Tsanin Kaddara Complele Book Zahra Star.docx

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 40

18K to 21K   out of 118.4K words

bai kai da haɗewa da nashi ba, amma ya tallafe haɓarta haɗe da kamo ƙugunta.

Wani kalar haushi ne ya kama Intee bata san ma ta sakar masa tsaki ba haɗe da turesa da bala'in sauri tana kauda kanta da sauri ƙamshin nan nasa na ƙarasa kashe mata jiki.

Bata ce komai ba zata sake juyowa domin a mugun ƙagare take data fice masa daga Part taji ya sake riƙe hannunta wannan lokacin a zafafe ya juyo da ita, sai akai sa'a idonta ya faɗa cikin nasa, wani irin hawayen baƙin ciki ne taji sun fara taruwa a cikin idon nata, yadda ya wani tsare idonta da mugun kallon nan nasa, ga wani irin kwarjini haɗe da karfin idon nasa sun fara tasiri a gangar jikinta, dan haka jikinta lokaci ɗaya ya soma rawa bata san ma lokacin da hawayen da suka gama taruwa a kwaryar idonta suka suma subowa akan kyakkyawar fuskarta ba.

Tafiya ya suma yi yana nufarta itama kuma ta ja baya a hankali a hankali suke tafiya shi yana kusantota ita kuma ta sake ja baya kaɗan gabanta na duka, shi kansa Hammad ɗin yana iya hango yadda ƙirjinta ke ɗagawa da ƙarfi ga hawayen dake mata zuba.

Sai da Intee ta kai jikin bango babu ta yadda za'ai ta sake matsa wa sai kawai ta samu kanta da faɗin.

"Please Y Hammad.....".

Sai kuma tayi saurin yin shuru.

Ido cikin ido yake kallonta saboda yasa wannan mayen karfen ya hanata ɗauke idonta daga cikin nasa, shi yasa ba abunda take sai hawaye sune kawai ke zubo mata.

"Please Y Hammad mi? Oya ki faɗi abunda ke ranki".

Shuru ta sake yi, ya ɗago hannunsa kaɗan ya shafa kyakkyawar sumar kansa wacce take a gyare tasha gyara sosai kamar ta wani India, dan sumar har kwantowa take akan gadon bayansa kaɗan wadda hakan ba ƙaramin masa wani irin masifar kyau take ba.

Sake matsowata yayi gaban Intee ya sake yankewa ya faɗi tsoro duk ya cika ta, kawai batai tsammani ba taji ya kamo ɗan ƙaramin bakinta ya matsesa da ƙarfi, har bata san lokacin data saki wata ƙarar azaba ba da tayi mata dirar mikiya.

Yana dubanta ganin ta runtse idonta hawaye na sake zubowa ya sake matse bakin nata, ta kara kame jikinta saboda da wani raɗaɗi take ji kamar mi yadda ya wani matse mata baki tsabar mugunta irin tashi, shi ko yana dubanta ya ce.

"Oya ki buɗe idonki na ce, ni kike ma tsaki?, har yanzu baki san abunda nafi tsana shine amin tsaki ba?, wato ba zaki daina ba ko?".

Girgiza masa kai tayi tana son basa hakuri amma ya matse bakin maganar, bata yadda za'ai tayi magana.

Buɗe idon tayi a raunane, idonsa ya sake sarkewa da nata, wani irin bala'in abu take ji yana shagarta a cikin kwayar idonsa, shi yasa take wani tasiri a gangar jikinta take kashe mata duk wata lakkar jiki mai aiki a jikin nata, wani irin sanyin jiki da mutuwar jiki ne suke samunta mudun suka haɗa ido dashi ko kuma idansa na yawo a gangar jikinta.

Kafafunwata sun ƙasa ɗaukarta jikinta yayi mutuwar da bazata iya tsayawa da ƙafafun nata ba, dan haka yana sakin bakinta domin yaga ta ladabtu kawai yaji ta faɗo masa a jiki.

Wani irin yarrr Hammad yaji jin tudun dukiyar Fulaninta da suka saukar masa akan kirji, wani irin bala'in taushi yaji suna dashi dan haka cike da wata irin jarumta ya aro dan shima jikinsa ya fara ɗaukar wani kalar karatu na daban yayi saurin janye jikinsa daga nata, da kyar Intee ta tsaya da ƙafafunta tana wani irin layi kamar zata sake zubewa ƙasa.

Dai-dai lokacin daya sake ta dai-dai lokacin aka shigo parlon afujajan.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, dama Muhammad abunda Maryam taje ta sanar dani haka ne?, kana nan tare da ƴar iskar yarinyar nan zata lalataka wato?".

Saukar muryar Ummu da da Intee taji ne bata san ma lokacin data wartsake ba, cikin karfin hali ta kai dubanta inda Hammda yake suka haɗa ido tayi masa wani mugun kallon ka gani ko?, haɗe da murguɗa masa baki akan fatar laɓenta ya karanci abunda take faɗa, mugu kawai, shine abunda ya lura ta faɗi.

Murmurshin gefen baki ya saki wadda Intee ɗin ce kawai ta lura dashi dan haka da sassarfa ta juya domin ficewa daga parlon kawai yaga Ummu ta wani jawota ta dawo da ita a gabanta cike da masifa Ummu zata ɗaga hannu domin wanke Intee da mari kawai taji an riƙe hannun nata.

Zaro ido waje Ummu tayi tana duban Hammad yayi saurin ƙarasowa inda suke bai san lokacin daya riƙe hannun Ummu ɗin ba, sai da yayi abun kamin cikin basarwa ya sakar mata hannu yana sosa kansa ya ce.

"Ummu Please Intee batai miki laifin komai ba, ni ne wadda idan ma laifin ne ni nayi, saboda Intee batai niyar zuwa nan ba ni ne wadda ya kira ta tazo".

"Innalillahi Hammad ni zaka kalla kake gaya min haka?, saboda baka son laifin wannan aljanar yarinyar wacce uwarta ta gama shanyeka?, har ni zan ɗaga hannu na mare ta ka riƙe min hannu?, shikenan wallahi ta tabbata dai an gama da kai ba shakka, to wallahi Allah idan na yarda Allah ya tsan.....

"Dan Allah Ummu kiyi hakuri, duk irin wannan rantsuwar bai dace ba Please Ummu".

Shuru kawai Ummu tayi saboda wani irin abu da Hammad ɗin keda shi a tare da itama, wani lokacin idan ya faɗi magana bata iya cewa ƙala, saboda gaskiya ce ya fita, kuma Ɗa ne da take mugun so wadda shine kwallin kwal ɗaya a duniya wadda take mugun so.

Maryam dake tsaye ta riƙe ƙugu ta wani cije yatsa ba haka taso ba, so tayi Ummu ta wanke Intee da mari komi zai faru ya faru, amma Y Hammad ya wani zo ya hana, haushinsa ya kamata a kafaice ta fara hararsa.

"Marar kunyar banza marar kunyar wofi, zaki bar wajan nan ko sai na nayi miki dukan da uwarki zata kasa gane ki?".

Da sassarfa Intee ta juyawa ta raɓa su ta wuce wani kalar abu ya tare mata wuya, ba wadda ta ɗora alhakin hakan a kansa sai Y Hammad komiye akai mata Y Hammad ne yake ja mata, kuma bata jin zata yafe masa.

"Wai shin Hammad bance ka daina shiga harkar wannan yarinyar ba?, tun kan takai haka Hammad nake fama da kai amma yadda kasan kunnan ƙashi ne da kai Hammad gobe sai ka sake zuwa inda suke, wai miye abunda suke dashi ne da har ka kasa barinsu?, Hammad kafa dawo cikin yaccinka, Maryam tazo ita baka kalleta da arziƙi ba sai waccar wacce aka gama da kai akanta ko?, to bari kaji wannan ɗin dai ita ce zaɓi na, ita ce na aminta daka aura, ko bayan raina ban aminta ka auri wata idan ba Maryam ba".

Hammad bai san lokacin daya ɗago yana kallon Ummu ba, gabansa na faɗuwa kaɗan yana jin wani abu na yawo a jinin jikinsa, Maryam dai? yarinyar da ko kaɗan bai taɓa mata wani kallo ba sai na Ƙanwarsa.

"Kware kuwa ai kaji abunda na ce dan haka kama shirya, idan ma wani tunani ne a ranka to tun wuri kama fidda shi a zuciyarka, domin idan ba haka ba rayuka ne zasu taru su ɓaci a cikin gidan nan, ranar sai waccar Matar ta gaya min abunda tayi ma ɗana ya zama kamar bawanta".

"Ya Salam Ummu Please ki daina faɗar magana irin haka".

"Kai ni kamin shuru na ce, ni dai na gama magana ta, kama sakata a ranka ka riƙeta dan babu abunda zai hana auranka da ƴar uwarka Maryam nama gaya maka kaji da kyau".

Maryam dake tsaye sai sakin wani irin murmurshi take na tsananin murnar abunda Ummu ke cewa. Hammad wani kallo ɗaya da ya waigo inda take yayi mata sai da tasha jinin jikinta wani kalar tsoronsa ya rufeta haɗe da wani irin bala'in shakkarsa ta saukar mata, amma duk da haka bata jin ko yankar naman jikinta yake yana cinyewa bazata fasa auransa ba wallahi sai dai idan ta aure san ya kashe ta.........

*TSANIN ƘADDARA*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

Chapter 8

*House No: 34, Tudun Wada Estate, Funtua Local government Katsina State Nigeria*

Tunda suka zauna Abba yake faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, Inna tayi ƙasa da kanta baƙin cikin duniya ya isheta, Humaira ko haɗiyar zuciya kawai take tana jin haushinsa sosai, saboda kwata-kwata bai bari su yaji ta bakinsu ba, suna shigowa ya kama masu faɗa daga Innar har Humairar ya haɗa yake ta masifa kamar wadda zai ari baki tsabar yadda yake faɗan.

Daga jin yadda yake masifar kai kasan anje ne anyi wani mugun shirri an faɗi abunda bashi kenan ba.

Daga ƙarshe ya ce.

"Idan har Nana kin san wa'innan Yaran naki sun zo min gida ne domin su hana Yarana zaman lafiya a gidan Mahaifinsu to suyi maza su haɗa kayansu su bar mini gida, ai babu lallai babu dole dama ba wani ya kawo su ba sune suka kawo kansu, kuma arziƙi suka zo ci ba tsiya ba, daga taimako baza zo a rinƙa samin ciwon kai ba. Kuma naji wai itama ɗayar Ƴar taki yau ta zo cikin daren nan, wani abun ne ya sake faruwa ne?, to gaskiya zan gaya miki idan ma zaman gidan nan ne sai daifa na iya riƙe miki ɗaya ki zauna da ita, dan haka gaskiya kisan yadda zakiyi da ɗayar, dan bazan iya riƙe harsu biyu ba".

Abba ya faɗa domin tabbas yasan tana son taimako, ta ɗago tana dubansa taji daɗi tunda ya amsa zai riƙe ɗaya ko Humaira ta samu ya riƙe mata ta gode ita kam, saboda haka insha Allah zata san yadda za'ai ta samarma Sakina inda zata zauna itama.

Zata buɗe baki tayi magana taji Muryar Maami cike da mamakin Abba take magana.

"Alhaji ban fahimci zaka riƙe mata ɗaya ba?, kana nufin ɗaya daga cikin ƴaƴanta ya dawo nan gaba ɗaya da zama har sai tayi aure tukunna zata bar cikin gidan nan ko yaya kake nufi?".

Ba shakka ko wani ɗar a wannan lokacin ya buɗe baki ya ce.

"Kware kuwa hakane nake nufi, ko banyi dai-dai bane?, ai Yaro na kowa ne, dan ma banda abunda zan riƙe mata su duka ne shi yasa, kina gani duk mai son gaskiya da zuciyar taimako yasan Nana tana buƙatar a tallafa mata, so kike na bari Yaran nata suje su lalace a yawan inda za'a je a riƙe so?, na sani ko banza zan samu ladar hakan. Ke kuma Nana ki daina ganin na koma na goyi bayan ƴaƴanki su zauna gidan nan su samu waje su ce zasu rinƙa abunda suka ga dama, hakan bazai yiwu ba, su tsaya iya matsayinsu kin fahimta?".

Ɗaga kanta kawai Nana tayi tana jin daɗi ita dai dama kullum cikin tunani take da zullumin inda zata kai Humaira ta zauna sai ga Sakina itama sai abun yazo mata a cakuɗe ta rasa inda zata saka kanta, sai ga mafita kuma Allah ya kawo mata.

"Ai lallai Alhaji to miye idan wa'innan Yaran nata sun lalace?, dama baka gansu bane a lalacan suke ba?, Yara sai rashin kunya da rashin mutumci cike da ciki, to wallahi Allah idan har wannan yarinyar a nan zata zauna to kuwa saina gyara mata zama, nifa Alhaji gani nake kamar an gama shanye ka ne, yo ai abun da mamaki, kaida baka taɓa riƙe ɗan wani ba, kasha faɗa baka son riƙe ɗan wani, amma sai gashi akan wannan Matar taka ka ce zaka riƙe mata Ƴaƴanta, ba shakka lallai Nana wallahi kin more Malami fa, amma ki sani na rantse da Allah ni duk wani asirinki bazai taɓa ci na ba, kuma nan gani nan bari Kazar mayiya. Aikin banza kawai ke Ma'u tashi mu tafi, ai idan tusa na hura wuta ayita ta hura ɗin mu gani".

Tana ƙare maganar taja hannun Ma'u da ƙarfi suka fice daga parlon. Ma'u ma ta cika da haushin Abban ba haka taso ba, so tayi yayima su Humairar kurar Kare a cikin daren nan subar masu gida, sai gashi yayi abunda basu taɓa tunanin zaiyi ba.

Suna fita Inna ta sauke ajiyar zuciya mai zurfi tana duban Humaira ta harareta ta ce.

"Godiya zakiyi ma Abban naku ko sai na ce itama kiyi masan?".

"A'a ki barta kawai ku tashi kuje, kawai dai saita kiyaye ta kuma tsaya iya matsayinta, ta rinƙa tunawa nan ɗin alfarma akai mata ta zauna shine zai hanata yin duk wani abu wadda ba dai-dai ba".

Ko kaɗan Humaira bata ji daɗin maganar Abban ba na cewa alfarma akai mata ta tsaya iya matsayinta, ai ko bai faɗa ba ta san alfarmar akai mata, duk dai inda kake gidan Mahaifinka yafi maka ko ina, amma sai gashi gidan nasu Uban ya zame masu gara ace su zauna a gidan da za'ai masu alfarmar, saboda duk irin rashin mutumci da cin zarafi da za'ai masu a nan bai kai ko kwatar na gidan Ubansu ba.

Girgiza kai Humaira tayi ta duƙa sosai tayi masa godiyar kamar yadda Inna ta umarta, suka miƙe tare suka fice daga parlon.

Suna komawa ɗaki suka iske Sakina nata fama da Ummi dake hannunta sai kuka take, da sauri Inna ta amshi Ummin ta zauna tana saka mata nono a baki sai tayi shiru, ta dawo da dubanta inda Sakina take ta kuma kalli Humaira kamin ta ce.

"Sakina gobe da asuba zanje Kano na mayar dake gidan Aunty Sakina, ko wajan aiki ne ta samar miki ki koma gidan aikin da zama, tunda tasan mutane sosai a cikin garin Kano, ni dai kawai ki riƙe mutuncin ki a duk inda zaki tsinci kanki karki sake wahala ko runtse yasa ki zubar da mutuncinki na ƴa mace dan Allah, kuma kiyi hakuri Abban Ummi ne ya ce Humaira kaɗai zai iya riƙewa a halin yanzu, dan haka nasan yadda zanyi dake, zuwa gobe dole mu tafi Kano ni da ke na roƙi aunty Sakinar da cewa ba dole saita riƙe minke ba ta samar miki gidan aiki inda zaki koma can da zama".

Da wani irin sauri Humaira take kallon Inna zuciyarta na tsinkewa sosai bata san lokacin data furta.

"Inna kina nufin aikatau Sakina zata tafi kenan?".

Inna ta watsa mata wani irin kallo ta ce.

"Ki fita ido na na rufe Humaira, shi yasa na zaɓi da ita Sakinar da je aikatau ɗin, saboda idan kece duk inda aka kai ki sai kinyi yadda kikai aka koro ki daga wajan, nasan Sakina ita bazata taɓa iya irin abunda kike yi ba, Sakina ta fiki hakuri nesa bama kusa ba, ko yawan magana Sakina bata dame ta ba haka ma Bilkisu kusan halinsu ɗaya, ke ko yadda kasan ba'a tsatso na kika fito ba, sai shegen rashin jin magana ga tsurfa kala-kala, Humaira nasan ki tun kina Yarinyarki haka kike".

Humaira tayi ƙasa da kanta haka kawai taji wani irin bala'in tausayin Sakina da Bilkisu dake can a hannun kishiyoyi marassa imani da tsoron Allah, Allah kaɗai yasan itama miye abunda ake mata a can ɗin. Sai gashi kuwa Sakina ta saki murmurshin daya fi kuka ciwo tana duban Inna ta ce.

"Shikenan Inna hakan ma yayi, nima so nake na samu inda zan riƙa aiki ko mun samu abun rufama kai asiri, insha Allah zanyi aikin nan ko danke, kuma Allah yasa Aunty Sakinar ta amince ta samar min".

"Zata amince nasan wacece ita, amincewar kuwa ba zai wuce itama zata rinƙa samun wani abu daga cikin kuɗin aikin naki ba, idan har aka samu, saboda zai rinƙa zuwa ta wajanta ne kamin ta aiko min dashi nan, sana zan saka a rinƙa baki haƙƙinki kema ko dan ki rinƙa rage wasu abubuwan na rayuwa".

"A'a Inna ni miye zanyi da kuɗi idan har an samu aikin kawai ki ɗauki kuɗin da Aunty Sakinar zata baki ba sai an bani wani abu ba, tunda naji idan gidajen masu kuɗin nan suka ɗauke ka aiki komai suna ɗauke maka, wani gidan ma idan suna da adalci da mutumci har makaranta suna sakaka".

"To Allah dai ya kaiki gidan da za'a riƙe min ke da mutumci Sakina, Allah kuma yayi maku albarka ya fiddo maku da abokan zama na gari kuyi auranku ku huta da duk wani raɓe-raɓen zama gidan mutane".

Da amin suka amsa kawai Humaira ba abunda take sai bin Sakina da wani irin kallon tausayi tsantsarsa, ji take kamar ta ce ita Sakinar ta zauna tare da Inna ita kuma a barta tabi Aunty Sakinar, ji take kamar ta ce ita zata je aikatau ɗin, sai dai tasan tabbas kamar yadda Inna ta faɗa bafa tada hakuri ko kaɗan, dan duk inda taje aka nuna za'a wulaƙantata to zata shanye na ɗaya na biyu, to na uku idan aka sake ba lallai ta iya hakura ba, haka take bata jurar wulaƙanci.

Washe gari tunda safe Inna tayi wanka haɗe da ma Ummi wanka ta shirya ta, hakama Sakina, ita kuma Humaira ta shiga kitchen domin ɗora abun karin safe, dan su Inna suci wani abun kamin su ɗau hanyar Kano, dan jiya a wajan Abba ta kwana ya kuma sallameta da kuɗin Motar da zai isheta ya dawo da ita, dan haka ma yau da safen wucewa kawai zatai ba sai sunyi sallama ba dan tun jiyan sukai sallama, sai kuma Allah yayi mata dawowa.

Humaira na cikin aiki Ma'u ta faɗo kitchen ɗin tana wata uwar hamma ta dubi Humaira dake jefama su Inna ɗanwaken fulawa, ta haɗiye yawu ta ce.

"Ke ki samin ɗanwaken nan, sana ki dafa min indomi da soyayyan kwai a ciki, ina jiranki idan kin gama zanzo na ɗauka".

Abu ɗaya Humaira ta tuno alfarma da Mahaifinsu yayi masu shine yasa kawai ta amsa da to babu wani muso.

Kamar yadda tace ɗin ta dafa mata Indomi ɗin da soyayyan kwai ta ɗibar mata ɗanwaken

7 / 40