Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
kyar ta samu tayisa saboda bata jin fitsarin a yanzu, amma dai an samu tayosa kaɗan, na ɗauki jinin nata da komai kuma na auna ya nuna cewar......
Shuru Doctor Halisa tayi tana kallon yanayin da suka shiga.
"A'a ya kikai shuru kuma Doctor ya nuna cewar mi?".
Faɗin Huda da Mome har suna haɗa baki wajan faɗar hakan.
Wani irin kallon take masu zuwa can ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"To gaskiya iya bincike na ya nuna bata da wani shigar ciki, kawai wani zazzaɓi ne mai zafi da take fama dashi wadda shi yake sata cikin irin wannan halin na kamar masu shigar ciki ƙarami, amma bayan nan banga komai a tattare da ita ba gaskiya, na dai bata wasu magunguna tasha na tabbatar nan da jibi ma zata iya dawowa dai-dai".
Tana jin lokacin da suke sauke wata irin ajiyar zuciya mai zurfi suna dafe saitin zuciyarsu suna sauke lumfashi kaɗan Mome ta ce.
"Uhmmm Allah ya taimake ta ashe gaskiya take faɗa mana, dole ne ko na sake ɗaukar wani matakin akanta, ta yadda ko kallon Mace Sadeeq bazai sake yi ba a sunan sha'awa, wai mima yasa bansa Malam ya shanye masa Gaba bane ta yadda babu wata Ƴa Mace da zai sake gani yaji yana Sha'awar ta, nayi kuskure ta nan amma dole na gyarasa".
Mome ta faɗa tana barin Parlon gaba ɗaya.
Tare suka fita da Doctor Halisa da Huda. Ba abunda Doctor Halisa ke kitsawa a ranta sai na dole ne ma ta ɗauke Sakina daga cikin gidan nan yau zuwa gobe, shi kuma Sadeeq Allah bazai taɓa basu iko a kansa ba yanzu...........
Chapter 28
*Unguwar Hayin Ruwa, Dutsanma local government Katsina State Nigeria*
Sake kai mata rankwashi tayi akai tana faɗin.
"Shegiya annamimiya munafika kawai".
"Dan Allah Inna Asabe kiyi hakuri".
"Dalla rufe mini baki makira, idan har Babanku ya dawo ya iske wannan maganar ta Malamin nan naku na sonki wai, wallahi na rantse da Allah Bilkisu yanka ki zanyi a gidan nan mudun dai kika sake kika amsa cewar ai kema son nashi kike".
Binta dake kusa itama tsabar baƙin ciki bata san lokacin data kaima Bilkisun wata hanɓara da kafarta ba tana cewa.
"Wai mi yasa Inna dan Allah duk wani abunda zan so sai wannan shegiyar mayiyar yarinyar ta zo tana ƙoƙarin kwace sa ne?, Malamin da na ɗora buri akansa shine rana tsaka zanji wai labari a cikin gari wai kuna haɗuwa harda su zaije ya sami Baba domin ayi maganar aure ne ma ko ba haka bane makira?".
Da wani irin sauri Bilkisu ta shiga girgiza kanta tana hawaye ta ce.
"Wallahi ba wadda kike nufi bane Mlm Aminu ne ya ce min yana sona zaije kuma wajan Baba ya bashi izinin neman aure na".
Tana jin yadda lokaci ɗaya suka saki wata irin ajiyar zuciya a tare, Inna Asabe na sake dubanta ta ce.
"Ubangiji ya taimake ki da naji cewar ba wadda Binta take so ne ba, Allah Bilkisu gara na datse miki lumfashi a doran duniya dana bari ki auresa, wannan ɗin ma dan kawai babu yadda zanyi dake ne, hankalina yana wajan shawo kan shi ɗayan ne hankalinsa ya dawo kan Binta tukunna na iya dawowa kanki".
"A'a Inna kawai kibarta ta aure san tunda dai kinga ba wancan ɗin bane wadda nake mutuwar so ɗin, barta taje tayi ta fama da ɗayan ai tasan dai na zarce ta nesa bama kusa ba idan har na auri Mlm Japhar".
Shuru kawai Bilkisu tayi tana jadadda ƙarfin hali irin na Inna Asabe da kuma ita kanta Bintar. Lallai kam ina zasu iya da Mlm Japhar wadda kwata-kwata tunda take zuwa inda suke bata jin ya taɓa mata koda kallo na minti ɗaya ne, kallo ɗaya yake mata ya kauda kansa daga nan baya taɓa sake koda kallon inda ta tsaya ne har tabar wajan nasu, duk da irin sabon da tayi da abokinsa Mlm Aminu wadda har soyayya kaɗan da sabo ta fara shiga tsakaninsu, amma babu wata maganar kirki da suka taɓayi da Mlm Japhar ɗin, garama Mlm Naseer shi suna magana dashi sosai, amma shi kam miskili ne naƙin ƙari shine Mlm Japhar ko kaɗan magana bata dame shi ba.
"Tashi dalla can kiba mutane waje. Saura kuma naji labari a cikin gidan nan, waccar Matar ko Ƴarta suji wannan maganar wallahi Bilkisu ƙila idan hakan ta faru saina saka Reza na datse miki harshe sai dai a kaini gidan yari".
Inna Asabe ta faɗa tana kamo kunnan Bilkisu dake duƙe a ƙasa ta murɗe da ƙarfi, yasa Bilkisu ɗan kame jikinta tana sake bata hakuri.
Yama za'ai ta fara wani gaya masu, wadda tabbas tasan ba magana take da su ba suma a cikin gidan, ita da maganar ma ba wani damunta tayi ba, bare ace Inna Ladidi wacce ko harkarta bata cika shiga ba, Amina ko bata ce ta tsane ta bane, a'a kawai maganar arziƙi ma ba yinta suke ba, sai tazo ta wuce ko a cikin gari suka haɗu bata tanka mata bare wata magana ta haɗa su, garama su Bintar da Inna Asaben wa'inda dama sune masu musguna mata a cikin gidan da hanata rawar gaban hantsi.
*****************
"Amma Aminu kana ganin abunda muke ƙoƙarin yi ya dace kenan?".
"Hmmm"
Ya faɗa yana sake gyara zamansa ya dubi Naseer dake masa maganar kamin ya ce.
"To wane gata zamuyi masa wadda ya wuce wannan gatan?, saboda duk irin son da yake mata, wannan shegen miskilancin nashi da zurfin ciki bazai taɓa bari ya mallaki yarinyar ba, koya fallasa abunda ke cikin zuciyarsa ba, idan muka kyalesa haka zaita cutar da kansa, akan abunda zuciyarsa ta daɗe tana mutuwar so, shi kuma bazai taɓa yarda bane cewar wai son nata yake. Zan kira Mimi ma zamuyi maganar nasan tabbas bazata ƙi son yarinyar da muke masa kwaɗayin samu ba insha Allah, shi kuma da kaga yana wannan cika yana batsewa shima fa Allah ƙila ya fara sonta ne, amma dai zamu gane ne nan gaba kaɗan".
Lumfashi kaɗan Naseer ya sauke ya ce.
"Da idan har hakan ta faru tabbas zaka yi sanadiyar ceto yarinyar nan daga halin da take ciki a gidansu gaskiya, dan kwana biyun da muke da ita, ina fahimta kamar akwai matsala a cikin gidan nasu".
Ɗan tashi daga jinginar da yayi, yayi akan kujera yana sake kallon Naseer dake zaune ƙasa saboda kujera ɗaya ce a ɗakin nasu sai katifa guda Uku kowanne da tashi sai ƙaramin table dake a tsakiyar ɗakin, daga gafe kuma akwai Firiza sai toilet sai ɗan kitchen ƙarami duk a cikin ɗakin sai ya kasance kamar wani parlo ne guda aka maida komai da komai.
"Eh gaskiya mun taɓa maganar da ita, ta taɓa faɗa min cewar Mahaifiyarta bata gidan ne, to inaga gaskiya kamar tana shan wahala ne a wajan Matan Mahaifin nata".
"Da alamar hakan gaskiya, daga ganinta ma abun a tausaya mata ne, ace mutum kullum cikin talla yake baya samun damar kanshi? karatun ma da kyar take samu tana yinsa fa, dole abun a tausayawa rayuwarta ne ga duk mai cikakken imani".
Faɗin Naseer a yanzu. Motsin da suka ji ne yasa suka maida hankalinsu ga ƙofar shigowa.
Ganinsa ya shigo yana wannan tafiyar tashi kamar wadda baya son taka ƙasa yasa suka bisa da kallo kawai.
Harya zauna suna kallonsa, dan sauke lumfashi yayi kaɗan yana ɗan kwanciya akan katifa yana sake sauke lumfashi.
Ɗan sake tashi yayi kaɗan ya ɗago yana binsu da kallo can ya ce.
"Mine kuke kallo na haka ne?".
Murmurshi suka saki a tare, kansa ya ƙara ɗaurewa Aminu ya ce.
"Kawai munga ka shigo a gajiye miya tsaida kai akan hanya ne?".
Taɓe bakinsa yayi kaɗan yana jin ɗan haushin kansa mima yasa ya wani tsaya jiran ganinta ne?, haka nan shima ya sami kansa da son tsayawar yaga koda ta zo school ɗin, sai dai har ɗalibai suka gama fitowa bai wani ganta ba, duk da kuma yaga babu alamarta a cikin class ɗin nasu saboda ya shiga tun safe, duk ɗaukarsa ko ta zo da aka koma break ne, amma har aka tashi ɗalibai suka gama ficewa daga school ɗin baiga koda mai kama da ita bane.
"Mtswww ba komai kawai na tsaya yin wani abu ne a Office".
Kusan a tare suka saki murmurshi dan sun kusa harbo jirginsa.
Naseer ne ya ce.
"To dama muna so na sanar da kai cewa Aminu fa yaga iri a garin nan kuma zai fara zuwa neman auranta".
Gaban Japhar ne ya ɗan faɗin, duk da irin bugawar da zuciyarsa tayi da basa tabbacin ko wacece Aminun zai fara neman auren nata, kai tsaye ya waske yana shanye duk wata fargaba ko bugawar zuciyar data riskesa ya ce.
"Ohh ka ce kai harka faɗa?, wacece kuma?".
"Wace kuwa ai kasan cewa mutuniyar tashi ce Mai kawo mana tallar Dambu Bikinsu kuma ɗalibarsa".
Sai da zuciyar Japhar ta shiga tsintsitsinkewa bai san lokacin daya miƙe daga kishingiɗan da yayi ba, yana zubama Aminu ido ba bai san lokacin da ya ce.
"Bilkisu?, ka rasa wacce yarinya zaka so sai Bilkisu?".
"Ah ah akwai abun wani aibu ne a tattare da ita wadda ban sani ba kai kuma ka sani?, ai yarinyar naga tana da hankali bata da wata matsala a rayuwarta kwata-kwata, duk wadda yayi nasarar samunta ma a matsayin Mata ai more ne, saboda gata da sanyin hali bazata taɓa sa maka ciwon kai ba, dama irinta na daɗe ina son samu a matsayin Matata dama".
Faɗin Aminu yana kallon yanayin Japhar ɗin da ɗan shiga halin ruɗani, amma da yake Namijin gaske ne baka isa ka ce ga halin da yake ciki ba.
Gani sukai ya taɓe baki yana komawa ya kwanta kaɗan ya ce.
"Ohh night tayi kam babu laifi Allah yasa alkhairi to".
Abunda ya iya faɗa kenan ya rufe idonsa kamar mai jin bacci.
Yana jin firar tasu duk kusan akan Bilkisun suke yinta, wadda yasa gaba ɗaya ma firar ta da suke ta fara bashi haushi sosai dan ji yake wani irin abu na masa yawo a zuciyarsa har ƙirjinsa na masa zafi kaɗan-kaɗan, tun yana ɗauka ko gajiya da yayi ce tasa haka har dai ya gane kamar maganar da suke ce zuciyarsa bata son ji kwata-kwata dan haka ya miƙe tsam yana dubansu kamar yadda suke kallonsa da mamakin tashinsa kamar wadda aka tsikara.
"Lafiya dai Japhar?".
Faɗin Naseer yana dubansa.
"Please ku ɗan rage maganar yarinyar nan mana, kun fara isata da zancen ta, haba sai ka ce ita ce kuka fara budurwa akanta".
"To miye laifinmu dan kawai mun yaba hankalinta da kyakkyawar zuciyarta?".
"Mtsww please idan baza ku daina ba ni zan fice na bar maku ɗakin, and idan ya so kuka gama na dawo, kunyi abu ɗaya ai sai ku sassuta haka nan Night?".
"To wai duk miye naka a ciki?, ka koma kayi kwanciyarka kawai shikenan za'a daina, amma fa sai kayi hakuri damu dan yarinyar ce tayi ƙarshe ce ita ɗin".
Kusan a tare sukaga yadda ya wani runtse idonsa da ƙarfi, bai sake magana ba yabi hanyar ficewa daga ɗakin.
Yana fita suka shiga tafa hannu Naseer na faɗin.
"Kai abokina, abunda fa kake faɗa ya kusa tabbata, kai jama'a ace ayo mutum sai zurfin cikin tsiya?, wannan miskilancin da zurfin cikin nasa wata rana sai ya cutar dashi fa, mai iya zama dashi ai sai irin wannan yarinyar mai tsananin hakuri da juriya".
Dariya Aminu ya saki yana cewa.
"Tabɗi jam ai a tunaninka ita zai mata hakan ne idan suka saba son nata mai tsananin ya kamasa?, ai wuyarta dai su zauna waje ɗayan, to ai irinsu ma basa taɓa yima Matansu haka komai zaka ga suna yinsa kamar basu bane, nan ne kawai da yake baya son a kawo masa raini yake nuna mana hakan".
Murmurshi kawai suka saki a tare suna girgiza kansu suna mamakin abokin nasu, da irin halayensa masu matuƙar wuyar fahimta, duk dama su sun saba da halayen nashi, indai zaka ga yana sakin dariya da murmurshi sai idan yana tare dasu ne kawai da kuma Mimi da Ƙanwarsa Khairat.........
Chapter 29
*House No: 34, Tudun Wada Estate Funtua Local government Katsina State Nigeria*
Shigowarta a hargitse parlon kamar wacce aka jefo yasa Maami ɗaga kanta tana dubanta da mamaki ta miƙe tsaye tana kallon Maryam ta ce.
"A'a ke Maryam lafiya da dawowa haka a hargitse?, wani abu ne ya faru a can ɗin?".
Ta faɗa tana sake matsowa sosai inda Maryam ɗin take tsaye.
Wani dogon tsaki taja tana komawa ta zauna tana dafe kanta ta dubi Maami dake tsaye a kanta tana kallonta da mamaki.
"Maami akwai fa matsala a gidan Ummu".
Ai Maami bata san lokacin data zauna kusa da Maryam ba tana ƙara zuba mata ido sosai ta ce.
"Matsala fa kika ce?, tukunna ma miye abunda ya faru?".
"Hmmm, Maami duk wani abunda baki tunani ma ya faru fa".
"Ke da'allah ki sanar dani kina sani cikin ruɗani, kina kuma ja min rai haba".
Maami ta ƙare maganar a ɗan tsawace dan Maryam ɗin ta fara bata haushi kuma.
"Maami waifa Ummu yaji tayi saboda kawai Abbi ya hana Y Hammad ya aure ni, ni ɗaya dole ya ce sai an haɗa da wannan yarinyar Intee mai kama da aljanun farko".
"Kamar ya sai da Intee?, kenan ma ku biyu za'a aura masa rana ɗaya ko miye ake nufi?, ita kuma ta amince Aunty Mansurar?".
"Noo ni dai Maami ban san abunda ya faru ba tahowa ta, da komawarta gidanku, amma ki kirata kiji, ko ki kira Umma kiji, abunda shi Abbu ya ce a can ɗin data koma, amma da wuya kin san Abbu ya goyi bayanta fa".
Sauke lumfashi tayi kaɗan tana girgiza kanta tabbas sunfi kowa sanin wanene Mahaifinsu Abbu, shi ɗin kaifi ɗaya ne, baya magana biyu, shi yasa ma da wuya kaga sunyi yaji wai da sunan su koma gidajen iyayensu su zauna na wani lokaci, baya ɗaukar wannan shirmen, da kansa zai ɗaukeki ya maida ke ɗakin mijinki ya tabbayi ba'asin dawowar daya ga kinyi, idan har ke ce da laifi to kowa bazai taɓa goyan bayanki ba, sana ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci.
Ƙara sauke ajiyar zuciya tayi tana jawo wayarta ta dubi Maryam ta ce.
"Tashi kije ciki, ki ɗan huta zanyi waya da ita yanzu, naji abunda ya farun".
Tashi Maryam tayi tana jan ɗan akwatinta zuwa cikin bedroom ɗinta, sai kuma taja ta tsaya tana faɗin.
"Maami ina Aunty Ma'u ne?".
Waigowa Maami tayi tana faɗin.
"Yanzu zaki ga ta shigo tana can kitchen".
Amsawa kawai tayi da kai tana shigewa cikin bedroom ɗin.
Tana shiga Maami ta shiga kiran number Ummu bugu ɗaya biyu ta ɗau kiran.
"Aunty Mansura yanzu Maryam ke isuwa gida take bani wani labari marar daɗin ji, mike faruwa ne yanzu?".
Daga cikin wayar Ummu taja wata irin ajiyar zuciya tana jin ranta na sosuwa da abunda zata ce ɗin ta ce.
"Hmm, ai komai ma ya faru fa, yaya zanyi da Abbu tunda yazo ya kawo ni gida yanzu nan ya dawo dani, ya gama rugaza min duk wani shiri da nayi na fasa auran nan da Alhaji yake son ƙullawa da Ɗiyar makirar Matar can, dole fa tasa na amince da auran dan cewa yayi mudun ban aminta ba to kuwa sai dai gaba ɗaya a fasa aura masa har Maryam ɗin da nake son ya aura ɗin".
"Tsakani da Allah Abbu ya rusa mana shiri, amma ni da kinyi shawara dani kamin ki koma gida da duk hakan bata faru ba, domin bazan taɓa cewa kije gida da sunan yaji kika je ba, da ni kaɗai nasan inda zan tura ki inda sai kin ɗan kwana biyu kamin ki dawo gidan, ta yadda babu yadda za'ai shi kansa Muhammad ɗin ya iya runtsawa kina fushi dashi da wannan auran da baki so, ace kuma shine silar barinki gidan Mahaifinsa, ko baya so dole ne yaje ga Alhajin ya ce ya fasa auran zaɓin nasa ai".
Wani kalar huci Ummu ta saki tana faɗin.
"Hausar da banba kenan ta sanar dake ai, amma ai duk da hakan Ƴarta bazata taɓa zaman lafiya a gidan ɗana ba wallahi, zata gane shayi ma ruwa ne".
"Uhmmm wannan aikin ai ki barsa a hannun Maryam ita kaɗai ma ta isheta wallahi ba dai zaman kishi damu ba hmm, ita kanta Nuratun mun buga da ita tasan mu su waye ai, bare Ƴarta data girma a gabanmu ita ce har zata gagaremu?".
Ma'u ce ta shigo tana danƙara wani uban zagi haɗe da tsaki, hakan yasa Maami sallama da Ummu da sauri tana yanke kiran tana ce mata zata kira ta zuwa anjima.
"Ke kuma lafiya?".
Faɗin Maami tana dubanta.
"Inafa lafiya Maami kina nan zaune ana can an kusa kema a mallake miki Ɗa".
Da wani irin sauri ta miƙe tsaye tana sake kallonta kamar idonta zasu zazzago ƙasa ta ce.
"Ban gane ba wane ɗan kike magana?, su waye ke son mallakesa?".
"Haba Maami wanne gida muke ba'a cikin gidanmu muke ba?, sana wacece kuwa idan banda wannan yarinyar Humaira, wai kinga yadda take ma Y Harun kuwa?, tana wani kashe masa murya haɗe da lankwasa harshe, shi kuma yana biye mata, kamar wani sakarai, ai ban taɓa tunanin zanje Part nashi na iskeshi tare da ita ba har suna musayar harshe a tsakaninsu, kamar shi mai ji da kai da isa da izza amma wai wannan ƴar iskar yarinyar ita sai naga yana wani sakar mata fuska yana wani washe mata baki, kai na yadda da aka ce Namiji sakarai ne akan Mace wallahi".
"Buhun bur*ub*an nan kayyasa nan, abunda nake ji kina faɗa haka yake ne ko kodai wasa kike min Ma'u?, kar naje nayi abunda bashi kenan ba Ma'u?".
Maami ta idasa maganar jikinta na rawa tsabar wata masifa dake ciyota, danta rantse da Allah ita bazata taɓa yarda ayi mata yadda akai ma Aunty Mansura ba.
"Hmm Maami kenan