Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   35 / 40

102K to 105K   out of 118.4K words

tare suka tare a gidan Alhaji ya ɗauka ko Haj Mansura zata hakura ne a zauna lafiya, sai dai cin mutuncin gobe da ban na jibi ma daban da take yima Nuratu, ta hanata yin komai cikin kwanciyar hankali, kullum sai tasa baiwar Allah kuka, dan akwai wani sati da Sha'awa ta sake zuwa suka taru har Haj Mansura suka yima Nuratu dukan kawo wuƙa lokacin cikinta ya isa haihu dan dole naƙudarta ta tashi lokacinta baiyi ba, tsabar yadda suka dake ta, ga tashin hankali yasa naƙudar zuwa babu shiri.

Nanfa ne Alhaji ransa ya ƙara ɓaci, akanta aka fara kishiya?, kuma duk ba laifin Haj Mansurar bane yaja koma miye ya faru. Yayi ma Sha'awa mugun gargaɗin idan ta sake zuwar masa gida to a bakin auran ƴar uwarta, domin yaga idan tazo gidan bala'in da take janyowa yafi wadda Haj Mansura take masa ita ɗaya, domin idan tazo sai tasa anyi gagarumin tashin hankalin da baya taɓa tsammani.

Kuma yaje ga Abbu domin yaga shine kawai zai iya ja masu kunne a lokacin suji, domin Sha'awa ta fara ce masa sai mi idan ya saki Yayarta?, akwai maza da yawa fa a duniya.

Ganin abun nasu bamai ƙarewa bane yasa kawai ya yanke hukuncin sanar da Mahaifinsu.

Lokacin da Abbu yaji yayi baƙin cikin mi yasa tun farko ba'a sanar dashi ba?.

Ai ko sunga ɓacin ran da su duka basu taɓa ganinsa a wajan Abbu ɗin ba, sai da suka rinƙa binsa gida suna basa hakuri kamin ya zauna ya sauraresu, yayi masu faɗa sosai inda ya ce Sha'awa baya son ƙara ganinta a gidan ƴar uwarta idan ba wata hidimar ce ta taso ba ta dole sai tazo ba.

A ranar Nuratu sai da akai mata aiki aka sake fiddo mata ƴan biyu, duk mata sai dai wa'innan ƴan biyun basa kama da junansu, kamar ma ba ƴan biyu ba, shi yasa Alhaji yasa masu sunan Hanan da Ameera.

Sadiya dake can Nuratu bata gaya mata duk irin abubuwan da suka rinƙa faruwa da ita ba, kawai ta gaya mata cewar yanzu Haj Mansura tasan da zamanta domin gida ɗaya ma suke zaune, sai dai Sadiya tasan tabbas ba'a banza ba, akwai abunda Nuratun ta shaƙa kamin komai yazo dai-dai su kasance gida ɗayan.



Sadiya sai da Japhar ya cika shekara kusan sha biyar kamin ta sake samun wani cikin.

Wata ranar da Sadiya da Nuratu baza su taɓa mancewa da ita ba, ranar da Intee ta kira waya tana shaida masu cewar Allah yayima Inna rasuwa, lafiyarta lau kuma ta kwanta lafiya lau ba'a tashi da ita ba, domin ita kanta Intee kusan sumanta biyu sai da kyar makwaftansu suka kaita asibiti data farka ta samu waya ta kira su tana wani irin kuka ta shiga sanar dasu duk abunda ya faru.

Zan iya cewa tashin hankalin da suka shiga Allah kaɗai ya sani, a ranar su duka suka nufi Rimaye, daka masu kallo ɗaya a ranar duk sun zafge sun rame idonsu ya faɗa na tsabar kukan da suka sha tun kamin su iso.

Lokacin da zasu iso har an shirya gawar Inna, addu'a sukai mata suna wani irin kuka mai cin rai, duk wadda ya gansu a lokacin sai sun baka tausayi suna kuka suna faɗin sun yafe mata duniya da lahira Allah yasa ta tafi a sa'a.

Lokacin da za'a fice da gawar Inna sai da Sadiya ta zube a sume da kyar aka samu ta farfaɗo tana wani irin kuka har jikinta na jijjaga, lokacin har an tafi kai Inna, sai da aka danganta Sadiya da asibiti saboda cikin dake jikinta, kar a samu matsala kuma.

Kwana Uku da mutuwar Inna Sagir ya zo da wata maganar da suka kasa ɗaukarta, wai wani a basa ƴarsa Intee, ta fito yana son Intee kuma dama shine Ubanta haƙƙin aurar da ita yana kansa dan haka a bashi ƴarsa zai aurar da ita ga wadda yaso.

Tofa ba ƙaramar rigima akai dashi ba wacce har ta kaisu ga zama Koto, dole tasa Hammad dawowa yasa aka kama Sagir ransa ya ɓaci sosai jin abunda Sagir ke son yi.

Abbi ya ƙara basa goyan baya aka shiga Koto, Koto taga Sagir kwata-kwata baida gaskiya hakan yasa aka yanke masa hukuncin zaman gidan gari, saboda a Koton sai da yayima alƙali rashin kunyar ai ƴarsa ce babu ubanda ya isa hanasa iko da ƴarsa, wannan rashin kunya da yayima Koto na faɗa tana faɗa yasa aka yanke masa hukuncin zaman gidan Yari Wata shidda.

Inda kamin a wuce dashi ya fara masifar cewar duniya ta shaida ya sallama ƴar tasa babu shi babu ita, bata daga cikin ƴaƴansa a yanzu, tsabar yadda aka tozarta shi akan ƴarsa, kuma gani yake ai isa tunda shine Ubanta. Ranar Intee sai da aka sake kwantar da ita a gadon asibiti saboda firgice da ɓacin rai, ga mutuwar dama Inna bata gama sakinta ba dan haka abun ya haɗe mata.

An shafe kusan kwanaki arba'in kamin Intee ta ɗan dawo dai-dai, Alhaji yasa ta kwaso duk kayanta ta koma kusa da Mahaifiyarta, Sadiya taso ɗaukarta amma Alhaji ya hana ya ce shi zai riƙe Intee kamar ƴarsa tunda har Mahaifinta ya furta ya barwa duniya ita, to shi ya ɗauka yana sonta kuma zai riƙe ta kamar sauran ƴaƴansa.

Lokacin da Haj Mansura taji mutuwar ko gaisuwa batai masu ba har suka dawo, abun ya ƙara bata haushi ganin wai hakan yasa Hammad dawowa yabar karatunsa yazo akan wasu banzaye, ranta sosai ya ɓaci ta shiga bige masa wornig ɗin ya cire hannunsa daga duk wani al'amarin Nuratu da ƴaƴanta idan ba haka ba zata saɓa masa, zatayi masa abunda basu taɓa yi ba tunda yake a duniya.

Da kyar dai ya samu ya koma India yana ci gaba da karatunsa. Intee kuma ta koma Kano itama ta ci gaba da karatunta.

Hammad ya rigata gamawa da shekaru Uku kamin itama ta kammala nata, lokacin da zata dawo gidan da maza ta lura da irin cin mutumcin da Haj Mansura ke yawan yima Ammi ɗinta wadda wani lokacin har kuka ita Intee ɗin ke yi, idan aka shigo har parlon Ammi akai mata wannan cin kashin, domin ta lura kamar jin daɗin hakan suke yi kawai suci mata mutumci suyi mata zagin rashin daraja.

Lokacin da Inna zata cika shekara ɗaya da mutuwa Sadiya lokacin ta haihu ta samu ɗiya Mace aka sa mata sunan Innar wato Khairat, dama sunan Inna kenan.

*DAWOWA LABARI*

Sauke ajiyar zuciya mai zafi Ammi tayi tana ɗago da Intee a jikinta bayan ta gama tunano irin rayuwar da suka fuskanta a baya, idonta jawur itama tunowa da abubuwan da suka shuɗe wadda bata so tunowa dasu ba har abada, amma sai gashi da tsiya ansa komai yana shirin dawo mata kamar sabo.

"Tashi kije ciki ki watsa ruwa za'a kawo miki abinci, bance kuma ki zauna kina wannan kukan ba kinji ko?, ki manta komai kamar ma ba'ai ba".

Tashi Intee tayi daga jikin Ammi tana nufar Bedroom ɗinta tana jin har lokacin zafin maganganun da Ummu ta yaɓa mata daga shigowarta gidan, har lokacin idan ta tuno zagin da cin mutuncin sai taji zuciyarta na mata zafi kamar wacce ake watsa ma barkono, jiki a sanyaye ta ƙarasa bedroom ɗin nata.......

Chapter 42

*House No: 17, Aurora Wrestling Estate Kaduna State Nigeria*

Zaune Ammi take bayan Intee da su Ameera sun wuce school sai ita ɗaya a Parlon, da kyar ta samu Intee ta iya fita yau ɗin zuwa Office, wayarta dake kusa da ita ce ta shiga ringing.

Kai dubanta tayi inda ta aje wayar, ganin Sadiya ce mai kiran nata yasa ta sakin murmurshi kaɗan tana ɗaukar wayar ta kara a kunnanta.

"Assalamu alaikum Aunty Nuratu ina wuni?, yasu Intee da Ameera dasu Hassana ɗina?".

Sadiya ta faɗa cike da son yaran Auntyn nata Nuratu.

Itama cike da son ƴar uwarta ta shiga tabbayar nata ƴaƴan, tana jin Muryar Sadiyar dake cike da farin ciki.

Ammi ta kasa hakuri ta ce.

"Shin wai Sadiya ko dai abun farin cikin ne ya ƙaratomu ne ban sani ba?, naji sai murna kike kina ƙarawa".

Dariya mai sauti Sadiya ta saki tana cewa.

"Wallahi kuwa Aunty, kinga fa Ɗanki Japhar ne ya samo mata a can wajan da yake bautar ƙasar sa, amma fa Abokansa suka sanar dani, cewar yarinyar mai hankali ce kuma ta fito daga gidan Mahaifinta tana shan ƴar wahala a wajan Matan Ubanta, dan hakane ma yasa suka ƙara jin tausayinta, gashi zata dace da Mai sunan Baban naki, amma fa shi har yanzu bai furta cewar yana sonta ba, miskilancinsa da jin kai ya hanasa faɗa mata, sunce bazasu sanar dashi ba dole sai an ɗaura auren a ranar zai san dawa aka ɗaura, shine na ce zan kira ki na sanar dake mi zai hana a haɗe bikin nasu dana su Intee, idan yaso sai su Alhaji suje neman masa auran, na gaya ma Mahaifinsa kuma shima ya aminta da hakan, domin yasan halin ɗan nasa na rashin shiga harkar kowacce Mace, sai gashi Allah ya kawo wacce yake so ɗin, amma ya kasa furtawa, baccin abokansa suna tsaye a kansa da yanzu sai dai fa yayi asarar soyayyarsa, na rasa wane irin mutum ne shi wallahi, karki ji yadda Khairat ke jin daɗi, dama kuma ita ce keta addu'ar Allah yasa ya samo mata Aunty a can, sai gashi Allah ya amsa ta tata".

Cike da fara'a haɗe da wani irin farin ciki Ammi ta ce.

"Kai Masha Allahu, wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba, kai ai haka ake so, nasan ma ƙila zuwa yanzu shi Abbi ɗin nasu ya sani, yaji a wajan Khabeer ɗin, tunda basa ɓoye ma juna komai bare wannan da shi Abbi ɗin shine maɗaurin auran Mai sunan Baban, amma gaskiya naji tausayin yarinyar wallahi, Matan uba ai zama dasu wata ƙaddara ce babba mai wahalar cinyewa sai mai hakurin gaske kam".

"Wallahi Aunty hakane, shi yasa ma kawai naji yarinyar tun kamin na ganta ma ta kwanta min a raina".

"Bari nima harta bani tausayi sosai, kuma dama nasan bazai wuce su haɗe bikin ba ayi gaba ɗaya, amma fa ni Sadiya gaskiya haɗin auran nan da Hammad da Intee kwata-kwata bai wani kwanta min ba, bisa yadda uwarsa ke nuna ƙiyayyar auren nan ƙiri-ƙiri fa, abun nata ma gaba yake sake yi fa Sadiya, shi yasa abun tun ina son haɗin har nima ya fara fice min a rai, jiya fa sai da ta tare Intee a waje tayi mata cin mutunci harda su gorin ubanta ɗan iska ne mai shan Giya, kinji fa duk mi ya kawo wannan kana babba?, Yaro na maka kallon uwa amma kana son zubar da darajarka da kimarka da Yaro yake gani".

Daga cikin wayar Sadiya ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta babu daɗi ranta kuma ya sosu ta ce.

"Nima fa haɗin nan ba wani son shi nake ba, dandai kawai iyaye Maza sun dage sai anyi, sai kuma shi Yaron da nake tausayi, saboda sun shaƙu da Intee yayi hadima da rayuwarta sosai, babu wadda ya cancanta da auran Intee sama da Hammad gaskiya, amma uwar tashi ce kawai matsala harga Allah amma shi baida matsala ko kaɗan".

"To ya za'ayi idan har Matarshi ce babu yadda ita kanta zata iyayi dole ta hakura, ni dai fatana Ubangiji yasa idan akai auran ta so Intee koda kaɗan ne".

"To Allah ya sassauta zuciyarta, amma kam Haj Mansura tayi nisa ne bata jin kira, ni ban taɓa ganin wacce abu ya kasa wucewa a wajanta ba sai Haj Mansura, ta kasa mantacewa da komai ta yafe?, sai kace mai zuciyar ƙafurai?".

"Hmm to Allah ya sassauta matan kawai shine".

Haka suka ci gaba da tattaunawa akan yadda abubuwa zasu kasance na shirin bikin ƴaƴan nasu dake tunkaro su.

*Unguwar Hayin Ruwa, Dutsanma local government Katsina State Nigeria*

"Ke tsaya wai shin Binta ko dai asiri akai miki ne?, ina faɗa kina faɗa, cewar ke ga wadda kike ra'ayi ba zaɓin dana zaɓa miki ba?, waye ya canza ra'ayinki ne wai?".

Inna Asabe ta ƙare maganar tana kafe Binta da ido.

Binta ta wani juya ƙeya tana faɗin.

"Nifa gaskiya Inna na haƙura da auran Mlm Japhar fa, yafi ƙarfin tunanina, domin duk wani abu da kika bani nasha na shafa amma ko kallo ban ishe shi ba, ni kuma gaskiya ma bazan iya da izzar shin nan ba da isa, kofa ta inda nabi baya kallo bare yasan da zamana a duniyar ma, mutunen dake da muguwar shiriya da wata isa da izza, zance zan kwallafa raina a kansa?, shi yasa kawai na ce ni gara na koma akan abokinsa Mlm Naseer kuma wallahi yafi shi sauƙin kai tunda har mun dai-daita mun fara fira yana ɗan sakar min fuska, gara ace na tsira da koda shine, ki duba abun nan fa".

Sauke ajiyar zuciya mai zafi Inna tayi tana jawo hannun Binta suka zauna ta ce.

"Kuma fa hakane Binta, na goyi bayanki, kuma insha Allah ma mun daina musguna ma Bilkisu tunda ta sanadiyarta ne kika samo miji na kere sa'a, tunda ko a cikin abokan nashi ai suma masu abun hannu ne, dan haka nima ina goyan bayanki yanzu, amma fa kiyi shiru da bakinki kar waccar ƴar hana ruwa gudun taji ki".

"Haba Inna sai kace sakarai?, babu yadda za'ai na sake har suji, tunda dama Baba yasan maganar neman auren Bilkisu sai ki faɗa masa cewar nima ana nan zuwa domin mun fara maganar da Mlm Naseer nafa yi sa'ar samun Naseer ɗin nan shima Allah Inna kyakkyawa ne".

Dariya suka saki a tare kamar wasu ƙawaye.

*****************

"Ke wai da gaske kike abunda naji kina faɗa domin Allah?".

"Wallahi Inna da gaske ne?".

"To amma Amina shi Mlm Aminun ne ya ce miki da bakinsa yana son auranki, sana, tayaya akai hakan ta faru ma?, kuma bayan naji kamar ance wai Bilkisu yake nema ba?, naji ne a wajan su Asabe, ya za'ai kuma ace ya dawo kanki?".

"Inna ki zauna ki fahimce ni sosai, munyi magana dashi ya ce min bashi ne wadda zai auri Bilkisu ba ɗayan abokinsa ne Mlm Japhar, suma kansu basu sani ba, sai ranar ɗaurin auran zasu sani, domin yana son Bilkisu amma ya kasa faɗa mata, saboda duk ya fisu jin kai da izza ko dan yaga ya fisu kyau ne Ohoo?".

"Ohhh ikon Allah kinga yanzu kowa sai ya daina ma Bilkisu gori ko mugunta yanzu ai, tunda itace duk silar samun Mazajen ku a yanzu, amma fa kar naji maganar a bakin wani bayan mu nan, domin waccar Matar idan taji sai tasan yadda tayi ta rushe wannan haɗin, duk da tana ganin ƴarta ta samu kuma duk abokan juna ne, amma hakan zata iya murje ido domin ta baƙanta min kawai wajan rushe auran nan naki".

"Baza tai ba Inna domin ni yanzu komai na aje shi gefe tunda na samu mutum kamar Aminu ai na more wallahi, kuma kinga dama mu ai bama yima Bilkisu mugunta, kawai dai harkarta ce bama shiga".

"Hakane kuma fa".

Da haka suka rufe firar. Tun lokacin Bilkisu ta fara ganin sauyi a gidan kowa ƙoƙari yake ya faranta mata, ta kasa gane hakan na miye?, ko mi yasa?, ita dai kawai tana ganin ikon Allah, domin basu bata ƙofar da zata fahimci na miye ba, sai suka shiga riƙon ta yafe masu, kai tsaye ta ce Allah ya yafe mana baki ɗaya, tun lokacin bata sake zuwa tallar dambu ba, ta zama kamar kowa a cikin gidan dan haka ta kira Inna tana bata labari, sosai Inna taji daɗi dama ta daɗe tana addu'ar Allah ya kawo sauyin da zaisa itama Bilkisu taji daɗi a gidan Mahaifinta.

*****************

"Kai Friend ka kawo shawara mai kyau fa Allah".

Murmurshi Aminu ya saki yana shafa kansa ya kalli Naseer ya ce.

"Ai wato duk Yaran gidan kyakkyawa ne, shi yasa kawai naji zuciyata ta aminta da kawai mu aure su gabai ɗaya, kuma idan mu kai haka zai taimaka wajan rage gaba da wahalar da Bilkisu da suke, saboda dama ni tunda naga Aminar naji ta kwanta min, nayi alƙawarin nima fa auran nan dani za'ayi shi, shi yasa kaima na ce tunda Binta na nuna tana yinka kawai ka bata dama, tunda kaga ai su Yaran ba laifin su bane, kawai kishin iyayensu ne".

"Hakane kam tabbas, mu kuma Matanmu a gida ɗaya suke uba ɗaya, Ohh ikon Allah kenan fa?".

Dariya mai sauti Aminu ya saki yana jin son Aminarsa sosai abun kamar almara, sai gashi sun fara soyayya har yake gaya mata shirinsu akan Bilkisu, shi yasa ma basu haɗuwa idan zasuyi fira inda Bilkisun zata gani, ko tayi zargin wani abu, suna so shirinsu ya tafi dai-dai ne, har sai ranar auren ake so su sani.

Shi ko Naseer dama Binta ta daɗe ta ɗan nuna masa amma yana shareta dan gani yake da can nunawa tayi Japhar take so, shi yasa ma yaji da ta fice a ransa, sai gashi shima Aminu ya bashi shawarar shawo kanta haɗe dasawa ta manta da Japhar ɗin lokaci ɗaya, sai gashi yana fara sakar mata fuska suka fara fahimtar juna, tama manta da wani Japhar kwata-kwata Naseer ɗinta kawai take gani a yanzu, wadda yaga alamar ya kame ko ina a cikin zuciyarta yanzu.

Shi yasa idan suka famtsama fira Japhar ya dawo yayita mitar sun tafi wajan ƴan matansu zance, saura Yara suzo su raina su a banza a wofi, idan yana faɗan sai dai su girgiza kai su bishi da dariya suna tafa hannu, hakan da suke masa yana sake hassala shi ainun, dan gani yake kamar ma sun maida shi shashasha ne.

Shi yasa ya ɗauke zama a cikinsu ganin yadda suka taso shi a gaba da shegiyar tsokanarsu, amma duk da hakan idan suka tashi janshi har waje suke binsa su cika shi da surutu suna masa tsiyar da suka saba masa a kwanakin......

Chapter 43

*House No:

35 / 40