Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
34, Tudun Wada Estate Funtua Local government Katsina State Nigeria*
Mamaki ne kware da gaske ya kusa kashe Inna da jin abunda Sakina take faɗa, bayan sun gama wayar da ita Inna ta dubi Humaira ta ce.
"Kinji wai wannan Matar bata da kunyar kira na ta kalli tsabar idon na take tabbayar ko Sakina na nan waje na?".
Humaira ta ɗan miƙe tana jin haushin Aunty Sakina ta ce.
"Ai ni wallahi Sakina tamin dai-dai data gudu daga gidan nan, haka kawai aje a zubar mata da ciki bayan akwai ubansa?, kuma an same shi ta hanyar alal?, ai mamaki ma ki daina indai akan Aunty Sakina ne, shi yasa musa masu ido kawai mu nuna muma bamu san inda take ba, duk ranar data bayyana kuma asirin ƴan gidan nan ne zai tuno, Allah ne dama ya kai Sakina gidan ne domin ta kawo ƙarshensu, kuma ni Doctor ɗin ta birge ni da bata bari sun san da zaman cikin ba, kinga ko ita Aunty Sakinar tunda bata sani ba ai an zauna lafiya, ranar da aka haifesa ya girma lokacin ne zasu sani, kuma Sakina tayi farar dabara data fahimtar da Doctor Halisa cewar a sanar damu komai, kinga hankalinmu ya kwanta mun san inda take, su kuma gani sukai babu ciki shi yasa ma suka rabu da binciken nemanta, shine ita Aunty Sakina zaƙal take son sanin inda take ko hmm?, ai ni naji daɗin ɗaukar cikin da tayi ma".
Murmurshi kawai Inna ta saki zatai magana suka ji an shigo Parlon Maami ce ya shigo a hargitse kamar wacce aka koro daga wajan.
Inna ta kalle ta mamakin ganinta a haka zatai magana ta rigata cewa.
"Kinga Malama ai ba sai kince min komai ba, burinki zai ciki na Ƴarki ta aurar min ɗana, kamar yadda akai ma Aunty Mansura haka nima ke son faruwa dani, wata ƙila ƙadddarmu a haka tazo ta kishiyoyi masu son zuciya da sun kansu, to bari kiji bazan taɓa son ƴarki ba har gaban abada, mu zuba ni da ke ne Nanaah a cikin gidan nan".
Tana gama faɗar haka ta juya ta barsu da mamaki bare Inna ta kasa hakuri ta dawo dubanta inda Humaira take ta tsare ta da ido kallo irin na tuhuma take mata, sai Humaira tayi ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Tabbas sun daɗe suna ƴar soyayya a ɓoye da Ya Harun, wacce ba komai ma a cikinta sai faɗa, domin shi isa da nuna shi Yayanta ne, kuma babba a wajanta ya isa da ita, ita kuma rashin kunya take masa wani lokacin, amma a haka suke wata irin bahaguwar soyayya wacce basa jin zasu iya rabuwa da ɗayansu, shi yafi ta shan wahala tunda Maami ke zuwa tana masa gargaɗi mai zafi akan ya kiyayi shiga harkar Humairar, ya kasa cireta a ransa duk lokacin da zasu zauna inuwa ɗaya yana samun wata natsuwar da janta faɗa kaɗai da yake yi, shi yaga tana turo baki haɗe da shagwaɓar nan kashesa suke da soyayyarta, soyayyarta tayi ƙarfin da dole babu yadda ya iya har yaje ya kasa daurewa ya sanar ma Abbu duk abunda ke faruwa, domin yasan Abbu ne kaɗai zai iya fahimtar shi, yasa abun ya yiwu ba tare da ɓacin rai ba ko wata hayaniya ba.
Abbu ne ya kira Abba ya shaida masa komai kuma Abban yaji daɗin maganar domin kota ina shi baiga aibun Humairar ba, dan haka kai tsaye suka yanke hukuncin tsaida ranar auransu da Y Harun da Humaira ba tare da sanin mata ba, sai jiya ne Abba ya kira ita Maami ya kira kuma Abbu a waya ya bata shine ya shiga mata bayanin komai, lokacin ta shiga ruɗani kamar zatai hauka, ganin fa da gaske abunda ke shirin faruwa da Ummu shine ke shirin faruwa da itama, su kam a haka ƙaddarar tazo iri ɗaya ta hanyar ƴaƴansu su auri Agolar dake gidajensu?, wa'inda basu ɗauke su a bakin komai ba, sai gashi zasu aure masu ƴaƴa rana tsaka, kuma babu yadda suka iya, tunda har Abbu yasa baki bata isa ta ce a'a ba, domin su suna shakkar Mahaifinsu suna masa biyayyar da kowa ya shaida hakan, domin nan take ta amsa da cewar ta amince tana kashe wayar Abba zai fara yo mata wani jawabin daya ƙara mata haushinsa da zafinsa na amincewa da yayi shima kai tsaye ba tare da ya nemi shawararta ba, sai kawai aje wani haɗata da Mahaifinta dan kawai a cuceta ta amince, kuka ta sakar masa na baƙin ciki, bai ce mata komai ba ya shanye maganar dake bakinsa domin yaga a ƙullace take dashi, idan ya ce zai ci gaba da yin magana abun na iya dawowa kansa yasan wace Haj Sha'awa itama wata irin birkakkar Mace ce itama wacce mai iya tanƙwarata sai Abbu ɗin kaɗai, kamar yadda Haj Mansura ta tanƙwaru, shi yasa ko can baya lokacin da zai auri Nanaah sai da aka danganta da Abbu tunkunna har Maamin ta aminta badan taso ba.
"Ina tabbayarki kinyi banza dani?".
"Uhm...uh.....In....Inna nifa ban san komai ba Allah".
Humaira ta ƙare maganar tana sosa ƙeya alamar rashin gaskiya ƙarara a jikinta.
Murmurshi mai ciwo Inna ta saki ta ce.
"Ina tsoron miki dangin mijinki Humaira, nasan tabbas ko baki ce komai ba a fuskarki ta nuna kina son Harun, bazan ce karki auresa ba, tunda har ina ganin alamar manya ma sun san da zancen, shi yasa ma har ita Maamin ta shigo tana min wannan gargaɗin, ke kika ji zaki iya Humaira amma kinga wa'innan sai kin tashi tsaye da addu'a domin Allah ya sassauta zuciyarsu ko kaɗan ne su daina nuna miki ƙiyayyar nan, idan ba haka ba zaki sha baƙar wahala ne a wajansu, amma kinga ita Bilkisu tayi sa'ar samun miji da danginsa, naji komai ta hanyar kirana da Asabe tayi ta sanadiyar Bilkisu kinga sun shiryu sun daina duk wani abu da baya da suke yi, kinga ita za'a kaita inda dangin mijin nata suke sonta hatta shi Aminu abokin wadda zata aura ɗin sai da Amina ta bashi number ta ya kira ni muka gaisa, ai duk kina gani aka haɗa ni da mahaifiyar shi Japhar ɗin daga gani Matar tasan duniya da abunda ke cikinta tasan ya kamata tana da kirkin da baki ma bazai iya faɗarsa ba, naso ace kuma kun samu Mazaje kamar irin na Bilkisu inda zaku je a tarairaye ku, ku samu soyayyar miji data danginsa shine zaku ji daɗin zaman gidan aure ba tare da wani mugun ƙalubale ba".
"Inna insha Allah su Maami zasu soni, ni dai kawai kimin addu'a tunda shi Y Harun ɗin yana min son da shi ya kasa hakura da gargaɗin data masa ya ɓillo da wata hanyar, na tabbata bazai bari a wulaƙanta ni ba Inna".
"Hmm tabbas hakane Allah ya kawo komai da sauƙi to".
Da amin Humaira ta amsa tana jin wani irin daɗi ya lulluɓe ta, saboda zata mallaki wadda take muradi, tunda tasa shi a idonta ganinsa na farko data yi ta fara sonshi bata sani ba, sai gashi wasa-wasa soyayya mai ƙarfi ta ƙullo a tsakaninsu daga shi har ita.
Inna na tashi tayi bedroom tana faɗin bari taje tayi wanka ta watsa ruwa kamin ta fito ta kula da Ummi dake bacci a kujerar da Innar ta miƙe ta amsa mata da to kawai.
Kamar jira ake Inna ta tashi Humaira taji an banko labule an wani shigo.
Ɗago kanta tayi ba inda fuskarta ta sauka sai akan Maryam da Ma'u dake mata wani irin ɗan iskan kallo.
Tashi tsaye tayi ganin yadda Maryam ta tako har inda take zaune tayi mata ƙere-ƙere a saman kai, yasa ta miƙewa ba shiri kaɗan ta matsa saboda irin kusancin da suka samu sosai da Maryam ɗin data tare mata gaba tana riƙe da ƙugunta tana wata irin jijjaga tana mata wani irin kallon uku saura kwata.
Ma'u ce ta fara cewa.
"Wato ke dai kin rantse da Allah sai kin auri Yayanmu Harun ko?, to bari kiji wallahi nesa tayiwa Yaro nisa sai dai ya ɗaga kai yayi kallo, amma tunda haka kika ce ga fili ga mai doki nan saura sukuwa kawai ta rage miki Humaira".
Murmurshi mai ciwo Humaira ta saki ta buɗe baki ta ce.
"Shin wai Aunty Ma'u da Maryam mina tare maku ne fisbilillahi?, mi nayi ma rayuwarku ne?, ko dan kawai nazo a matsayin Ɗiyar kishiyar Mahaifiyarku ne duk na cancanci wannan ƙiyayyar ne?, Inna fa na zaune daku tsakani da Allah ne, dai-dai da rana ɗaya bata taɓa ƙoƙarin cutar da waninku ba, mi yasa ku baza ku mance da komai ba ku aje komai a zauna lafiya ba?".
Wata irin muguwar harara Maryam ta fara jefama Humaira, tana mata kallon sama da ƙasa, kamin ta nunata da yatsa tana nunata dashi har tana dungure mata kai tana sane kuma ta ce.
"Ke dalla rufe ma mutane baki, har akwai wa'azin da zakiyi mana mu aminta dake ne?, ai tun a zamanin da can baya ba'a yarda da kishiya ba, bare a wannan zamanin daba tsoron Allah a ran mutane, dan haka an riga da anyi ma sunan kishiya wani irin baƙin fyentin da har gobe bazai goge ba, dan haka dama ace bata wannan tsatson kuka fito ba da mun iya amincewa dake a matsayin Matar Yayarmu Harun".
Wani irin maida hawayen dake shirin zubo mata Humaira tayi tana maida su tana kallonsu cike da takaicinsu ta ce.
"Kuma wata rana ma idan Allah ya so a haka zaku aminta dani a matsayin Matar tashi ba".
"Ke dalla can waye kike gaya magana a nan ciki kina banza dake?, ƙasƙantacciyar wacce Mahaifinta ya kasa riƙe su a gidansa ai anji haushi dai wallahi".
Ma'u ta faɗa tana yinƙurowa kamar zata kai mata duka.
Sosai maganar ta fara ɓata ran Humaira idan akwai abunda ta tsana a rayuwar nan shine ka kushe mata iyaye, komin lalacewar Mahaifinsu lokacin da Inna ta aure sa yana ciyar da ita, kishiyarta ce ta hana ta zaman gidan sai da tasan yadda tayi tasa Inna ta bar mata gidan, tabar su Humairar a gidan, sunsha wata irin ɓakar azabar data kusan halaka su a wajan Matar uban nasu, sai wata rana da ƙannan Inna suka kai masu ziyara suka ga irin izayar da Matar ke gana masu yasa suka tada rigimarta sai an basu su Humaira sun koma dasu, anyi ɗauki ba daɗi da ƙar uban nasu ya aminta saboda shima baya son irin izayar da ake gana masu yana gani kuma ace babu yadda zaiyi?, dan haka ya aminta ranar sunsha tashin hankali da Matar tashi, a haka suka koma gidan Kakanninsu da zama, sai dai shima ƴaƴan kishiyar Kakarsu sun taso su a gaba da shirri kala-kala, wai suna ƴaƴa mata sun kai matakin aure amma sun masu zaune a gida, suna masu gorin ko uwarsu ta dawo gidan yanzu bata da wajan zama a cikinsa bare su, Humaira ce mai zagewa ta kwatar masu ƴanci sai rana ɗaya suka runtsa ta duka ranar kuma suka ce sai ta bar masu gidan, shine musabbabin dawowarta gidan su Ma'un, ita kuma Sakina ashe ƙaddar ce ta fitar da ita itama, sai dai duk da hakan gidansu Bilkisu Inna tafi zama a cikin tashin hankali, domin su rigima ce ake babu dare babu rana da Inna Asabe take tada ta, har dai Allah ya kawo ƙarshen zamanta a gidan su Bilkisu lokacin Bilkisu nada Shekara sha uku tabar gidansu, lokacin da Mahaifin Bilkisu ya saki Inna sai taji kamar an sauke mata wani gungumemen dutse ne a saman kanta, hamdala kawai tayi da rabuwar auran, saboda kwata-kwata Inna bata son tashin hankali, shine ta dawo gida da zama akaita ɗauki ba daɗi da kyar wani makwafcinsu yaga irin halin matsin da Inna take ciki a gidan nasu ma bata tsira ba, domin zaman babu daɗi ko kaɗan gasu Humaira ga ita, shi yasa zaman duk ya isheta, makwafcin suna mutumci da Matarshi, ya samo mata wani abokinsa Abba kenan Mahaifin su Ma'u, ya ce ta aure shi zata ji daɗi har abada ta gama kukan gidan aure sai dai abunda ba'a rasa ba, ita kanta Inna taga alamar hakan saboda duk yafi sauran Mazan data aura nagarta da sanin ya kamata, dan haka bata wani jaba ta amince da auran nasa, akai auran ta tare a gidan su Ma'u, tana fuskantar matsi da takura a wajansu, saima yanzu ne abun ya ɗan kwanta.
"Ke matsiyaciya ana miki magana kinyi kunnen uwar shegu da mutane tsabar raini da rainin wayo?".
Ma'u ta faɗa tana dungure mata kai.
Wani lumfashi mai zafi Humaira taja ta faɗa dogon tunanin duk yadda Innar tasu tayi rayuwa a kowanne gidajen aure bata shiya ma hakan ba, kawai tunanin ne ya faɗo mata a kwakwalwar kanta.
"Mi zance maku ne Aunty Ma'u, cin mutuncin har sai an haɗa da Mahaifi na?".
"To Mahaifin naki uban waye shi a ƙasar nan da baza'a zage shi ba?".
Humaira bata san lokacin data ɗaga hannunta tana niyar sauke ma Maryam datai maganar mari ba.
Kamar an jefo Inna ta faɗo parlon tana cewa da ƙarfi.
"Kul karki kuskura hannunki ya kai jikinta Humaira".
Da sauri Humaira ta dunƙule hannun nata tana runtse idonta da ƙarfi zuciyarta na soya tana mata wani irin zafi, ko banza tana fa son Mahaifin nan nata, ai ba banza ya koma haka ba, yanzu wama ya sani ko yana raye?, ya yake ma? Allah kaɗai ya sani, domin rabonta dashi tun lokacin da suka bar gidansa, ba'a ƙara bari sun doshi inda yake ba, soyayyar uba daban fa take, koda ace uban nan mahaukaci ne.
"Kuyi hakuri su Ma'u dan Allah".
Ba haka suka so ba Innar ta basu hakuri ba, so Maryam tayi hannun Humaira ya kai jikinta, tayi mata ɗan banzan dukan da yau zata kasa tashi, so tayi faɗan karya ƙare yanzu ayita yi har komai ya wargaje.
Juyawa sukai suna sakin wani dogon tsaki haɗe da yana maganganu masu zafi akansu.
Inna ta runtse idon tana jin ciwo sosai kamin ta dawo da dubanta akan Humaira zatai magana Inna ta ɗaga mata hannu, hakan yasa ta tsuke bakinta tayi shuru kawai kanta a ƙasa.
"Mi zaki ce min Humaira?, ashe baki da hankali da wayo ban sani ba?, kin san su waye dangin miji kuwa?, kike ƙoƙarin ɗaga hannu kice zaki mari ƙanwar wadda kike son aura?, anya kina tunanin abunda ya dace daya kamata kuwa?, to ya kamata ki shiga taitayinki Humaira ki gyara ma'alarki dasu, komiye zasu faɗa miki ki shanye ki kauda kanki, hakan ne kawai zaisa ki mallake su kansu da shi Mijin naki, kece fa kika ce kinji kin gani zaki aure masu Yayansu, dan haka ma ki ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan saurin fushin naki da saurin kai hannu a jikin mutum, ba komai kike gani ana biye ayi faɗa akai ba ko ayi cece kuce ba Humaira, shifa hakuri da kike gani mai yinsa ba'a taɓa cin galaba akansa, da ace tun lokacin da suka shigo baki biye masu ba da yanzu bai kaiku da hakan ba, da yanzu sun gaji da ɓaɓatunsu sunyi gaba, baki gani bane dana fito na basu hakuri duk da nafi ƙarfin hakan, amma na basu hakuri dan kawai na tura masu aniyarsu?, sai gashi babu abunda suka ƙara iya cewa suka fice ba?".
Sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi Humaira tayi tana komawa ta zauna ta ce.
"Hakane Inna".
Inna itama ta zauna ta ce.
"To haka ya kamata kema ki rinƙa daurewa komai ki rinƙa shanye sa, ki maida komai ba komai bane Humaira kinji, sai fa kin kai zuciyarki nesa zaki ci ribar zamanki dasu, su wasu irin mutane ne sai an daure an toshe kunne tunkunna zaki ga komai yazo ya wuce".
"Tabbas Inna zanyi ƙoƙarin yin duk abunda kika ce, amma Inna zuciyata ce bata da haƙuri irin naki fa, Inna kina ji yadda suke ci ma Ubana Mutunci mutunan da bai ma sansu ba, bai san mi akeyi ba?".
"To kuma komai lalacewarsa a hakan za'a tafi a nemi auran naki a wajansa ba".
Daɗi ne ya rufe Humaira saboda itama tunaninta kenan kar ace za'a ɗaura mata aure ba tare da an nemi dangin ubanta ba, gara aje can komai lalacewarsu a dai je a ɗauro auran nata a can, domin ma kar su Ma'un da uwarsu su ƙara samun ƙofar wulaƙantasu.......
Chapter 44
*House No: 13, Surure Estate Lagos Nigeria*
A hankali ta zauna tana miƙe ƙafafunta, ta dubi Doctor Halisa dake zama akan kujera dake parlon, shigowarta kenan ta dawo daga Hospital, Doctor Halisa ta sauke lumfashi tana kallon Sakina data miƙe ƙafafuwanta da suka dan kunbura saboda yadda cikinta ya zama tsoho, haihuwar na iya zo mata ko yaushe ne ma, saboda daka gani zaka san cikin nata ya shiga watanshi na haihuwa, ko bai kai watan shi na haihuwa ba ƙila yana gaf da shiga watan haihuwar, cikin nata yayi wani irin ƙasa da yawa, gashi yayi tsini haɗe da girma sosai, shi yasa duk ya hurata ta zama ƙatuwar ƙarfi da yaji.
"Sannu da gida Sakina, ya jikin naki?".
Sakina ta sauke ajiyar zuciya mai zurfi tana ƙara miƙe kafarta sosai yadda zata ƙara jin daɗi, sosai cikin ke mata nauyi ainun yana mugun takurata haɗe da wahalar da ita, ko bacci da kyar take yinsa, data juya cikin nata ke mata harƙeƙe, nishi da shaƙar iska da kyar take yinsu, gaba ɗaya abun ya uzzura mata.
"Alhmdllhi Aunty Halisa".
Sakina ta faɗa da yake yanzu haka take kiranta da Aunty Halisa kawai, saboda yadda ta bada gudunmawa wajen kulawa da rayuwarta da abunda ke cikinta wadda take jin bala'in sonshi har ya zarce yadda take son kanta, sai kuma uban cikin da soyayyar cikin yasa take ƙaunar jininsa.
Kunna Tv Halisa tayi tana miƙewa ta kamo mata tashar labaren hausa, tana niyar shiga cikin bedroom nata, saita ɗan tsaya tana dubanta ta ce.
"Bari naje ciki