Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 40

57K to 60K   out of 118.4K words

ba zai iya ba, sai dai ya kira ni ta waya ko?".

Ya faɗa a zuci yana sake sakin murmurshi ya juyowa yana duban Bilkisu ya ce.

"Ayyah kiyi hakuri na tsayar dake, kije zuwa gobe zamuyi magana".

Kamar dama akan ƙaya take yana faɗar haka bata ce komai ba ta juya da sauri ta bar wajan.

Shi kuma ya nufi inda Japhar yake Naseer shima dai-dai lokacin ya ƙaraso wajan, jerawa sukai suna tafiya a tare Japhar ya ce.

"Mtsww wai kai Aminu ka cika shiga harkar Yara wallahi, ka wani tsayar da Yarinya da alama ma badan taso ta tsaya ba, dubi yadda take amsa maka magana kamar bata so, nifa shi yasa bana son haɗa huɗɗa da Mata, da zarar ka fara sakar masu fuska zasu fara kawo maka raini ne".

"Abokina duk miye na wannan dogowar maganar?, kai da na sani kaima baka cika shiga abunda bai shafe ka ba, kawai ka rabu dashi yaji dashi can shi".

Naseer ya faɗa yana dafa kafaɗar Japhar.

Kallon juna da Naseer da Aminu sukai suna sakin wani murmurshin da sune kaɗai suka san ma'anarsa, suna kyafta ma juna ido.

Tsaki yaja kawai yana yin gaba ya rabu dasu, shima kansa ya rasa gane mi yasa idan har yaga Aminu da Yarinyar can yake kasa hakuri sai yayi mitar yaje ya tsaya da Ƴar mutane, yana jin wani irin abu ne idan har ya ganta da wani a tsaye, haka kawai ya fara jin ciwon tallar da take yi a zuciyarsa a kullum, da kuma tashi makarantar da take yi a lokacin da bai kamata ta tafi ba, sai kuma fashin school da take yawan yi dan a sati ya lura bai wuce ta shigo sau uku ba ko biyu, abunda yasa yayi saurin gane hakan shine yana ɗaukarsu a class nasu hakama Aminu yana ɗaukar tasu, Naseer ne kawai baya ɗaukar class nasu Bilkisun.............

Chapter 23

*House No: 17, Aurora Wrestling Estate Kaduna State Nigeria*

Zama tayi tana ɗaukar wayarta dake ringing ranta a ɓace yake a kwanakin nan, tabbas tana buƙatar ɗaukar mataki akan Nuratu da wannan aljanar ƴar tata.

Ɗaukar wayar tayi tana kallon mai kiran ganin Maami ce yasa ta ɗauka.

Ɗaga kanta tayi bayan taji abunda Maami ta ce daga cikin wayar ta ce.

"Eh wallahi Maryam zata taho zuwa gobe insha Allah, ya kamata muzo mu fara shirye-shirye dan a kusa-kusa nake so ayi abun a gama cikin ƙanƙanin lokaci ta yadda zai mance da waccar figagiyar yarinyar wallahi".

Daga cikin wayar Maami ta ce.

"To Alhmdllhi yanzu naji magana Aunty, amma har kun gama magana da shi Alhaji ya amince da haɗin?".

"Yama za'ai ya kasa amincewa, ai bazai taɓa yuwu ba wallahi, yadda ni ce na zuƙƙunna na haifi Hammad to ko babu wadda ya isa na yanke hukunci akansa ya ce min ba haka ba, ɗana ne ina da iko dashi".

"Hakane Aunty tabbas, koma miye ake ciki nima zan kira ki na gaya miki, ita kuma Maryam ɗin sai ta iso zuwa goben".

Sallama sukai daga haka ta yanke kiran, tana kallon cikin wayar, samun kanta tayi da danna kiran number Hammad.

Sai da tayi ringing harta katse bai ɗauka ba, zuwa can tana yankewa ko minti biyu ba'a cika ba ya kira, dama tasan baya taɓa ɗaukar kiranta har sai ya yanke sai ya kira ta, haka ɗabi'arsa take a wajanta.

"Ina son ganinka yanzu nan a Part nawa ina jiranka"

Abunda ta faɗa masa kenan ta yanke wayar.

Minti kaɗan saiga shi ya shigo parlon da muryarsa mai taushi yayi sallama, ga wani irin ƙamshi da Ummu taji gaba ɗaya Parlon ya sake ɗauka, duk da irin son ƙamshinta da irin turaren da take amfani dashi amma Hammad ɗin nata ƙarshe ne ta wajan iya saka turare yasan takan turaruka masu mutuƙar ƙamshin daɗi.

Zama yayi a ƙasa a kusa da ita yana gaida ita cike da wata irin girmamawa wacce Ummu idan yana mata hakan jinta take tafi kowa sa'ar samun Ɗa a duniya, saboda ita kanta ta sani Hammad yana bata wani irin girma a matsayinta na Mahaifiyarsa, yana mata biyayya iya baƙin ƙoƙari ta sani.

"Ummu gani kin ce kina son gani na".

Gyara zama tayi tana fuskantarsa kamin ta ɗanyi gyaran murya ta ce.

"Hakane magana ce zamuyi da kai ta ƙarshe Hammad akan maganar auranka da Maryam, naje wajan Abbinku mun gama magana dashi, amma shi yana faɗin wai sai dai a haɗa ka da Mata biyu harda yarinyar can wacce duk duniya nafi tsanar uwarta da ita kanta. Hammad ina baka umarnin kaje wajan Mahaifinka ka faɗa masa cewar baka son Intee Maryam ce zaɓinka ita kaɗai ce wacce zaka iya zama kuyi rayuwar aure da ita".

Tunkan ta idasa maganar ma ya shiga cikin halin ruɗani tsantsarsa, daka kalli fuskarsa zaka gane hakan, a ruɗe ya ɗan zabura yana kallon tsakiyar idon Ummu yadda yake hango iya gaskiyarta ce ta fito har zuci take gaya masa bata ƙaunar Intee. Shi kam ta ina zai fara mata bayanin babu yadda za'ai ya iya watsama Abbi ƙasa a ido, bama wannan ba bazai taɓa iya kallon Ammi itama ya ce mata bazai auri jininta ba, Matar data daɗe a rayuwarta tana bauta masa, tun yana ƙarami ita ce cinsa, ita ce wanke ƙashinsa fitsarinsa komai nasa ita ke masa, ta dalilin kula dashi duk ta faɗa cikin wata irin jarabawar rayuwa wacce har zuwa yau bata daina ganin wannan jarabawar ba. Kai ina bazai iya ba wallahi.

Saukar muryar Ummu da ya ji ne tana magana shiya katse masa dogon nazari daya faɗa a firgice yake dubanta yadda take masa maganar a tsawace haɗe da zallar ɓacin rai take faɗin.

"Ka maida ni ƴar iska ina magana kayi banza dani?".

"Kiyi Hakuri Ummu".

Ya faɗa da sauri kansa a ƙasa.

"Mtswww ni dai kaji abunda na faɗa maka, tun muna shaidar juna Muhammad kaje kayi kawai abunda na ce maka, akan wannan maganar Muhammad zamu iya samun mummunar matsala da kai harda shi kansa Mahaifin naka, idan har kuwa aka ce dole sai ka auri wannan tsintacciyar Magen to tabbas zan tafi na bar maku gidan nan, saika zauna kaida Uban naka Nuratu ta zama Mahaifiyarka, tunda dama naga kamar ta fini iko da kai a yanzu, na tabbata da ita ce tayi maka maganar nan da yanzu kabi abunda take so, tsabar ta gama min da kai".

Girgiza kansa yayi da sauri ya ce.

"Ko kaɗan Ummu ba haka bane, babu yadda za'ai na iya haɗaki da kowacce Mace a duniya, ke ɗin ke ce komai nawa Ummu dan Allah kiyi hakuri".

"Hmmm, ba wani ni ce komai naka, ai da kana ɗaukar cewar ni ce komai nakan da yanzu kaje kayi abunda na ce maka Hammad, amma da yake ita Nuratun ta mori Malamai an gama mallake min Miji da Yarona dole ta ce sai abunda take so mana, ai tsakani na da Nuratu har gobe zan faɗa Allah ya isa wall.....

"Pleaseeeee Ummu kibar maganar nan dan Allah, why ace har zuwa yau komai ya kasa wucewa ne?".

"Tashi ka bani waje Muhammad tun kamin raina ya sake ɓaci akanka, nayi maka abunda ban taɓa maka shi ba a duniyar nan".

Ta ƙare maganar tana nuna masa ƙofar fita daga Parlon fuskar nan tata a murtuke.

Ganin yadda take yasa shi tashi jiki a sanyaye ya fice daga parlon dan yaga kiran Abbi shima yana son ganinsa. Kansa ne ya fara ɗaukar zafi. Ya suke so yayi ne dan Allah?, umarnin Ummu zai fara bi? ko kuwa na Abbi zaibi?, ya rasa wanne tunani zai farayi akai ma.

"Ummu!! Ummu!! Ummu!!!".

Faɗin Maryam data fito tana kiran sunan Ummu, sai dai Ummu Hammad yana fita tayi zurfi cikin tunanin neman mafita, dan ji take ko yawo zata rinƙa yi tsirara bazata taɓa bari Hammad ya auran jinin Nuratu ba, Matar da tazo cikin rayuwarta ta gama wargaza mata duk wani buri data ci a cikin gidanta, ta shinfiɗa rayuwar gidanta ne daga ita sai mijinta da Yaronta kwaya ɗaya takk wadda Ubangiji ya bata, ba irin neman maganin haihuwa da bata nema ba, babu irin ƙasashen duniyar da bata je ba domin neman haihuwa ko Allah zaisa ta ƙara haihuwa, tun kamin makirar Matar can ta zo ta gama tarwatsa mata komai, domin garin zuwa yawo ƙasashe da take ta tafi ta barta da kulawa da ragamar gidanta da Ɗanta da ita da ƴar uwarta wacce itama ta samu ta aure Ɗan uwan Mijinta suna can a Niger zauna zaune, hankalinsu kwance, wadda ada can baya abun tausayi ne neman taimako kawai suke inda zasu samu su ɗan raɓa suyi rayuwa, amma yanzu sun zama wani abu har suna so ta haɗa jininta dasu, tsabar ma basu da hankali.

Jin kiran da Maryam ke mata yasata ɗan firgita tana sauke lumfashi kaɗan ta dawo da dubanta inda Maryam take riƙe da waya a hannunta.

Da murmurshi ta fito amma ganin Ummu ɗin a haka yasa ta shanye murnar data fito da ita tana kallon Ummu ta ce.

"Ummu lafiya kike kuwa?, tun ɗazo nake a wajan nan ita kiran sunanki amma shuru ba amsa, mi yake faruwa ne Ummu?".

Wata ajiyar zuciya Ummu ta sake saki tana kallon Maryam ɗin sosai kamin ta ce.

"Miya faru kike kira na haka?".

Zama Maryam tayi tana faɗin.

"Wai Maami ta kira ni gobe zan koma gida za'a fara min gyaran jiki, ta ce wai baza'a ɗau lokaci ba za'a fara shirye-shiryen bikinmu da Y Hammad".

"Eh hakane ya kamata kizo ki koma domin mu fara shiryaki da wuri, insha Allah komai za'ayi yadda na tsara shi".

"Amma Ummu itafa maganarsa da Intee ɗin can, Allah yasa an fasa wallahi Ummu ina son Y Hammad, ji nake bazan iya haɗasa da wata Macen ba".

Dafata Ummu tayi ta ce.

"Ai jinin Nuratu in har ina lumfashi bazai taɓa haɗuwa da nawa jinin ba, kima kwantar da hankali kawai".

Murmurshi mai sauti Maryam ta saki wani daɗi na lulluɓeta.

******************

"Zauna mana Muhammad".

Abbi ya faɗa yana aje ƙofin shayin da Intee ta kawo masa babu daɗewa ta fita, sunsha banban basu haɗuwa ba ko a hanya.

Zama yayi a ƙasa yana tankwashe ƙafafuwansa yana bawa duk wani hankalinsa ga Abbin bayan ya gama gaidasa.

"Muhammad abunda yasa na kira ka shine, kasan tun kan ka kai haka, nake da burin haɗaka aure da Intee, ko ban faɗa ba nasan kasan hakan?, sai dai kuma Mahaifiyarka nason kawo min matsala da cikar burina, sai dai bata isa ba, kamar yadda take da iko da kai nima haka nake dashi akanka, nama fita iko da kai, dan haka na riga da na yanke hukuncin cewa sai dai ka haɗa duka biyun zaɓinta da zaɓina ka aura, amma da alama duk da hakan bata amince ba".

Abbi yana dire maganar kamar an jefota ta shigo tana faɗin.

"Ban amince ba, kuma bazan taɓa amincewar ba.......".

Wani kallo da Abbi ya jefa mata yasa ta shanye sauran maganar data shigo da ita a bakinta. Shi yasa ma suna gama magana da Maryam kamar tasan Hammad ɗin nan zai taho wajan Abbi yasa kawai ta taso ta biyo bayansa, dan so take ya amsa a gabanta cewar baya son a haɗasa aure da Intee ɗin.

Kansa ne ya fara sarawa sosai yana runtse idonsa da ƙarfi zuciyarsa na bugawa. Miye abunda Ummu ke son jawo masu ne dan Allah?.

Hammad yake tabbayar kansa a zuci.

Maganarta ya sake ji tana cewa.

"Abbin Hammad wai harka manta da irin cin amanar da Nuratu tayi min ne a rayuwa?, dan haka bazan taɓa yarda jini na dana Nuratu su kasance waje ɗaya ba, idan har ni ce Mahaifiyar Muhammad ban amince da auransa da Intee ba, na faɗa na sake faɗa, sai dai komi zai faru sai dai ya farun".

"Haka kike ce ko?".

Abbi ya faɗa a hargitse dan ji yake kamar ya miƙe ya rufeta da duka, sa'a ɗaya take ci da albarkacin Mahaifinta daya tallafi rayuwarsa da kuma Ɗanta Hammad amma da tuni yayi maganinta, yasa tayi nadamar da bata shirya ba.

"Kware kuwa haka na faɗa, kuma indai ina lumfashi bazan taɓa bari hakan ta faru ba".

"Yayi kyau to hakan, ni kuma zan nuna miki na isa da Muhammad harma nayi yawa, zan aura masa Intee idan yaso dan Allah Mansura kiyi bindiga ki mutu saboda kawai an aura masa Ƴar maƙiyiyarki kinji ko?".

A zabure take kallon Abbi tana haɗiyar wani abu mai ɗaci a maƙoshinta, zuciyarta na wani irin bala'in zafi ta ce.

"Idan har Hammad ka bari Mahaifinka ya aura maka wannan yarinyar tsintacciyar Magen to wallahi tabbas zan iya yi maka baki".

Da wani irin mugun sauri su duka suke waigo da wani irin maɗaukakin mamakin furucinta suke kallon Ummu dake wannan furucin babu ko ɗar take faɗin hakan.

Tashi Abbi yayi yana kallon Ummu a mamakance ya ce.

"Mansura kin san miye kike faɗa kuwa?, kina hayyacinki kuwa?".

"Nasan abunda nake yi Alhaji ina cikin hankalina, ka ɗauka wasa nake yi ne akan furici na ko?, shin wai Ɗana Hammad shine kaɗai namiji ne a duniya da baza'a kyale min shi ba, taje can mana ta auri waninsa mana dole ne aka ce sai shi zata yi rayuwa dashi?, ko an gaya maka sonshi take yi ne wai?, ko kuwa shi Muhammad ɗin ne ya gaya maka yana son Intee ɗin haba?".

"Mansura yau ni kike kallo kina gaya ma wa'innan maganganun?".

Ganin yadda ta wani juya masa baya tana taɓe baki, tabbas yasan Mansura tayi nisa bata jin kira dan haka yana kallon Hammad da yayi tsuru-tsuru yana kallon iyayen nasa hankalinsa tashe yana dafe da kansa danji yake kamar zai rabe gida biyu.

"Muhammad kaje zamuyi magana daga baya".

Tashi yayi jikinsa a Mace ya fice daga parlon.

Yana fita Abbi ya dawo da dubansa inda Ummu take tsaye ya ce.

"Idan har kika ce zakiyi ma Muhammad baki, wai ko kuma ki ɗauki wani mataki akan auransa da Intee to wallahi Mansura a bakin auranki kemaaaaaaa".

Kamar saukar aradu haka taji furucin nasa, har bata san lokacin data juyo gaba ɗaya tana kallon Abbi ba, zuciyarta na wani irin bala'in tsalle a ƙirjinta, dafe ƙirjin nata tayi ido a waje ta ce.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Alhaji yau ni kike buɗe baki kake cewa zaka sake ni akan Ƴar Nuratu?, akan kawai nace ban amince da Ƴarta ta auri Ɗana ba?. Lallai ba shakka na ƙara yarda wallahi Allah Nuratu ta wanke ta baka kasha, yanzu duk irin baƙin ciki da Nuratu ta ƙunsa min da cin amanar data yi min duk baka ganin laifinta sai nawa?, hmm shikenan na san miye zanyi".

Ta faɗa tana barin Parlon da sauri kamar zata kifa a ƙasa tsabar ɓacin rai har hawaye take jin suna saukar mata akan kumatunta bata damu data tsaya ta share su ba, tayi gaba kawai bata ma gani sosai tsabar ranta da yake a jagule.

Tana fita Abbi ya zube akan kujera yana dafe kansa. Tabbas yasan ta wani wajan Mansura idan ta hana Ɗanta auran jinin Nuratu batai laifi ba, duk da babu laifin Nurau ko ɗaya akan ƙaddarar data faɗa mata a baya a tsakaninsu, hasalima laifin duk nashi ne da kuma na Mansurar, mi yasa lokacin da tasan shi mutum ne mai tsananin sha'awa da buƙatar Mace kullum a tare dashi amma ta ture komai nasa da buƙatarsa take fita ƙasashen waje?, taje ta daɗe bata dawo ba, duk akan wai tana zuwa neman haihuwa, ta barsa da ƴan aiki, wani lokacin ma da kansa idan yana matuƙar buƙatarta yake biyan kuɗin jirgi yaje har inda take, tayaya dama tana hakan wani abu bazai iya faruwa ba?, tabbas kaso hamsin a cikin ɗari laifinta ne..........

Chapter 24

*SAKINA POV*

A hankali ta miƙe tana ganin wani irin jiri dake ɗibarta, ga wani irin zazzaɓi kwana biyu da take fama dashi.

A hankali a daddafe ta shiga toilet ta watsa ruwa jikinta na rawar ɗari ta fito.

Zubewa tayi a ƙasa tana maida lumfashi a hankali zuciyarta na wani irin gudu, kwana biyun duk yanayinta ya canza, ta rasa mike damunta, ga wata irin kasalar jiki ga zazzaɓin da take kwana dashi ga jirin da take gani idan har ta miƙe tsaye, abinci ko wani irin ci take masa idan har ta dafa sai tayi ci uku huɗu a rana.

Wasu hawaye ne suka shiga zubo mata a jiki a sanyaye zata saka hannunta domin ta share kawai taji tattausan hannunsa yasa yana ɗauke mata hawayen. A hankali ta ɗago tana dubansa babu ƙarfi a tare da ita kwanciya taga yayi a jikinta ya rungumeta sosai shima duk kamar bashida lafiyar haka kawai taga jikinsa yayi sanyi a kwanaki biyun.

Ta fara ganin canji a tare dashi tunda ta fara basa addu'o'i da Inna ta turo mata ba kamar daba, yanzu kwata-kwata wannan ciwon nasa na kamar hauka idan ya tashi yake faffasa abubuwa ko ya kamata mutum ya shaƙe ko kuma ya kwanta jinyar da baya iya komai duk sun daina tashi, sai dai har lokacin bayayin magana, gashi nan dai sai kace yana gane abubuwa amma har lokacin idan ka kalli yanayinsa zaka shaida akwai sauran rina a kaba.

Motsin data ji ne a Parlo babu sallama da sauri zata miƙe taji jiri ya ƙara ɗibarta da sauri ta dafe kanta, ta ɗan tsaya tana maida lumfashi kamin ta dubisa tana masa alamar ya zauna yanzu zata dawo.

Ɗaga mata kai kawai yayi yana komawa a ƙasan ya kwanta yayi lamo.

Tana fita parlon ta iske Huda ta riƙe ƙugu tana kallon ƙofar bedroom ɗin, ganinta ta fito da kyar kamar wacce zata kifa a ƙasa gashi duk ta rame yasa Huda ƙara ware idonta tana dubanta tana cewa.

"Ke kuma miye abunda kike yi a bedroom nasa a yanzu?, da har baki fito kika fara gyaran parlon nan ba, baki duba kiga yadda yayi kaca-kaca bane?".

Kallon Parlon Sakina ta shiga yi, tabbas

20 / 40