Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
zuwa cikin babban parlon gidan Aunty Sakina na kallon yawan ma'aikatan gidan, ko a bakin get masu bawa get ɗin tsoroma kawai abun tsoro ne, wannan irin gidan idan ba wadda ka sani bane a cikinsa ai baka isa kai tsaye ka ce zaka tunkaro koda bakin get ɗin gidan bane, ai baka da ma izzar hakan.
Wani irin bushashshan miyau Aunty Sakina ta haɗiye wadda bata shirya ba, bakinta ne ya ƙara hangamewa buɗe ganin uwar dukiyar da aka narka a parlon da zata iya kiransa Aljannar duniya kawai kai tsaye, kota ina a parlon kalar ruwan zinari ne hatta kujeru da labulayen parlon kalar zinari ne, kai hatta kafat ɗin da aka mamale a parlon shina kalar zinari ne, idonta ya gane mata wani uban darning table mai tsawon gaske sai kace wani gari guda zasu zauna a kansa domin cin abinci, tsabar tsawonsa da girmansa, kai ko wajan da darning table ɗin yake abun kallo ne, ƙamshin dake tashi a parlon ko daban ne wani irin ƙamshi ne mai daɗin shaƙa wadda Aunty Sakina kai tsaye zuciyarta ta bata tunda take bata taɓa shaƙar ƙamshi mai daɗi irin wannan ba, ga wasu irin kujeru iya tsaruwa da kyau kam sun tsaru, a parlon kusan kujeru kala Uku ne zan iya kiran da hakan kusan parlo Uku ne a waje ɗaya, domin ko ina da wata irin narkekiyar Tv wacce ta kusan cinye bangun da aka maƙalata akai dan har wani lauyawa take tsabar girmanta, ga wata irin Ac dake busuwa kota ina Parlon.
Iya kallonka zaka sha kallo a parlon nan, wai a haka iya ma Parlon ƙasa ne nan, inaga an shiga wasu parlons ɗin dake, ko wasu sassa na cikin gidan?.
Zama kawai sukai a ƙasa Aunty Sakina ta ƙasa shuru ta ce.
"Kai jama'a Innalillahi wannan wacce irin dukiya ce haka da masu gidan nan Allah ya damƙa masu?, lallai talaka na can nashan azaba, yama za'ai masu kuɗi na irin wannan narkeken gida ace su wani iya tunowa da talaka bawan Allah, tsakani da Allah kana a irin wannan gida ai ko ruwan sama bana jin zaka ji ƙarar saukarsa, sai dai kawai ka fito kaga anyi ruwan an ɗauke kawai, bare aje ga wata susan ana zafga rana ai wallahi kana cikin irin wannan gida baka taɓa ganewa ma ana wata rana a waje, wai wayyo Allah garin daɗi na nesa. Yo ke Sakina ko naman jikinki ake ɗeba a wanga gida ai kin zauna, ko banza kin aje tarihi ta hanyar auran tsatso daga gidan nan wallahi, wai wai Allah na".
Gaba ɗaya Aunty Sakina ta ruɗe tama rasa abunda ya kamata ta ce, zuba zance kawai take.
Ganin ruɗewar tayi yawa yasa Haj Bharaka ɗan zungurarta, da kyar ta iya dawowa dai-dai amma duk da haka kalle-kalle kawai take a cikin parlon.
Sakina ko bama tana natsuwar kallon irin haɗuwar parlon da yanayin gidan, komai tana kallonsa ne a mugun tsora ce.......
13
*SAKINA POV*
Duk jikinta a mugun sanyaye yake tunda su Aunty Sakina suka juya suka tafi suka barta cikin wannan murɗanɗan gida, tunda Haj Hauwa ta fito ta sallami su Haj Bharaka kallo ɗaya Sakina tayi mata na shaida yadda take da isa da kuma izza dake yawo a jininta, dan kyar take amsa gaisuwar da su Haj Bharaka ke miƙa mata, ita ko, ko kallon arziƙi bata jin Matar nan tayi mata.
Hasalima a nan ta barta tana ji tana gani su Aunty Sakina suka tafi. Ji tayi kamar ta kurma ihu kota samu taji sanyi a ranta, yadda zuciyarta ke a cinkushe kwata-kwata bata gane komi.
"Ke wacece ke?, tukunna ma waye ya shigo dake parlon nan?".
Da wani irin sauri Sakina ta waiga, idonta ne ya faɗa akan wata matashiyar budurwa sanye take da wasu mtsiyatan ƙananun kaya tasha uban gashin doki akanta, sai wani kafcecen gilas data manna a idonta, ta wani ciresa ta riƙe a hannunta tana duban Sakina dake zaune a ƙasa tayi tagumi hannu biyu, yanzu kuma saita saki tana kallon matashiyar budurwar a ɗan tsora ce.
"Da kurma nake magana ne?".
Ta sake faɗa a yatsine tana sake jefama Sakina wani irin ƙasƙantaccan kallo.
Girgiza kanta Sakina ta shiga yi tana son furta wani abu amma kamar wacce aka danne ma baki tama ƙasa magana.
Budurwar zata sake magana Haj Hauwa sakko daga saman bene tana cewa.
"Huda harkin dawo?".
Wacce aka kira da Huda ta juyo tana duban Haj Hauwa kamin a hankali ta ƙarasa inda take ta ɗan cire jakar dake hannunta ta ce.
"Mome na gaji ne wallahi. Waccan fa Mome wacece ita?".
Kallon inda take Mome tayi tana ɗan taɓe baki kaɗan ta ce.
"Waifa matar Sadeeq ce".
"Ohhh Mome cewa zaki Matar nakasashshen can ce, to miye take a part ɗin da har ba'a kaita wajansa ba ta fara aikinta daga yau?".
"Yanzu nake so ai Baffah ya shigo ya kaita inda yake".
"Mome Baffah zai iya ɓata miki aiki, ki ɗakko mata abunda ya kamata kawai naje na rakata".
"Hakane fa bari ki gani".
Ta faɗa tana yin saurin hayewa sama.
Jim kaɗan ta sakko ɗauke da wata baƙar leda babba tana nufo inda Sakina take, kan kujera ta zauna tana duban Sakina a tsanake ta ce.
"Kinga dubanni nan, Sakina ko sunanki?".
Sakina ɗaga kanta kawai tayi dan har zuwa lokacin tsoro ne fal ranta.
Mome ta dube ta rai a ɗan ɓace ta ce.
"Magana zaki yi min Malama, bana son gidadanci dalla".
Da sauri Sakina tasha jinin jikinta a hankali kanta a ƙasa cike da tsoran dake a ranta muryarta na rawa ta ce.
"Eh Haj sunana kenan".
"Madallah".
Ta faɗa tana kallon ledar dake hannunta kamin ta dawo da dubanta inda Sakina take ta ce.
"Kinga Sakina kike ko wacece ma ni bai shafe ni ba, ki kallo ni nan".
Wani irin abu Sakina taji a ranta amma ta ɗago a hankali tana kallon Mome dake nuna mata ledar dake hannunta ta ce.
"Kinga wannan ledar?".
"Eh Haj na ganta".
"Yawwa magungunansa ne a ciki duk rana zaki rinƙa basa safe da dare, karki min shirme a cikin magungunan nan safe da dare kawai na ce miki ana basa, sana Malama Sakina bana son shishshigi a rayuwata, ki tsaya iya matsayinki na mai kula da Sadeeq, duk wani abu daya shafi gidan nan idan har ba ni ce na sakaki ba karki sake naga kin zura jikinki, idan har ba haka ba to zaki rasa aikinki sana kuma na ɗauki mummunan mataki akanki kamin kibar gidan nan".
Mome na maganar tana fiddo magungunan da kwata-kwata babu suna a jikin kwalaben bare takardar da zata nuna daga asibiti suke, ko ingantattu ne.
Sosai kan Sakina ya kulle tana kallon magungunan iya saninta ba haka magunguna suke ba, shuru kawai tayi tana nazarin gidan da kuma matar gidan, sosai ta zurfafa a kogin tunanin anya wannan Matar ita ce ta haifi Sadeeq kuwa?, kwata-kwata ba alamar hakan a tare da ita. tana cikin tunani taji an kwatsa mata tsawa a saman kanta, wacce tasa ta zabura ba shiri tana duban Huda dake mata tsawar.
"Ke wacce irin ƴar ƙauye ce ne?, ana miki magana kina wani jin mutane zakiyi banza dasu, sa'anninki ne mu?, ko kuwa munyi miki kama da wa'inda zasu rinƙa miki magana kiyi banza dasu?, ke kifa dawo hankalinki, bana son rainin wayo yanzu nan sai in kikkifa miki Mari ba abunda ya shafe ni".
Da sauri Sakina ta miƙe danta lura Huda irin mutanen ne masu faɗa da saurin fusata sosai.
"Kiyi Hakuri dan Allah".
"Mtswww ki biyo ni".
Ta ce mata kawai tayi gaba, da sauri Sakina ta ɗauki ledar magungunan da Mome ta bata tana bin bayan Huda.
Parlon suka fita suka fito harabar gidan, wani part taga sun nufa wadda yake kusa da nasu sai dai akwai ƴar tazara a tsakaninsu.
Tunda ta buɗe parlon suka shiga gabanta ya yanke ya faɗi bata san lokacin data saki ledar magungunan ba.
Saboda ganin wani bawan Allah a kwance a ƙasan parlon duk kayan dake cikin parlon anyi masu raga-raga gaba ɗaya parlon babu kyan gani, ga wani ƙarni dake tashi a parlon.
Da sauri Huda ta wani tsaya tana toshe hancinta ta dubi Sakina dake tsaye ta saki ledar magani ta ce.
"Karki sake magungunan su fashe domin zaki gane baki da wayo ne, sana kamar yadda aka gaya miki safe da dare zaki rinƙa basa saura kije kiyi shirme wajan basa maganin, ni zan koma daga haka kingasa nan sai kiyi a sannu tun kamin yau na farko kici na Jaki a wajansa".
Huda ta faɗa ko a jikinta ta juya kuma tayi tafiyarta haɗe da jawo ƙofa ta rufe.
Wata zabura Sakina tayi hatta jawo ƙofar da Hudar tayi saida gabanta ya faɗi gaba ɗaya ta gama shan jinin jikinta bala'in tsoro ne ya rufe ta.
Kallon Parlon take wadda da alama a da can ba ƙaramin kyau Parlon yake dashi ba, a yanayin yadda ta hasaso idan yana samun gyara to sai dawo yaccinsa.
Sadeeq dake kwance ƙasa yayi rufda ciki hakan yasa kwata-kwata Sakina bata ga fuskarsa ba, sai gashin kansa wadda ya sakko masa har bayansa sai marar fatarshi da take gani har wani sheƙi take kamar wadda ke samun kulawa ko mai lafiya.
Kayan jikinsa duk sunyi datti sun yamutse gaba ɗaya.
A hankali Sakina ta shiga tafiya inda yake kwance zuciyarta na duka, taku ɗaya idan zatai zuwa inda yake kwancen sai taji zuciyarta na bugawa da ƙarfi gaske.
Ɗan tsayawa tayi tana dafe ƙirjinta ta haɗe wani miyau mai zafi hawaye na ɗan zubo mata wadda bata san dalilin zubowar tasu ba.
A hankali ta kai ƙasa lokacin data ƙarasa gaf dashi, cikin ƙarfin hali ta tattaro sauran jarumtar data rage mata tasa hannunta a hankali ta birkito shi.
Wata wawar bugawar zuciya ce ta same ta haɗe da zabura da ƙarfi, ta zaro ido waje ƙirjinta tsabar duka har wani sama da ƙasa yake bakinta ta rufe da tafin hannunta jikinta na ɗaukar rawa tana nunasa da ɗayan hannun nata.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, na shiga Uku ni Sakina, miye wannan kamar Aljani?".
to amma ga kama nan a jikinsa suna kama da Huda har Momen, ganin farko data masu taga tsantsar kyau ne dasu, to sai ga wadda yaci uwarsu a kyan, amma tabbas suna kama sosai wacce nan take kana ganinsu zaka san sun haɗa jini har Mome.
To amma ya akai Mome take ma ɗan data haifa haka?, kai ina ko dai ba ita ta haifesa ba?. Girgiza kai tayi tana sake kallon fuskarsa tana sake jin tsoro sosai
tsabar yadda tayi tozali da kyakkyawar fuskarsa mai ɗauke da wani irin kyau, tunda take a duniya bata taɓa cin karo da mai tsananin kyau irin na wannan bawan Allah dake a gabanta ba.
Kamar ba mutum ba, gashi nan dai kwance idonsa a rufe girar idonsa ta kwanta sosai kamar Macen da aka sama gashin ido irin na idon Mata, amma nashin bai kai yawan wadda ake ƙarama mata ba, girarsa mai yawan da har ta kusa haɗewa da ƴar uwarta, bakinsa ko anan karshen kyau yake ɗan mitsitsin bakin nasa kamar na jirarin da aka haifa yau ɗauke yake da jan leɓe, sai hancinsa da yake a miƙe siriri wadda ya dace da kyakkyawar fuskar tasa, kyau ne dashi irin kyan nan da zaka kallesa lokaci ɗaya ka ce yana da wani irin bala'in kyau mai fisgar mutum, fuskarsa tayi ja kaɗan haɗe da ɗan baƙi da alama duk rashin kula ne.
Wata irin ajiyar zuciya Sakina ke saki a ajere-ajere zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi.
Ta daɗe tana kallonsa cike da tsananin mamakin kyawu irin wadda Allah ya zuba ma wannan bawan Allahn, ai ko a jaruman India wannan ɗin ƙarshe ne.
Wata zaburar ta sake yi ganin yadda fatar idonsa ke motsi yana son buɗe idonsa, kamin tayi wani yunƙuri ma ya buɗe idon nasa tarwai a kanta.
Runtse idonta tayi da ƙarfi ƙirjinta na sake bugawa ganin kalar idonsa, wani irin ido ne dashi kamar Mage, sosai idonsa ke mata kama dana Mage ga wani irin haske dake garesu daga ciki ga girma tubarukalla, idonsa kaɗai saiya saka mutum ruɗewa.
Kallonta kawai yake shima a tsora ce baya iya tashi tunda wancan ciwon nasa ya sake shi, dama da ya sake shin baya iya koda ɗaga ɗan yatsansa ne.
A hankali ya shiga buɗe bakinsa muryarsa ta tsinkayo mai bala'in daɗin sauti da daɗin sauraro ya ce.
"Yin...yin...yinwa nake ji....".
Ya faɗi maganar a rarrabe da kyar.
Da sauri ta shiga buɗe idonta akansa ta sauke ganin yadda yake kallonta yana kiran yinwa yake ji, wani irin bala'in tausayi ne ya rufe Sakina a hankali ta shiga jikinsa sosai tana dudduba ko zai iya tashi, sai da kwata-kwata kamar yadda aka gaya mata bazai taɓa iya tashi ba, wani irin sansanyan kuka ta saki na tausayinsa da ya kamata lokaci ɗaya.
Binta yake da kallo kawai ganin yadda take masa kuka, tunda yake bai taɓa ganin wani yayi kuka a bisa ciwonsa ba, sai wannan baƙuwar fuskar da yake gani, duk da baya cikin hankalinsa haka kawai yaji ta kwanta masa a rai, a mamakin Sakina sai taga yana girgiza mata kai alamar baya son kukan nata.
Rufe bakinta tayi da sauri tana sakin wata ƴar dariya kaɗan ta share hawayen tana dubansa.
Ta ce. "Na daina zaki ci abincin idan na dafa?".
Ɗaga kansa kawai taga yayi farin cikin duniya ya rufe Sakina bata taɓa tunanin haka zai farka mai saukin kai a gareta ba.
Tashi tayi da kyar ta fara kiciniyar ɗaukarsa, sai dai yayi mata masifar nauyi, sai nishi take ita ɗaya, da kyar da kyar ta iya tallafesa a jikinta zuwa cikin bedroom ɗinsa, kusan sau biyu suna faɗowa kamin sukai bedroom ɗin, gaba ɗayansu duk sun jigata, sai nishi kawai Sakina ke saki, da kyar ta shinfiɗesa akan godansa tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tana kin jikinta na amsawa yadda yayi mata nauyi da yawa.
A hankali ta taka ta fice zuwa parlo, gyarasa tayi dandanan ta gyarasa ya dawo yaccinsa kaɗan, sai dai wasu abubuwan sun gama aiki na cikin parlon saboda an fasa su, dole tasa ta tattarasu ta waje ɗaya ta sami wani kwali ta ajesu a ciki.
Kitchen ɗin parlon ta gani ta shiga ko ina yayi ƙura dan haka shima gyarasa ta shiga yi da sauri kamin ta fara kiciniyar ɗora masa abunda zaici, kwata-kwata ta rasa mi zata dafa masa mai sauki da saurin gamawa, tunda ya ce yinwa yake ji, da alama kuma rabonsa da abincin an daɗe, danta lura kwata-kwata bama sa son shigowa inda yake, tunda suna zuwa Huda ta wani doɗe hanci wai wari parlon yake, ita kam ko kaɗan bata ji wani wari ba.
Indomi ta dafa masa irin dahuwar nan mai ban sha'awa, ta soya kwai a sama ta saka.
Turaran ƙamshi tasa a Parlon kamin ta wuce kai masa a bedroom ɗin.
Tsayawa tayi a razane tana kallon yadda ya faɗo daga kan gadon da sauri ta aje abincin data dafa masa tana tallafosa jikinta da kyar tasa hannunta ta ɗakko abincin data dafa masan tana nuna masa ta ce.
"Gashi na dafa maka zo na baka ka ci".
Da sauri ya ɗaga kansa yana kallonta, danshi kallon yarinya kamar shi yake mata, donshi gaba ɗaya ƙwaƙwalwarsa irinta kamar Yara ce ƙananu, itama lura da hakan saita maida kanta kamar ƙawarsa kuma abokiyar wasansa.
Tana masa wasa haɗe sa fira take basa abincin harta samu ya ci da yawa.
Ganin dare ya fara yasa ta tuna magungunan da Mome ta bata.
Ajesa ta ƙara yi akan gadon da kyar ma ta iya ɗorasa taje parlo tana ɗakko magungunan.
Sadda zata dawo harya sake faɗowa saman gadon harya ji ciwo yanzu a goshinsa.
"Wayyo Allah sannu baka iya kwanciya a samansa ko?, kai ɗaya?".
Ta faɗa cike da wata irin kulawar da bata san yaushe ta fara masa ita ba, haka kawai dai ta tsinci kanta da tsananin tausayinsa da sakewa dashi lokaci ɗaya wadda tana kyautata zaton Allah ne yasa mata tausayinsa a ranta, domin tana ji zata iya zama dashi komiye zai mata zata bashi kulawa har illa lokacin da zai samu lafiya ya dawo cikin tunaninsa wadda tasan dole ma ya sake ta, ya za'ai ma mutum kamar wannan a halin rashin lafiya ma yana maka kwarjini inaga ya dawo dai-dai cikin hankalinsa?, ai tasan ita kam ba ajinsa ba ce.
Sake ɗagosa tayi tana zama sosai, kansa na kan cinyarta ta fara fiddo da magungunan dake cikin ledar. Tsayawa Sakina tayi da fiddo da magungunan da sauri tana kallon yadda jikinsa ke rawa yana wasu irin hawaye yana girgiza kansa da sauri.
Cike da mamaki take kallonsa a hankali ta riƙesa sosai tana sake kallonsa da tsananin mamaki.
Ganin ta aje maganin yasa taga ya daina girgizar da yake haɗe da rawar jiki.
Sake ɗakkowa tayi tana son gane wani abu a tattare da magungunan.
Again yadda yayi a farko haka ya sake yi wannan lokacin ma kamar zai shiɗe, lura tayi kwata-kwata baya ƙaunar a basa maganin ne kawai.
Don haka ta samu kanta ta tashi ta je ta aje maganin can nesa dasu, tana dawowa taga ya lumshe idonsa ƴan guntun hawaye na zubo masa ta gefen fuskarsa.
Tsayawa tayi kawai tana sake shiga nazari da tunani mai zurfi akan wa'innan magungunan, dama fa ita ganin farko bata yarda dasu ba, yaya za'ai ace haka magunguna suke?, babu wani alamar na asibiti ne?, illa kwalaban da aka ɗora maganin a ciki sune kaɗai suka kasance kamar na maganin asibiti amma kwata-kwata basu da shaidar hakan a tare dasu, ko irin takardar nan da ake sakawa ka karanta wane irin magani ne a jiki da yadda ake shansa duka fa babu a jiki, tabbas akwai lauje cikin naɗi, tabbas akwai dalilin daya saka Sadeed ɗin ya koma haka, a hankali zata so sanin abunda ya faru dashi baya, da labarin gidan ma