Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   40 / 40

117K to 118.4K   out of 118.4K words

rigata samun komai nasa ne?, har kuka tayi ta kira Ummu tana shaida mata, a mamakinta sai taga Ummu na murnar samun cikin Intee ɗin da duk ba wani sosai ta nuna ba, amma hankalinta fa ya tashi dan haka kai tsaye ta canza akalar kiran zuwa wajan Maami tana kuka take gaya mata komai.

Ai ko Maami ta shiga damuwa domin tasan ƴar uwarta da son ƴaƴa akan Yara zata iya aje komai ta rungume Intee komai ya wuce, dan haka ta ce mata itama ta dage ta ɗauki nata cikin, dan ita yanzu jikinta yayi sanyi itama ƙalau dan jiya Harun ke sanar da ita wai Humaira ma nada ciki ƙarami na sati Uku, ta nuna murnarta amma a ɓoye, sai kuma washe gari wai aka zo mata da maganar wai mijin Sakina ya biya masu Makkah daga ita har Abba da Inna, tama rasa bakin magana ko kallon idon Inna ta kasa yi, mima zata ce mata?, kunyar duniya duk ta hanata sukuni, shi yasa fa da ƴaƴa da dukiya ba'a nuna masu baƙin ciki domin baka son wadda zai fara taimakonka ba, ita kanta Ma'u ta rasa da wanne ido zata kallesu ma, ganin basu banbanta uwarsu da tasu uwar ba, da ace sune suka samu hakan da sun tabbata uwarsu kaɗai zasu kai Makkan, amma sai gasu su basu nuna komai ba, ko su tuna irin wulaƙanci da suka rinƙa masu.

Koda Maryam taji haka itama sai jikinta yayi sanyi ƙalau, dan haka ta ture komai itama ta fara addu'ar samun nata rabon itama.

Ganin ta tuba ta kwantar da hankalinta yasa Hammad ƙara sonta, itama ganin yadda yanzu take ma Intee hidima ba laifi sai dai fa kishin nan na nan kawai tana kai zuciyarta nesa ne tana shanye komai dan wani lokacin har kuka take a ɓoye, abunda bata sani ba Intee ɗin ta fita kishin Mijin nasu dannewa kawai take bata taɓa nuna a fili, duk yadda zatayi zata yi ne domin nuna komai ba komai bane, saboda ta wannan halin tayo gadon Ammi ne, sai da cikin Intee ya kai kusan wata biyar kamin itama Maryam ta fahimci tana da shigar ciki harna sati biyu duk da ƙarami ne, sosai shima ya nuna tsantsar murna wacce tasa Maryam ƙara aje komai a gefe tunda ta lura itama yana sonta ya damu da ita, bai taɓa kuskuren nuna wata tafi wata ba a gaban waninsu, ko yafi jin son cikin wannan da waccen, hakan yasa kowacce take ji da kanta da jin ita wata ce a wajan mijin nasu, Ummu sosai tayi murnar samuwar cikin Maryam shima.

A ɓangaren su Bilkisu wani irin zama suke wadda bata taɓa kawo tunanin zasuyi sa ba, wani irin rawar jiki yake da Matarshi Japhar akan Matarshi ya zama wani sususu, komai sai abunda take so, tun bata jin sonshi har itama ta kamu da mugun sonshi mai tsananin gaske, shi ɗin ƙarshe ne wajan iya nuna kulawa da soyayya, ƙaryar Mace ta a zauna dashi koda bata sonshi bata soshin ba daga baya, soyayyar da yake nuna mata har taso tayi yawa ma.

*Bayan wasu shekaru*.

"Uhum uhum ni Allah bazan bayar ba, kai kenan komai Yaronka?, nifa to?".

Murmurshi kaɗan ya saki yana kallon Intee a ko yaushe ita dai yarinya take ƙara zama yana murmurshi ya ce.

"Kinga ma dariya yake miki, My Abbi na".

Ya kalli Yaron dake a ƙasa yana rarrafawa shi sunan Abbi yaci Yaron akwai wayo sosai kamar mi, itama Maryam ta haihu amma ta samu Mace itama sosai yake son Ƴaƴansa ba nuna wani banbanci ko wani yafi wani a wajensa duk ɗaya yake ɗaukarsu, Ummu kuma ta aje komai ta rungumi surukan nata har zuciya ɗaya, amma fa har zuwa yau bata taɓa ruƙan cewar wai Ammi ta yafe mata ba, amma ita Ammi ɗin ganin yadda ta sakko yasa ta yafe kawai dama ta daɗe da yafewar Allah ya yafe gaba ɗaya, ta aje komai duk wani yada magana da take yawan yima Ammi a baya ta daina, shi yasa shi kansa Abbi har wata ƙiba yayi ta kwanciyar hankali, Hammad ma yayi kyau yayi ƙibarsa abunsa saboda Matansa basa faɗa ko cacar baki basa yi, basu cika zama ma waje ɗaya ba kowacce na ɓangarenta bare suyi faɗan ma, shi hakan ma yafi so, domin da ace suna yawan haɗuwa dole wata rana zaka ga ana yawan saɓawa.

Sosai ta ƙara taɓe baki zata sakar masa kuka yayi azamar jawota jikinsa yana sunsunar wuyanta kamar wani maye.

Kuka ta fara masa na sangarta tana son turesa ai ko ya sake riƙe ta batai aune ba ya ɗagata sama yayi bedroom da ita, tana kukan shagwaɓa tana turturjewa, kamin su ƙarasa ya jefa mata bakinsa a cikin nata, yasa dole tayi makwas tayi shiru.

**********

"Kin san Allah kizo nan, zan kama ki ne fa".

Humaira ta juyo tayi masa gwalo, tana sake matsawa sosai daga inda yake, ganin zai kamata ta nuna masa Ƴarsu dake kwance akan gadon Baccinta wacce taci sunan Ummu yana bala'in ƙaunar yarinyar kamar yadda yake son Mamanta.

"Minene kuma?".

Sake taɓe baki tayi tana sake nunata zata sakar masa kuka yayi azamar kamota jikinsa yana matseta sosai har tana nishi da kyar, murmurshi ya saki yana kallon kyakkyawar fuskarta da take shirin sakar masa kuka a hankali ya kai fuskarsa akan tata yana manne goshinsu waje ɗaya, hancinsu na gogar na juna ya ce.

"Kefa kishin ma sai kin nuna akan ƴarki ko?, Allah ya shirya min ke".

Turo baki tai zatai magana ya sake rufe bakinta da nasa bakin yana aika mata da wani irin kiss mai hargitsa kwanyar kanta, dole tasa ta riƙesa sosai tana shanye kukan shagwaɓar da take shirin masa.

********************

Gudu take a parlon tana jefa masa fulon kujerun parlon, yana dariya ya ce mata please ta tsaya haka nan ya gaji fa, amma ina tana ƙara ƙaimin gudun nata, sa'ar cafke hannunta yayi yana nishi tana yi itama, ta bayanta ya rungumeta suna sakin ajiyar zuciya a tare ya ce.

"Wai ke baki girma ne iyee?, kin aje ƴaƴa har biyu".

Taɓe baki tayi tana kallon Sadeeq ɗin nata kamin ta juyo gaba ɗaya tana fuskantar shi ta ce.

"Hmm ai idan dai har ina tare da kai wane girma gareni ni?".

"Hakane ba?".

Ya faɗa yana sakar mata hucin lumfashinsa akan fatar wuyanta yasa Sakina damƙe rigarsa sosai tana jin tsigar jikinta na tashi kaɗan, wani irin abu yake bin sassan jikinta dashi daya ƙara kashe mata jiki, ganin tana shirin zubewa ƙasa yasa shi ɗaukarta kamar baby yana yin hanyar bedroom da ita, a hankali tana jikinsa kamin su ƙarasa ya jefa bakinsa a cikin nata yana kamo harshenta ya fara mata tsotsa kamar ya sami alawa, itama tallafe kansa tayi tana kamo nashi ta fara basa haɗin kai, Allah ne kawai ya kaisu bedroom ɗin lafiya domin shima neman zubar dasu ƙasa yake, yadda take tsotsar bakinsa yasa shi jikinsa fara rawa.

*ALHMDLLHI ALHMDLLHI ALHMDLLHI*

*Ƙarshe na sadaukar da wannan book nawa gare ka Abun alfahari na (Daddy J❤️🥰😘) Ubangiji ya ƙara roƙo da hannayenka, kai ɗin abun koyi na ne, Shugaba adali😍, wadda bai san wasa ba ta fannin aiki da jajurcewa💪👍, ina sonshi irin sosai ɗin nan Alkhairin Allah ya kai maka a duk inda kake, na sadaukar da wannan book nawa a gareka kayi yadda kake so dashi My Lovely Daddy nah*

*Duka duka a nan na kawo ƙarshen book ɗin nan nawa, kuskure da nayi ciki Ubangiji ya yafe min. Kuyi hakuri idan na manta bansa wani abunba, ɗan Adam azizi ne, sana iyaka labarin kenan idan na ce zan ƙara wani abun gaskiya ban san ma abunda zan rubuta ba, iyaka abunda Allah ya yassare min ya bani kuma ikon rubuta maku kenan, ni dai fatana shene Allah yasa a ɗauki darasin dake cikinsa ayi watsi da akasin hakan.*

Taku ce har kullum dai.

*Zahra Royal Star ce*.

*Ki biya ka biya ka karata cikin salama, idan ka karanta min book ba tare daka biya ba kaje kaida Ubangiji*

Idan ka shiya biyana haƙƙina ga account number nan a ƙasa 👇

8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank.

Shaidar biya👇

08130479973

40 / 40