Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
neman afko masu har cikin gida.
"A'a miye haka zan gani Nuratu?".
Wata irin ajiyar zuciya Nuratu ta shiga saukewa akai-akai tana jan lumfashi da kyar ta fisgo magana a bakinta ta ce.
"Inna a bige fa yake ya zo nan".
"Mtssww to sai mi idan a bigen yake iyee?, shine zaki wani shigo ma mutane a haka sai ka ce wacce mutuwa ta biyo?, ai kin tsaya ku gama dai-daitawa da juna ko?".
Saurin kallon Inna tayi tana buɗe baki cike da mamakin Innar ta ce.
"Inna a bige fa yake yaya za'ai mu iya fahimtar juna dashi yana a haka?, kwata-kwata baya cikin hankalinsa a yanzu ɗin".
"So kawai kike dama ki samu kofar zillewa, amma mudun ina raye baki da Miji sai Sagir wallahi".
"Inna ai bance komai ba".
"Idan ma kince ɗin shine nake ƙara gaya miki ai".
Ta faɗa tana zama akan tabarmar data tashi shigowar Nuratun a guje yasa ta miƙe ba shiri.
Abinci ne a gabanta tana zubawa ta miƙa ma Nuratun tana faɗin.
"Gashi nan sai kuzo ku ci, babu abunda kuke tsinana min sai kuci ku kwanta kawai, ai gara kizo kiyi auran kona samu na rage nauyin da kuka ɗora min, an mutu an barni daku an barmin nauyin da bani ya kamata na ɗauka ba".
Ɗaukar abincin kawai Nuratu tayi tana jin wani iri tayi ɗakinsu.
Tana shiga ta iske Sadiya zaune tana kuka har lokacin sai shashshaka kukan take tana kallon kofar shigowa ɗakin nasu tana haɗiyar zuciya.
Aje abincin Nuratu tayi tana matsowa kusa da Sadiya da sauri ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Haba Sadiya nasha gaya miki bai kamata kina sa'insa da Inna ba, yaushe zaki ɗauki maganar da nake gaya miki ne?, ke ce masha wuya fa, kar Allah yayi fushi dake Sadiya saboda irin yadda kike ma Inna, ya kamata ki rinƙa hakuri da duk abunda zata rinƙa yi mana, na faɗa miki ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba watan wata rana komai da kike gani zai wuce ne ya zama tarihi kamar ba'a taɓa yinsa ba".
Riƙe hannun Nuratu dake ƙafaɗarta tayi tana ɗan kwantowa a jikin Nuratun kamin ta ce.
"Amma Aunty ai ita ce Allah zaiyi fushi da ita saboda irin yadda take ƙuntata mana, kuma ni nake ganin ai gaskiya ce kawai nake faɗa mata. Aunty Nuratu yanzu auran wannan Mashayin Giyar nan zakiyi Sagir?".
Ƙasa da kanta Nuratu tayi tana jin wani irin abu a zuciyarta kamin ta ɗago idonta ya cika tab da ruwan hawaye ta ce.
"Yaya zanyi ne Sadiya dole nabi maganar Inna, bana son abunda zaisa tayi mana baki, so nake kawai mu rabu lafiya da ita".
Tashi tayi daga jikin Nuratun tana kallonta kallo irin mamakin maganar data faɗa.
"Aunty sai mi idan Inna ta tsine mana?, akan gaskiyarmu da son lalata mana rayuwa da take akan kawai zamu bijire mata wajan illata rayuwarmu da take yi, idan ta tsine mana Allah ma bazai taɓa amsar tsinuwar tata b.......
Tsinketa da wani mari Nuratu tayi wadda ita kanta Nuratun bata san lokacin data ɗaga hannunta ta wanke Sadiyar da marin ba.
Gaba ɗayansu kallon junansu suke ƙirjinsu na bugawa kamar zai fita daga jikinsu.
Sadiya dafe take da kumatunta tana kallon Nuratu kawai dake kallonta itama zuciyarta na daka sosai.
Nuratu bata san lokacin data jawo Sadiya ta ƙanƙameta a jikinta ba tana sakin wani irin sassayan kuka.
A hankali Sadiya ta saki ajiyar zuciya tana jin hawaye masu zafi itama na zubo mata kamar an buɗe fanfo.
"Aunty dan girman Allah karki bari a kashe rayuwarki a banza a wofi, karki bari ki auri irin mutum kamar Sagir, idan kika yarda kika auresa ki shirya amsa tambayoyin da ƴaƴan da zaki haifa zasuyi miki wata rana, domin zakiyi ma rayuwarsu babban taɓon da bazai taɓa gogewa a cikin rayuwarsu ba".
Wani kalar kuka mai taɓa zuciya Nuratu ta ƙara saki tana sake riƙe Sadiya sosai dake jikinta ta ce.
"Babu yadda zanyi ne Sadiya, Mahaifiyata ce ina so na gama lafiya ne da ita, kawai shi yasa kika ga ina ƙoƙarin yin duk wani abunda take so, zanyi ne kawai domin bana so Allah yayi fushi dani a ranar gobe, kema kuma bana so daga yau ki sake faɗar cewa Inna ta tsine mana, kima cire wannan maganar daga bakinki daga yanzu daga rana irinta yau, karki sake kar naji kin sake faɗar haka Sadiya".
Shuru kawai Sadiya tayi tana ɗaga kanta alamar taji, tana kuka mai sauti itama.
Motsin Inna da suka ji ne tana niyar shigowa ɗakin tana mitar data saba tana cewa.
"Wai shashshakar kukan ubanmi nake ji ne a ɗakin naku?, ko haɗuwa kukai kuna kuka kuna zagina, ta yadda idan wani yayo sallama ya shigo ace ina yankan naman jikinku ina cinyewa?, ko kuma ace min ni kishiyar uwarku ce ba?".
Da sauri suka saki junansu Nuratu na share hawayenta da sauri itama Sadiya ta shiga goge nata hawayen.
Jawo kwanon abincin Nuratu tayi a gabansu tana kallon abincin da yau Innar ta basu.
Jin bata shigowa ba daga can ne ƙofar ɗakin take wannan mitar tana daga zaune yasa Sadiya kallon abincin tana dawo da dubanta akan Nuratu ta ce.
"Aunty yanzu fisbilillahi Inna zata bamu wannan uban abincin babu ishashshan yaji da Mai yanzu a haka zamu ci abincin nan ba kayan haɗinsa?".
"Hmmm Sadiya kenan ai mu gode Allah ma duk mitar Inna da kyararmu da take yi bata taɓa barinmu da yinwa ba, zamu ci mu ƙoshi duk yadda zatai zata yi domin muci kawai, amma zata bamu abincin ne a yadda zamu ji haushi ma muce mun ƙoshi ita kuma haka take so ta yadda zata ƙara banka mana haushi ta ci gaba da zagin Mahaifinmu kin sani, shi yasa hakuri zamuyi koda gaya take bamu mu ci a haka nan wata rana baza mu ci irin abincin nan ba insha Allah mai rai da lafiya zamu ci kinji ƴar ƙanwata?".
Murmurshi kaɗan Sadiya ta saki tasa hannunta a cikin kwanon abincin ta ɗebo tana kaima Nuratu a bakinta, kallonta Nuratu tayi tana kallon hannun nata daya ɗebo abincin, ta saki murmurshi kaɗan tana buɗe bakinta a hankali tasa mata abincin, ta shiga taunasa a hankali tana haɗiyewa idonta haka kawai ya fara kawo ruwa a cikinsu ganin yadda ƙanwar tata take mugun sonta da kulawa da duk wani al'amarinta, duk wani duka da Inna zatai ma Sadiyar yawanci akan Nuratun ne idan tana shigar mata faɗan da Innar ke yawan yiwa Nuratun wani lokacin..........
Chapter 33
Bayan wasu kwanaki.
Gidan cike yake da tarin jama'a ƴan unguwar wa'inda Inna ta gayyata saboda taron bakin Nuratu da Sagir da yau aka ɗaura auren nasu, babu irin ramar da Nuratu batai ba kamin bikin yazo ta rame ta lalace duk tayi wani irin zuru-zuru kamar wacce cutar ƙanjamau tayi ma mugun kamu, sai ɗan wuya kawai da farar fatarta ta sake haske kamar wacce bata da jini a tare da ita.
Ƙanƙame suke da juna suna wani irin kuka mai cin rai kamar wa'inda mutuwa zata ɗauke ɗaya tabar ɗaya, jikin Sadiya na rawa muryarta na rawa ta ce.
"Aunty Nuratu yanzu tafiya zaki yi gidan wannan Sagir ɗin Mashayin Giya?, zaki bisa inda zai wargaza rayuwarki, dan Allah Aunty Nuratu kice kin fasa auran nan komai zai faru sai dai ya faru ni zan tsaya miki".
Girgiza kanta Nuratu tayi tana ɗan tashi daga jikin Sadiya kaɗan tana kallonta hawaye kwance akan fuskarta shaɓe-shaɓe ta ce.
"Bazan iya watsa ma Inna ƙasa a ido ba, a cikin kundin ƙaddarata ki sani akwai auran Sagir dama can Allah yayi dole saina auresa, dan haka addu'a kawai zaki yi min Allah Ubangiji ya bani ikon cinye wannan jarabawar da Allah subhanahu wata'ala ya ɗora min".
"Wallahi Allah bashi ya ɗora miki ba aka ɗora miki dai dan.....
"Haba Sadiya saɓo fa zakiyi?, komi da kike ganin yana samun bawa to dama can Allah ya rubuta masa hakan a cikin littafin ƙaddararsa ne fa".
Girgiza kanta kawai Sadiya ta farayi kamar wata ƙadangaruwa tana hawaye sosai tana sake kallon Nuratu kallo irin na ban tausayi tsantsa.
"Wai ina Nuratun ne?, ta zo ƴan ɗaukar amarya sun zo ita kaɗai ake jira".
"Innalillahi Aunty Nuratu kiyiwa girman Allah kirki tafi ki barni. Ki duba makomarki mana, ki duba yadda akai auran nan Inna fa ko tsinke bata saya miki ba, a haka za'a kaiki daga ke sai wata ƴar katifar data saye ta da kyar, wannan wanne irin cin mutumci ne haka ta siya mana a wajan mutane?".
Nuratu ta ƙasa cewa komai tayi sai haɗiyar zuciya da take yi tana sauke lumfashi kaɗan-kaɗan kamar wacce ke shirin sumewa.
"A'a mi kuke a ɗakin ne wai?".
Faɗin Inna data faɗo ɗakin tana binsu da kallo ganin yadda suke hawaye kamar wa'inda akaima albishir da mutuwa, yasa ta tsayawa tana riƙe baki ta ce.
"Au kuka kuke ma?, cewa akai za'a ɗauki ɗaya daga cikinku a kaishi gushewa ne yau banda labari?".
Wani irin kallo Sadiya ta shiga yima Inna bata san lokacin da bakinta ya fara furta.
"Ai Inna da ace ni ce gara wallahi Allah a kaini Kabari gushewata da akai ni gidan Sagir, ai gara gushewa ma akan gidan Sagir dai, kin rufe idonki kin ƙasa gane gaskiyar da aketa sanar dake, Inna kiyiwa girman Allah kisa a warware auran nan domin.......
"Sadiyaaaaaa!".
Nuratu ta kira sunanta da bala'in sauri tana girgiza mata kai.
Wani miyau ta haɗe tana kallon Inna dake jafa mata wani irin kallo.
"Ai ki barta kawai ta gama faɗar duk abunda take son faɗa ɗin, tunda dama ai ni ta gama raina min hankali, ta gama gano gadon bacci na, kina so kifi ƙarfi Sadiya ne ko?, to bari kiji ban haifi Yaron da zaifi ƙarfi na ba, ko kece na ce ki auri Sagir na rantse da Ubangiji sai kin auresa, sai mu gani idan kece kika haifi ne, marar kunya kawai, ke kuma maza ki fito za'a tafi miƙa ki ɗakin ki".
Inna zata juya ta nufi waje taji Sadiya na faɗin.
"Aunty Nuratu kuje amma ni ƙafata baza taɓa taka gidan wannan Mashayin Giyar ba".
Da sauri Inna ta tsaya tana dawowa baya kaɗan tana kallon Safiya ta ce.
"Ai ko ni ban lamunci kije gidanta ba kin gane, bazai yiwu kije ki kashe mata aure ba, an samu an ɗan lallaɓa ya aureta bazai yiwu kuma ace kije yadda kika tsani auran nan tsaf na sani zaki iya duk wani abu da zai kashe auran, dan haka tafi nono fari kiyi zamanki a gida hakanma sai yafi ai".
Ta ƙare maganar haɗe da yin gaba ta fice daga ɗakin.
"Please Sadiya ki taimaka ko ba yanzu ba kije inda za'a kaini, bazan taɓa jin daɗi ace nayi aure baki je gida na ba".
"Wannan har aure ne kikai dama?, ai banga aure ba ni nan, auran wucin gadi ne fa kikai, domin nasan wannan auran babu inda zaije kawai dai na yarda da kika ce akwai auran Sagir ɗin a cikin littafin ƙaddararki na yarda da wannan, amma wannan auran ni banga aure ba a nan, kwata-kwata babu albarka a cikinsa".
"Haba Sadiya baza kiyi min fatan ta sanadiyar aurena da yayi ba ya shiryu?".
"Meee?, Allah ya kyauta wallahi, ni nayi ma wannan auran fatan alkhairi har abada wallahi, kuma insha Allah auran nan sai ya mutu, da yardar Ubangiji Sagir bashi ne wadda zaki mutu da auransa ba kanki, zaki auri mutum nagartacce mai hankali mai arziƙin da Innar take so amma a lokacin da hakan bazai taɓa mata amfani ba".
"Miye kike cewa ne haka Sadiya?".
"Kinga Aunty Nuratu baza ki fahimce ni ba yanzu kam, kije kawai Allah karya bashi ikon yi miki wani abu daya danganci abunda ke cikin aure, kije kawai".
Wasu irin hawaye ne masu zafi Sadiya ta share lokacin da take ganin Nuratu ta juya jikinta a mugun sanyaye ta fice daga ɗakin nasu, zubewa kawai ƙasa Sadiya tayi tana sakin wani irin kuka mai cin rai, ba abunda zuciyarta ke fata da addu'ar datse wannan auren a cikin gaggawa kawai take.
************
Zaune take idonta sunyi ƙunburi sosai, saboda irin kukan data daɗe tana yi babu kowa a ɗakin da aka kawo ta a matsayin nata ne ita da Sagir, ashe ma gidan haya ne mai ɗauke da mutane maban-mabanta gasu nan, wasu ma ƙaruwai ne, wasu sun iske su suna shan taba ce wiwi ce shaye-shaye dai kala-kala gashi nan.
Haba da walaƙin goro a miya, irin wannan gidan da Sagir ɗin yake dole ya lalace sosai, babu irin ta'asar da ba'ayi a cikinsa, duk wadda ka gani ko dai zaman kanshi yake ko kuma haya ya kama a cikin gidan, maza ne da mata a cakuɗe, hakan yasa Nuratu ƙara tsorota da Sagir ɗin haɗe da ƙara yin kuka bayan an tafi an ƙyaleta taci kuka kamar ba gobe, ɗakin katifar da Inna ta siya ce da kyar ita kaɗai ce a ɗakin dan ko ledar ƙasa ma babu, sai wasu tarkacen kwanoni da Innar ta haɗuta dasu.
Cikin dare har bacci ɓarawo ya fara ɗaukarta taji an banko ƙofar ɗakin da ƙarfi an shigo.
Da wani irin sauri ta miƙe jikinta har yana rawa wajan ware idonta tana kallon wadda ya faɗo mata ɗaki.
Shi dai ne tsaye, yasha yayi maƙis, hannunsa riƙe da tafa yana zuƙa yana fesar da hayaƙin tabar ta baki ta hanci, cike da kwarewa yake shan tabar yana feso mata ita akan fuskarta.
Tari Nuratu ta fara lumfashinta na yayyakewa saboda kwata-kwata ta tsani warin taba bare yanzu da yake feso mata ita akan fuskarta.
Hannunta tasa tana toshe hancinta da sauri taja baya tana jin gabanta na faɗuwa ƙirjinta na duka kamar zai rabe gida biyu.
Wani irin layi yake yana tari yana wasu irin surutai wa'inda basu da kan gado.
Gani tayi yana nufo inda take gadan-gadan yasa Nuratu zabura tana furta.
"Innalillahi na shiga uku".
Ta faɗa bakinta na rawa.
Batai aune ba taji yasa hannunsa da ƙarfi ya jawota jikinsa ya fara shinshine jikin nata yana wani irin gurnani haɗe da sun haɗe bakinsu waje ɗaya.
Nata san lokacin data sa dukkanin ƙarfinta ta shiga turesa ba tana fashewa da kuka mai sauti haɗe da tofa masa miyan bakinta akan fuskarsa duk dan ya sake ta.
Da wani irin haushinta da watsa masa miyan da tayi yasa shi kamo gyalenta da ƙarfi ya cire mata shi a jikinta, ya sake damƙe gaban rigarta sai dai Nuratu taji yajata da mugun ƙarfi ya rabata gida biyu ya yagata.
Da wani irin bala'in sauri Nuratu ta ƙare ƙirjinta da hannuwanta tana kuka, ta fara masa magiyar ya ƙyaleta yayi hakuri dan Allah, amma yadda kasan sake zugasa take wajan ƙaimin abunda yake son aiwatarwa a kanta.
Zanin dake jikinta yasa hannunsa shima yaja shi ya kwance ta zama tunɓur babu abunda yayi saura a jikinta sai Bra da ɗan fat da yayi saura a jikin nata.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta saki tana ƙare kanta tana ja baya yana sake matsowa inda take.
Faɗawa tayi kan katifar dake malale a tsakar ɗakin, da sauri ta shiga ƙoƙarin tashi amma yasa hannunsa yana riƙe ƙafafunta da ƙarfi yajawo ta jikinsa yana shirin aiwatar da manufarsa dan sauran kayan dake jikinta ma nan take ya yaga su da masifar ƙarfi ya watsar dasu a tsakar ɗakin.
Wani mugun cizo ta kai masa a gefen fuskarsa, daya sa shi sakinta ba shiri yana dafe inda ta kafta masa cizon, wani irin kallo ya jefa mata, gani tayi idonsa sun kaɗa sunyi jawur ta jikin hasken kwan wutar NEPAr da basu kashe ba, daya gauraye ɗakin.
Gani tayi kamar ma ya dawo dai-dai dan gani take layin nan da yake na wadda yasha Giya ya bugu kamar Giyar ta sake sa ma a lokacin.
Da ƙarfi ya jawota ta dawo jikinsa baiyi wata-wata ba wajan ɗauketa da wani kyakkyawan mari wadda yasa Nuratu sakin kuka ta ƙanƙame jikinta.
A wannan dare Nuratu taga zallar rashin imani da bata taɓa kawowa wani mahaluki zai mata hakan ba, saboda babu wata nuna soyayya ko tayar da sha'awa kawai ya afka mata.
A lokacin ta fasa wata irin uwar ƙarar da tana da tabbacin wa'inda suke kusa da ɗakin sunji ta, amma da yake gidan, gidan bariki ne kowa harkar gabansa yake, babu wadda ya damu da wani.
Tunda take bata taɓa jin azabar data ji a ranar ba, yayi mata kaca-kaca yayi abun ya kai sau uku duk akanta, dan har suma tayi azabar data sumar da ita ita ce ke sake farfaɗo da ita, yakushi da cizo babu wadda batai masa ba, Allah yasa ko yasha tafi cikin kwando.
Yana biyan buƙatarsa kuma ya shiga kwarara amai a gefenta mai shegen ɗuyin da yasa Nuratu itama fara ƙaƙarin aman ba shiri ta gangara daga gefen katifar ta kwanta a ƙasa tana jin yadda jikinta ke amsawa ko ta ina ciwo yake mata jikin nata.
Tana jin yadda bacci ya kwashesa yana sakin wani irin linshari kamar rago na bacci babu daɗin ji.
Kuka marar sauti Nuratu ta saki tana jin yadda wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta lokaci ɗaya, muryarta ma bata fita sosai tsabar yadda tasha kuka a yau ɗin, gaba ɗaya jikinta yayi mata wani irin nauyin da ko ɗan yatsanta ta kasa ɗagawa..............
Chapter 34
A hankali take juyi akan katifar daya kasance ita ɗaya ce kwance a ɗakin, saɓin da, da suke kwana su biyu shi yasa jiya da kyar ta samu bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita, tunda ta kwanta take juye-juye baccin ya fisgeta ne ta faɗa yin wani mummunan mafarki.
A mugun zabure ta tashi zaune wata uwar zufa na wanke mata jiki, ƙirjinta ba abunda yake sai bugawa zuciyarta na bugawa sosai kamar zata tsaga ƙirjin nata ta fito, wani irin salati take yi tana ƙarawa.
Girgiza kanta ta shiga yi tana dawo dubanta inda Nuratu ta saba kwanciya, wasu zafafan