Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ni ne ai, kuma kike tada jijiyoyin wuya indai ina lumfashi babu Bilkisu babu yin aure a gidan duniya dai".
Karaf zancan ya faɗa a kunnan Bilkisu dake sawo kai a cikin gidan, wata wawar bugawar zuciya ce da faɗuwar gaba ta risketa lokaci ɗaya, bata san sadda ta wani ja uban birki ba ta tsaya tana ganin wani irin jiri-jiri na son kaita ƙasa lokaci ɗaya.
Wannan wacce irin Rayuwa ce?, mi hakan zai amfani Inna idan har ta hanata aure?, taga dai bata ƙaunar ta buɗe ido ta ganta a gidan, to mi yasa bazata barta ta tafi gidan aure ba ko yaya yake?, ko itama ta samu ta ɗan samu ƴancinta.
Saukar wani irin mari da Bilkisu taji shi har tsakiyar kanta yasa a gigice ta saki botikin dake kanta tsabar yadda marin ya zo mata a bazata kuma ya shige ta har tsakiyar kanta.
Allah ya so ta saida dambun bokitin ne kaɗai sai guda biyu da bata kai ga saida shi ba ya ɓare a ƙasa bokitin kuma ya ɗan tsage faɗowar da yayi.
Idonta data runtse ba shiri ta shiga buɗe shi akan Inna dake tsaye a kanta tana mata wani ɗan iskan kallo kamin cike da masifa ta fara faɗin.
"Wato ke ga mai kunnan ƙashi ko? har kin isa kan kai kawo saurayi har ƙofar gidan nan kuna zance?".
"Wallahi Allah Inna bani na kawo shi ba, shine da kansa ya biyo ni".
"Ya biyo ki yana cewa mine?".
Inna ta faɗa a da sauri.
Ƙasa Bilkisu tayi da kanta bakinta na rawa ta ce.
"Cewa yayi aure na yake son yayi da gaske".
"Ohhh ba shakka na gano inda matsalar take, wajan uwarki da kika je shine aka je akayo mugun abu za'a zo a kwace ma Binta Saurayin data daɗe tana so Sule?, to bari kiji Bilkisu idan uwar taki a ido biyu take kwana, to ni a tsaye nake kwana, dai-dai nake da ƙugun ko wanne shege a cikin gidan nan wallahi".
"Ahhh ahh ke tsaya Asabe da waye kike naji kina wani jam'i wai shegu?, su waye shegun a cikin gidan nan?".
Inna ta wani juyo tana duban Inna Ladidi data fito daga ɗakinta tana daura ɗankwali, tayi daurin ture kaga tsiya.
Amina ce biye da ita itama ta biyo bayan Inna Ladidi tana bin su Binta da wani kallon duk ina sane da abunda kuke yi.
"Ke Ladidi bada ke nake magana ba kin gane?, ki bari tukunna idan na sako ki sai ki tsomomin wannan wawan bakin naki a cikin maganata".
"Kan buhun uba ni zaki ce ma mai wawan baki?, bakin nawa ne wawa?".
Inna Ladidi ta faɗa tana wani sake matsowa sosai kusa da Inna Asabe suna ma juna kallon ido cikin ido.
"An faɗa ko akwai ubanda zakiyi akai ne?".
"Akwai kuwa akwai abunda zanyin, amma ba yanzu ba zaki ga sakamako nan bada daɗewa ba kuwa, yanzu bana da lokacin ki, ki jira jiran abunda zaiyi".
"Ke har kin isa kiyi min wani abu wadda Allah baiyi min ba a gidan duniya?, ke wacece ne Ladidi wai?, ba ƴar gidan tsohun tantirin ɓarawon nan bace Mlm Ɗan Liti wadda ya fake da rigar malanta yana abunda yaga dama ba".
Tunda Inna Asabe ta kawo karshen zancan Inna Ladidi ta wani zabura tana zare ido waje kirjinta na daka wani tsantsar ɓacin rai ya rufe ta fuskar ta sake murtukewa da wani irin ɓacin rai.
"Keee Asabe ni kika ma wannan cin mutuncin ni Ladidi?".
"Anyi ko ba haka bane magana ta?".
"Hhhhhhh koda yake naji nawa Uban sata yake kaɗai, kefa naki Uban? lalata fa yake da ƴaƴan mutane yana bi lungu-lungu yana latse ƴaƴan mutane, sana gashi wai Malami ashe rigar malanta ya shiga shima ashe boka ne yake kiran kansa Malami, shi yasa fa aka bi aka mallake komai dake cikin gidan nan duk wata Mace da zata zo gidan nan a matsayin kishiyarki da tsiya-tsiya kike fitar da ita, saboda anyo gadon bokaye ai dole, sai dai ni na zame miki ƙadangaren bakin tulu babu yadda kika iya dani zaman gidan nan yanzu na soma nida ƴata wacce baƙin cikin haihuwarta ya so kashe ki".
Tofa tunda Inna Ladidi ta fara magana kunyar duniya da wani irin takaici ne suka taru suka yima Inna Asabe dabaibayi, dama masu iya magana sunce idan ka faɗi magana baka san wacce za'a dawo maka da ita ba, sai gashi itama an tona abunda Ubanta tabbas halinsa ne wadda ya riga da ya daina sa yanzu sai Malamin zaure da ya zama yana bawa mutane magani, a matsayin wai taimako.
Wata irin zabura Inna Asabe tayi taci kwalar rigar Inna Ladidi kamin kace kwabo sun fara kaiwa juna duka kota ina yadda kasan wasu ƙananun Yara.
Su Binta dake kallo ko wanne su yake yaga ba'a ci galaba akan uwarsa ba.
Bilkisu ko wacce rigimar akanta ne aka fara ta shiga zamewa tayi ɗakinsu tana addu'ar gara da Allah ya ceceta ita kam suje can suci kansu, ace mutane basa gajiya da yin dambe a cikin gida, haɗa ƙirji da kishiya bama dole bala'in raini ya shiga tsakaninsu ba, kwata-kwata dai-dai da rana ɗaya basa taɓa ganin mutumcin juna kullum cikin zagin juna suke da aibata junansu, sai kace suna ganin hanjin juna a waje.
"Kai kai kai subhalallahi mi nake gani haka?".
Faɗin Babansu Bilkisu daya doko sallama tun a zauren gidan ya fara jin tashin hayaniya, dama yasan ba masu yin haka sai Matan nashi wadda kullum basa gajiya ko dan idon yaransu da suke gani su bari su fasa amma ina saima wani sabon salo iri-iri da zaka ga suna tsirfowa.
Dakatawa sukai da kaima juna duka, kowacce na sauke lumfashi da sauri da sauri, kowacce kuma na bankama ƴar uwarta wata muguwar harara kamar idonsu zai faɗo ƙasa.
"Wai ku dai a kullum baku jin daɗi sai kunyi faɗa?, ku kenan kullum kamar wasu Kaji?, ku koma kunyar idon Yaranku gasu nan bakwa ji?, to wallahi ku dukanku ku shiga hankalinku ko kuma na ɗau mataki wallahi, kusan dai irin matakin da nake ɗauka, na fara gajiya da wannan halin naku, so kuke ku samin hawan jini?, ku kashe ni tun lokacin mutuwata baiyi ba".
Kowacce ta fara ƙunƙuni ƙasa-ƙasa, dan sun san tabbas idan ya ce zaiyi hukunci shine ya hana kowacce abinci ranar aikinta da yinwa za'a wuni Yaransa kawai yake bi yaba kuɗin abinci suje waje suci abinci, su ko sai dai su ci da kuɗinsu, sana kuma ya ƙaurace ma maki har sai lokacin da kanki zaki roƙi dayayi hakuri zai daina miki ko magana ne sai idan ta kama dole, kuma hukuncin sosai yake wahalar dasu, duk da irin haka tofa idan ta kama gobe sai sun ƙara, amma fa idan baya gidan akai rigimar ya dawo to basa bari ya sani, shi yasa kullum suke dambacewarsu yadda suke so, dan sunsan idan ya tafi Kasuwa sai dare yake dawowa, to yau kuma ɓacin rana aka samu ya dawo da yamma.
"Kowacce ta wuce ta tafi ɗakinta".
Baba ya faɗa babu wasa.
Simi-simi ko wacce taja Ƴarta suka shige ɗaki.
Inna Ladidi na shiga ɗakinta Amina ta fara cewa.
"Inna wallahi karki sake ki yarda nima wallahi ina son Sule".
"Ishurunki ai idan baki same sa ba to kuwa sai dai kowa ya rasa a tsakaninku, ba taƙama take da Ubanta ba Malamin zaure ne, to nima dai-dai nake da ita, zai naje inda aka taka Ubanta nata aka shanye indai wajan sulkulle ne, da ni take zancan, ai da ace ba'a tsaye nake ba da yanzu Matar can ta fitar dani a gidan nan, sai dai abunda bata sani ba ta riga ni tashi ne ni kuma na rigata sammako".
"Yawwa Inna wallahi shi yasa bana jinki, wai Inna na auri Sule a unguwar nan tamu ai nayi zarra ɗan gayu dashi gashi gidansu da rufin asiri dan gidansu duk unguwar nan sunfi kowa kuɗin".
"Ni ko nasan haka ai kawai kiyi shuru da bakinki zaki ga abunda zai faru".
A wajansu Inna Asabe ma suna shiga ɗaki Binta ta fara zazzaga masifa tana faɗin.
"Wai Inna mi yasa har zuwa yanzu baki yi yadda kikai kika fitar da wancar Inna Ladidi daga gidan nan bane wai?, nifa kwata-kwata wannan rigimar taku bata kwanta min ba ta yau, danna ga Amina sai wani min kallon uku saura kwata take min, na kasa gane inda ta dosa fa?".
Wayarta kawai Inna ta ɗakko tana lalubar wata number bugu ɗaya aka ɗauka.
"Hello Baba akwai ɗan abu ne da yake faruwa a gida na, to gaskiya ina son ɗaukar mataki a kai, kar sai na sakankance ayi min sakiyar daba ruwa, dan nasan wace Ladidi".
Daga cikin wayar aka ce.
"Ba dai akan wannan kishiyar taki bane?, domin kuwa nasha gaya miki itama fa a tsaye take, dan wallahi itama inda take shaga ta fita ma yafi naki".
"Baba nifa kawai so nake ko da tsiya ko da arziƙi asa Sule ɗan gidan wannan Ɗan Sandan dake nan unguwarmu ya zo neman auran Binta ko bai shirya ba, ni ba'a kanta bane, dan naga take-takenta, amma ban san miye shirinta ba itama, tunda kaga itama tana da Ɗiya Mace, to komai itama zata iyayi domin kawai ta samu Ƴarta ta samu shiga itama, nasan wacece Ladidi nasan miye abunda zata iya, zata iya rugaza min burina dan kawai tayi min dariya".
"Tunda wannan ne aikin bazai gagara ba, ki kwantar da hankalinki kawai gobe da safe ki zo gidan ki amshi abubuwan da zakiyi amfani dasu".
Murmurshi kaɗan Inna Asabe saki tana kashe wayar ta kalli Binta dake murmurshi itama ta ce.
"Kai wallahi shi yasa nake son Kaka ya iya aiki gashi duk cikin Ƴaƴansa kece kawai yafi miki aiki dandanan".
"Yo ba dole yayi min aiki yadda nake so ba, tunda idan yayi min ina basa ɗan wani hasafi ai, ba haka nan kawai yake min ba na taso na taho, su fa?, duk sauran a bati suke zuwa yayi masu, dole kuwa yayi masu aiki irin na ha'inci".
Dariya suka saki a tare ransu fas domin sun san idan har yayi aiki kamar yankan wuƙa haka yake, Inna Asabe tana da tabbacin idan har taje gobe ya bata abunda zata yi ba'a wuce ƴan kwanaki Sule zai aiko yana son Binta.......
*TSANIN ƘADDARA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
Chapter 7
*House No: 17 Aurora Wrestling Estate Kaduna Nigeria*
Tsaye yake da jallabiyar bacci a jikinsa ruwar ƙasa wacce tayi masa wani irin masifar kyau da ɗaukar hankali.
Wayarsa ya ɗauka ya fito daga bedroom yana tafiya a nitse zuwa kan darning table da aka riga aka aje masa abincin da Ammi ta fada wadda ya ce yana bukatar tuwon samo zaici yau shi yake marmarin ci, shine aka tayar da Intee tana turo baki da sababi tayi tuwon amma taƙi kawo masa part nashi sai aka sa Hassan ya kawo masa, yaji ɗan ba daɗi so yayi ita ta kawo masa, amma ya kyale zasu haɗu ne zuwa gobe, sai kuma wani tunani yazo masa ya saki murmurshin gefen baki wadda ya zame masa kamar al'adarsa.
Wayarsa yake latsawa kwata-kwata bai lura da wacce take tsaye kamar gunki sai binsa take da wani irin kallo na ƙurulla kamar zata cinye sa ɗanye.
Maryam dake tsaye ƙamshinsa daya cika mata hanci wani irin yanayi take ji da shaƙar ƙamshin nasa, jikinta da gangar jikinta har wani narkewa suke da tsananin ƙaunarsa har bata san lokacin data ji muryarsa ba da alama waya yake.
Sauke ajiyar zuciya tayi tana sake baza masa na mujiya.
"Bake na ce ki zo ki kawo min abinci ba wato shine kika bawa su Hassan ko?, saboda kin raina ni ne dama ko?".
Gaban Maryam ne yayi wata wawar bugawa tana zare ido waje ƙirjinta na duka.
Da Mace fa take ji yana waya?, har wani kwantar da murya yake kamar mai shirin lallashinta.
"Ki haɗu min shayi ki kawo min yanzu nan".
Abunda ya ce kenan yana yanke kiran.
Wani kalar baƙin ciki ne Maryam taji haka kawai ya rufe ta, kota rantse baza tai kaffara ba wannan shegiyar Agolar gidan ce Intee wacce tun kan sukai haka Maryam ke zuwa gidan, dama can basa wani zama inuwa ɗaya bare Maryam dama can ta tsani Intee ji take kamar ta kamata tayi mata Jakin duka, saboda hassada take mata ganin ta fita kyau tako ta ina ta fita komai.
Hammad dake tsaye har lokacin yana latsa wayarsa, yaji motsin mutum tabbas yaji kuma alamar kamar ana kallonsa, amma ya wani basar duk wadda ya matsu zaiyi magana ne.
Saina ya samu waje akan darning table ɗin yaja kujera ya zauna, bai ko dubi cikin parlon.
Maryam ta haɗiye wani miyau tabbas taji a jikinta yasan da ita a parlon wallahi, kai wannan bawan Allah ƙarshe ne wajan iya basar da mutum.
"Y Hammad Barka da dare".
Sai da ya gama zuba abincinsa ya ɗakko chokali ya fara kai loma ɗaya a bakinsa ƴar kaɗan kamar baya son ci, a hankali yake motsa ɗan mitsitsin bakinsa, yana taune abincin dake cikin bakin nasa.
Maryam data gama shan jinin jikinta haka kawai taji duk ta muzanta, kallonsa take yadda abincin ma sai an masa iyayi wajan ci, komai cike tsantsar natsuwa yake yi.
Batai tsammani ba ya waigo yana zuba mata idanuwansa masu masifar ƙarfi haɗe da kwarjini na masifa.
Da wani irin rawar jiki tayi saurin ƙasa da kanta tana kallon ƙasa, kyarma jikinta ya farayi rawa bakinta ya farayi ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige.
"You baki iya sallama bane?".
"Uhmmm hm..hm Y Hammad nayi sallama amma lokacin baka parlon sab..
"Kinga bana son yawan surutu oya ki koma kiyo sallama".
"Amma Y Hammad..."
"Kiyi min shuru ki koma kiyo sallama na ce, idan ba haka ba ki fice min a nan wajan na daina ganinki".
Wani kalar abu yazo ya tsaya mata fuskarta cikin tsantsar kalar tausayin kanta ta juya kenan zata koma tayo sallamar kamar yadda ya ce, kawai taji wata daddaɗar murya tayo sallama a cikin parlon.
Ɗaga kan da zatai idonta suka faɗa a cikin na Intee dake riƙe da wani kyakkyawan ƙofi wadda yake ɗauke da shayi wadda sai tashin ƙamshi yake yana tururi a hannunta.
Baƙin cikin duniya dana Intee ne ya rufe Maryam idonta sun rufe ba abunda take iya gani sai tsantsar kyawun Intee, dan gani take kamar ma sake canza Intee ɗin ake, dan ganin yadda ta sake wani yin firash da ita tayi wani mugun kyau na ɗaukar hankali, sanye take da Hijab iya gwaiwarta sai wandon bacci daya sakko mata har ƙasa, Hijab ɗin bata wani kama mata jiki ba, amma duk da haka zaka iya hango tudun dukiyar Fulaninta da suka taso sosai kamar zasu faso cikin hijab ɗin tsabar girmansu, zaka iya shaida a tsaye suke ƙam saboda bata saka Bra idan har zata kwanta, sai mai yawan kallo na ƙurulla ne kawai zai iya lura da duk hakan, itama Maryam ɗin tsabar wani kallo da take mata ne yasa duk ta ga irin halittar da Allah ya zubama Intee ɗin, ai bata sake tsinkewa ba sai da taji wata daddaɗar murya Intee ɗin tana mata sannu, ai gani tayi kamar sannu ɗin ta tsantsar rainin wayo ce, a yadda ta wani faɗa da muryar iyayi, dan ita gani take iyayi ne tsantsarsa zata wani maƙale murya, tsabar ta iya duniyanci.
Gabanta ne ya faɗi bata shirya ba saboda ganin yadda Intee ta wuce ta tabi bayanta da kallo yadda wani uban Hibs nata ke juyawa daga cikin ƙaramar Hijab ɗinta, ga ɗuwawu masu ɗan girma da faɗi da Allah ya bawa Intee ɗin, kai ta komai fa Intee tayi babu yadda za'ai wani Ɗa namiji ya iya kallonta lokaci ɗaya ya iya hakurin ɗaukar kansa.
Baƙin ciki da wata irin hassada tsantsarta ta rufe Maryam ƙirjinta har wani zafi yake, maƙoshinta kuwa wani abu mai ɗaci ne taji yazo ya riƙe mata shi.
Tunda Intee ta doshi inda yake take turo baki cike da tsananin jin haushinsa ta karsa inda yake, aje masa Shayin tayi a kusa dashi a hankali cike da natsuwarta ta juya kawai zata tafi, tunda gani take ai ta gama aikin daya kawo ta.
"Cewa nayi ki tafi ne?".
Taji saukar Muryarsa mai zurfi haɗe da wani kalar taushi.
Cakk ta tsaya bata waiyo ba tana jin mi kuma zata tsaya tayi masa ne?, wai mi yasa Y Hammad ke son kaita ƙarshe ne?.
Bai sake magana ba ya barta a tsaye yadda take, itama ƙarfin hali taja ta tsaya bata kuma waiga ɗin ba.
Sai da ya gama cin abincinsa kamar bazai cinye ba a haka a haka dai ya ɗauki tsawon lokaci yana ci, kamin yana gamawa ya ɗauki Shayin nasa yana ɗan kurɓar shanyin a hankali yana kuma nufo dai-dai inda take.
Maryam da tai mutuwar tsaye gani take ma sun wani manta da tana cikin parlon ganin yadda ya wani matsa sosai a inda Intee ɗin take tsaye kamar zai shige jikinta, ai bata san lokacin data saki kuka ba ta fice daga parlon da gudu.
Sai lokacin Hammad ya ɗago suka bita da kallon mamaki shida Intee, shi duk ɗaukarsa ta tafi ne tun ɗazo.
Taɓe ƙaramin bakinsa yayi yana ɗaga kaɗarsa alamar hakan bai dame sa ba.
Intee ta sauke ajiyar zuciya zata fara tayi domin barin part ɗin dan tasan yau sai an jisu da Ummu tunda taga Maryam ta fice da gudu da kuma kuka tabbas yau sai anji masifarta dasu.
Batai aune ba taji yasa hannunsa ya janyota gaba ɗaya ta taho zata faɗa jikinsa, ita kuma Intee da ƙarfin da Allah ya bata tayi saurin turjewa, sai Allah yasa ta tafi zata gurɗe ƙafa Allah yaso yayi saurin sake janyo ta sukai baya saura kaɗan su faɗi yayi saurin sakin kofin shayin dake hannunsa ya tarwatse a ƙasa.
Da duka hannuwansa yasa yana riƙe ƙugunta sosai, sun ɗan rankwafa ƙirjinta