Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   30 / 40

87K to 90K   out of 118.4K words

nuna abunda zata haifa a matsayin ɗanka ka isa, to a nan ne zan nuna maka kalar nawa rashin mutumcin".

Tana faɗar haka taja hannun Nuratu sukai gaba Sadiya ce ƙarshe, sai ta tsaya ta gama ƙare masa tass kamin tabiyo bayan su Inna da sukai mata nisa.

Koda suka isa gida Sadiya ta iske yadda Inna ke kuka tana bawa Nuratu hakuri, Nuratu cike da damuwa ta fara ce mata ita dama basu taɓa ganin laifinta ba, bare su riƙe ta rai, sosai Sadiya taji daɗin ganin yadda Inna ta sauya duk ta sanadiyar samun cikin Nuratu.

A hankali suka shiga kulawa da Nuratu da abunda ke cikinta, wani lokacin tare da Inna suke zuwa asibiti awan ciki, sosai suke bata kulawa duk da halin matsin rayuwa da suka fara shiga, sosai ko wacce sana'a Sadiya ke ƙoƙarin yinta domin dai su samu abunda zasu saka a bakin salati.

A hankali rayuwa ta ƙara matsawa cikin Nuratu yayi girma sosai dan har ya shiga watan haihuwa.

Sosai Inna ke ƙara lilka kulawarta akan tada da take bata sosai ta ɗora son duniya akan cikin Nuratun.

Wata safiya Sadiya na zaune a kusa da Nuratu sai Inna dake gefe Sadiya ta gyara zamanta ta ce.

"Inna na samo mana wani aiki amma fa a can cikin garin Kaduna ne, Inna aikin aikatau ne amma fa akwai albashi mai tsoka da suke biyan ƴan aiki dashi, sana kuma mutum biyu suke so, ni kuma na amsa na kama mana nida Aunty Nuratu amma fa na ce har sai ta haihu Yaronta yayi wayo, zaka iya tafiya da ɗanka tunda aikin Mace ɗaya da suke so zata ba Ɗansu kulawa ne, sai ɗaya kuma zata kula da abincin masu gidan ne, ba ita zata dafa ba amma zata rinƙa da kula da ficen harkar kitchen da gidan ne kawai".

Inna ta gyara zama taji anyi maganar samun kuɗi ta ce.

"Amma fa aikin nan abun dubawa ne, amma fa gaskiya Kaduna tayi nisa Sadiya, amma Nuratu kina son aikin nan?, sana ke Sadiya a ina kika ji ana son masu aiki?".

Sadiya ce ta fara cewa.

"Inna a wajan wata makwafciyarmu ne ta nan bayanmu tazo siyan wainar fulawa a waje na jiya da yamma take sanar dani ko muna so, domin dai taga kamar muna neman taimako irin haka".

"Tabbas hakane na tuna ta, amma ta kyauta mana, sai dai ni nisan Kadunar nake gani fa".

Nuratu ce ta ce.

"Inna indai neman halal ne ai waje baya nisa, na aminta da aikin insha Allah dana haihu Yaro na ko yarinya tayi wayo zamu iya tafiya".

"Tom ai shikenan amma fa duk lokacin da aka yaye ta to za'a maido min ita nan waje na na ci gaba da riƙe ta, domin ba lallai ace suna sun masu goyo a masu aiki ba, kin san yanayin masu kuɗin nan".

"Hakane Inna nima abunda nake gani kenan, duk dai ita matar da take gaya min samuwar aikin ta ce babu wata matsala, amma dai su masu kuɗin nan iya masu sai Allah kawai".

"Ai shine Sadiya Allah yasa mu dace kawai ya iya mana muma".

Faɗin Inna tana maida hankalinta wajan Nuratu dake ɗan yamutse fuska kamar wacce ke shirin fashewa da kuka, Inna zatai magana taji yadda Nuratu ta saki wani Salatin daya sa Inna da Sadiya rufar mata a tare suna tabbayar lafiya a ruɗe?.

Bata da bakin magana sai yarfa hannu take tana riƙe ƙaton cikin nata, idonta a rufe tana salati tana sanar da Ubangiji.

A guje Sadiya ta fice waje ta samu masu abun hawa dan daga gani haihuwa ce ta taho mata ba shiri.

A tare suka kamata suka sata a abun hawan suka hau suka wuce asibiti kowannensu hankalinsa a mugun tashe yake.

Sunyi sa'a suna zuwa aka amsheta aka shiga da ita ɗakin haihuwa, a mamakinsu bata wani jima da shigar da ita ba ɗakin haihuwar wata likita ta fito tana shaida masu cewar ta sauka lafiya ta sami Ɗiya Mace.

Sosai suka shiga farin ciki har suka kasa hakuri suka faɗa ɗakin sai da wata Doctor ta fito dasu aka gyara Nuratu da Ƴarta wacce tayo kamarta data Mahaifinta dan kusan hasken fatarshi ta biyo da idonsa masu girma sai kuma hancin irin na Nuratu ne, lokacin da aka basu Okay ɗin zasu iya shiga kusan da gudu Sadiya ta faɗa ɗakin.

Kai tsaye wajan Nuratu ta nufa tana faman mata sannu, ɗaga mata kai kawai take tana lumshe idonta dandanan bacci ya kwashe Nuratun, Inna ko yarinyar ta ɗauka tana rungumeta a jikinta a nan take Inna tayi mata huɗuba da sunan Inteesar bata tsaya tabbayar kowa ba ko jin ra'ayin wani ba akan sunan data sa.

Sadiya na kallonta tana murmurshi danta san sunan da Nuratun ta daɗe tana faɗa ne cewar tana son suna Inteesar, shine yanzu Inna ta saka ma Ƴarta, sosai Sadiya take murmurshi tana godema Allah da sauyawar Inna........

Chapter 37

Cikin wata irin soyayya suka shiga rainon Intee wacce ta taso tare da wani irin farin jinin jama'a, dan sai suna zaune a gida makwaftansu su aiko a kai masu ita, yarinyar bata da rigima kwata-kwata danma wani lokacin Inna ke hana a bada ita ga kowa, sosai Inna ke nuna mata wata irin soyayya shi yasa yarinyar ta taso tasan Innar sosai kuma wani lokacin ita ce kaɗai batai mata kyaiya.

Sagir ma yasha zuwa domin ganin Ƴarsa yana tunƙaho da cewar ƴarshi ce dai-dai da rana ɗaya tunda ya ganta sau ɗaya a hannun wata bai sake sata a idonsa ba, dan koda yazo Sadiya ke fita tayi masa tas kuma ta ce indai Intee ce bashi ba ganinta idan har tana lumfashi.

A hankali rayuwa ta ci gaba da gudu yau gashi har Intee tayi wayo suna cikin wata na shidda da haihuwarta, dan haka babu abunda bata ci ko sha. Suka fara shirye-shiryen tafiyar su aikin da sukai al'ƙawari zuwansa da zarar Intee tayi wayo, sunyi a dai-dai domin yanzu ne gidan da zasu je suka buƙatar masu aikin, da basu zo a lokacin bama zasu iske an samo wasu ne, wacce tayi masu hanyar aikin ce ta sanar dasu hakan, shi yasa suka fara shirin tafiya.

Inna tayi-tayi da abar mata Intee tunda ba abunda bata ci da sai a yayeta, amma Sadiya taƙi tana nuna mata duka fa watan Intee shidda tayi haƙuri ko shekara ɗaya ne tayi da watanni sai a maido mata ita wajanta.

Jikin Inna badan ya aminta da wannan aikin bane kawai ta barsu suka tafi ta bisu da addu'a cike da tsantsar kewar jikarta suka rabu dan Innar har hawaye ta matse a kafaice.

Sun shigo Kaduna cikin dare dan sai wajan bakwai suka isa, kai tsaye dama anyi masu kwatancen unguwar da sunan mai gidan da zasu faɗa Alhaji Ahmed Mai Gwal, babu wadda bai san shi a garin Kaduna da kewayanta ba, bare idan ka shiga unguwar da yake da zama ko farkon unguwar ka shiga ka ambati sunansa tsaf za'a kaika har ƙofar gidansa.

Dan haka basu sha wata hawala ba aka kaisu har bakin ƙaton get ɗin gidan, wadda tun kan su shiga cikin gidan kyan get ɗin gidan haɗe da hango irin tsarin ginin gidan haɗe da hango benen gidan mai tsawon gaske ga wasu irin fitilu da suka haske gaban gidan da cikin gidan masu ɗaukar hankali.

A hankali Nuratu taji gabanta ya yanke ya faɗi haka kawai kallon gidan kawai da tayi yasa ta riƙo hannun Sadiya tana faɗin.

"Sadiya anya wannan shine gidan aikin namu kuwa?".

Sadiya ma data cika da mamakin irin kyau na gidan da yadda aka tsara gininsa yasa ta kasa cewa komai, domin tunda suke a duniya basu taɓa ganin ginin daya tsaru ya ƙawatu irin wannan da suke gani a gabansu ba, ginin kansa kamar na masarauta haka aka tsara shi fentin gidan irin na sarauta ne, har wani ɗaukar ido yake.

Wani miyau Sadiya ta haɗe tana jin wata fargaba haka kawai ta shigeta ta ce.

"Tabbas idan har nan ne gidan Alhaji Ahmed Mai Gwal to nan ne gidan aikin namu, sai dai idan ba nan gidan bane".

Sauke lumfashi kawai Nuratu tayi tana jin motsin Intee dake bayanta tana motsawa kaɗan-kaɗan alamar tana gaf da tashi ne dan haka da azama suka matsa bakin get ɗin gidan.

Sun kwankwasa get ɗin ya kai sau nawa amma ba'a buɗe ba, har sun sare ma da za'a buɗe masun, kawai suka ga an buɗe ƙaramar ƙofar get ɗin gidan, wani matashi ne ya fito daga gani mai tsaron bakin get ɗin ne, dan sanye yake da wasu kaya kamar uniform.

"Kai ku kuma bayin Allah lafiya zaku zo ƙofar gidan nan kuyi tsaye?, ko masu neman taimako ne?, to Alhaji da Hajiya basu ganin mutane a irin wannan lokacin sai zuwa safiya, a safiyar ma sai sun bada lokacin fitowarsu tukunna, dan haka kubar ƙofar gidan nan yanzun nan".

Tashi Sadiya tayi tana jin wani irin abu daya ɗarsu a ranta kamin ta dubi mai gadin da yake masu kallon ƙasƙantattu kwata-kwata sai taji kamar aikin ya sire mata ma kamar ta ce su koma gida, sai kuma ta ɗaure ta ce.

"Ba wa'inda kake tunani bane, mu ƴan aikin gidan nan ne wa'inda ba'a daɗe da ɗaukarsu ba, munzo ne daga nesa shi yasa mu kai dare".

Wani kallon uku saura kwata yayi masu kamin ya ce.

"Kai tafi daga can mun saba ganin irinku ai, kuna zuwa kuna cewa wai aiki aka ɗauke ku a gidan nan ashe idan kuka samu aka buɗe maku ƙofar get kuka shigo sai labari ya canza, kuna ganin masu gidan zaku fara roƙon da kuka saba, a taimaka maku, dan kunga shi Mai gidan Alhaji baya da rowa ko kaɗan idan har ka ganshi sai ya baka kyautar da zata girgiza ka, shine kuke fakewa da aiki ko, to sai dai abi wani sarkin wannan dai baku zo da sa'a ba, dan haka ayi gaba".

Yana ƙare faɗar haka ya banko ƙofar get ɗin ya rufe ya barsu sake da baki.

"Innalillahi Aunty Nuratu yanzu ina zamuje?, kaga ɗan iska?, irin wa'innan mutane nan fa suke hana ruwa gudu, ko taimakon kazo a baka irin wannan suke hana a baka shi, dube shi don Allah shiba kowa ba sai shishshigin tsiya, yana wani cika yana batsewa sai kace mai wani matsayi a gidan".

Ƙara gyara zamanta kawai Nuratu tayi tana kwanto Intee dake baya harta fara ƙananun rigingimo dan haka ta fidda nono ta bata ta fara sha sai tayi shuru.

Tana duban Sadiya ta ce.

"Kawai ki zauna idan da rabo mu kwana a ƙofar gidan nan ne kuma babu yadda muka iya ai, saboda idan muka ce zamu bar nan ina zamu je ma?, kawai mu bari zuwa safiya idan har bamu samu shiga gidan nan ba sai mu kama gabanmu mu koma Rimaye kawai ya zamuyi?"

"Yanzu Aunty Nuratu haka zamu kwana a wajan nan dan Allah?, sana kawai idan bamu shiga gidan gobe ba sai mu haƙura da aikin nan da zai taimaki rayuwar mu gaba ɗaya?".

Sadiya ta faɗa tana komawa ta zauna itama tana saka hannunta tayi tagumi dashi, tana jin wani kalar baƙin ciki haɗe da jin haushin mai gadin nan.

"Hmm to ya muka iya ne Sadiya?, sufa dama masu kuɗi idan har kika ce zaki fara zuwa wajansu ba tare da wadda aka sani ba a wajan to tabbas ki saima kanki wulaƙanci ne kawai, hausar da bamu yi ba shine kawai mu sai waya mu kira ita wacce tayi sanadiyar kawo mu gidan nan, da sai ta kira ita Hajiyar gidan a sanar da ita zuwanmu, ni wayar ce kwata-kwata bata dame ni ba shi yasa ma banda ita, ke kuma kinata so ki sayeta babu kuɗin sayen".

Sauke tagumin Sadiya tayi tana sauke wata irin ajiyar zuciya kamin ta ce.

"Kuma fa hakane, amma munyi kuskure rashin waya a hannunmu, amma rashin kuɗi ne duk ya kawo haka, amma insha Allah albashina na farko zan cire wani abu na sai wayar dashi da yardar Allah".

A cikin zuci kawai Nuratu ta amsa, a nan suka zauna har dare wasa-wasa ya fara kunno kai, sosai suka fara tsorata da yanayin wajan, sai kukan Karnuka kawai kake ji a unguwar da yake irin unguwar masu kuɗi ce sosai, ko ina an banza Karnuka irin masu bada tsaron nan.

Sosai suka cure wajae ɗaya Allah yaso Intee tana shan nono bacci ya ɗauki yarinyar, su ko yadda suka ga dare haka suka ga rana, bacci ɓarawo harya fara ɗibarsu sanyin asuba ne ya farkar dasu a hankali Sadiya ta miƙe tana wata irin miƙa wacce gaɓoɓin jikinta sai da suka amsa, a hankali ta shiga ɓata fuska yadda duk daren jiya Sauro yaci ubansu da cizo ko ina na jikinta taɓon cizon sauro ne, garama Nuratu data sa gyalenta ta rufe jikinta ita da Intee cizon bai masu yawa ba kamar na Sadiya.

Sadiya takaice ya isheta da haushi ta dubi Nuratu data shiga lallashin Intee data farka itama tana kuka saboda bata saba kwana ba'a watsa mata ruwa ba, shi yasa ta tashi da kuka da kyar ta samu tayi shuru dan nonon ma data bata ƙin amsa tayi miƙewa tsaye tayi ganin yadda garin ya fara haske kaɗan ta tsaya saboda itama zaman ya isheta, ka kwana a zaune ai dole zama ya isheka.

Sun ɗauka ko za'a buɗe get ɗin ne da safe wani ya fito sai dai hatta Masallaci akwaisa a cikin gidan shi yasa har rana ta fara takewa wajan Goma na safe amma babu alamar za'a buɗe get ɗin gidan, sosai hakan yasa Sadiya ƙara jin zafin zucin da take ji haɗe da zallar haushin wannan ɗabi'a ta masu kuɗi.

Nuratu ko sosai abun ya fara damunta ga Intee data fara kuka sosai yarinyar domin tana buƙatar ruwan sha, sauƙinta ɗaya tana bata nono tana sha, amma itama kanta Intee ɗin harda gajiyar Mota ta jiya ga kwanan waje da sukai dole abun ya haɗe mata itama.

"Kinga Aunty Nuratu na gaji fa, tsakani da Allah tunda akwai ƴan kuɗaɗe a waje na kawai mu koma tashar Mota mu hau mu koma Rimaye, yo ina dalili haka kawai wannan wulaƙanci ai yayi yawa ma".

Nuratu zatai magana sukaga an shiga buɗe babbar ƙofar get ɗin, sai da ta aka buɗewa hancin wata hamshaƙiyar Mota ƴan ubansu ta shiga fitowa daga cikin gidan.

Sauke ajiyar zuciya sukai a tare suna sake matsowa kusa da Motar sosai.

Mai gadin daya hanasu shiga sosai ya cika da mamakin naci da kafiya irin na wa'innan mutanen, ashe basu tafi ba dama?, kar dai a nan suka kwana?, yana kallonsu yana tabbayar kansa a zuci, Sadiya ko ɓalla masa wata uwar hararara tashiga yi kamar zata jawosa tayi masa dukan tsiya tsabar yadda take jin zafinsa a zuciyarta.

Gilas ɗin Motar aka sauke fuskar wani kamilin Mutum ta bayyana mai cike da wani irin kyau haɗe da kwarjini a fuskar tashi ga wani gemo haɗe da saje mai ɗan yawa gashi baƙi daya zagaye fuskar tashi, ga wani irin kyau da Allah ya zuba mashi mai ɗaukar hankali.

Ganinsa yasa Sadiya da Nuratu ruɗewa domin Allah tunda suke basu taɓa ganin bawan Allahn da kuɗi da kyau haɗe da isa da izzar da suka dace dashi ba kamar wannan da suke gani a yanzu, tabbas ya cancanta da ya mallaki wannan gida dama dukiyar da suka fi wannan da yake ciki ma, komai Allah ya bashi shi kam.

Har suna haɗa baki wajan gaida shi, tunda Alhaji Ahmed ya ɗora idonsa akansu yaji haka kawai yaran sun birgesa haɗe da jin daɗin yadda suka ɗuka har ƙasa suka gaida shi.

Amsawa yayi cikin sakewar fuskar data basu mamaki sun ɗauka ko zaiyi jin kai da izza ne irin na masu kuɗin nan da, da yawansu suke yi.

Tabbayarsu yayi ko akwai wani taimako da suke nema ne a gidan?.

Sadiya kalmar taimakon nan tana bata haushi fa, amma ta shanye ta shiga sanar dashi abunda ya kawo su.

Sosai ransa ya ɓaci da jin a ƙofar gidan suka kwana, dan haka yasa aka kira Mai gadin ya rufesa da faɗan danmi wai suke saurin wulaƙanta duk wadda yazo gidan ne, da neman taimako, dan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kenan ana kama su da irin wannan.

Haƙuri ya shiga basu da kansa sunyi mamaki sosai, dan kamin ya tafi sai da ya ɗauki Intee dake ta rigima a hannun Nuratu sosai ya ƙara kashe su da mamakin yadda baya ƙyamar talaka kwata-kwata, sosai yaji yarinyar tayi masa shi yasa ya miƙa hannu ya ɗauketa yana ɗaukarta yaji son yarinya ya shigesa dan haka ta daɗe a hannunsa kamin ya miƙa masu ita, ya kira Haj Mansura ya sanar da ita baƙin ƴan aikin data sa a kawo mata yayi mata bayanin tun jiyan suka iso amma basu samu damar shigowa ba sai yanzu, bata wani damu ba ta ce a barsu su shigo, ta aiko ƴar aikinta mai kula da duk wani al'amarinta Lare mai aiki tazo har ƙofar get ɗin ta shigo dasu.

Tunda suka shigo gidan suke kallon ikon Ubangiji yanayin yadda tsarin gidan yake haɗe da zallar maƙuɗan kuɗaɗen da aka kashe wajan tsarashi da yinsa ma kaɗai idan ka tsaya kallon irin kyawun gidan zaka iya yankema kanka hukuncin irin uban kuɗin da aka narka wajan yin ginin gidan.

Sosai kuɗin masu gidan ya shallake tunaninsu dama duk wani hasashensu.

Lokacin da aka masu iso a parlon Hajiyar gidan sun ƙara cika da zallar mamakin haɗuwar parlon kansa, ashe basu ga komai bama, sai yanzu ne suke shan kallo.

Koda ta sakko kai daka ga yanayin tsarinta da isarta da wani irin kyan shiga da sura da Allah ya zubama mata zaka san ba daga gidan tsiya ta fito ba ita kanta, ko ace gidan miji ta sami wannan gatan, daka kalli Haj Mansura zaka shaida dama can gidan iyayenta masu dashi ne, kallo ɗaya zakai mata

30 / 40