Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
canza komai dai-dai da tsinke ba'a bari ba, kamin ya shiga Part ɗin nasa, domin ma karya iya tunowa da rayuwa da yayi da wata Mace, kar kuma yaci karo da abunda zaisa ma tunaninsa wasi-wasin kamar ya taɓa rayuwa da wata.
Sai dai Allah ba azzalumin bawansa bane da kansa Sadeeq ɗin ba wani ya bashi labari ba ya fara jin kamar akwai abunda ya kamata ya tuno ya kasa, domin P'A nasa da yasan komai nasa ne yake faɗa hakan, lokacin shi kansa P'A ɗin nashi sai da suka bige masa wornig mai zafi, duk da dai bai san abunda suke shiryawa ba, a lokacin da yake halin rashin lafiya dai-dai da abokan arziƙinsa basa bari su Haj Hauwa azo inda yake, sunyi masa wani mugun takunkumin da ba mahaluƙin da ya isa zuwa inda yake, shi yasa basu san komai ba dangane da auren da yayi dake Sakina, shine fa yanzu Alhaji Abubakar Imam yake shirin dawowa ƙasar domin tasa hankalinsa ya dawo kan ya dawo kawai ɗansa ya samu lafiya za'ai auransa da Huda wadda can baya akai alƙawari dama, da yake tayi mugun gamawa dashi sai abunda ta ce yasa shi fara shirin dawowa ƙasar, yanzu haka naji ance yana gaf dawowa ƙila sai ana saura kwanaki ɗaurin auren zai dira a ƙasar.
Sauke lumfashi mai tsawo Halisa tayi tana ƙara sauke ajiyar zuciya ta gyara zamanta tana kallon yadda Sakina ta shiga wani irin mugun yanayi tana shashshakar kukan tausayin labarin Mijinta da irin tagayyara rayuwarsa da aka su ayi, anma yi kawai Allah ne bai basu ikon idasa tagayyara rayuwarsa, kuka kawai take idonta sunyi jawur.
"To kinji labarin Sadeeq Mijinki, daga farko har ƙarshe, shi yasa na ce miki su Haj Hauwa hatsabibancin su ya wuce duk yadda kike tunani, akan cikar burinsu zasu iya yin komai ciki harda kisa, kisa ai sunma yishi ba sau ɗaya ba, tunda sune sanadiyyar salwantar da rayuwar Mahaifiyar Sadeeq ɗin".
Runtse idonta Sakina tayi ƙirjinta na duka mararta taji ta ƙulle tsabar tashin hankalin labarin daya sata, wasu irin mutane ne su Haj Hauwa?, wa'inda basu san komai ba sai tsabar rashin imani da son kansu, wacce irin rayuwa ce muke ne yanzu?, ace ƴar uwarka ku fito ciki ɗaya kayi ma wannan babbar illar ina ga wani kuma?, tabbas idan tayi mata ai ba komai bane tunda har tayi ma wacce ma suka fito ciki ɗaya, rashin imanin Haj Hauwa ya zarce na kowa ma take gani.
Mararta ce ta ƙara ɗaurewa da yasa Sakina dafe cikinta tana salati ƙasa-ƙasa, wani irin ciwo ya fara taso mata abun kamar wasa.
Doctor Halisa hankalinta ya tashi bata taɓa kawowa labarin zai sata cikin halin damuwa da kiɗima irin wannan wadda ta ganta ciki ba, har hakan na ƙoƙarin taso mata da naƙuda bata shirya ba.
Dan haka da sauri Doctor Halisa ta kamata da kyar da kyar suka fita daga harabar gidan nasu, Allah yaso tana Motar da aka mallaka mata ita a wajan aiki, saboda a rage mata kashe kuɗin zirga-zirga.
Sata tayi a Motar suka nufi asibitin da take aiki.
A ruɗe Halisa ta ƙarasa asibitin ganin ita ce da kanta tazo da marar lafiya yasa aka tarbe su cikin sauri da girmamawa.
Kai tsaye harda ita aka shiga ɗakin haihuwa da Sakinar.
Sakina tasha wata irin ɓakar azabar da tunda take bata taɓa hasaso haka dama ake ji ba wajan haihuwar, tayi mugun laushi haɗe da sadaƙarwa mutuwa ma kawai zatai.
Ƙarfafa mata gwaiwa da Halisa keyi ne ya ƙarasa mata ɗauriya tasha wahala tayi dogowar naƙudar da ba'a su kamin Allah yasa ta sauka lafiya, ta haife ƴaƴa Mata su Uku sai dai ɗaya nan take bata zo da rai ba.
Halisa tayi wata irin murnar da harta rasa inda zata saka kanta, yanzu da wannan kyautar Allahn za'a zubar na ƴaƴa har Uku?, to da ina zata kai zunubin nan?.
Ita kanta Sakina kuka ta rinƙa yi tana kallon Yaran, taji babu daɗin da aka ce ɗaya bata zo da rai ba, amma a hakama ta gode Allah da irin ni'imar da Allah yayi mata, wacce ba kowa yake yimawa ba.
A ranar ta kira su Inna ta shaida masu, Allah Sarki uwa da ɗa, Inna harda hawayen murna Humaira ko ji take kamar tayi tsuntsuwa ta kai kanta inda ƴar uwarta take, murna harda tsalle, ranar Harun ta kasa gane kanta tsabar yadda take murmurshi ita ɗaya ko ta saki dariya kamar sabuwar kamu, ita da Inna saika rasa wanne yafi wani murna da sauka lafiyar da Sakinar tayi?, daɗin daɗawa ma ƴaƴa har Uku ɗaya ce kawai ta koma, Inna ta rarrasheta tana addu'ar Allah yasa ɗayar mai ceto ce.
Sosai Inna ta ƙara kwantar mata da hankali saboda ta gaya mata tana hauhawa ba daɗewa zasu dawo gida su fuskanci su Haj Hauwa, tana jin tsoron shirri irin nasu Haj Hauwa, inda Inna ta ce insha Allah cutar da suke ma bayin Allahn nan ta kusa zuwa ƙarshe, ƙarta wani damu ta ci gaba da gayawa Allah, Allah zai ɗorasu akansu, sana ta gaya mata cewar itama Humaira ta samu Miji harta sanar da ita waye.
Sakina ta ɗan shiga fargaba inda take ce ma Inna anya abun nan zai yiwu kuwa?, saboda tasan su waye su Maryam da uwarsu, Inna ta ce to Sakina ya zanyi da ita?, tunda ta ce taji ta gani, kawai ni na bita da addu'a ne kawai haɗe sa addu'a Allah yasa shine mafi alkhairi.
Itama Sakinar addu'a tabi ƴar uwar tata dashi kawai sukai sallama inda ta ce zata turo ma Humaira photon Yaran saboda yanzu tana da wayar kanta Humaira Harun da sai mata, wayar da akayi ta ɗauki ba daɗi da sai matan da yayi, da kyar Abba ya kashe maganar, domin Maami faɗi take tun yanzu za'a mallake mata Ɗa, sai abunda suka ce zai rinƙa yi, tun yanzu ya fara kashe mata kuɗi inaga ya aure ta?, ai sai abunda ta ce dashi kawai.
Da kyar Abba ya kashe maganar amma duk da hakan su Maryam sai da suka ci gaba da gaya mata maganganu masu zafi, tayi ƙoƙarin kauda kanta kamar yadda Inna ta gargaɗeta, amma sai da tayi yaƙi da zuciyarta sosai kamin ta iya shanye baƙaƙen maganganun da suke gasa mata.
Tana ji Abba ya ce za'a haɗe bikin Maryam da nasu ayi lokacin ɗaya, dan haka ba wani ɓata lokaci gidan taga su Maryam an fara zuwa gyaran jiki an fara hidima kamar mi, itama Inna batai sanya ba wajan fara gyara ƴarta ciki da bai, dai-dai ƙarfinta, ta shiga sanar da ƴan uwanta, wasu daga ciki sun fara mata surutun bata gudun shirrin kishiya da har zata ɗauki ƴarta tabawa Ɗan kishiya?, ita dai ta toshe kunnenta ta ce duk wadda bazai zo ba babu dole ta hutar da kowa, ƴan gidasu Maza wannan aure na Humaira yaso tada fitina ganin wai Inna ta kai ɗaurin auren nata wajan dangin Mahaifinta, kuma lokacin Mahaifin nasu Humaira na nan raye ya rabu da Matar nan tashi sai dai yana fama da wata irin jinyar da baya iya zuwa ko ina sai gida, kuma yaji daɗin yadda Innar ta bashi girma ta hanyar zuwa neman auran Humaira a wajensa, sai dai ta aiko masa cewar yayi hakuri auran Sakina yazo ne bakatatan shi yasa har ba'a zo wajensa ba, kuma Insha idan komai yayi dai-dai Sakina zata zo da Mijin nata har inda yake su gaishesa, bai nuna wata damuwa ba shi dai yayi murnar kawo auran Humaira a wajensa.
Hakan ya sake hassala ƴan gidansu Inna Maza dan gani suke Mai abun hannu Humairar zata aura dan haka ne suka fara wata kankanba ta banza suna yada maganganun cewar ai dama basu ɗauke su ƴan uwa ba kaza-kaza, har sun manta cewar sufa suka koro mata ƴaƴa rana tsaka, amma har sun mance da abunda sukai, da yake abun duniya ne suka gani yasa suke ta haƙilo, ita dai Inna ko wacce magana aka kawo mata zata toshe kunnenta tayi kamar bata ji ba, domin tasan su waye su sai dai ta bada labarin su kawai.
A can gefe guda Aunty Sakina sai da ta taho bikin tunda wuri takanas saboda so take ta gani shin da gaske Sakina bata wajan Inna, ta kuwa gani bata nan ɗin, dan kwata-kwata sai suka nuna mata ai tana can gidan aikin nata data kaita ai sun ɗauka tana can, ganin kamar asiri na shirin tonuwa allura ta tonu girma yasa Aunty Sakina tsuke bakinta tayi shuru kawai aka ci gaba da hidimar biki tare da ita.
Aunty Sakina taso ace ta bigi cikinsu ta san inda Sakina ta gudu koda ace sun sani, saboda Haj Hauwa tayi mata alƙawarin idan ta gano inda take to zata yi mata babbar kyauta, sai gashi kuma ta kira ta ta ce mata tabar wannan binciken, domin bashi da amfani tunda dai Sakinar lokcin data gudu an tabbatar masu da babu wani ciki dake gareta, dan haka sun rabu kenan.
Gefe guda ma su Sakina an sallamo su daga asibiti da Yaranta dake mugun kama da Mahaifinsu, yaran ƴan ɓul-ɓul dasu gwanin sha'awa, gasu da cikakkiyar lafiya, itama kanta ta samu lafiya saboda irin yadda Halisa ke kulawa da ita, sosai take ƙara gyara mata jiki ciki da bai, danta ce sati na zagayowa zasu wuce Kano, sosai Yaran suke ƙara girma suna yin ɓul-ɓul nonon Sakinar nada wani irin kyau da yake sasu ƙara ƙiba dandannan, kuma nonon yana isarsu sosai shi yasa Sakina ke samun abinci mai yawa na gina jiki tana ci, sosai Halisa ta dage ta wannan fannin ta ƙara bata abinci masu gina jiki, gefe guda kuma ta gyara mata jiki kamar wata amarya, ko wata amayar ma sai haka, ta ƙara wani irin kyau tayi ƙiba saboda ƙibar cikin har lokacin bata sake ta ba, ta ƙara zama babbar Mace, Sakina na jin Yaran nata kamar mahaifinsu ne a tare da ita, tana masu son da baki zai faɗu ba, idan tana kallonsu sai taji kwarin gwaiwar tunkarar su Haj Hauwa.....
Chapter 46
Zan iya cewa kusan rana ɗaya ne akai shagalin bukukuwan su Intee gaba ɗaya, har su Humaira da Bilkisu kusan rana ɗaya ta kama.
A ɓangaren su Intee sosai Hammad ya shiga wani irin busy mai tsananin gaske, sosai yake kewar Intee domin rabonsa da ita tun ana saura wata ɗaya bikin bata ƙara fita waje ba, bare taje Office, sosai Ammi da Mimi data baro Niger ita da Khairat suka dawo gidan Aunty Nuratu aka dawo da bikin harna Japhar ɗin duk kusan rana ɗaya, ɗaurin auran yayi yawa sai wasu aka bari sai Asabar wasu aka ɗaura juma'a.
A bangaren su Bilkisu ranar Juma'a aka ɗaura aurensu ita dasu Amina da Binta, yadda su Inna Asabe suka zage damtse wajan gyara ƴaƴansu haka suka zage itama suka gyara Bikinsu babu nuna son kai ko nuna cewar Bilkisun ba tasu bace, sosai Bilkisu yanzu take jin daɗin zama dasu take kuma alfahari dasu, ta samu ƴanci sosai fiye da tunanin mai tunani a gidan nasu.
Sai da aka fara shailar ɗaurin aure kamin Bilkisu dashi kanshi Ogan naku Japhar ya shaida dashi aka ɗaura auran Bilkisu sauran ɗaurin auren nasu Naseer ya biyo baya.
Mamaki fa ya kasa kashesa domin tsabar ruɗewa yama kasa cewa komai, dama tun jiya yake mamakin wai su Abba da Abbi suna nan tafe ɗaurin auran su Aminu, kuma gani yake ai tunda shi yana nan ba sai sun halicci ɗaurin auren abokansa ba, saboda har sun gama Bautar ƙasar su sun koma da wata ɗaya bikin yazo, shi yasa ma su tun ana gobe ɗaurin auren suka taho suka kama hotel.
Abun ya ƙara ɗaure masa kai sosai, su Naseer ana idasa ɗaurin aure suka cikasa da tsiya iri-iri tun yana sharewa har ya fara biye masu, domin ba ƙaramin faranta ransa so kai ba, yama rasa da bakin da zai gode masu, da har ya sadaƙas cewar Aminu zai sami Bilkisu, harga Allah bai san cewa sonta yake ba sai da bikin ya ƙarato yana gani abokinsa na shirin auran wacce yake bala'in so, amma zuciyarsa da gangar jikinsa sunƙi basa haɗin kai cewar sonta yake, gani yake kawai tausayi ne take basa, sai da yaga dimi-dimin zai rasata ya yarda cewar tabbas sone yake mata na haƙiƙa, baya jin ko Aminun zai sota yadda yake jin sonta a ransa.
Yayi mamakin yadda har Mimi ta sani da Khairat, suka kira shi suna masa murnar ya zamo ango, suna kuma masa tsiya kamar ba ƙanwarsa da Mahaifiyarsa ba, sai ka rantse abokan wasa ne.
Ya rasa wane irin farin ciki zaiyi ne, sai kawai ya faɗi yayi sujjada ga Ubangiji yana gode ma Allah haɗe da rungume abokansa yana jinsu kamar jininsa uwa ɗaya uba ɗaya, ganin yadda yayi laushi ya zama ba kamar Japhar ɗin da suka sani ba, mai kauda kai mai yin abu kai tsaye marar son magana gashi da kwarjini da kame kai, ga wata izza da isa, sai gashi yau duk babu su ya zama kamar bashi ba. Ganin hakan yasa suka rabu dashi suka daina masa tsiyar ta kasa tunkarar wacce yake so yaƙi yarda da son nata yake yana shirin rasata.
Ita kanta Bilkisun lokacin da labari yazo mata cewar itafa yanzu bada Aminu aka ɗaura auranta ba da Japhar ne, kuka kawai ta saki, ta kuma rasa na baƙin ciki ne kona murna ne?, bata dai jin auran a ranta sosai haka kuma bata ƙinsa.
Ta taya Amina murnar samun mutum mai barkwanci kamar Aminu, ta ƙara taya Binta murnar samun miji itama irin Naseer.
A ranar aka ɗauki kowacce aka nufi gidanta da ita, da yake duk ba gari bane yasa aka raba tafiyar, sai da aka fara ɗaukar Bilkisu aka kaita Funtuar wajan Inna dake fama da jama'ar biki itama na auran Humaira da aka ɗaura shi a ranar suma, taje ta gana da Inna kamin aka wuce da ita Kaduna kai tsaye.
A gefe guda Sakina taso halaltar bikin ƴan uwanta su duka amma abun bai yuwu ba, saboda a can suna ta shirin tahowa Kano itama, fargabar abunda zai je ya dawo ne ya hana Sakina sakat danma Halisa na ƙara kwantar mata da hankali sosai.
A ɓangaren su Maryam ma ana ta hada-hadar miƙata Kudana saboda da wuri Abba ya ce za'a miƙa kowacce ita Humaira a cikin garin Katsina Y Harun zai ajeta saboda a nan yake aiki, amma Maami ta ce ayi mata alfarma a bari kai Maryam sai gobe, dan haka aka ɗage kai Maryam sai washe garin ɗaurin auren, Maami ta so a aje Humaira a garin da take, amma Abba ya ce tayi hakuri tunda ga inda yayi ginin gidansa.
Ranar ma sai da aka fara tada ƙananun maganganu wa'inda suka kusan saka ayi faɗa mai tsananin gaske kuwa, sai da maza suka dawo ɗaurin aure aka tsawatar tukunna abun ya ɗan lafa, amma ƴan uwan Inna da sun fito sai ƴan uwan Maami sun tirkesu da wata baƙar maganar, danma suma ba baya ba wajan yaɓa baƙar maganar, kana faɗa masu zasu amayar maka kaima.
Sauƙin ɗaya ma Ummu bata halacci bikin ba tana can itama da hidimar bikin ɗanta da ake aurama ƴaƴa har biyu, shi yasa kowanne ya tsaya hidimarsa dolensa.
Bilkisu tunda akaje da ita gidan Ammi taga wata irin tarairayarta da ake yi kamar jaririya ayi nan-nan da ita, yasa hankalinta ya ƙara kwanciya, sai dai taji ba'a ma ƙasar za'a aje ta ba Niger zasu wuce ranar Lahadi, bayan an gama bikin mutane sun ɗan watse.
Intee tun ranar Juma'a da aka ɗaura aure aka nufi gidanta da ita dake cikin garin Kaduna, a tare zasu zauna da Maryam da aka ɗaura aurenta bayan anyi na Intee ba'a kawo Maryam ba sai ranar Asabar, kowacce da Part ɗinta mai kyan gaske ga bene kowanne a Part nashi, Part Huɗu ne a gidan a tsarin Hammad nashi Part ɗin daban sai na Yara idan Allah yasa sunzo duniya sai kuma na Matan gidan, wadda cikinsu yawan bedroom na kowanne Part zai isa har ka sauke baƙinka idan wata rana sunzo, kowanne Part shaƙe yake da kaya na kece raini anyi bajinta tako ta ina.
Tunda aka kawo Intee take ta faman kuka kamar ba gobe tana kukan rabuwa da Ammi ashe dama haka ake ji?.
Tayi kuka har sai da idonta suka kunbura sosai.
Batai tsammanin zata ganshi a ranar ya shigo ba, ta ɗauka ko sai an kawo Maryam ne, bata san shi baccin Abbu da Abbi da suka tsaresa da nasihar idan har baiyi adalci ba a tsakaninsu to tabbas ya kuka da kansa da fushin Ubangiji, domin shi kansa yasan gaskiya ba son Maryam yake ba, hasalima kallon Ƙanwa yake mata shi yasa auran nata yake jinsa sai a hankali kawai.
Intee lokacin da taji saukar lumfashinsa akan wuyanta yasa bata san lokacin data yaye gyalen data rufe fuskarta dashi ba, tana jefa masa wani irin kallo mai wuyar fassarawa, a kwanakin da suka daɗe basu haɗu ba gani tayi ya ƙara mata wani irin mahaukacin kyau mai ɗaukar hankali mai tsananin gaske.
Bata san lokacin data lumshe idonta ba tana sake kame jikinta ƙamshin mayen turarensa na ƙara kassara mata gaɓoɓin jiki, ga gajiyar bikin da tayi mata rufdugu duk da ba wasu shagulgula akai ba wa'azi ne kawai akayi ranar Alhamis sai ɗaurin auren da akai juma'a shikenan.
A hankali taji yasa hannunsa mai bala'in taushi kamar na wata Macen ya janyota jikinsa, bata hanasa ba hasalima ji tayi, tayi bala'in kewarsa ainun, kewar faɗan da suke yawan yi, kewar rashin kunyar da take masa yana mata mugunta, komai ma nasa kewarsa take.
Wani irin azababben abu take ji yana taso mata akansa, runtse idonta tayi da ƙarfi tunowar wai fa ba ita ɗaya keda shi ba ko?.
Tunda take bata taɓa jin kishinsa ba irin na yau ɗin, tunda take bata taɓa jin ciwon haɗasa da akai da