"A'a Inna kiyi zamanki zanje nayi ni ɗaya kawai".
Komawa Inna tayi ta zauna ta ce.
"To ai shikenan dan Allah kiyi abun a tsanake bana so ana kawo min ƙararki ko ace bakiyi dai-dai ba, bana son ƙananun maganganu Allah".
Da to kawai Humaira ta amsa tana ficewa daga parlon ta nufi babban kitchen ɗin gidan.
Tunda ta fara aikin ba wadda ya fito harta ci galabar aikin sai lokacin Ma'u ta fito tana nufo kitchen ɗin jin wani irin ƙamshin girki na bugar mata hanci har wani ƙara buɗa hanci take tana shaƙar ƙamshin girkin.
Tsaye tayi tana kallon yadda Humairar ke yin aikin cike da tsafta haɗe da natsuwa.
Taɓe baki tayi tana saka hannu a dambun namar da Humaira ta gamasa yanzu sai miya ce kawai ta rage bata gama ba, amma sauran duk ta idasa tana ajesu a kuloli masu kyau wa'inda Ma'un ta aje mata wadda zata saka abincin a ciki.
Motsin mutum data ji ne yasa Humaira waigowa inda Ma'u take ganin yadda ta wani cika baki da dambun naman data aje gefen kanta ta kitchen ɗin yasa Humaira ɗan kallonta ta ƙasan ido.
Sai da Ma'u ta haɗe dambun namar dake bakinta kamin ta ce.
"Wato ke tsabar mugunta irin taki kin san kin iya girki har haka mai mugun daɗi shine mu kwana biyu kike buga mana abinci marar daɗi ko?, wannan ai mugunta ce wallahi dubi fa yadda gidan nan ya cika da ƙamshin girkin nan naki, ko da yake dai mun gode a hakan ma tunda Y Huran ne aka gwangwanje, amma muma daga yau wallahi kin gama mana abinci marar tashin ƙamshi a hanci da kuma ɗanɗano a baki kamar haka, dole ne ma ki canza a'ato haka kawai kiji mugunta dan Allah?".
Shuru kawai Humaira tayi mata dan yanzu shurun nata shi yafi zama alkhairi, amma shurun nan fa da take yawan masu shike sake sawa suji wani irin bala'in haushinta ya kama su bare Ma'un dake magana yanzu haushi ne ya cika ta bata san lokacin data ce.
"Ke wai miye haka ne ina magana kin wani yimin shuru kamar wacce ke magana da kurma?, ko mahaukaciya kika ɗauke ni ne ban sani ba?".
Murmurshi kaɗan Humairar ta sakar mata wadda ya ƙara ƙule Ma'un ta ce.
"To Aunty Ma'u miye kike so na ce miki?".
"Mtswww Oho miki mana aikin banza kawai".
Girgiza kanta tayi tana sakin murmurshi na gefen baki again dai ta ce.
"To kuma banda abin cewa ne shi yasa kika ga nayi miki shurun".
"Kar Allah Ubangiji yasa kiyi abin cewar Mtsww".
Ita dai Humaira shurun tayi danta ga yau Ma'u so kawai take ta tanka suyi faɗa abun ya dawo kanta ace ita ce mai laifi, su ko masu gida ai kullum haka suke basa laifi.
Tana kallo ta sake cika hannu ta kai dambun a bakinta, wai duk dan tayi magana, bata san tuni ta zuba ma Y Huran ɗin nashi ba a cikin wani mazubi mai kyau ta aje can daga gefenta Ma'u bata ganshi ba, wannan wadda ta aje ta aje ne domin kawai ta ɗanci ta kuma kaiwa Inna itama taci, danta rantse komi ta dafa saita cisa, bazai yiwu ace tasha wahalar yin abu ba amma ita ko a bakinta, danta sha masu girki tazo ta iske an cinye ko irin abun nan ace Humaira gashi domin ke kika dafa, a'a gani suke ai aiki take ana biyan uwarta, kuma dai take ganin duk wani abu da zasu ce a dafa ɗin nan fa daga hannun Mai gidan yake fitowa, dan haka idan ma har ita bata da iko data dafa wani abu ai Inna nada ikon dafa duk abinda take so itama, amma gani suke hatta Innar sai abunda aka dafa da rana ko dare ko safe ne kaɗai take da ikon cinsa kawai bawai taji sha'awar wani abuba itama tazo ta ce a dafa mata ba, shi yasa Humaira duk sadda zata yi girki sai ta tabbayi abunda Inna take son ci zata kuma dafa mata ita ɗaya ta kawo mata basu ma sani ba, abincin ranar kuma ta dafa abunda ta gani a rubuce wadda duk Ma'u ce yanzu ta tsurfo da dole sai abunda suka so shi za'ai dafa, shi yasa Ma'un harda wani rubuta liss na abubuwan da za'a rinƙa dafawa duk satin duniya.....
Chapter 12
*HAMMAD POV*
A hankali ya ɗago kansa yana dubanta ya watsa mata idanuwansa masu kaifi, da sauri tayi saurin kauda kanta gefe tana turo baki magana take ciki-ciki.
"Shi wai wannan mutunan bazai daina taƙura min bane wai?".
"Mi kike cewa?".
Da sauri tayi tasa hannunta tana rufe bakinta sai kuma ta basar kanta a ƙasa ta ce.
"Ni kaji na ce wani abu ne?".
Murmurshin gefen baki ya saki kaɗan yana nuna mata wata leda dake aje gefe ya ce.
"Ki ɗauki wannan ledar"
Waigawa tayi tana duban ledar, sai kuma ta dawo da dubanta garesa ta ce.
"Minene zanyi da ita?".
"Take it and I just said it, right?".
Sake zunɓuro baki tayi gaba tana ƙunƙuni taje ta ɗauki ledar haɗe da buɗe cikinta aɗan mamakance ta fiddo da wata Hijab dogowa mai azabar kyau da tsadar gaske kalar Jaah ce sosai. Ta dubesa tana faɗin.
"Wannan fa ta wace?".
Yana aiki a Computer bai kalleta ba sai da ya sha ƙamshin nasa kamin ya ce.
"Taki ce".
Kawai ya bata amsa a taƙaice.
Wani irin kallon Hijab ɗin take tana kuma sake kallonsa da mamaki sai kuma ta fara bin jikinta da kallo, itafa bata ga wata aibun shigar data yo ba, hasali ma a lifayar duk ta fi suturta mata jiki, ko Hijab ta saka baya hana aga tudun mazaunanta ko Hijab ɗinta, ko kuma tudun dukiyar Fulaninta, kawai wata irin halittar jiki ce Allah ya zuba ma Intee ɗin mai mutuƙar ɗaukar hankali da kuma haɗari a wajan wasu Matan wadda idan Allah ya basu Sura kamarta Intee sai su rinƙa amfani da ita wajan jan hankalin samarinsu wajan yin iskanci suna fito da ita a fili suna tallar kansu.
Ita ko iya ƙoƙarinta dana Ammi bata taɓa bari Intee tasa kaya wa'inda zasu kama mata jiki sosai su matse ta ba.
"Miye zanyi da ita a yanzu?".
"Put to you will do it now, domin baza ki sake fitowa babu Hijab ba daga yau".
Baki buɗe take kallonsa bata san lokacin data furta.
"For what reason do you think about it..
Maganar ce ta maƙale mata a baki domin kwata-kwata abunda zata faɗa ɗin sai taji bai dace ta faɗa masa haka ba, tunowa da irin abubuwan da yayi mata baya, da irin babbar gudunmawa daya bada a rayuwarta ta baya data so lalacewa, shanye maganar tayi sai kawai ta fara ɗan satar kallonsa taga yanayinsa, ganin hankalinsa baya kanta aikinsa kawai yake zata sake magana taji ya ce.
"Kije yanzu nan ki saka Hijab ɗin tun kan raina a ɓaci a kanki".
Wani abu ne ya tsaya mata a wuya ta kallesa ta ce.
"Amma Y Hammad please idan nasa Hijab ɗin nan na fita kuma bayan ansan ga kayan dana shigo dasu, sai nake ganin kamar mutane zasuyi mana wata fassarar, tunda ansan ga Office naka ga nawa kusan duk haɗe suke waje ɗaya, Please Y Hammad ka bari zan saka gobe dan Allah".
"Shhh kimin shuru kije kiyi kawai abunda na ce".
"Amma Y Hammad......
"Shhhhhh"
Ya faɗa yana tasowa sosai ya matso kusa da ita yana ɗora ɗan yatsansa akan ɗan ƙaramin bakinta.
Ƙasa tayi da kanta tana jin yadda ƙirjinta ke duka saboda kusancin da suka samu, dan haka da sauri ta ɗan matsa tana sauke ajiyar zuciya mai ɗan ƙarfi.
Bata ce komai ba dan tasan ko kwana zatai tana masa magiyar ya fahimce abunda take hangowa ita, to bazai taɓa yarda da ba, shifa kawai idan ya yanke hukunci saifa anyi bare ma idan har kana ƙasansa kuma yake ganin wannan hukuncin da ya yanke maka shine dai-dai to babu ruwansa da wata maganar mutane, domin shi kwata-kwata basa ma gabansa harkarsa kawai yake kai tsaye bai wani damu da maganar jama'a ba, can su ta dama.
Badan taso ba ta warware Hijab ɗin ta saka akan Lifayar tata, lokacin da zai ɗago ya zuba mata ido bai san lokacin da furta Masha Allah ba, saboda gani yayi Hijab ɗinma tafi mata wani irin bala'in kyau, ga wani irin kwarjini da Hijab ɗin ta ƙara mata, ƴar fuskarta mai tsananin kyau mai ɗauke da ƙurucciya tsantsarta ta sake fitowa kamar wata baby bakin nan nata ɗan ƙaramin da take turo shi gaba sai yayi kamar na wata ƴar yarinya ƴar goye.
Da sauri ya lumshe idonsa yana tasbihi ga Ubangiji ya koma ya zauna akan kujerar daya tashi yana sake kallonta ta ƙasan ido.
Wani irin abu ke taso masa akan Intee ɗin dan haka yayi saurin cewa.
"Here is the job I sent you at the Camputer in your office, make sure you finish it today and tomorrow, and gobe zuwa jibi muna da turo na Campany".
"Okay"
Kawai ta iya cewa ta juya a hankali cike da takunta mai jan hankali ta fice daga Office ɗin nasa.
Tunda ta juya ya samu kansa da binta da kallo harta ɓace ma ganinsa, tsaki ya saki kaɗan ƙwaƙwalwarsa na sake hasko masa yadda ta juya albarkatun jikinta na na motsawa, yadda kasan ba Hijab ta saka ba.
"Mtswww, this girl, when did she go back like that?, mi zata saka ya suturta jikinta ne?".
Shi kaɗai yake magana dan gani yake kamar ma a banza koda tasa Hijab ɗin.
Sai faman sakin tsaki yake yana dafe da kansa.
Computer ya jawo amma kwata-kwata ma ya kasa tsaida hankalinsa yayi aikin daya dace abu kaɗan yaja tsaki, gaba ɗaya Intee zuwanta Campany nin ta gama dagula masa lissafi ransa babu daɗi kwata-kwata, shi fa shi yasa da Abbi yabi ta tashi da Intee batai wani aiki ba, amma Abbi ya wani dage dole sai tayi, yanzu ba gashi ba tazo kowa sai kallonta yake ba.
Sai faɗa yake a ransa, dan wani ɗan abu ne a hannunsa yana matsawa daka kalli yadda yake matseshi a hannun nasa zaka gane ransa a ɓace yake sosai.
Dan gani yake kowa ma sai daya kalleta data ratso cikin uban wannan Campany nin nasu mai ma'aikata Maza da yawa da Mata ma, danshi fa hatta Matan ba wani yarda yayi dasu ba, suma akwai ƴan iska masu bin ƴan uwansu Mata.
Ya sauke lumfashi ya kai sau nawa yana yin baya da kansa a hankali ya lumshe idonsa, hakan da yayi sai ya ƙara ma fuskarsa kyau ta yadda zaka kalleta son ranka, gashin idonsa ya kwanta sosai kamar wadda yasa ƙarin gashi ba ƙaramin taimakawa yake ba wajan sake fiddo da ainafin kyan da Allah ya basa haka kuma gashin Sajensa siriri baƙi suɗik dashi, gashin gemunsa ma mai matsakaicin yawa a gyare yake sai sheƙi yake mai ɗaukar hankali, kai gaba ɗaya halittar da Allah ya zuba ma Hammad ɗin abar ɗaukar hankali ce game kallonta.
*House No: 18 Kawo Estates Kano state Nigeria*
Gaba ɗaya jikin Intee ƙara ɗaukar sanyi yake haɗe da wani irin tsoro da yake sake rufeta.
Tunda suka fara shigowa cikin gidan wadda yanzu yake a matsayin Matar ɗan gidan ce wai ita?, wadda sai jiya take jin sunansa wajan Haj Bharaka mai suna Sadeeq. Yaune karo na farko data fara sako ƙafarta a irin wannan unguwar ta masu kuɗin gaske, saboda tunda suka shigowa unguwar gine-gine ne kawai take gani masu bala'in kyau da tsari kamar ka shiga ƙasar Turawa bawai a Nigeria kake ba. Tun shekaran jiya da sukayi da Inna ba'a ƙara sanar da ita komai ba sai ana gobe za'ai kawo ta gidan Aunty Sakina ke sanar da ita wai har an ɗaura auranta dashi, sun riga sunyi magana da Haj Bharaka domin basa so ta shigo gidan ba tare da an ɗaura ba, a can Family nasu suka kira aka tabbayi cikekken sunanta da sunan Mahaifinta akai mata waliyai da komai daya kamata aka ɗaura, dan yanzu hakama ga sadakinta nan kusan dubu ɗari biyar an ba Haj Bharaka ta kawo ma Aunty Sakina.
Ranar Sakina tayi kuka tayi kuka kamar zata mutu har saida taba Aunty Sakina haushi ta kuwa shiga ɗuɗɗura mata na maguzawa, daga baya kuma sai ta dawo lallashi, domin kaɗan ta ɗan bata tausayi tunda bata san mutum ba bata san ya dangin nasa ya suke ba, amma anje an aura mata shi babu wani dogon nazari ko tunani, wannan wacce irin rayuwa suke ciki ne haka?.
Bata damu da kuɗin ba kai tsaye ta ce a tura ma Inna ta aje a wajanta kawai, kuɗin da aka turo mata na fara aikin nata ma bayan Aunty Sakina ta ɗibi kasonta ta turo ma Inna sauran inda Inna saida ta ƙara turo mata kusan dubu ɗari biyu wai gashi itama tayi wani abu dashi, bata san ma tuni ta ɗibi kasonta ba, kuma a haka ta sake amshiwa tana jin daɗin gara da akai haka, ai ita gaba ta kaita gobarar titi.
Inna tunda aka turo kuɗin ta bawa Aunty Sakina nata ko waiwayarsu bata sake yi ba, dan ko Humaira ma bata san da zaman kuɗin ba, Inna tun ranar da aka ce itama an ɗaura auran ta kwanta ciwo wani irin zazzafan zazzaɓi ne ya rufe ta dan ko waya basu yi da Sakina ba.
Ita kanta Sakinar dauriya ce kawai take amma ji take itama kamar zata kwanta rashin lafiyar.
Ranar da Haj Bharaka tazo tafiya da ita lokacin data fito suka ga wasu irin jifga-jifgan motoci sunzo ɗaukarta, ba ita kaɗai ba hatta Aunty Sakina sai da ƴan cikinta suka kaɗa, ta ƙasa hakuri ta ce.
"Haj Bharaka anya wa'innan mutanen basu haɗa iri da jinin ɗan ƙaruna ba kuwa?, yo wannan ina zasuje da dukiya haka?, ina zasu kaita? wannan ai ko jikokinsu sai sunzo sunci wannan daular".
"Hmm Sakina kenan ke nan mi kika gani ma, ai motocin gidan kawai fa kika gani, hmm to ai kallo yana gidan da zamuje nan ne zaki ga zallar kuɗin da aka kashe akai wannan uban gidan dashi, ke daga gani ba sai an tsaya gaya miki ba ke zaki yanke hukunci da kanki, ai su kam gidan duniya dai sun gama dacewa sai kuma idan munje lahira".
Riƙe baki kawai Aunty Sakina tayi tana kallon Irin motocin, yadda suke ɗaukar ido kamar na wani shugaban ƙasa.
Da yake harda Aunty Sakinar za'a je domin taga inda Sakina zata zauna saboda gudun wata rana.
Zan iya cewa tunda suka shigo unguwar tun kan ma akai da sun shiga gidan Aunty Sakina ta fara ruɗewa tana santin kyawun unguwar da irin haɗuwar gidajen dake cikin unguwar, sai ka ce ba hannu ne ya gina su ba, tsabar yadda aka baje fasaha aka ɗora ginin na gani na faɗa iya kallonka har sai ka gaji. Saboda itama duk zamanta a Kano Allah baisa ta taɓa biyo kota wajan irin wa'innan unguwannin ba.
Tunda taga motocin sun nufi wani irin ɗan bala'in gini mai masifar kyau da tsaruwa, zata iya cewa tunda suke wuce gidaje a bayansu bata ci karo da wadda yayi haɗuwar wannan dake a gabansu ba.
Bata ƙara tsinkewa da al'amarin ba sai da ta gansu a harabar gidan, yadda kasan wani gari guda ne aka gina a wannan gida. Ginin ne anyi shi da tsantsar fasaha haɗe da kwarewa ta musamman daka kalli yadda gidan ya tsaru yayi kyau zaka shaida wa'inda sukai ginin gidan ba ƙananan kwaro ne ba ta fannin iya gini.
"Wow kai jama'a Haj Bharaka nama ƙasa cewa komai, amma wannan ginin gidan ba dai mutum ba sai dai Injin ko?, kai wannan gini ma ba dai Mutanen mu na hausawa ba sai dai can suka samo Turawa sukai wannan uban gidan haka".
Dariya kawai Haj Bharaka ta saki dan ganin yadda Aunty Sakina ta gama ruɗewa gaba ɗaya sai zuba santin haɗuwar gidan take, bakinta yama ƙi rufuwa sai bin gidan take da kallo sosai baki buɗe, da zallar mamakin irin uwar dukiya ta masu gidan.
Sakina ita gaba ɗaya jikinta ne ke sake mutuwa idan ta ɗaga kai ta kalli irin haɗuwar gidan da irin dukiyar da aka narka domin yinsa, iya hasashenka baka isa ka ƙiyasta nawa aka kashe wajan gina wannan katafaran gidan ba.
Lokacin da akai masu jagora